← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 76

Sashe 11

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikuma yana Dawowa ya Shigo Bangaren Anty Rahilan nan ya Ganta Zaune da Farko ma ya Zata yar Aiki ce Dat Why bai Damu ba sai ma Tsawa Daya Dakamata yace Ta Daukomai Ruwa,Itako Aneeesa Dama ga Rashin Kunya da Tsiwa mikewa Tayi tana mai Kallon Sama da kasa Kafin Tayi Tsaki Ta Juya zata Tafi Da Wani Irin Zuciya ya Damkota Ya Fizgota ya Dauketa da Maruka lafiyayyu Guda Biyu Wanda Sai da Aneesa Ta Zauna Kasa Saboda yadda Marukan Suka Gigitata

Kan Cafet din Dakin Ta kwanta tana Kuka Tana Ihu Hawaye na Zubar mata tana Kiran Sunan Babanta,Tsayawa kawai Bello yayi yana kallonta Cikin Ranshi Kamar yayi Bindiga Saboda Haushi Kafin yayi mgana sai ga Anty Rahila Tashigo Gidan Ganin Aneesa Akasa Tana,kuka Ga Bello Tsaye tasan Karon ba Dadi kafin ma Tayi mgana Aneesa Ta Mike Tana Sharban Kuka Ta Shige Shashen Daada Tunkafin Bello ya Tambaya Anty Rahila tace mai kanwarta ne Daga Borno Suka Daukota Ita da Muktar.

Jin Haka yasa bai ba mganarta Muhimmaci ba Ammh Cikin Ranshi yana Tunanin Rashin Kunyar Aneesa,Ficewa yayi daga Sashensa Ita ko Aneesa Kayanta Tashiga Hadawa Tana Kuka Wai Ita Zata Tafi Abun mamaki Har Wajen Haraban Gidan Daada Ta Biyo Aneesa Tana lallashinta,Itako Anty Rahila Abun ya bata Haushi Dama Anty Nafi Ta Kirata tana Bata Shawaran Tun Wurima Ta Dawo da Aneesan Domin bazata iya zama da Ita ba,Mganar gaskiya Taji Haushin yadda Aneesa Ta Gudu Daga Gidanta.

  Yana Daga Saman Shashenshi yana Hango Diramar Aneesa Bata Yadda Ta Koma Cikin Gida ba sai da Muktar ya Dawo ya Lallasheta kana,Bello Ko Acikin Ranshi Tsanar Aneesa ce Ta kamashi Yana ganin Duk Rashin Dukane yasa Takema Mutane Kukan Iskanci,Aiko Ranar Kwana Tayi Kuka Da Rigima kamar Wata Karamar yarinya Washegarima Asheshen Daada Suka Hadu sai da ya Bata Rankwashi Ya murdemata Kunni Wai bata gaisheshi ba,Daada na mai mgana Ammh Sai da ya Karisa Mangare mata kai kuma yace In Ta Sake Tamai kuka Sai na Lahira yafita Jin Dadi.

Aneesa Duk Iskancinta Sai da Ta Natsu saboda Bello ya Wuce Duk Tunaninta Duk iya yadda Takai ga Tsiwa da rashin Kunya sai ta gagara yimai Sai da ta dai Ta Dinga Kunkuni Tana Fadin Allah ya Isarmata Ashe yajita Ranar Kuwa Kamar Aneesa Zata Mutu Saboda Kuka Harda Majina Domin Kneel Down ya Sakata Ya Dankwashi kanta Sosai Daga Karshe ya sata Up and Down,Haka su Anty Rahila Suka Shigo Suka Samesu Shashen Daada Wacce Tayi ma Bello mgana kan ya kyale Aneesa yafi Akirga yayi banza Da Ita.

Ya muktar Shi ya Kwaceta Hannun Bello,Wanda Tundaga Lokacin Aneesa Ta sanyamai Suna Mugu,Batasan Cewa Akwai Wata Muguntar na Zuwa ba,Domin Ranar da yaji Ya Muktar da Anty Rahila na Zencen Halayyar Aneesa Sai yake Tambayan ya Muktar Nan yake gayamai Dalilin Taho da Aneesa da sukayi Mirmishin Mugunta yayi yace Karsu damu Su bashi nan da Sati Uku Aneesa Zata Tafi Makranta Kuma Dole Zatayi karatu,Sanin Halin Bello na Rashin Son Wasa ne ya sanya Muktar ya bashi Dukkan Dama  akan Aneesa Wacce batasan Wainar da Ake Toyawa ba Domin Ta Kulle Duk Wata Kofar da zai Hadata Da Bello Saboda Taga alamun Shi Din ya Girmi Iskancinta.

Shiko Bello Tunda yaji lbrin Irin Iskancin Aneesa yasan Ba Inda Za"ayi mganinta sai Bording Sch,Nan ne za'a goge mata Duka Iskancinta da Aljanun Rashin Karatun Nata Haka ko Akayi Ta Waya Sukayi mgana da Prinpcipal din Makrantar Ya Sanar da Ita Komai kafin Sati Biyu Duka Shiryen Shiryen Komai na Tafiyan Aneesa ya kamallah Ta samu Gurbin Shiga Jss1 a mkrantar GGUSS kwatar kwashi,Amtsayin Sabuwar Daliba Da Sun Koma hutu,Ko su Ya Muktar basu sani ba sai da yarage Saura kwana Uku Hutun Makrantan ya kare kana ya Sanar Dasu Abunda ya yanke Anty Rahila Taji Dadi Ammh Sai Ta Nuna Fargaban Aneesan.

Ganin Haka yasa Bello da kanshi yace tayi kitso ta gyara kanta Domin Jibi Zata Tafi Makrantar Kwana Wannan Lbrin ya Kusa Zautar da Aneesa Haka ta Baje Akasa Tana Gunjin Kuka bai Dauki Abun Serious ba sai da ya Dawo da Yammah ya Isketa nan Tsakar Falon Daada Tana Cigaba da Gunjin Kuka,Already Jakar mkranta da littafanta da Takalmin Makranta sai Akwatinta Trolley da Sauran kayan provision Sun Kammallah ganin Abun nata bana Karewa bane,Yasa ya Zare mata Ido ya Ciro belt yafara Zubamata Daada ce ta Hanashi Dole ya kyaleta.

Aneesa Kuwa Ta Kwana Kuka Tatashi Tanayi Haka take Birgima tana Kuka ganin Haka yasa Anty Rahila ta Kira yaya Ali ta Sanar Dashi baice mata gashi zuwa ba sai ana gobe Ranar Tafiyansu Aneesa sai gashi ya Iso Ranar Sai da Daada ta Kwaceta Domin Dukan Tsiya Yaya Ali yayi ma Aneesa sai da ya Barta Kwance ya Kuma Ja mata Kunnin In bata Tsaya Tayi karatu ba Wlh Har mkranta zai bita yaci Ubanta ko kwana baiyi ba ya Juya zuwa Borno bayan ya Jadaddama Bello ko Amkrantan Karya sake yama Aneesa Da Wasa Yarin ka Cin Ubanta,Ranar Kowa ya Tsausayama Aneesa banda Bello Wanda yaji Dadin Hakan Sosai ko Banza Ta Rage iskanci da Rashin Kunya baison Duka baya ladabtar da Aneesa ba.

  Washegari Kuwa Da Duku Duku Direbansu mallam Inuwa ya Daukesu Ita da Bello Sai Kwatar kwashi Ita da Kayanta Da Zata Tafi Haka ta Rumgume Daada Tana Kuka Hakama Anty Rahila Su kansu Sunji Kewa Sosai Daada kamar tace abar karatun Saboda yadda Aneesan ke kuka kamar Ranta Zai Fita,Aneesa bata ta Zaton Zata Dandani Azaban data Dandana A mkrantan GGUSS kwatar Kwashi ba.

Ranar da Sukaje,Kwana Biyu ne da Dawowa Hutu,Dalibai Duk Basu Dawo ba Su kansu Sabbin Daliban Jss1 din Basu Wuce su Goma ba,Office din principal Suka Fara Isa yamata Sauran Cike Cike Aka bata Uniform da Hostel Maryam Hostel,Aneesa Kuka Takeyi Wurjajan kamar Wacce Aka yanka Tunda Taga Dajin Allah da Bello ya kawota Wai da Sunan Mkranta babban Abunda yafi Daga mata Hankalin Dutsen nan Na Kwatar kwashi Ya Firgita Aneesa Duk sai Taji Duk Wani Hayakin kanta ya Saketa Saboda Fargaba da Tsoro Zuwan Farko Suka Fara Haduwa da Jidda Ita kuma New Student ce SS1 inda Bello ya Kirata yace ta Dauki kayan Aneesa Zuwa Maryam Hostel Dogon Daki.

Jidda Ta kaita Har Hostel dinsu Inda Ta Dinga Tambayanta ita kanwar Mr.Bello ne,Ko kallonta Aneesa batayi ba banda Kuka Babu Abunda Takeyi,Ganin Haka sai Jidda bata damu ba Azatonta Irin Farkon Zuwan nan ne na kowani Dalibi Haka kowa yake yi sai yayi Kukan Rabuwa da Gida For d First Time Jidda Ta Hadasu da *SALAMATU S JIBIYA* Wacce Suke Gado Daya da Aneesa Ita tana sama Ita Kuma Kasa Kuma Itama Jiya Aka kawota nan Ta Hadasu kafin Ta Fice Zuwa nasu Hostel dinsu Tana Jin Dadin An kawo Kanwar Mr.Bello domin Tunda tazo Mkrantan Ta kyalla Ido Akanshi Taji ya Tafi da Imaninta..

S.jibiya Ita ta Jerama Aneesa kayanta Cikin Dirowar gadonsu Ammh Duk da Haka Aneesa bata Amsa mata Ko Daya Daga Cikin tambayoyin Data ke mata ba, Ko Sunata Dakyar ta Iya Sanar da Ita Aneesa Tsoro Duk ya kamata ganin Mabambatan Mutane Kuma Hostel din nasu guda Biyu ne Dogon Daki nasu na Musulmai gajeran Daki kuma na Kabila ne,komai Dai gashinan Yamata Wani Iri Tundaga Check din da Suke Sakawa Cikin Hostel,su nasu na House dinsu Ita da S. Jibiya Red Colour ne,Daddare Haka S Jibiya ta Tarata Suka Tafi Suka karbo Dinner Dare Tuwo miyar Kuka Ranar Aneesa Sai Da Tayi Kuka Tana Tunanin Kila Bello ya Kawota inda Za"a Kasheta lokacinta baiyi ba bata iya ci ba S.Jibiya ta Hada musu Complex Suka Sha Suka Kwanta bayan,ko Masallacin basuje ba a hostel sukayi  Sallar, Domin Aneesa Tace Tsoro Takeji,Haka Ta Kwana Batayi barci ba Saboda Tsoro Dutsen na kwatar kwashi Take gani Yana ci Da Wuta.

  Washegari Suka Fara Zuwa Aji Ita da S.Jibiya,sai 10 Suka Tashi Breafsat suka Koma Duk Da Haka Aneesa bata Saki Jiki ba Sosai Shiko Mr.Bello Saboda Aneesa aka maidoshi Master din Jss1a Domin ya Dinga Lura da Ita da Karatunsa Ammh Duka Makrantan Yake koyar Dasu Darasin Lissafin,Kwanan Aneesa Uku da Zuwa Aka kawo *BILKISU KABIR KAITA* ita kuma Hostel dinsu Daya Kusa da Gadonsu Shikenan Sai Suka Kulle Su Uku Kuma Akayi Sa"a Ajinsu Daya Kuma Wajen Zamansu Daya Ammh Duk Da Haka Aneesa na Musu Wuyar zama Domin bata da Sakin Jiki ga Masifa da Saurin Zuciya,Ko Sati Aneesa bata Rufe ba a mkrantan ba Lbrinta ya Zagaya Ko'ina Ana Fadin kanwar Mr.Bello Tazo Karatu Jss1 yan Matan Mkrantan Suna ta Zuwa ganinta Musamman ma Seniors Dinsu da Sunzo Sun ganta Sai kiji Ana Fadin Ya Haka..? Ita baka Kuma basu kama Itadai Aneesan Ko Ta kansu batayi,Tana Jin yadda Ake Zuzutashi Acikin Makrantan Itakuwa Abun ma Haushi yake bata ba Kadan ba Tana ganin Duk Duniya bata da Makiyi kamar Bello.

Aneesa Da Wuya da Komai ta Fara karatu Domin Duka Takeci Wajen Bello ba Kadan ba Kuma yabama malamai Da dama Daman in Aneesa Bata maida kai Akaratu Su Daketa Shiyasa Wuyar yamata Yawa ga Wahalan Makranta ba Wadattacen Ruwa sai Sun Tafi Korama ga Muguntar Senoirs dinsu,Wani Lokacin ma Ana Ragamata Saboda Ita Kanwar Mr.Bello ne Mussaman ma Wadanda Ke Haukan Sonshi,ga Toilet dinsu ma baka iya Shiga Abude Babu Kofa Ga Aljanu Sun ma Mkrantan Yawa Domin Duk Ranar Jumma"a Sai Anyi Bikin Aljanu Hatta da Aneesa Sai Da Ta Kwashi Aljanu Domin Lokacin da Abun ya Faru Bello Aka Kira Dayazo ya ganta bai Dauka gaske bane ya Zata Iskancinta ne Sai Daga baya ya fahimci itama ta kwasa A Nan dai Aka samata mgani Ta Dawo Cikin Hayyacinta
Chapter 11 · 0% Book details