← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 78

Sashe 69

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Turai ko ta dad'e tana lallashin Hassana sannan taba Hassana gu".

B'angaran Habib ko ya na zuwa Farida ta ke jin jiki ta tashi ta zauna. Farida cikin murya irin ta mara lafiya ta ce, "Oga Habib dan Allah ka aure ni, auran ka ka d'ai ne zai iya zaman towa sauk'i gareni, idan baka auran ba mutuwa zan yi... ". Habib rufe ma Farida baki ya yi, dan sosai ya tausayama halin da ta ke ciki, Habib cikin miskilancin shi ya fara magana kamar haka" ki bar yawan magana kin ga baki da lafiya, kuma nina ce zan aure ki, ba sai kin sake min Maganar ba, ina sa ne". Habib ya d'an jima sannan ya yima Mahaifiyar Farida sallama tare da ce mata zai samu Mommy shi su yi magana".

Habib ta gidan shi ya biya ya d'ebo wasu daga cikin kayan sawar shi, sannan ya wuce gidan Hajiya Turai, dan can zai koma baya jin dad'in zaman shi nan shi ka d'ai"

Habib a falo ya samu Hajiya Turai. Zama ya yi sannan zuwa can ya kalli Hajiya Turai ya ce, "Mommy dama Maganar yarinyar nan da nace zan aura, shine mahaifiyarta tai min magana yan zu". Hajiya Turai wani ban zan kallo tai ma Habib sannan ta ce, "Zan yi abu ne yan zu, zuwa gobe kazo sai mu yi magana". Ita ko Hajiya Turai ta yi haka ne, dan tafi son ta ce ma Habib tom ya yi auran karta nuna mai ko mai, tasan idan ya farga yaga ba Hassana, tana da tabba cin ba zai samu na tsuwar auran ba, inda tafi kowa sanin Habib auran tausai zai ma Farida ba wai so ba".

Habib ko jin abinda Hajiya Turai ta ce ne yasa ya tashi ya nufi bedroom d'in Hassana da niyyar duba ta. Hajiya Turai dakatar da Habib ta yi, ta hanyar cewa, "yan zu bacci ya kwace ta karka shiga ka tada ta". Habib ba dan ya soba ya juya ya koma side d'in shi".

Bayan Habib ya yi sallar issha'i ne ya nufi side d'in Hajiya Turai, amma abin mamaki a rufe Habib ya iske k'ofar falon, waya ya ciro ya kira Hajiya Turai, amma bata d'aga ba. Habib sai da ya yi ma Hajiya Turai kira kusan biyar sannan ta d'aga, ta ce mai ta yi bacci sai gobe kanta ne ke mata ciwo wai ta riga ta kwanta".

Habib cikin sanyi ya ce, "Mommy dan Allah ki turo min number Yarinyar nan dan Allah in ji ya jikinta". Hajiya Turai kashe wayar ta yi, ta tura ma Habib number Hassana, tana tura mai ta nufi bedroom Hassana, Hajiya Turai kallanta ta yi, ta ce, "Daughter za'akiraki yan zu kar ki picking Habib ne". "Tom". Cewar Hassana ".

Habib ko ta ke Hajiya Turai na turo mai number ya kira Hassana, amma bata d'aga ba. Habib sai da ya yi ma Hassana kira Uku sannan ya hak'ura ya tura mata Text kamar haka.:Sanat Please na san biki bacci ba, ki zo ki bud'e min k'ofar falo ina son ganin jikinki kafin in kwanta".

Hassana share hawayanta ta yi da ta gama karanta text d'in , Sannan ta gyara kwanciyarta". Habib ko haka ya gaji da tsayuwa ya tafi. Sosai ya ji haushin shasshare shi d'in da Hassana ke yi, gashi yana son ya rabu da ita amma ya kasa. Habib yana tsaki ya koma side d'in shi".

Hajiya Turai ko cikin dare ta shirya ma Hassana kayanta na tafiya,dan tafiyar wuri ta ke so suyi, dan yau zata dawo, Sannan bata son Habib yaga tafiyarsu, tasan zai fi jin zafi idan yazo yaga ba Hassana ".

Asubar Fari Hajiya Turai ta tada Hassana ta yi wanka ta shirya cikin wani brown less, masha Allah Hassana ta yi kyau sosai. 7:00Am Hajiya Turai ta fito da babar jakar kayan Hassana taba Bilya ya sa a but. Habib ko da fitowar shi kenan da niyyar zuwa gaida Hassana.Habib tun daga nesa kafin ya k'ara so ya ke mamakin Kayan da yaga Bilya na sawa abut, ga Hajiya Turai da shirin tafiya a tsaye, Habib cikin zuciyar shi ya ke cewa dama yau Mommy zata tafi bata fad'a min ba..... Tunanin Habib cak ya tsaya ganin Hassana ta fito daga side d'in Hajiya Turai da alamun har da ita za ai tafiyar, ta ke tafiyar Hassana danginta ta fad'o ma Habib".

Habib kusan atare da Hassana suka isa wajan motar, Hassana ko naganin Habib ta yi saurin d'auke kanta, inda shi kuma Habib ya kema Hassana kallan mamaki".

Habib cikin sanyi ya gaida Hajiya Turai. Hajiya Turai ko da taji haushin ganin tafiyar su da Habib ya yi, dan taso ace sai bayan tafiyarsu ya sani tasan haka sai yafi bashi haushi, hakan yasa Hajiya Turai ta k'ara shan mur, Habib kuma cikin alamun damuwa ya ce, "Mommy yau zaki koma ne? ". "Eh". Hajiya Turai ta ba Habib amsa".

Habib kallan Hassana ya yi da ke shirin shiga mota ya ce, "Ke fa, rako zaki yi? ". Kai Hassana ta d'aga ma Habib, Habib ganin haka, ya kalli Bilya ya ce, "Billya bari in kai Mommy ". Hajiya Turai cikin alamun ba wasa, ta ce, "Sauka Bilya zai kai mu dan tafiyar mu da nisa, yau Hassana zata koma dan ginta, ban dai so ta tafi da auran ka ba, amma inda kak'i sak'i sau wa k'e mata babu komai, ahaka zata tafi! ".

Habib da Maganar Hajiya Turai ta soki zuciyar shi kamar an buga mai mashi haka ya ji, ta ke zufa mai d'imi ta fara keto mai.Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, 'Daughter shigo mu wuce".

Habib hannun Hassana ya kamo da sauri ya ce, "Mommy ki yi hak'uri ba bu inda Hassana zata". Habib ya fad'i maganar cikin d'aurewa ".

Hajiya Turai wani banzan kallo tai ma Habib ta ce, "Idan ka isa ba sai ka hana in gani ! ". Hassana ko so take ta shiga cikin motar, amma Habib ya rik'e hannunta sosai, Hajiya Turai fitowa ta yi daga motar tazo taja hannun Hassana, amma Habib ya rik'e hannun Hassana da kyau, Hajiya Turai kallan Habib ta yi, babu alamun wasa ta ce, "Habib sakar ta ". "mommy ki yi hak'uri Hassana babu inda zata".,

Hassana ko cikin murya irin ta mai son yin kuka ta fara magama kamar haka, "Mommy ki ce mai ya sakan, dan duk Maganar da yake bashi da wani iko akaina, a halin yan zu, dan ya ban takarda ta tun jiya, yan zu haka tana hannuna". Habib da mamaki ya kalli Hassana ya ma kasa magana. B'angaran Hajiya Turai ma da mamaki ta ke kallan Habib. Hajiya Turai Cikin b'oye fushin ta ta kalli Habib ta ce, "Habib da gaske ne ka saki Hassana? ". "Mommy ki tambayeta, amma ni ban sake ta ba".

Hajiya Turai mai da kallanta ga Hassana ta yi, ta ce, "Daughter fad'a min gaskiya, yau she Habib ya sake ki!? ". Hajiya Turai cikin fad'uwar gaba ta idasa Maganar, dan tana tunanin tabbas kukan da Hassana ta yi jiya, na sakin da Habib ya yi mata ne"

Hassana Cikin tabbatar wa ta ce, "Mommy Wallahi da gaske nake". "kawo min takardar na gani". Cewar Hajiya Turai ". Habib sakin hannun Hassana ya yi, Hassana kuma ta nufi bedroom d'in Hajiya Turai d'akko ta kardar".

Hassana babu inda bata duba ba amma bata ga takardar ba, haka ta dawo. Hassana kallan Hajiya Turai ta yi ta ce, "Mommy na duba banga takardar ba, amma abinda na fad'a miki haka n... ". Tsawar da Habin ya yi ma Hassana ce ta sa ta yi shiru, Habib cikin b'acin randa Hassana bata tab'a ganin shi da shi ba ya ce, "Idan kina son tafiya ki tafi mana, sai me, amma akan me agabana zaki min k'arya! ".

Hajiya Turai sosai kanta ya d'aure da abinda Hassana ta ce, kuma tabbas ta yadda da Maganar Hassana, dan ta lura da halin da Hassana ta shiga jiya bayan fitowarta side d'in Habib.tom kuma a yananin Maganar Habib kamar bai saki Hassana ba. A zaman da Hajiya Turai tai da Hassana ta lura da yarinyar bata da k'arya, kuma ta lura Hassana na son Habib, ba za tai mai k'arya ba. Hakan yasa Hajiya Turai tai tunanin k'ila Habib d'in ne ya koma daga baya ya d'auke ta kardar, inda ta san shi da fushi, tom k'ila ya yi fushine ya saketa daga baya kuma ya koma ya d'auke ta kardar".

Hajiya Turai ranta b'ace sosai ta ce, "Daughter shiga mu tafi! ". Habib saurin rik'e Hassana ya yi, ya ce, "Mommy na yarda ta tafi, amma sai in ta fad'i gaskiya, dan ni k'arya ta ke min ban saketa ba". Habib ya fad'i maganar ran shi b'ace".

Hajiya Turai da ranta ke ab'ace, kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib ni zaka raina ma hankali ko, ka saketa na ce!". "Mommy ki saurare ni Please, Wallahi ban aikata abinda ta ce ba".
Hajiya Turai d'aga hannu ta yi ta wanka ma Habib mari ta ce, "Sakar mata hannu na ce!". Habib wujijjiga Hassana ya yi, ya ce, " Fad'i ma Mommy gaskiya mai na rubuta miki jikin takardar da na baki........ ✍️

Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.

Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy Baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://www.facebook.com/groups/301023561618950/
Chapter 69 · 0% Book details