← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 78

Sashe 10

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ba, hakan yasa manager Kallan Hassana ya ce, "Biyo ni in nuna miki site d'in worker's d'in gidan. Shi dai Habib na jin manager bai ce mai ko mai ba. Haka manager da kan shi ya kai Hassana b'angaran masu aikin gidan. Bayan ya kaita ne, ya koma yima Oga Habib sallama. Habib kallan manager ya yi, ya ce, "Manager ya zama First and last, ban hanaka d'aukar staff ba a company, amma ba dai zama nan ba, dan duk wata worker da ka gani agidan nan, Hajiya kawai suke ma aiki, amma ba Company ba". Manager hak'uri ya ba Habib, sannan ya ce, "Insha Allah, M. D, haka ba zai kuma faruwa ba, wannan ma tausai ta ban, ganinta mace bahaushiya da nayi, kuma daga ganinta tana buk'atar tai mako, amma ka yi hak'uri ". Banza Habib ya yi da shi. Manager tafi ya yi, dan ya san fushin kafin gobe ne, Oga Habib akwai saurin fushi, amma kuma baida wuyar sauka. Hassana ko da ta k'arasa b'angaran masu aikin, cikin girmawa ta gaida su, sai dai duk kansu wani irin kallo suke ma Hassana.Hassana cikin tsarguwa da kallan da suke mata ta gaidasu,. D'aya daga cikin su ce, ta ce, ma Hassana, "Baiwar Allah daga ina? ". "Nima ma aika ciyace kamar ku, sai dai ni ba acikin gidan nan zan rik'a aiki ba, a Sanat yoghurt zan rik'a aikina". Da mamaki dukkan su suka kalli Hassana, dan su aiya saninsu 'yan aikin gidannan ne kawai Hajiya turai ta yadda da su zauna anan. Wata wadda ake kira Jimmai daga cikin su, kallan Hassana ta yi, ta ce, "Baiwar Allah waye ya kawo ki gidannan? ". "Oga Habib". Hassana ta basu amsa kai tsaye , dan ta gaji da tambayoyin da su ke mata. Hassana guri ta samu d'an nesa da su ta kwanta, dan ta gaji sosai dan ma Allah ya tai maketa ta yi sallarta. Hassana kallan ma'aikatan gidan ta ke tana mamakin tom aikin me sukeyi haka, suke da yawa. Hassana kwanciya ta yi, tana kwanciya bacci ya d'auketa. Ma'aikatan gidan Hajiya turai sun sabo tun k'arfe shida na safe kowa ke tashi ya yi aikin da ya ke mazaunin nata. Hassana ko saboda gajiya kasa tashi ta yi. Jimmai wadda ta ke kusan sa'a da Hassana zuwa ta yi, ta bubbuga Hasana da ke kwance tana baccin gajiya. Hassana bud'e ido ta yi tana kallan jimmai. Jimmai ma kallan Hassana ta yi, ta ce, Baiwar Allah ki tashi hakanan, ki yi sallah mana. Hassana tashi ta yi tana kallan jimmai, ta ce, "Dan Allah ina make wayinku? ". Jimmai hannun Hassana ta kama ta ce, "muje in kai ki. Jimmai har toilet d'in su na ma'aikatan gidan ta kai Hassana sannan ta juyo ta dawo. Hassana da sauri ta yi sallah sannan ta kalli jimmai ta ce, "Dan Allah idan zani Sanat yoghurt, idan zan hau keke napep ina zan ce? ". Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "amma dai ke ba 'yar garinnan ba ce ko? ". "Eh ni ba 'yar nan ba ce ". "Ok, in kin samu keke napep ki ce zone, e nepar Sanat yoghurt duk wanda ya ke garin Abuja ai yasan sanat yughurt, za akaiki, har Sanat yoghurt. Hassana godiya ta yi ma Jimmai sannan ta kalli jimmai ta ce, "Dan Allah ko zaki ranta min kud'in keke napep d'in zan bi yaki, wallahi banda ko sisi". Jimmai kallan Hassana ta yi da tausayawa ta ce, "Nawa zan baki? ". "Nawa su ke kaiwa? ". Hassana ta tambayi jimmai. Jimmai d'ari biyu ta ba Hassana ta ce, "Gashi D'ari biyu ne ai ba nisa". Hassana amsa ta yi taima Jimmai godiya. Hassana har ta juya zata tafi Jimmai ta kirata ta ce, "Ba dai da kayan jikinki zaki tafi ba ko? ". Jimmai ta tambayi Hassana ganin kamar da kayan jikinta zata tafi.Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Banda kaya haka nazo ni kad'ai ". Jimmai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ya su nan ki ne?, kuma dan Allah ko zan iya sanin labarinki". Hassana ji tai zuciyarta ta aminta da Jimmai hakan yasa ta ce, "Sunana Hassana, kallo d'aya nai miki sai naji zuciyata ta aminta da ke, dan haka zan baki labarina amma ba yanzu ba, yanzu ina sauri zan tafi". Hassana na kaiwa haka ta juya zata tafi. Da sauri Jimmai ta kamo hannun Hassana ta ce, "Duk da baki ne mi sanin Sunana ba, Sunana Jimmai, idan ba zaki damuba kirik'a sa kayana kafin ki samu naki". Hassana sosai ta ji dad'in abinda jimmai tai mata, dama sosai ta ke jin kunyar fita da kayan jikinta dan sunyi datti sosai. Jimmai ko ta kurama Hassana ta yi tai wanka ta yi break fast sannan tata fi. Lokacin da Hassana ta isa sanart yoghurt, lokacin k'arfe goma na safe, ita da aikinta sharane da goge-goge su da ake buk'atar su je da wuri kafin kowa ya je dan su yi aikinsu. Hassana na shiga gurin ta na cin karo da manager. Sosai Manager ya yi ma Hassana fad'a akan zuwanta lale da ta yi, bayan yagama yi mata fad'ane ya mik'ama mata file d'in hannun shi, ya ce, ta kai Office d'in Oga Habib. Hassana tsayawa ta yi, tana kallan file d'in, sannan manager ad'an tsawace ganin bata amsa ba, ya ce, "Ki amsa mana ki kaima Oga Habib, ki ce mai ya yi marking d'in abubun da muke buk'ata ". Hassana amsa ta yi dan bata da yadda zata yi, amma bata so har ta gama aiki agurinba ta kuma shiga office d'in Oga Habib. Hassana cikin sanyinta ta tura k'ofar office d'in Habib ta shiga. Habib ko alokacin ya na kishingid'e kan sit, ya ji anturo k'ofar Office d'in shi an shigo.... ............
Chapter 10 · 0% Book details