← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 76

Sashe 69

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 12 na safe su Ya muktar suka shiga kaduna State C.I.D Koda suka iso sun iske su Abba garba,Abba kabiru kuwa karfin Hali kawai yake yi Domin Tun ranar da Suka bar kaduna bai da lafiya Dauriya kadai yake sun iso ba Dadewa Aminu ya iso nan da nan ko aka Fito da kasim wanda yagama Ramewa ya lalace Duk da ba Duka ba Zagi ammh zaman Cell ba Wasa ba, Duk Fuskarsa ta kode da Kuka Da cizon Sauro yana Shigowa Office din da Bello yafara cin karo Tsaye kan kafafunsa yana Sanye da Ameriacan Suit Baki da Ruwan Toka ya matse Wuyansa da Tie baki Fuskarsa Toshe da wani bakin glass na Rashin mutum su kansu su Abba kabiru basu iya kallonsa ba saboda Shakka Dukka da Sun Shirya karban Hukunci Tun agidan Duniya

Cikin mamaki kasim ya Shiga Nuna Bello yana Fadin"ka...ka...warke ne....? Yafada yana zaro ido.

Cikin Mirmishin sai ka Raina kan ka Bello ya kariso gaban kasim yana Fadin"Eh na warke Tun Wata Hudu da suka Wuce baka so haka ba ko..?kaso Abunda makaryacin bokanka ya Fada akaina ya tabbata ko..? Toh kayi kuskure kasim Tun ina yarona Ni Bello muhammed Jikamshi bansan Faduwa ba Nasara na sani..koda Kasheni ka sa akayi Har Abada Aneesa bazata zama mallakinka ba.."Yafada yana Dukan Kafadarsa.

Cikin Mutuwar Jiki kasim ya Sulale kasa,zai yi mgana Hashim ya saka hannu ya Tsinkeshi da mari yana Fadin"Bama son jin bakinka anan wajen...Ka zama Dabba acikin Mutane,Bayan ka karbi Sakamakon anan zaka koma gida ka karbi Cikin Shigen da kama Budurwanka.."Yafada Daidai Lokacin da Zainab da Mahaifinta Alhaji isa suka Shigo Cikin Offishin kuma a kunnansu Mganar da Hashim ya Fada sun manta sam sun suka kira Alhaji isan Suka sanar dashi an samu kasim din a State C.I.D Basu taba zaton zasu iya zuwa ba.

Gabadaya sai kallo ya koma sama cikin Firgici zainab ta Dafe kirji Tana Fadin"Ciki kuma...? Tafada tana kallon Kasim daya kwalalo ido Cikin Karfi Hali Hashim yace"Kwarai kam...Kuyi hakuri mun Rufeku ammh azahirin batu Kasim bai chanchanci Auran yarku ba.."Yafada yana kallon Kasim din baya Zainab taja tana Kallon kasim Hawayen idanuwanta na Zuba

Cikin Kunar Rai Hashim ya cigaba da Fadin"Aisha Tsohuwar Budurwanka Daka yaudara kama ciki Ta haife maka Cikin kuma ta kawo Abunda ta Haifa yanzu haka tana katsina an  ijiye maka Abunda ka Shuka,in kazo ka girbeta kai kadai..."Ido kasim ya waro kafin yace"Aisha...."Idanuwan Hashim sun kada yace"Eh Aisha maiduguri...Kuma Haruna ya Tabbatar da gaskiyan labarin..."

Kai kasim ya sadda yana Jin Nadama da danasani sun gama Lullubeshi wannan Shi ake Kira yau ma Tubulal sara"i...Ranar Tonin Asirinsa gaban iyayensa Gaban matarsa,da Danginta,Kaico kaico na kasim yake Fada acikin Ranshi kafin ya Daga kansa Yana hawaye ya fara Fadin.."N.....

Kibiya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/22/20, 10:25 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�38*

...."Na tuba nabi Allah...Don Allah Abba,ya Hashim kuman Aikin Gafara..."Yafada Hawaye suna kara zarya asaman Fuskarsa.

Ya Hashim ya kallesa cikin Raunin Murya yana Fadin"Kasim ba mu zaka nema gafara ba...Kanka ka cuta da Rayuwarka Bello zaka nema gafara domin shi kafi Cuta...Bayan ka mai Asirin zama cikin lalaura na tsawon wani Lokaci bai isheka ba sai da kabi matarshi har gida Da Niyyar keta mata Haddi...Yanzu ya kai karar ka Kotu sai kace bai maka adalci bako..?.."Yafada cikin Kunar Zuciya.

Kasim ya Dago kansa yana kallon Bello yana Fadin"Nasan Ni mai laifi ne awajenka..Kuma ban Chanchanci yafiyar ka ba....Karka ga laifina Sharrin Shedan ne Dana Zuciya da kuma Zugan mugun Aboki Don Allah ku yafemin Nayi Nadamar Duk Abunda na aikata na Shagalan Duniya banta Tsammanin akwai Ranar Da Asirina zai Tonu Lokaci Daya ba.."Yafada yana Gunjin kuka gwanin ban tsausayi.

Abba garba yace"Kana fadin Shedan...? Waye Shedan din in ba kai ba...Tsakani ga Allah ka Cutar da Rayuwarmu kuma ka Cutar da kanka domin ko D'aya bamu da Masaniya da Abunda Muguwar Zuciyarka ke kitsa maka."Kasim na Hawaye yana Fadin"Nasani Abba...Kumin aikin Gafara don Allah..".

Abba kabiru Dake kuka Hawaye na Zubar mai ya saka hannu ya Sharbe yana Fadin"Hakika Dama Haka Rayuwa ta gada..Duk yadda ka kai ga muguwar Zuciya,sai ka samu wanda ya shanyeka...Ni na kasance abaya bani da Zuciya mai kyau sam,wani Lokacin ni nake Dora Garba kan wata Cutarwa..Bayan mun tuba mun gane gaskiya bantaba tsamanin Watarana Abunda na aikata zai bibiyeni ba..Sai gashi ya bini Ta hanyar bani D'a irinka Kasim..Bazan maka baki ba sai da zan Roki Allah ya Sa wannan Abun ya zama Hanyar Shiriyanka,Kuma bana bukatar amaka afuwa a kaika kotu ta yankema Hukunci Daidai da Abunda ka aikata.."Yafada yana Kuka Sosai Abba garba na Dafa Kafadarshi Cikin Alamun lallashi.

Alhaji Isa Mahaifin Zainab dayayi Tsuru yana kallon Ikon Allah Cikin Ransa kuma yana kara godema Allah da Lokaci bai kuremai ba Jami"an tsaro kuwa sai Daukan Bayanai suke suna jiran Umarni Zainab ce Dake kuka ta karisa gaban Kasim ji kake Kau...kau..! Ta Daukeshi da Maruka Har biyu cikin kunar Rai Take Fadin"Dama Halinka kenan..? Dan Akuya ne kai Ko nace Bunsuru ne mai Haikema ya"yan Jama"a kuma kake Tunanin ka zama mijin Zainab..? Kayi kuskure kasim Har Abada ni Zainab Alhaji isa bazan taba Zama da Fasiki mazinaci irinka ba...Ka Bani Takardan sakina yanzu ko kuma ka Fada da bakin ka sakeni in ba Haka ba Wlh sai na Shigar dakai kara akotu mutumin Banza da Wofi.."Tafada tana Jifansa da wani Wulakantattacen kallo Lokaci Daya tana Zubar kwallah.

Dafe kuncinsa Kasim yayi yana Bin Zainab da kallo Alhaji isa Dake Tsaye yace"Kimin Daidai Diyar albarka...Koni ban goyi bayan ki cigaba da zama da Bara gurbi irinsa ba...Ka sakarmin yata ko ni nayi karanka akotu.."Yafada yana Kallon Hashim wanda ke kallonsa cikin Takaichin Abunda kasim din ya jazamusu..

Kafar Zainab Kasim ya kamo yana Fadin"Haba zainab taya zaki ce Haka.? In kika bar ni a halin Danake ciki Wazan kama...? Ki Rufamin Asiri Don Allah Whl nayi miki alkawarin Daga Rana mai Kama ta yau na Daina Shaye Shaye da Neman mata...Aneesa kuma bazan kara Shiga Sha"aninta da Mijinta ba Har Abada..."Yafada yahada Hannuwansa alaman Roko Da Sauri Zainab ta kwace kafarta tana Fadin"Au ashe ma kai Mugayen Halayyan naka basu da iyaka bayan Duk wadanan Harda Shaye Shaye ma kakeyi...Tab...? Wlh baka isa ba sai ka sakeni.! Ka sakeni yanzu ina Jiranka na gwamnace a sakani Layin Zawaran Layinmu da asakani Cikin Layin Da Auren Zainab gwara zaman gida ba..."Tafada tana Jifansa da wani Wukatattacen Kalo..

Kasim ya juya yana kallon Ya Hashim yana Fadin"yaya don Allah ka saka baki...In zainab ta rabu dani wazai sake bani yarshi..? Abba kabiru yayi Saurin Taran Hashim yana Fadin"Babu...Domin ka Riga gama yima Rayuwarka wani bakin Fenti wanda har Abada bazai Taba goguwa Daga Jikinka ba,Tana da gaskiya nima na goyi Bayanta..Maza ka saketa yanzu Tun kafin Dan gutun Kimarka Dake cikin Idanuwana su sake Zubewa.."Yafada cikin bacin Rai Kasim na Kuka yana kallon Ya muktar wanda ya so saka baki Bello ya Dafa Kafadarshi yana Dagowa ya girgizamai kai alaman Ba Ruwanka Dole ya Tsuke bakinshi.

Bello kuwa Hannuwansa ya Harde Bisa Kirjinsa yana Watching din komai cikin Nishadi Domin Harga Allah Zuciyarsa bata samu wajen da Zata Tsausaya musu ba...Uncle Aminu ma yana gefe akasan Ransa kuma yana jin Tsausayin su Abba kabiru da Kasim.

Kasim ya Sadda kai yana Kuka kasa kasa yace"Na sake ki zainab Saki Daya..."Cikin Farinciki Tace"Madallah nagode...Ko kaga kayi D'aya karka saka acikin Ranka zan iya Dawowa gareka...Nagodema Allah da baka Doramin idda ba.."Tafada Lokaci Daya Tana Share Hawayen Idanuwanta Ta Fice daga wajen da Gudu Alhaji isa ya mara mata baya,cikin Tsausayin Halin Da ya jefa yarshi Shima Rashin Bincike ne yajamai haka saboda samun Tushe mai Asali,Suna hanya ya Kira gida yace maza atura mota ta kwaso kayan Zainab Daga gidan kasim,Bai tsaya Neman Yayi karin Bayani ba ya Datse kiran.

Gabadaya Kukan kasim ya cika wajen ya muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Duk abar wannan mganar...Bello ka saka hannu abada Bellin kasim..Koma miye in muka karisa gida sai mu Cigaba Da Tattaunawar.."Bello bai yi gaddama ba aka bashi Takarda ya saka Hannu Shima kasim ya saka Bayan kuma an yi Takardan iyaka wanda in aka kara kamashi da irin Wannan laifin ba Shakka sai yaje gidan yari......

Tun kafin agama cike Takardun Abba Kabiru ya koma mota saboda Jirin Dake kwasarshi,Basu Dauki Lokaci ba Aka bada Belinsa,Bello dai Tawagar ya Muktar yabi suka koma Abuja Uncle Aminu kuma Daganan ya koma kano,Su kuma su Abba kabiru suka iza keyar Kasim zuwa katsina,Tun da suka shiga gidan yake ta Rufe Fuska Saboda Kunya Umma kuwa Haka ta zauna gabanshi tana kuka mai Cin Rai tana Fadin"kasim meyasa ka kunyatani a idon Duniya...? Kacutar da Zuciyata kuma kabama yardata akanka Kunya.."Take Fada Tana kuka Su mama Sahura suna nan basu koma ba Hakama Wasu Daga cikin Dangin Umma,inna Rukayyah ma tana nan ita ta karbi Jaririyan Dake Hannun mama Sahura wacce Duk ta Koma wata karama Saboda Rashin Nonon uwa ta Ijiyema kasim bisa Jikinsa

Kura mata ido yayi yana kallonta yana Hawayen Tsausauyin Kanshi Da kuma Nadama mganganun Aisha na Karshe suna mai amsa kuwa acikin Kunnuwansa,Runtse ido yayi yana Fitar da kuka mai Sauti bama wanda ke Tsausayinshi Domin Komai ya Faru Shine Sila,Kasim yadda yaga Rana Haka yaga Dare kwana yayi kukan Zucci dana Sarari,Allah ma ya taimaka Mama Sahura na Kula da Jinjiran da ko suna ba"a saka mata ba,Da Farkoma Inna Rukayyah Cewa Tayi abashi ita ya kwana da Ita bamai wahalan Iskancin daya aikata Daga baya yazo ya bar Mutane da aiki.
Chapter 69 · 0% Book details