← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 76

Sashe 62

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Mirmishi Bello yace"Daada,ya mukatar,Anty Rahila...Nine dai...Jiya Allah yayi ikonsa Na tashi Bisa kafafuna ni na Hana akiraku saboda ina so na baku mamaki ne."Yafada kamar zaiyi kwallah ai sai Ya Muktar ya Zube kasa ya Daga Hammu sama yana Fadin"Alhamdulillah...Alhamdulillah...Allah mungode maka..Allah mungode maka kai ne Shugaban Halittun Duniya...Baka Haifa ba kuma Ba"a haifeka ba...Godiya ta tabbata ga Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam.."Yafada Lokaci Daya Hawaye suna kwaranyowa Daga kwarmin idanuwansa,Daada da Anty Rahila suma godiyar sukema Allah suna Share kwallah Cikin Farimciki Bello ya Saki Hannun Aneesa ya karisa ga Dan"uwansa ya Duka suka Kamkame juna Lokaci Daya Cikin Tsantsan Farincikin ahaka suke mike tsaye Daada tazo ta Hadasu ta Rumgumesu cikin kuka take Fadin"Allah mungode maka...Allah Abun godiya.."Ita kanta Aneesa sai da taji Tahowar kwallah Cikin Sanyin Jiki ta karisa ta Fada Jikin Anty Rahila suka Rumgume Juna,anan ne taji jikinta da Zafi da sauri ta Dagota tana Fadin"Aneesa baki da lafiya ne..? Jikinki ya Dau zafi.."?

Da Sauri Bello ya saki ya muktar da Daada yana Fadin"Eh bata jin Dadi...Taho my Anee kije ki kwanta ko zamu tafi kiga Dr ne.."?Yafada yana Rikota kai ta girgiza tana kwanciya Bisa kafadansa cikin Sanyin murya tace"Zan kwanta.."kura mata ido yayi yaga har ta Dan Fada Rikota yayi sosai Bisa Jikinsa yana Fadin"Oya muje ki kwanta ki Huta...In kin tashi in zazzabin bai sauka zai mu tafi kiga likita ko..?kai ta gyada mai suka Fara Tafiya su Daada suka bisu da kallo Cike da Sha"awa tafiyar Aneesa ne ta Fallasata Mirmishi Anty Rahila tayi cikin Ranta tana Fadin"Aneesa ta girma..."cikin jin Dadin mara misaltuwa Ya muktar ko baki yaki Rufuwa Shi ya Dauki waya ya kira y Ali yana Labatarmai wannan Daddalan Labari kowayaji sai ya saaki kabbara cike da Farinciki Ita kuma Daada ta kira Adamawa ta sanar ma Baffa hardo Shima haka yayi ta kabbara yana Zubama Allah kirari yaji Dadi sosai kuma ya tabbatar da Babu Abunda ya karfin Allah Tabbas Kudaran Allah ne yasa wani Abu ya Giffta aka hako wannan Jakin da aka binne da Rai wanda akayi Ma Bello Shihiri dashi.

Haka Abun yafaru dama an binne Abun atsakanin Dajin Abuja da Minna ne, Cikin Ikon Allah sai Titi yabi ta wajen nan da nan Turawa suka saka inji suka markade kasar wajen suka hako abun batare da sun sani ba,dama kuma makarin karyewar Asirin Shine ahako wannan Jakin Dake cikkin Rami wanda aka Daure Wuyanshi da layan Sihirin,toh wajen hako Abun Inji ya Darkake jakin Shi kuma layar ya bar Wuyan Jaki bayan injin din yayi Fata Fata dashi ,wannan Shine Dalilin Daya sanya Bello ya Taka da Kafafunsa kamar bai taba wani Abu mai kama da Jinya ba.

Dakinta na da ya shiga da ita ya kwantar da ita bisa gado ya lulluba mata blanket yana kallon Fuskarta yace"I love...U my Anee...Banajin Dadin ganinki ahaka..Ki gafarce ni banyi da niy..."Bai karisa ba ta rufemai baki tana girgizamai kai tace"Kadai na bani Hakuri kada Allah yayi Fushi dani Abunda yake mallakin ka ne fa ka karba B.love...Ko yanzu kace kana Bukatata ni mai mika Wuya ce...Kasani ni matarkace kuma Rufin Asirinka...Ina sonka Gwarzona ina Kuma alfahari da samunka amatsayin mijin Aurena..."Tafada tana Sakarma Hannunsa Kiss Dadi ya kamashi ya Duka ya bata sumba mai tsawo kafin ya mike ya zauna kusa da ita yana matsa Tafin Hannunta yake Fadin"Kece Abun Alfaharina Aneesa...Naso na Tafka asara da na bari kasim ya Aureki da yanzu bana cikin Farincikin  Danake ciki yanzu..I realy Love u my wife.."Yafada yana Kara matsemin Hannu Lumshe ido nayi cikin so da Kauna nace.."Love u...Forever and Ever...B.love.."Nafada ina jin kamar na Bude Zuciyata na sakashi Saboda yadda Zuciyata ke Bugawa da kowani Harafi na Soyayyarsa.

Yana ta matsa min Hannuna yana min kalamai kauna mai Tsayawa azuciyar Masoyi Har barci ya kwasheni sai da nayi barci kana ya lallaba ya Fito Falon Daada nan fa aka hadu ana ta Hira kafim kace kwabo labari ya kai kunnen yan"uwa da abokan Arzuka sai kiran waya ake ana Tayasu murna,Uncle Aminu ma sai gashi ya kira kila Ammi ta gayamai Su Abba kabiru ne kadai ya muktar ya manta dasu bai kirasu ba,kuma ba wanda ya Tunamai yan'uwana sai kiran wayata suke domin Tayani murna ammh basu samuna Domin ina kwance ina barci Anty Rahila ya baiwa wayar take dauka tace nazo bana jin Dadi ya muktar kuwa yana Cikin Farinciki wanda saboda murna yace gabadayansu zasu tafi su sauke Farali wannan Shekarar Harda Baffa Hardo Tunda Daada ta sanar da Bello komai na taimakon shi Dayayi kan wannan Ciwon nashi Bello yaji Dadi kuma yace insha Allahu zai taka har Adamawa ya kaima Baffa hardo gaisuwa tare godiya Modibbo kuwa Tundazu ya koma shashen Bello ya Shige ya kwanta yana ta waya da Raihana,yana sanar da ita Wannam Shekaran Allah ya kirasa zai sauke Farali nan tayashi Murna kafin su shiga Hiran Soyayyahrsu.

Aneesa bata tashi ba Sai Bayan la"asar kana ta tashi Shima Anty Rahila ce ta tada ita ta mike tana Mika Lokaci Daya tana Fadin"Anty Rahila anyi Azahar ne..? Hararan wasa ta kai mata tana Fadin"Eh lalle toh har la"asar anyi Azahar kuma sai dai na gobe..ki tashi kiyi sallah mijinki ya hana atasheki yanzu ma yatafi shashenshi ne,yasa na shigo na Tadake."Saukowa Tayi Daga kan gadon Tana Fadin"Allah Sarki B.love.."Tafada tana gimtse baki jin kasanta na mata Zafi Da kallo Anty Rahila ta bita kafin tace"Kin shiga ruwan zafi kuwa..? Cikin jin kunya Ta Daga kai batare Data waigo ba Anty Rahila bata mata mgana ba ta nufi Tiolet din ta Hada mata ruwa mai Zafi ta Fito Tana Fadin"Ki gasa jikinki sosai...In kina so kidaina Dingishi kuma wajen yayi Saurin warkewa..Ba"a taurin kai awannan harkan in baki kula da kanki ba ke kika sani.."Tafada tana rabata ta Fice Daga Dakin Kunya ta kara kama Aneesa tayi mirmishi ta Fada Tiolet din.

Taji Dadin Ruwan Dumin sosai Ruwa biyu ta chanza kafin tayi wanka ta Dauro alwala ta Fito,cikin kayan ta Tun na gida ta saka wata Doguwar Rigar Atamfa Tunda kayansu na Mota ba laifi taji Dadin Jikinta ta Daina ma Dingisa kafar sai da nayi sallar Azahar nayi la"asar na sallame kenan Bello ya Turo kofa ya Shigo yana Fadin"Anee wannan barcin yayi yawa.."Yafada kenan sai kuma ya ganni tsaye ina Kokarin kwabe Hijabin jikina

Mirmishi ya sakarmin yana Fadin"Ashe kin tashi..? Kaina Gyada mai ina Fadin"Anty Rahila ce ta tasheni nayi sallolin dake kaina.."Na fada ina hamma Riko ni yayi yana karba Hijabin hannuna ya ijiye yana Fadin"Sai da fa nace karta ta tasheki..ya zazzabin..? Ya sauka..?kai na Damgwabe ina Fadin"Daidai nake jina sai dai yunwa dana ke ji.."Mirmishi yayi yana lakacemin Hanci yace"Oya muje na baki abinci ki ci ki koshi har ki kasa tashi.."ware ido nayi shi kuma sai ya Riko hannuna yana Dariya kan Kafadarsa na yada kaina Muka Fita Daga Dakin Zuwa Falo.

Babu kowa cikin Falon na Daada,Zaunar dani yayi kan kujera yaje ya Karbomin Abinci a kichen yazo ya Zauna kan Cinyarsa ya Zaunar dani yana Bani abinci har sai da na koshi,Yana cikin bani ruwa sai ga Daada ta Fito Daga Daki baki ta rike tana kallonmu Lokaci Daya take Fadin"Lalata..Kai Bello miye haka nan fa ba gidan ku bane.."

Kallonta yayi yana Fadin"Daada ki koma ciki kawai in dai bazaki iya gani ki kyale ba...Nifa bana iya zama ban rabi my Anee ba itama Haka.."Dariya Aneesa tayi ganin yadda Daada tayi,bata samu Zarafin mgana ba Modibbo ya Shigo ganin mu Ahaka yasa ya shafa keya yana Fadin"Au Daada kema kin gani ko..? Haka nake fama muna kano Baffale na kan keke ya iya barna.."Yafada yana Dariya Hararansa mukayi Duka Tare Kada kai Daada tayi kafin tace"Umh...Naga alama Marasa kunya.."Tafada tana juyawa zuwa Cikin Bedroom dinta muka Bita da Dariya,Modibbo ko Waje yayi yana Fadin"muma mun kusa shiga wannan Stage din..".

Mudai bamu bi ta kansu ba..Bayan ya gama bani Abinci Muka koma muka lafe Bisa kujera ina kan Jikinsa ina waasa da Sajensa muna Hira sama sama sai da aka kira sallar mangariba kana muka rabu yatafi masallaci ni kuma na shiga daki nayi tawa ina idarwa sai ga Hibba ta shigo Dakina da gudu tana Fadin oyoyo Anty Anee..Rumgumeta nayi na Dagata sama ina Murnan ganinta Daganan muka Fita Falon Anty Rahila inda na isketa tana waya da Ya Sunusi har tabani muka gaisa yana min Barka da Arziki naji kunya sosai,nan ya bama su Mama Yana da Falmata mukayi Mgana suna kara nuna Jin Dadinsu Ashe hardasu a wadanda Ya Muktar ya zana zamu hajji bana naji Dadi sosai.

Dakyar Daada ta kori Bello ya koma Shashensa Da yace anan zai kwana ga matarshi bazai kwana da kato ba Modibbo na Dariya yana Fadin Allah ya sakamun Baffale nine kato,hararansa Bello yayi yana Fadin"Toh in ba kato bane mace ne kai.."Daada ko ta iza keyarsa tace ya Fice mata Daga Shashe bata son Rashin Kunya bai da yarda zai yi Haka ya Tafi Ni kaina banji Dadi ba Domin na saba kwana Bisa Kirjin Mijina Nima ina Tura baki da kunkuni na Nufi Dakina ina Fadin"Daada wai ina ruwanki da Shiga tsakanin miji da matarsa.."Tace an shiga din ba anan zaku man rashin kunyarku na Diyan zamani ba..Su ya muktar naji suna Dariya Dole dai kanwar naki Hibba nace tazo Tatayani kwana,ammh Kusan Raba Dare mukayi muna waya na Tambayeshi ina Modibbo yace yana cikin Daki shi kuma Falo ya Fito bayaso yaji Sirrin ma"aurata Dariya kawai nayi muka cigaba da Soyewarmu.

*******
*Kaduna...*
 
Kasim da Aisha kuwa suna Cigaba da soyewarsu bata Tunanin wani Abu zai iya Faruwa anan gaba cikin wannan Halin ne ta fara ciwo,zazzabi komai taci baya zama acikinta Tunda kasim yaga Haka Hankalinsa yatashi yafara zargin Ciki ne nan ya dauketa suka tafi Asibitin Barau dikko dake Kaduna agwajin Farko Ciki dan Wata uku ya bayyana ajikin Aisha

Ta firgita sosai nan ta Shiga Rusa kuka,Ammh sai Kukanta ya tsaya Jin Kasim na rokar likitan ya taimakamai ya Zubar da Cikin Jikin Sadiya cikin mamaki ta waro ido tana kallonsa kafin tace"A zubar fa kace..? Toh saboda mene..?.
Chapter 62 · 0% Book details