← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 76

Sashe 34

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna Fitowa ya Muktar ya juya ya karbi Hibba yana Fadin"Ka koma Ciki...Gud Nite.."Mikamai ita Yayi Tana Dagamai Hannu Shima Dagamata yayi Har Suka Sauka Daga kan Steps din Suka Nufi Shashen ya Muktar din Suna Tafe Suna Hira ya Dade yana kallonsu Har Suka bacema ganinsa Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya koma Cikin Falon Lokaci Daya yana Kulle Kofar Dakin da Makulli kallo Daya yayima Aneesa Dake Durkushe Inda Su Anty Rahila Suka barta ya sake Hade Rai,Wucewa yayi Zuwa bedroom dinsa cikin takun Sa na isa yana Shiga ya Turo Kofar lokaci Daya kuma ya saka ma Kofar key da Harara Aneesa Ta bishi kafin Ta Dago da kanta Lokaci Daya Tana yaye,Lifayan Jikinta,Doguwar Rigar Atamfa Dake Jikinta ta Bayyana,Kan kujera ta Hau Tana Karema Falon kallo lokaci Daya Tana Tabe baki Aranta tace"Falo kamar na wata mace.."Domin Ita Tunda Take bata Taba Shigowa Shashensa sai Sau Daya Shima Anty Rahila ce ta matsa mata ta kai mishi Coffea Wai bayason su Alheri na Shiga mai Part lokacin kuma Data Shigo bata lura Da Falon ba Sosai

Saboda leke leken Aneesa Har Kichen Ta leka Tana Dube Dube Tana Tabe baki,ammh Sanda Take kar yaji motsi ya Fito Kichen Din Shima kamar na wata macen Aure,komai na Bukatar Girki akwai aciki Cikin Frigde din Kuwa Shake da Madaran Hollandian da Kayan Marmari Tabe baki tayi Tana Fadi afili.."Oh wato Shiyasa bai damu ba Cin Abinci ba,ashe ga Abunda yake sakama Cikinsa nan..."Fitowa Tayi Daga Kichen Din Cikin Takaichi,Gashi Wayarta Batasan Wanda ya karba ba Tun a borno bata kara ganinta ba,Tana so tasan Halin da Kasim yake Ciki,ammh ba Hali kan Doguwar kujera ta Haye,Tana Tura baki ita kadai Cikin Ranta Tana Fadin Andai Cuceta an Hadata da Mugun Mutum kuma wai Kowa Ahaka gani yake ta dace,Kodai Bata Dace ba.

Tun Tana Tunani da Zencen Zucci Ta gama Tunanin kasim da Halin Dayake Ciki,Har sai da Tayi kuka Daganan Batasan Sadda barci ya Kwasheta ba,Dama already Tun Adakin Daada Tayi sallar Isha"i Dinta Hade da Shafa"i da Wuturi Shiyasa Taasaki Jiki bisa Kujera tana ta Sharar barcinta hankali kwance Kamar tana Dakinta Saboda Gajiyar Baki dama gashi kwana 2 bata samun Barci ba Sosai.

Bangaren Bello Kuwa Da Gayyah ya Rufe Kofar Bedroom Dinshi Saboda Kar Aneesa Tayi karambanin Shigowamai Daki,Bedroom ya Fada yayi Wanka tare da Dauro alwala yana Fitowa ya Zura kayan Barcinsa Pjs,Riga da Wando masu Ruwan Kasa bai kwanta ba Sai Da yayi Shafa"i Da Wuturi Har ya Kwanta sai ya Tuna bai Sha Mgungunansa ba Gashi kuma Cikinsa na Kiran Yunwa,Mikewa Yayi ya Zura Takalminsa na Bedroom ya Bude Kofa yaFito Falo nan yaga Aneesa Ta Dunkule Kan Kujera tana barci Har Dankwalin kanta ya Sabule,Kitsonta kanana 2 Step Wanda Anty Aisha Ta mata Suka Bayyana Awaje,kallo Daya yayi mata ya kauda kai kichen ya Shiga ya Dauko Madaran Hollandian Guda Daya da karamin Kofi kashe Wutar kichen din yayi kana ya Fito Har Ya Wuce Zai Shiga Bedroom Dinsa sai kuma ya Dawo Baya Ya Saka Hannu Daya ya Dauki Remot din A.C din Falon ya Rage mai Iska Lokaci Daya kuma ya Rage Wutar Falon Ya kunna mata Dumlight kafin ya Kada kai ya Shiga Bedroom ya Rufo kofarsa yana Sakin karamin Tsaki

Sai da yasha Madaran kana ya Balli magungunar yasha,ya maida Komai bisa Side Drower din gadon kafin ya Shige Cikin Blanket Lokaci Daya yana kashe Hasken Dakin ya Kunna Dumlight,sai da ya kashe Wayarsa kana ya Dora kansa Bisa Filo yana Lumshe ido,Tunanin Abunda Likita ya Fadamai,Ya dawo mai Fadamai Jininsa ne yayi sama Saboda Damuwa kuma baya barci kwana Biyu yayi kokarin Ya Dinga Samun barci Ajiyar Zuciya Ya Sauke kafin ya Runtse idanuwansa Lokaci Daya barci mai Nauyi ya kwasheshi.

Bai Farka ba,sai Wajen 5am Shima Kiran Sallan Mallam Inuwa ne ya Tadashi Domin Dama In bai kira ba Mallam Inuwa ke Kira Watarana ma Har sallah ma yana Badawa,Tashi yayi Zaune yana Mika Lokaci Daya Yana Salati,Wayarsa ya Dauka ya Kunna nan yaga 5 ta Wuce Kafafunsa ya Zuro Zuwa Saman Cafet din Dake Dakin,Takalminsa Dake bakin gadon ya Zura lokaci Daya mikewa Wutar Dakin ya Kunna haske ya Gauraye ko"ina kafin ya Fada Tiolet,Wanka yayi agurguje kafin yayi alwala ya Fito Wardrope dinsa ya Nufa yana Goge Jikinsa da Karamin Towel din Dake Hannunsa,Jallabiyansa Baka ya Ciro Ya saka Da Hula,gaban Dressing Mirrior Dinshi ya Isa ya Dauki Turare yana Fesawa Hanzarin Fita yayi jin kiran Sallah na Biyu Wayarsa ya Dauka Lokaci Daya ya Bude Kofar Bedroom Din ya Fita Yama manta da Wata Halltta Aneesa Shiyasa ya Fice kai Tsaye Daga Falon Batare Daya Damu ba.

Bai Dawo part Din Nashi ba Sai Wajen 6am na Safe Domin yau Mallam Inuwa ya bada sallah Shikuma ya Tsaya yayi karatu,yana Shigowa Falon Cikin Takunsa na Jarumta idanuwansa Suka Mai Tozali da Aneesa Dake Kwance Tana Barci Saboda Dadin Barci Tayi Rigingine Ta matse Lifayanta Awajenta Cikinta Gabadaya Cinyoyinta Suna Waje,Saboda Doguwar Rigar Tayi sama Saurin kauda kai yayi yana Tsaki Lokaci Daya kuma da Karfi Wanda ya Farkar da Aneesa Daga Barcin Datake sha.

Tana Mitsike Ido Ta Hango Wucewarsa Kamar Wani Sarki yana Wani Taku D'aid'ai da kallon Rainin Kallo Ta bishi har ya Shiga Cikin Bedroom Dinshi zai Rufo kofar kenan ya Waigo Suka Hada Ido da Sauri ta Kauda kai tana Sakin karamin Tsaki Ido ya Waro yana kallonta Cikin mamaki ya Fasa kulle Kofar sai ma Fitowa Dayayi yana Fadin"Ke Don Ubanki wa kika ma Tsaki yanzu.." ?Yafada Yana Sakarmata manya Idanuwansa

Saurin Mikewa Tayi tana Raruman Dankwalinta ta Maida Bisa kai Bakin nan ta Tura gaba cikin Ranta tana Fadin"Badai ubana ba Sai dai na Mutum Tunda Uba baifi Uba ba.."Tafada Tana Tura baki,Tsaye yayi yana kallonta Cike da Bacin Rai kafin ma ya Sake magana Ta Dauki Lifayanta ta Yafa ta kama Hanyar Fita Bakin nan kamar ya Fado Saboda Kunkuni ..

Cikin Kuluwa yace"Ke...ke...Bada ke nake Mgana ba..."Yafada yana Maida Hannuwansa Cikin Aljihun Jallabiyansa Ko Waigowa Aneesa Batayi ba ta Fice da Sauri,Numfashi ya Fesar kafin ya Kada kai ya koma Cikin Bedroom dinsa Aransa yana Fadin Yarinyar nan ta manta ni ne Sai na kara Tunasar da ita komai.

Ya Cire Jallabiyan kenan ya Kwanta Wayarsa ta Dauki kara yana Dubawa Yaga Principal din Mkrantam Kwatar-kwashi ce Dauka yayi Bayan Sun gaisa Take Tambayanshi Ashe ya Dawo yace mata Eh Cikin Dariya take Fadin Mallam muna Jiranka fa"Mirmishi yayi kafin ya Fara mata bayanin komai Duk da Bataji Dadin Rashin da GGUSS,tayi ba na Malami kamarsa ba Ammh Tasan ko bajima Dole Mr bello zai Tafi Sakamakon Ko Kudin da Suke Biyansa bai kai mtsayin Karatunsa ba kawai Ra"ayinsa ne Haka Har Sunyi sallama take Tambayanshi da Gaske lbrin Dataji Wajen Dalibai wai yayi Aure kuma Aneesa Bukar Bulama ya Aura.?mamaki yadda Lbrin yakai Mkranta yake bai mata Wani Dogon bayani ba ya Dai amsa mata da Hakane Fatan alheri ta mai kafin Su Yanke Kiran Ya barta Cikin mamaki Duk da Ta san Cewa Babu Abunda Zata samu Daga Bello Saninshi Marason Hayaniya,Daganan Kashe Wayarsa yayi gabadaya ya Kwanta bayason kuma Damu.

*****
Daada na Zaune Tana Lazimi Aneesa Ta Shigo Dakin nata Tana Tura baki Cikin Mamaki Daada Ta Dago Tana Binta da kallo Baki Bude bata samu Zarafin mgana ba Aneesa Tace"Daada ina kwana.."Bata amsa ba illah cemata Datayi.."Daga ina kuma Haka..? Kin manta yanzu ba da bane.."?

Tura baki Aneesa Tayi kafin tace"Yo Daada Nazo yin sallah ne da Wanka.."Dakuwa Daada ta Mika mata tana Fadin"Kinga naki Ja"ira Chan babu Wajen Yin Alwala da Wankan ne..?."Bata rai Aneesa ta karayi kafin tace"Toh wai ni Daada meye laifina Yafa Kulle Dakinshi kuma na Duba Falon ba Tiolet kuma ma ko Akwai bani da kayan Chanzawa..".

Tafada Harda Buga kafa kafin Ta Fice Daga Dakin Tana Tura baki Dayan Bedrrom Din ta Shige Tana Kunkuni,Da ido Daada Ta Rakata kafin ta Sauke idonta tana Fadin"Allah ya Shirya.."Cigaba Tayi da Lazamin ta bata kara jin Duriyar Aneesa ba sai da Tayi Wanka Tayi sallah TaChanza kaya Cikin Atamfa Riga da Sikat batayi Kwalliya ba Shiyasa Fuskarta Tayi Fresh Da Ita Dakin Daadan Ta Dawo Ta Haye gadonta tana Fadin"Allah ya isana Jiya A Kujera na na kwana Duk Wuyana ya Sage..."Tafada Tana Shafa Wuyanta ko mgana Daada Bata mata ba Tana dai Binta da Ido ..

Anty Rahila ce ta Shigo Ita da ya Muktar wanda ke Dauke da Junior Gefensu kuma Hibba ne,Dukkansu sun sha gayu gwanin Ban Sha"awa,Daga gani yau Ya Muktar din bazai Fita ba,Sanda Suka Shigo basu lura da Aneesa ba sai da Suka kariso Tsakiyar Dakin Cike da Mamaki Anty Rahila ke Kallon Aneesa Kafin Ta maida kallonta ga Ya Muktar Shima Wanda ke kallon Aneesa Harda gyara Kwanciya tana lumshe ido ..

Baki Anty Rahila ta Rike kafin Tace"Daada wa nake gani kamar Anee.."Daada tace"Nima Haka nagani na mata mgana tace Tazo yin Wanka ne da Saka kaya,daganan kuma aka Hau gado sai Tura baki take bansanin mata ba Don ko Tankata banyi ba.."Haushi yakama Anty Rahila ta Isa bakin gadon ta Dagamata Duka Lokaci Daya Tana Fadin"Tashi Don Ubanki ki koma Shashen Mijinki kiyi barcin achan.."Mikewa Tayi tana Soshe Soshen Wajen Tana Fadin"Kai Anty Rahila.."Tafada Harda Matse Kwallah.

Daada Tace"Wai ni kayan ma Datake Sakawa ba Maidama yaron chan za"ayi ba..? Ya muktar yace"No Yanzu da Safe Hashim ya Kirani yace Kasim yace Ya barma Aneesa Duka kayan..."Daga Daada Har Anty Rahila Hada baki Sukayi Suna Fadin"Allah Sarki.."Aneesa ko Kuka ta Fashe Dashi Tatashi ta Fita tana Fadin"Allah Sarki My Kasim Allah ya saka maka.."Da kallo Suka Bita kafin Anty Rahila Ta Daga Murya tana Fadin"Karki Dawo Nan ki Wuce ki koma Shashen Mijinki yanzu Jummai zata Hawo muku da Breafast dinku.."Aneesa na Jinta ta mata banza sai da ta koma Dakinta ta gama Kukanta kana ta Dauki Mayafinta ta Fita Bayan ta Kwalama Hibba kira tazo Suka Fita Tare...
Chapter 34 · 0% Book details