← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 76

Sashe 14

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bashi ya Dakata da Karatun ba Sai Wajen 4:30am na Asuba kafin ya Tattara ya maida Qur"anin Ma'ajiyarsa Cikin Wani Karamin Daki ya Shiga Inda Kayan Wutan Suke Daga Cikin Daki yafara Kiran Sallah Wanda ya Tada Mutanen Gidan Daga Barci,Ya Muktar ne Farkon Fitowa Shima alwalan yazo yayi Wajen Inda Famfuna Suke Bayan Masallacin,ya Shiga Cikin Masallacin Ya Tada Raka'atanul Fijir,kafin Lokacin Sallar Asuba ya Cika Yau din Bello ya bada Salla,Sai bayan An Idar da sallar ne Bello ya Dade Cikin Masallacin Kafin ya Fito nan ya Iske ya Muktar Tsaye yana Jiransa Karisowa yayi Cikin Zatinsa Yana Zuwa ya Rankwafa Yana Fadin"Barka da Safiya Yaya..'

Kafadansa ya Dafa kafin yace"Kai zan ma barka da Safiya Yallabai Mallam Muhd Bello.."Yafada yana Kallonsa Cikin Kunya Bello ya Sadda kai yana Sosa Keya kafin yace"Afuwan Yaya.."Mirmishi Muktar ya saki kafin ya Dafa Kafadarsa Su Fara Tafiya yana Fadin.."Ya zanyi Dakai Bello,Kun Dawo lafiya..?

Cikin Sanyin Murya Bello yace"Lafiya lau Yaya.."Yafada yana Kallon Kasa Mirmishi Muktar yayi yana Lura da yanayinsa Kafin yace"Ina Fatan Watarana Ka chanza Bello Allah ya baka Mata Tagari Wacce Zata Tayamu Chanzaka Bello.."Yafada Cikin Damuwa Shuru Bello Yayimai Still Suna Cigaba da Tafiya Gabda Mension Dinshi suka Tsaya ya Sauke Hannunshi Bisa Kafadanshi Dama bai Tsammaci Amsa Daga bakinshi ba Kafin yace"Kayi Hakuri da Zuwansu Zulfa Bello k...."Can we go Inside yaya..? Yafada da Sauri yana Katse Yayan Nashi Saboda Bayason Ranshi ya baci Tun kafin Gari ya Waye..

Fahimtar Haka ne yasanya Muktar yace"Why Not Muje Dama Daada na Cigiyarka.."Mirmishi kawai yayi,kafin yayi Gaba Hannuwansa Duka Cikin Aljihun Wandon Barcin Dake Jikinsa Har Zuwa Falon Gidan Wanda Ke Tsit babu Motsin Kowa sai Kamshin Tashin Turaren Wuta Wanda Har Ma"aikatan Gidan Sungama Tsabtace Ko"ina.

  Cikin Kasala Bello yace"Bari na Karisa Wajen Daada.."Yafada Yana Wucewa Bangarenta Cikin Dan Sassarfa Muktar na Tsaye yana kallonsa Har ya bacema ganinsa Kansa ya Shafa kafin ya saki Ajiyar Zuciiya yace"When zaka Chanza Bello..? Yafada yana Shafa Sumar Kanshi kafin ya Daga Kafa ya Fara Haura Stairs Zuwa Dakin Barcinsu

Koda ya Shigo Falon Daada Shima Babu kowa Dama bai Tsammaci ganin Kowa ba Ainihin Bedroom Din Daada ya Tura ya Shiga sai dai kuma Dakin Babu Alamun Mutum Wutar Dakin ma Akashe ne,Hannu ya saka ya Kunna Makunnin Wutar,yaga Dakin ba kowa Hannu ya saka ya Kashe Wutar Dakin kafin ya Fito Lokaci Daya Tare da Janyo kofar Bedroom din..

Dayan ya Tura ya Shiga da Sallama Daidai Lokacin Daada Ta Dago kanta Wacce ke kan Sallaya Sanye da Hijabi Carbi ne Ahannuta tana Lazimi.Tunda Ta Dago kai Suka Hada ido Ta maida kanta Kasa Daga bakin Kofar ya Coge yana Fadin"Au ni za"a ma Yar Shariya Allah sai na Koma Abuna.."Yafada yana Mirmishi ..

  Daada ta Dago kanta Tana makamai Harara batayi Mgana ba Dariya yayi Har Fararen Hakoransa Suka bayyana ya Kariso Cikin Dakin Hannunsa Cikin Aljihun Wandonsa yana Fadin"Nazata Ana Iya Fushi da Megina Ran gida.."Yafada Daidai Sanda Idonsa ya Sauka kan Aneesa Data ke baje kan Makeken Gadon Dake Dakin Tana barci Sanye Take da Doguwar Riga Red Colour Ta barci ce Ammh Tana da Tsawo ammh Saboda Mugun barci Har Daga kafafunta Duk ya yaye,Kanta kuma Ta bajeshi kan Filo kananu kalabarta Duk Sun Baje kan Filon Saurin Kauda Idanuwanshi yayi kafin ya karisa gaban Daada ya zauna daidai Lokacin Datake Shafa addu"arta Sai Suka Shafa atare Hannayenta ya Riko yana Fadin"Matata Kina lafiya..?

kallonsa Daada Tayi kafin Tace"Lafiyata lau Megida ba Cefane.."Tafada Tana Shafa Sumar kanshi kamar Wani Yaro,yar dariya Yayi kafin yace"Au Shine Matsalan karki Damu Cefane sai kin gaji Da gani.."Yafada yana Shafa gefen Fuskarta Cike da Kulawa Ta bude baki zatayi mgana kenan Aneesa Ta Motsa Lokaci Daya Tana Sakin Tusa mai kara Daga Daadan Har Bello da kallo Suka Bita Bello ne Yaji Wani Takaichin Aneesa ya kamashi yarinyar sam bata Da Hankali Jiwai Tana mace ammh Tana barci Tana Sakin Tusa.

Hade Rai Yayi yana kallon Daada yace"Daada yarinyar nan Ta Tashi tayi sallah kuwa..? Daada na kanne Dariyanta tace"inafa Nayi Tashin Duniyan nan Ammh Taki Tashi sai Cemin Take Wai achan Makranta ba"a barinsu suyi barci Sosai."Baki ya Rike ammh ba Domin yayi mamaki ba Indai Aneesa ce Mikewa yayi ya Isa bakin Gadon Yasaka hannu ya Toshe Hanci Domin Tusar ta Aneesa Ta bada Wari Gadon ya Daka da Karfi Wanda ya Tashi Aneesa Tayi Zumbur Ta Mike zaune Tana Mutseke Ido Cikin Barci Take kallon Bello Cike da Haushinshi Cikin Ranta Kuma Fadi take"Anan din ma baza"a bar Mutum ya huta ba kai dai baka Da Hali mai kyau.."Tafada Tana Turo karamin Bakinta gaba kamar zatayi kuka Tsawa Ya Dakamata yana Fadin

"Zaki Tashi Zuwa sallah kokuwa sai na zane miki Jikinki..? Yafada yana Sakarmata manyan Idanuwansa Aneesa Tayi Jim kafin Tafara Kokarin Tashi Ammh Kuma Tana Kunkuni kamar Wata yarinya Saukowa Tayi Daga Kan gadon Tana Mika kawai Ta kara sakin Tusa Daada Dake zaune ta saki Dariya Tana Fadin"Umh Aneesa yau ta zama Bodara.."Belle ko baya ya matsa kamar ya Shake Aneesa Cikin Hargagi yace"Get out Nonesess Kina Wani Bude jiki kina ma Mutane Tusa..."

Da Sauri Aneesa ta Waigo Tana kallonshi Harara ya sakarmata kafin yace"I said get out.."Yafada yana Nuna mata hanya ammh Hannunsa Daya kan Hancinsa Baki Aneesa Ta Tura tana kama Hanyar Fita tana Fadin"Dadin Abun dai Iska na Fitar na Cuta waya sani ma Ko Mutum Shima yayi nashi nawace Datayi kara ta bayyana.."Tafada kamar Badashi Take ba Yaji Abunda tace Cikin Hargowa ya biyota yana Fadin"Ke..ke Don Ubanki mekika ce..? Ni sa"an Wasanki ne..? Da Sauri Aneesa Ta Bude Kofa ta Fice Tana Dariyar Mugunta da Harara ya bita kafin yace"Bush girl.."

Daada Dake Dariya tace"Dawo ka zauna Kada Aneesa Ta zauta ka Haka Take bazata chanza ba yadda kaima bazaka Chanza ba."Tafada kai Tsaye tana kallonsa Fuska ya yamutsa kafin yace"Don Allah Daada ba Hadani da Wannan Bagidajiyar yarinya Mara Kunya ni ba Sa"anta bane na Mata Nisa Har Abada.."Daada na Dariya tace"Toh dama mana Megidana."Jagale yayi Hannuwasa Cikin Aljihun Wondon Barcinsa Zai yi mgana Kenan Anty Rahila ta Shigo Falon Ita da Hibba Sun Sha wanka Su Turburkallah masha Allah.

Ganin Bello yasa ya Ta Washe baki Tana Fadin"Teacher Uban karatu ko kuma malamai Magada Annabawa zan ce ne..? Tafada Tana yar Dariya Mirmishi yayi Lokaci Daya yana Daukan Hibba Data ke Kiranshi Kansa Tsaye yace"Ina Kwana Anty Rahila.."Tana zama Kusa da Daada tace"Lafiya lau Bello ya Yimana Yaji kuma.."?,bai yi mgana ba Illah cigaba da Wasa Da Hibba Dayake yi,itama bata damu ba Illah maida Hankalinta Datayi Wajen Gaida Daada ganin Haka yasa ya Juya ya Fice Dauke Da Hibba Zuwa Falon Anty Rahila

Yana Shiga Falon yaci karo da alheri na kaida kawo Tsakanin Kichen Da Dinining,Gaisheshi Tayi ya amsa Adakile yana Kokarin Ficewa Daga Falon ne Zulfa ta Fito Sanye da Wasu Riga da Wando yan pakistan kanta ta Sanya Wani bakin Veil Fuskarnan Tasha Makeup,Da Farko bata ganshi ba Don Hankalinta na kan Waya kamshin Turaransa Taji da Kuma mganar Hibba ta Dago da Sauri Karaf ko Suka Hada Ido Baki ta saki Tana kallonshi Cikin Salon Shauki da Muradi mai Girma Shiko Hade Rai yayi kamar bai Taba Dariya ba Sauke Hibba yayi yana Fadin"Koma Wajen Mommy.."Da gudu ko Ta Wuce Zuwa Shashen Daada Shikuma ya Juya cikin Izzarsa Zuwa Falon Farko Cikin Sanyin Murya Zulfa ta Furta

"Uncle Bello...."Ta Kirashi Cikin Wani yanayi Wani Kololon Takaichi ne ya Ciyoshi Wai Uncle Bello! yajuyo A harzuke Cikin Masifa da Tsawa yace.'

*How to pay....â‚?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?600...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �500 ne,VIP �1000, Single one �300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*🅿�8*

"Do i look like ur Uncle..? Nace Nayi kama da Wanda ya Hada Wani Abu Dake..? Yafada yana Sakarmata mayan Idanuwansa Cike da Fushi mai girma lokaci Daya da Wata tsawar Data nemi Razana ta.

Wanda ya Fito da Zubaida Dake Shirin Fitowa Daga Dakinsu Itama Sanye Cikin Wata Atamfa mai Ash da Red Dinki Doguwar Riga Wacce ta Fito Da Duka Suran Jikinta,Ganin Zulfa Tsaye tana Raba Ido ga Bello Tsaye Yana aikamata da Wani Kallo Yasa Ranta yamata Dadi Cikin Yanga da Iyayi ta kalli Zulfa kafin Tafara Taku Zuwa ga Bello Tana Fadin"Uncle Bello Gud Mrning..."Tafada Atsume lokaci daya kamar zata Riko Lallausan Hannunshi Cikin Wani Fushi da Bakinciki ya Saukema Zubaida Wani kyakyawan Mari Wanda Sai da Ta Duke kasa Tana Ganin Hazo Saboda yadda Marin ya gigita Marin ya Shigeta sosai domin bayan Hazo Harda jiri take gani kafin Ta Dawo Hayyacinta ya saka kafa ya Shureta baya tatafi kanta ya Bugu da Jikin Kujera Cikin Sakin Marayan Kuka Ta Furta"Wayyo Allah na..!

Zulfa Dake Tsaye Duk da Ta Tsorata da Bello ammh Jin Dadin Abunda yayima Zubaida ya Nuna saman Fuskarta baya taja bayan Tayi Foolling Din Hannuwanta Bisa Kirjinta tana kallon Zubaida gefe Daya kuma Tana mamakin Wata Irin Zuciya ne Allah yabama Bello yanzu ma Din Huci kawai yakeyi Cike da Zuciya,wannan Ihun na Zubaida Shi ya Fito da Daada da Anty Rahila Daga Shashen Daadan Itama Aneesa Tana Dayan Bedroom din bayan Ta Idar da Sallah Taji kamar Maganar Uncle Bello Daga Falon Anty Rahila da Gudunta ta Fito Daidai Sanda Bello ya Karisa gaban Zubida ya nunata da Yatsa Cikin Fushi da Tsana yafara Fadin"

"Bana ce kudaina Kusanto ni ba...? Nace bana Bukatarku Arayuwata..!ban Hada komai Daku ba..!ko mun Hada ne..? Kusani ku kara sani Ni muhammed Bello Jikamshi ku ba Ahalina bane bani da Wasu Ahali Awannan Duniyan Face Daada,Ya muktar,Anty Rahila,Hibba da Aneesa Sune Kadai Ahalina,Saboda Haka ku Fita Daga Rayuwata Bana Bukatar ganin ku kusa dani,Mgana ta Karshe Kuma Duk Wacce Takara Kuskuran Kiran Uncle Bello Abakinta Wlh Tallahi sai na Saka Almakashi na Datse mata Harshe..."Yafada yana Sauke Numfashi Saboda yadda Zuciyarsa ke Gudu lokaci daya.
Chapter 14 · 0% Book details