← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 76

Sashe 9

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bello da Muktar su suka koma wanke motoci da bama fulawowi ruwa wani Lokaci Bello ke nuna Taurin kai Sai yaki yi Haka  Abba Kabiru zai Ta Marinshi Ammah yakiyi,Yana da Saurin Saka Abu Acikin Ranshi Shiyasa komai yakasa Bacemai Hajiya Sahura ko da Hajiya Karima ba irin Wahalan da Basu ba su ba Kamar basu Taba Saninsu ba,Sunsha lakaba ma ya muktar sata,Mussmman Bello da ya cika bakar Zuciya yafi muktar shan wuya agidan Hatta da su Zubaida dake yara Suma Sun Iya Wulakanci Musamman ga Muktar Wanda baya da Fada da Hayani Wani Lokacin bello ke kwatanshi Shiyasa Duk yafishi shan Wahalansu, Cikin Shekaru uku Suka Chanza Kamanni Rayuwarsu Duk ta lalace Kamar basu bane ya"yan Hutu ba Tuni Hashim ya Dawo ya Zama Saurayi dayake yana da girman jiki Har yafara Aiki da Kamfanin da Abba Kabiru ya Hamdamai Wai Muktar ne ke Budemai get in zai zai Fita Yau ya Hau Wannan Mota gobe ya Hau Wannan yana Cin Duniyarsa da Tsinke

Basu da inda zasu je Ataimaka musu Dangin Babansu na Jikamshi Duk sun kare sai D'aid'ai na nesa wadanda suma fama suke da kansu,kuma na nesan ma wadanda ke cikin kauyuka,Malumfashi ma Sau Daya suka taba zuwa suma duk sun kare Dangin kakarsu ta wajen Uba basu san kowa ba,sai Dangin mamarsu na yola sai kuwa su Abba kabiru.

Kwatsam Sai ga Daada ta Diro Gidan Halin Data Tarar da Jikokinta Sai da ya sakata Kuka Ta Dingama Su Abba Kabiru Allah ya Isa Ba Kunya ba Tsoron Allah Sukace Allah ya isa ya Bita Dukiya ne suncinye In zata Kwatan musu ne Bismillanta Daada bata Damu ba ko Kwana Batayi ba Tattaro Muktar da Bello ta Taho Dasu Gidan yayanta Baffa Hadi,Daman bayan Rasuwar Mahaifin Hassatu Wajensa Take Zaune Ta karantamai Duk Abunda yafaru nan Take ya karbi su Muktar kuma yayi Alkawarin Rikesu Amana su kuma Su Abba Kabiru yace zai makasu kotu Daada ta hana tace ya kyalesu duk wanda yaci hakkin maraya sai Allah ya tambayeshi Badai cin Hakkin Maraya ba Zasu girbi Abunda Suka Shuka ne.

   Ya Maida Muktar Kaduna NDA Dole ya Dawo baya a karatunsa domin tuni yan batch dinsu sun dade da gamawa bai damu ba ya Cigaba da karban Horaswan Sojoji Shi kuma Bello ya Sanyashi Wata Makranta ta masu Hali Ya Dora Daga SS1 duk Abunda ya Faru bai bacema Bello ba ya Rikeshi Sosai Acikin Kanshi yakuma Ji Duk Duniya babu Wanda Ya Tsana kamar Su Abba Kabiru da Iyalansu,Shiyasa Ko Alama baijin Zai iya Hada hanya ko Wata Mu"amalan Arziki dasu har gaban Abada.

Lokacin Daya kamallah Secondry Sch Dinsa ya Tafi University of Ibadan Shikuma Muktar yagama Short Service dinsa ya Fito Amatsauyin Second Leutanant,Yana Aiki A barikin Jaji Dake Kaduna,Bello Dama Tun yana Karaminsa yake da Burin ya Zama malamin Makranta Yasha Fadama Daada Haka da Muktar Ammh Sai basu Daukan Abun da Muhimmci,Mathematics yake Karanta sai inda sun Samu Hutu yake Zuwa Gida.

Yana Kara Girma Duka Murdadun Halayansa Suna Kara Bayyana Koda da Rana Daya Bello bai Manta da Abunda Su Abba Kabiru Suka Aikata Garesu ba Ayayinda Shi Muktar Yake da Saukakkiyar Zuciya Tuni Abun ya Fitar Mishi Arai bai kuma Rikeshi Ba Sabanin Bello Wanda Ta Kowani bangare Suna da Bambancin Ra"ayi.

  Lokacin daya Kammallah First Digree Dinsa ne,Yatafi Makrantar GGUSS KWATAR KWASHI yayi musu Bautar Kasa Ko Alokacin Muktar yaso ya Hanashi Ammh Ya Nuna Shifa Abunda yake Ra"ayi kenan Lokacin Har Muktar yakai Matsauyin Captain ne yana Aiki a Barikin 1 Division Barrak Dake Kaduna.

   Bello yaji Dadin Bautar Kasar Daya Gudanar A Makrantan Kwana ta Kwatar kwashi,Wanda Suma Makranta Taji Dadin Zuwanshi Tunda dama suna da Karancin Malamin Lissafi Tun Alokacin Bello yayi yaki da Mata Sosai Saboda Yadda ya Tara komai na Cikar Zatin Da Namiji bai maida kai ba Tunda Kowa yasan Muhammed Bello Jikamshi bashi da Wasa ko kadan.

Batare da Saninshi ba yayanshi Muktar da Baffa Hadi Suka samarmai Wata Makranta a Babban Birnin America Wato U.S inda yaje ya Hado Masters Dinshi Akan Mathematics.

Rayuwa tayi ta tafiya yarda Allah ya Tsara Muktar na Aiki yana Kara Samun Girma Awajen Aiki,har yakai Matsayin Cononel Lokacin ne kuma Bello yadawo Daga America bayan ya Hado Masters Dinsa yana Da Shekara 26aduniya Shi kuma Muktar nada 40 alokacin kuma Baiyi Aure ba akuma Lokacin ne Su  Abba Kabiru Suka Nemesu bayan Duka Dukiyar da Suka Hamdemai Ta Gudu Ta barsu Dama Hakkin Maraya bazai Taba Zama ba.

Har yola Suka tako Duka Suda iyalansu Suna Kuka Suna Rokonsu Muktar gafara Sakamakom Sunga Bala"i kala kala Gashi komai na Dukiyar baya Cigaba ga Mugayen Mafarkai da Kuma Rabuwar kai Tsakaninshi da Abba garba Matayen Suma sai Cin Juna,da Fada Hakama ya"yansu basa zaman lafiya,Saboda Dukiya wacce kwata kwata batayi albarka ba Sauran kamfanonin ma Tuni sukayi gwanjensu saboda ba ma"aikata kowa ya gudu tunda babu albashi ba hannayen jari ba kuma ba Shugaban kwarai kafin kace kwabo komai Da suka Hamdame ya fara gudu ya barsu kamar kudaden suna kamawa da Huta gidaje da Filaye dama Tuni shi da Abba garba suka raba kowa yaja rabonsa suma basu kai labari ba saboda yadda suka sakarma matansu da ya"yansu Ragamar komai suna cin karensu ba Babba Da Dukiyar ta fara salwanta Kusan mugunta Fitsarin Fako ne sai suka fara Zargin junansu da cewa cikinsu ne wani ya sakama Dan"uwansa Hannu komai ya lalace shine Dalilin Rabuwan kansu Dana ya"yansu domin Daga Sahura har Karima kowa tabi bayan mijinta da ya"yanta.

Suna Kuka Suna Sanar Dasu Abunda Suka Aikata ga Muhammed da Matarsa Hassatu, da Muktar da Daada ne Keta Kuka Basu da Abun Cewa Domin ko haka aka Tsaya Sunga isharansu nan da nan Sukace Zasu Mika Sauran Dukiyan ga Muktar da Bello Shi kuma yace Su Rike kawai Sun bar musu Duk da bai Shawarci bello ba yafi kowa sanin Bazai Taba Karba ba,Shiko Bello Suna Zuwa Gidan ya Fita bai kuma Dawo ba Har Suka Tafi Abun yamishi Ciwo yadda yaga Muktar bai Damu ba har yana Sakar Musu Fuska Lokacin Su Zubaida da Zulfa Duk Sun zama yan Mata Kowacce na SS2 alokacin Ummu salma kuma Da Hamdiya Suna Wajen Inna Rukayya Dake Kano Hashim Kuma yayi Aure Har ya Haihu Sai Kasim dake Jami"a Alokacin sunji matukar mamaki da Muktar yace sun bar musu Duka Dukiyan Daya rage ahannunsu,Dama suna tunanin taya rayuwarsu zata kare in suka karbi komai tunda hatta hashim yanzu zaune yake baya aikin komai Tunda Duka kamfononin sun sanyasu akasuwa sun karbi yan kudadansu.

Muktar baiyi Aure ba Sai da ya keda Mukamin Major Shekarunsa Lokacin 44 aduniya Kana yayi Aure da Matarshi yar Garin Borno Kanuri ce gaba Da baya Mai Suna Rahila Wacce Suka Hadu Lokacin Daya Jagoranci Wata bataliya Zuwa Maiduguri.

   Bayan Aurensu ba Dadewa Ya Dauko Matarsa Daga Yola Zuwa Abuja Inda yake aiki a Abacha barrak,Shi kuma Bello ya koma Makrantan kwana ta Kwatar-kwashi Yana Koyarwa Wanda Muktar da Daada Sun yi Sunyi Ammh ya Kafe yace Shi zaiyi Hatta Jami'ar Dayayi Ta University of Ibadan Suna Nemanshi Su bashi lecturing Ammh yaki Dole Suka Sanyamai Ido Tunda Haka Allah yayi Shi da Taurin Kan Tsiya.

****

"" *ANEESA BUKAR BULAMA* Shine Cikakken Sunan Aneesa Kuma Itadin kanwa Take ga Anty Rahila matar Muktar,Ubansu Daya Uwa Kowa da Tashi.

Sun Fito daga Tsatson Yaren Kanuri na Garin Bornon Maiduguri Kanuri ne na Gaba da baya Irin bakaken nan masu Kyau da Tsari,Suna Zaune a Unguwar Damboa Road.

  Ahaji Bukar Bulama Shine Mahaifinsu Wanda ya Kasance yana Da Rufin Asiri Daidai Gwargwado Tunda Dan Siyasa ne Sosai yana da Matan Aure Biyu Wato *Mama Yana* sai * Mama Falmata* wacce Itace Mahaifiyar Aneesa.

  Su Bakwai ne agidansu Mama yana Keda ya"ya Bakwai Falmata Sai Daga baya Aka Aurota ,Babban Gidan Shine Yaya Ali,Sai ya Sunusi,sai Anty Nafi,Sai Anty Yagana,Anty Rahila sai Anty Aisha,Sai ni Aneesa Auta, Falmata Tafi Shekara goma bata samu Haihuwa ba sai Akan Aneesa,Wacce  Tun bayan Haihuwata na Taso Agidanmu Cikin gata Sosai Daga Duka bangoririn iyaye na Aneesa yarinya ce mai Shiga Rai Gata Auta Wannan Dalilin ne Alhaji Bukar Bulama ya Sangartata Sosai Duk Abunda Takeso Shi yake mata.

Aneesa Tataso Tun Tana Karamarta da Tsiwa ga Rashin Kunya da Rashin Tsoro Ko Falmata datake Mahaifiyarta Bata Isa ta Daketa ba yanzu Alhaji Bukar Bulama zai Fara Fadanshi na Fama Kan Aneesa Ko Kukanta bayaso yanzu Ran Kowa Zai  baci,Wannan Dalilin ne ya Sanya Aneesa Tataso Cikin Gatan Sangarta Ko yayyinta su Anty Nafi Ba Wanda ya Isa yaga Tana Abu yayi mgana Yanzu Zata Saka Kuka In ko Alhaji Bukar Bulama yaji Kukan Aneesa ka Shiga Uku..

Saboda Son Daya ke mata da Kuma Sangarta ta Dayayi ko Ina Zashi Tun Tana karamarta Tare yake Zuwa da Ita Koda Taronsu na Siyasa ne Shiyasa Duk Wanda Ke Tare da Alhaji Bukar Bulama yasan Wacece Shalele yar Auta,Tun Tana karamarta Har Zuwa Lokacin Data isa Zuwa Mkranta da Alhaji Bulama yayi Kokarin Saka Aneesa Amakranta Sai Rigimarta ya Tashi Kullum Da Dambe Ake Shiga da ita Makranta Su yaya Ali ne ke Kaita Watarana Sai Sun Hadamata da Duka Kuma Haka za"a Daukota Tana Kuka Batama Tsayawa ta Fahimci karatun Hakama Islamiya bata Zuwa Duk ko Ranar da Aka Matsamata Haka zata Wuni Kuka Har Alhaji Bukar ya Dawo Kuma In ya Shigo yaji Kukanta Ran Kowa sai ya baci Agidan Manya da yara.

Ganin Haka yasa yace akyaleta Tunda batason Karatun yarinta Ke Damunta in takara Girma Zatayi Haka ko Akayi Dakyar Aneesa Ta Kamallah Primary 2 Shima ba Kullum Take Zuwa ba Sai yan Rigimarta Basu Kusa,Yaya Sunusi da Yaya Ali Dukkansu Sun kamallah Karatunsu yaya Ali Ma"aikacin banki ne Shi kuma Yaya Sunusi yana Aiki A Hukumar Man Fetur ne Wato NNPC,Anty Nafi Tayi Aure acikin Garin Maiduguri Yayinda Anty yagana Tayi Aure Agarin Ibadan,Suma ba Wacce Batayi karatu ba,Aneesa ce Ta Bambanta Domin In Tana Kaunar Mutuwarta tana Kaunar Karatu.
Chapter 9 · 0% Book details