← Book details Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 78

Sashe 20

Oga Habeeb Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bilya ne ya kalli Hassana ganin ta fad'a kogon tunani, ya ce, "Hassana ke fa Hajiya ke saurare".
Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Eh Hajiya inanan". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Me yashigar da ke Office d'in shi alokacin?". Hassana Bilya ta nuna ma Hajiya Turai ta ce, "Hajiya Oga Bilya ne yaban ruwan tea in kaime". shiru Hajiya Turai ta yi, dan tabbas idan bata mantaba taji Hajiya Murja ta ce ma, Mahaifiyarta, indai Farida ta tabbata ta ba Habib ruwan tea d'in yasha shikenan, Hajiya Turai azuciyarta ta ce, "Tom ko dai had'a kai su kai harda Bilyan ma?, nan dai Hajiya Turai da taga bata da mai amsa mata, maida kallanta ga Bilya ta yi, ta ce, "Bilya waya ce ka kaima Habib ruwan tea bacin kasan daga nan ake kai mai? ".Bilya cikin natsuwa ya ce, "Hajiya shi yace in kaime, nima bansan dalilinshi ba nahakan". Hajiya Turai kallan tuhuwa taima Bilya sannan ta ce, "Tom meyasa baka kaime da kanka ba kaba Hassana? ". Bilya cikin full Confidence, ya ce, dan yaga kamar Hajiya Turai yau zarkin shi ta ke yi, hakan yasa ya ce, "Hajiya tun kafin in Tashi bacci Farida ta matsamin da kira akan sai dai in kaita Sanat yughurt, amma nace mata sai nayi wanka, rok'ona ta yi akan dan Allah in kaita, alabashi idan na dawo sai in yi wankan, tom ni kuma bazan iya musa mata ba, hakan yasa sai nace mata ganinnan zuwa, tom shine fa bayan takatse kiran ni kuma na yi sauri nashiga wanka. Tom ina fitowa daga wanka Oga Habib ya kirani akan in siyo mai tea in kai mai yanzu. Tom nasan idan Oga Habib ya na son Abu yadda yake, hakan yasa ina fitowa na manta da Farida na jirana na tafi, sai da nashiga Sanat company sannan natuna da tun d'azu Farida ke jirana. Tom nasan Oga Habib idan nashiga dakyar idan zai barni in fito yanzu zai iya sani wani abun, hakan yasa da naga Hassana na bata tea d'in nace ta kaime, ni kuma na dawo da niyyar d'aukar Farida, tom ahanyama muka had'u ta gaji da jirana ta taho a napep,na tsaida napep d'in na d'auketa. Shine fa muna shiga cikin Company muka ji wata irin razanannar k'ara Oga Habib ya yi".
Bilya kallan Hajiya Turai ya yi ya ce, "wannan shine abinda nasani Hajiya, amma ga Hassana nan sai ta idasa miki bayani".

Shiru Hajiya Turai ta yi dan tabbas a kwai alamun gaskiya a magan-ganun Bilya, hakan yasa Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "Hassana bayan shigarki Office d'in Habib me yafaru, alokacin? ". Hassana cikin sanyin murya ta ce, " Hajiya Duk da Oga Habib nada idan mutum ya yi nocking ya dad'e bai amsa mai ba, amma gaskiya a Jiya da zan shiga office d'in shi, naji shirun ya yi yawa, dan har saida nafara tunanin ko dai baya office d'in ne, sannan zuwa can yace in shigo, koda nashiga jug d'in hannuna na mik'a mai na ce inji Oga Bilya ya ce zai dawo yanzu". Shiru Hassana ta yi ta d'an numfasa, sannan ta ci gaba da cewa, " gaskiya tunda nashiga Office d'in Oga Habib zan ita cewa babu lafiya atattare da yadda naga yana yin shi, dan koda na bashi sak'on Oga Bilya, bai amsamin ba bai kuma kallan ba, sai dai ya tashi tsaye ayanayin yadda naga jikinshi kamar rawa yake, hakan yasa sai naji tsoro naja baya, sai ji nai ya mik'on hannun shi ya ce, dan Allah in rik'e mai. Tom ni dama gaskiya ko ayanayin yadda naji maganarsa nasan ba lafiyar shi k'alau ba, hakan ya sa naruga zan bud'e k'ofa in fita, amma kafin in fita har yarik'omin hannu, dan su Oga Bilya ne ma suka k'watan daga hannun shi".
Shiru Hassana ta yi sannan ta ce, "wannan shine abinda ya faru, Hajiya da nashiga office d'in Oga Habib kai mai tea d'in ".
Shiru Hajiya Turai ta yi tana kallan Hassana, dan akwai alamun gaskiya a maganar Hassana d'in, dan yanzu ta san abinda kunnan ta yaji mata hakane, Farida ce ta ba Habib wani tea d'in kenan, wato idan ta fahimta farida taso zuwa office d'in Habib kafin abinda ya sa mai ya sa mai.
Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana je ki abinki". Bayan Hassana ta tafi ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, Bilya kaje Zaria yau d'in nan ka tahomin da Baba lami, dan ina buk'atarta sosai, amma dan Allah kafin munje akaima Habib abin break fast, nasan tunjiya baici komai ba, inda bacikin hankalinshi ya ke ba.Bilya tashi ya yi Hajiya Turai, tafi bayansu suka tafi ganin halinda Habib ya kwana, tare da kai mai abin break fast. Bilya tsayawa ya yi daga k'ofar d'akin ya ce, "Hajiya ko za ki yi gaba? ". Hajiya Turai gaba ta yi batare da ta tankama Bilya ba.Hajiya Turai zaune ta iske Habib, sai dai kafin ta k'arasa inda ya ke Habib ya yo kan Hajiya Turai".

Wani irin rik'o Habib ya yi ma Hajiya Turai, yana wujijjigata. Hajiya Turai tun tana daurewa tana cewa, "Habib ni ce fa, Habib mahaifiyarka ce fa ni, Habib kamanta ni ne ?, sakanni Habib da zafi! ". Haka Hajiya Turai ta idasa maganar cikin tashin hankali. Daga k'arshe da taga Habib tabbas bacikin hankalinshi ya ke ba, hakan yasa ta fasa k'ara ta ce, "Wayyo Bilya kana ina zo ka tai makamin! ".

Bilya da saurinsa ya shiga, kan Habib ya yo, Habib ko na ganin Bilya ya saki Hajiya Turai ya yi kan Bilya, sai dai Bilya na ganin haka ya fita da gudu. Hajiya Turai ko ta k'ofar baya ta fita itama. Hajiya Turai falon bedroom d'in da Habib ya ke ta zauna tana, kuka. Bilya zagayawa ya yi ta baya yashiga falon Habib d'in, zaune Bilya ya iske Hajiya Turai tana kuka ".

Bilya k'arasawa inda Hajiya Turai ta ke ya yi. Bilya cikin lallashi ya ce, "ki yi hak'uri Hajiya shi kuka da kika gani babu wani abunda zai miki sai dai ya samiki wani ciwan, yanzu abinda ya kamata muyi musan abinda ke damun Oga Habib". Hajiya Turai d'aga kai tayi tana kallan Bilya ta ce, "Bilya na san meke damun Habib, shi yasa nake son ganin Baba lami da sauri, ka tafi Zaria yanzu dan Allah Bilya ka tahomin da Baba Lami". "Shikenan Hajiya babu damuwa insha Allah yau d'innan zaki ga Baba Lami. Bilya na fad'in haka ya yi ma Hajiya Turai sallama ya kama hanyar Zaria.
Hajiya Turai ko na nan zaune tana tunanin, magan-ganun Farida na d'azu, ta ce, "wato idan nagane maganar Farida tana nufin wadda Habib ya tashi ya farka a halinda ya ke yagani, zai iya yadda da ita kenan.kai wai tom meye niyyar Farida ne akan Habib?, ya Allah ka kawo min Baba Lami yau". Hajiya Turai fitowa daga falon Habib ta yi, tana fitowa ta had'u da Farida ita kuma da shirinta na barin gidan".

Farida cikin mamaki ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Kai Mommy ashe kin dawo?, yaushe kika dawo? ". Hajiya Turai ji tai kamar tai banza da Farida, sai da bata son ta nuna ma Farida komai, akwai lokaci acewarta. Hakan yasa Hajiya Turai ta ce, "Jiya da daddare lokacin kinyi bacci, Ina zaki ne haka? ". Hajiya Turai ta tambayi Farida."Sak'o Mommyna ta aikan in amso mata, yanzu zan dawo". "Ok". Hajiya Turai ta ce mata sannan ta juya ta tafi. Hajiya Turai Bilya ta kira awaya, Bilya na d'agawa tace, "Hello Bilya kana jina ko? ". "Eh Hajiya Ina ji". "Yauwa, Bilya idan baka riga katafi ba, ka je Sanat company yanzu dan Allah, ga Farida nan zata je yanzu, kayi k'okari ina son sanin abinda ya kaita". "Shikenan babu damuwa, bari inje kafin ta isa". Bilya na fad'in haka, ya juya yakama hanyar Sanat company".

Hajiya Turai nagama wayar sai ga wata binta da ke mata wanki, Hajiya Turai kiranta ta yi, ta ce, "Binta kiramin yarinyar da ke aiki a Sanat yughurt". Binta da saurinta ta juya ta tafi dan ida sak'on Hajiya Turai".

Hassana na zaune ita kad'ai dan soran worker's d'in Kowa ya kama gabanshi dan yin aikin da ya ke amazaunin nashi, binta tazo ta ce, "Ke Hajiya na kiranki, ta ce ki sameta a falonta". Gaban Hassana fad'uwa ya yi jin wai Hajiya na kiranta. Azuciyarta ta ce, "Tom bayanzu ta kirani ba ba dad'ewa, Allah dai kasa lafiya". Hassana tashi ta yi tanufi site d'in Hajiya Turai. Hassana zaune ta iske Hajiya Turai a falonta. Hassana cikin sanyin muryarta ta yi sallama, d'annesa da Hajiya Turai Hassana ta zauna, bayan Hassana ta zauna ne, ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Hajiya gani ance kina kirana". Hajiya Turai abin break fast d'in da suka kaima Habib suka dawo dashi ta mik'ama Hassana ta ce, "Kin san site d'in Habib? ". "Eh na sani". "Yauwa, Hassana dan Allah me ba Habib abinci ne baya nan, na aikai Zaria, shine dan Allah nake son ki kai mai".
Hassana cikin girmamawa ta ce"Tom". D'aukar abin break fast d'in Hassana tayi ta tafi.Hajiya Turai tashi ta yi ta yi bedroom d'in ta fita tashiga Falon Habib ta na jiran zuwan Hassana taga ikon Allah, ta ga maganar da Farida ta fad'a gaskiya ne kok'aya".

Hassana ko,
tambayr kanta ita kad'ai ta yi, ta ce, "Tom oga Habib ya warkene? ".Nan dai bata da mai bata amsa, haka Hassana ta nufi site d'in Habib da abincin gabanta na fad'uwa. kasan cewar Hassana ba taji labarin Habib na dukaba, hakan yasa ba wata fargabar hakan, ta bud'e k'ofar ta shiga kai tsaye.........

COMMENT
&
SHERE
PLEASE 🙏

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*

https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
Chapter 20 · 0% Book details