← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 76

Sashe 66

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin Abunda yace ne yasa nayi Dariya acikin raina sai da naga ya maida hankalinsa bisa Laptop dinsa yasa na Fara taku kamar zan shiga Tiolet na juyo naga baya kallona sai na Duke ina Fadin"Wayyo Allah...Zan mutu...Cikina zan mutu..."Nake Fada ina Dukawa harda yarfe hannu da Sauri ya Ture Abunda ke gabansa ya karisa gareni yana Rikoni cikin Rudewa yake fadin"Menene..? Ciki kuma Anee..?kinganni ko..?kinga Abunda nake gudu ko..?muje Asibiti kar asamu matsala.."Yake Fada yana Kokarin Daukana Tsab na Lamgwabe ya Daukeni har ina kara lafewa bisa Kirjinsa ina Dariyan mugunta,yana Sauri ya Dibi gudu zuwa Falo Dariyan da nake boyewa ta fito cikin mamaki yake kallona ganin haka yasa na gimtse Dariya,Ware ido yayi yana min wani kallo kafin ya ijiye ni yana Fadin"Oh....ni zaki hadama wayau ko..? Shagwabe Fuska nayi ina Fadin"Yo bakai bane kaki kulani ba.."Nafada harda matse kwallah.

Hannunsa yasa yana Zagaye Habansa cikin Daure Fuska yace"Ok...Wato ke nan mai wayau ko .? Jikinsa na fada ina Mai kukan Shagwaba cikin Matse kwallah lokaci daya ina matseshi cikin
Jikina ina Fadin"Am srry...Kaina bisa Wuya..bani da kwanciyar hankaki matukar gwarzon Aneesa na Fushi da ita..."Nafada ina kallonsa ido cikin ido Ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya Kara Rumgumeni yana Fadin"Ina da Kishi sosai akanki Aneesa...Bana kaunar naji kina ambatan sunan wani Namiji wanda kikaso kafin ni agabana...Kirjina na Zafi ina Ji kamar zan mutu in na tuna cewa shi kika fara so kamin ni.."Saurin Dage nayi na Hade bakina da nashi,Saurin Rike kaina yayi nima na rike kansa ina Shafa Keyarsa zuwa Dogin Wuyansa,Sai dai mukayi sumba mai tsawo kafin na sakeshi ina Fidda Numfashi cikin So da kaunar Mijina nace"Karka ka sake jin Zuciyarka na zafi saboda wani chan kasim..Wlh sai bayan na Aureka na Fahimci ban taba son kasim ba,kawai burgeni yakeyi,kai ne kadai namiji wanda nakejin Sonka na Zagaya dukkan Jinin jikina,Kallon kyakyawan Fuskarka kadai kan sakamin Natsuwa kaina Jarumina kuma gwarzona Uban ya"yana...I love u B.love ka yarda kai na fara so acikin Zuciyata..."Nafada ina kara Fadawa Bisa faffafan Kirjinsa Cikin magagin so ya kara matseni yana Fadin"Love u more....And more my Anee.."Yafada yana sakarmin kiss asaman kaina Lokaci Daya yana Dagani sama cikin Dariya yace"Muje na gwada miki cewa..U are my only one..."Sakala hannayena nayi ina Fadin"Nima zan kara gwada maka No one but u Mr Bello muhammed jikamshi..."Nafada ina hade bakinmu waje Daya Haka muka Nufi Bedroom dinmu bakin na cikin Na juna muna kara Rikita da juna da Salon da muka saba.

*********
*NAGERIA*
_Katsina..._

Tuni Shiryen Shiryen Biki ya Dade da kamkama baki na nesa dana kusa Tuni suka cika gida Umma sai wani Fariya take tana wani Bude hanci adole wannan karon dai tana maraba da Auren haka ta kakkane komai ko mama sahura ba wanda ya nema,Ita kuma sai taja kanta gefe ta sama Umma ido tana kallonta,Tun ana Saura kwana biyu biki Anty Rahila da Daada da hibba suka Iso gidan Abba kabiru wanda ke cike da baki zuwa yammah kuma sai ga matar Ya hashim da Zubaida sun iso Zulfa"u dama Tana gidan Duk da ba kwana take ba da yammah take tafiya gida ita da Mama Sahura Inna Rukayyah ma tazo ita dasu Hamdiya sai da kuma suka Raba Hali da Umma saboda yadda take nunawa kamar Kasim ba Danta bane ba,ba nuna kara ba komai Shine Inna Rukayyah tamata mgana  ta nemi zaginta har sai da takai ta tsinketa da mari,wanda ya harzuka Zuciyar Umma ta kama kuka har yan"uwanta suka Shigar mata suna Fadin maganganu Zubaida ma Sai da tayi mgana saboda mene za"a mari Ummanta Ran Inna Rukayyah ya baci itama ta Fashe da kuka.,Anty Rahila dasu Daada sune ke bada Hakuri Mama Sahura kuwa Abba Kabiru ta kira tana kuka Kissa tana Shaidamai Abunda ke Faruwa.

Cikin bacin rai ya Shigo gidan,Ai kuwa Umma sai da ta raina kanta,domin Abun kanta ya koma gaban yan"uwanta da ya"yanta Abba kabiru yaci mata Zarafi bai raga mata kuma ya bata Rashin gaskiya su kansu yan'uwan nata yace su shiga Taitayinsu ko kuma su bar mai gida yanzu sanin Halinshi na Tijara yasa suka kama bakinsu ita kanta Umma tana kuka tana komai ta shige dakinta Mama Sahura Tabi da kallon Kadan kika gani Zulfa kuwa da Zubaida sai Harare hararen da kallon Juna akarkarce suke haryanzu basu daina kishin Juna ba Duk da kowa ta Fidda ranta ga Bello har gwara ma Zubaida takan Tunashi Watarana ita kuwa Zulfa tunda ciwon nan ya sameshi taji ya Fita Ranta dama bashi take so ba kyanshi take so da lafiyansa yanzu ya nakasa bata Bukatarshi.

Dukkansu kowaccensu na aji biyu ne going to 3,gwarama Zubaida ya Hashim na saka mata ido tafi maida hankali kuma ya hanata tara samarin banza ammh Zulfa Duniyarta take ci da Tsinke duk ko da Sa"idon da mama Sahura ke mata.

Kasim kuwa yana kaduna bai Dawo ba Saboda suna chan suna ta partys kala kala,kamar ba Auren Sunna ba,Haruna ne Babban abokin ango,sakamakon Baban Zainab dan Siyasa ne yasanya Gabadaya kafafen yada labarai tagama yawo da sanarwa katin bikinsu,sosai kasim ya saki kudi akayi Hidima,gidanshi ya saka aka gyarashi sosai aka Fitar da Duka kayan gida aka saka wasu,dama tun na wanda aka sama Aneesa ne ba wanda yabi takansu,Ita kan Zainab din iyayenta sun mata bajinta sai wanda yagani,yamata akwatuna Wanda suka fi ma na Aneesa saboda yadda yakejin Zainab aransa kamar Tafi Aneesa ma Saboda yana Tunanin in har ya samu Zainab toh har Abada bai da wata damuwa da Aneesa kuma.

******
Rana bata karya sai da uwar Diya taji kunya ayau Asabar 03/03/2020 da misalin karfe 11:00am na safe aka Daura Auran Zainab Alhaji isa kinkinau,da angonta Kasim kabir jikamshi akan Sadaki mafi Daraja.

Daurin Auren Daya samu Hallatar manyan mutane kama Daga yan Siyasa Abokan Harkan Babanta da kuma Kososhi acikin gwannati kama Daga Tawagar Sojoji wato su ya muktar kenan da kuma Wasu Daga cikin yan Sanda yan kasuwa,da abokan aikin Kasim din Sun musu kara sosai domin itama Zainab din sun saba da ita,da yan"uwanta yan Corpas,An Daura Auren ne A babban masallacin Jumma"a dake Kinkinau,Inkaga Bakin kasim kamar Gonar Aduga saboda Yadda Fararen Hakoransa ke yawo awaje,yana gaisawa da mutane yana saba babban Riga ana cikin wannan Hayaniyar na gama Daurin Aure sai ga Motar yan Sanda guda biyu sun iso wajen Suna zuwa suka Sassauko Rike da Bindigogi babban Cikinsu ne yace ina kasim kabir jikamshi aka nuna musu shi yana kallonsu cike da mamaki kafin yayi magana sun fito da ankwa suna Fadin"Ure a under arrest..."Baki mutanen wajen suka Bude suna kallon Abun mamaki kasim bai samu Zarafin magana ba suka Sakamai ankwa Lokaci Daya suka iza keyarsa zuwa cikin mota ko kafin su haruna su kariso tuni motar yan Sandan ta saki Jiniya ta bar wajen

Su Abba kabiru na cikin masallaci suka samu Labarin Daya kusa girgizasu wai an kama kasim koda suka fito sai dai masu baida Zence,Cikin Tashin Hankali da dimuwa baban zainab yashiga kiran waya Heaquater dinsu yan sanda na Jahar kaduna ammh suka ce basu da wani lbrin mai kama da Haka wasa wasa dai ko"wani Offishin yan Sanda Dake Jahar kaduna ba kasim ba labarinsa Hankali fa sun Tashi Abba kabiru da Abba garba zufa kadai sukeyi Hashim kuwa kai ya Dafe yana salati,Ya muktar ne ke kokarin kwantar musu da hankali ta hanyar ce musu kar su damu za"a samu kasim.

Tuni mutane suka watse da Labrin Abunda ya Faru Duk yadda akaso Boye mganar sai da takai gidan su Zainab amarya na cikin kawayenta an gama Shiryawa Domin bayan andaura aure sun shirya Lonching lafiyayyiya,sai kuma sukaji mugun labari suma ne kadai Zainab batayi ba ammh sai da jiri ya kwasheta tayi kasa tana Gunijin kuka Nan da nan gidan Biki ya Rikice,Gashi kuma ba wani karin bayani domin ba wanda ya Dawo balle aji bakin zaren Daga bakinsu.....

*****
Gidan Abba kabiru ya Tumbatsa Da makota da yan"uwa da abukan Arzuka anata Shagali Sha D"aya nayi yan"uwan umma suka dau gud'an Lokaci yayi ammh bana mutuwa ba na Auren kasim,wanda dama bayan an Daura aure sunyi Lonching  katsina zasu wuto da amarya anan suka shirya dinner, zata fara zama a nan shahensa in sukayi sati sai su koma kaduna.

Umma kuwa an ci wanka cikin wani Dakakken leshi mai kyau da yarari sai wani Kai da kawo ake bakin nan har kunni, basu da labarin Abunda ke Faruwa a kaduna wajen karfe 12:30am na Safe sai ga Aisha sun Dira agidansu Kasim ita da Mamarta da W'anta Auwal Abunda zai kara Ruda mutane shine ganinta Dauke da Jinjiri sabon Haihuwa.

Aisha tacigaba da Renon Cikinta,har Allah ya Sauketa lafiya Kwana uku kenan da Haihuwarta ta samu ya mace Shine Yayanta Auwal yace maza ta Shirya su je har katsina su kaima iyayen kasim aikin Daya aikata mata in ma basu da labari ta"asar dayake ma ya"yan mutane yau su sani Adireshin Data Taba Dauka Lokacin da zata bar gidan kasim suka yi amfani dashi sai gasu kuwa har kofar gidansu kasim.

Tun shigarsu Haraban gidan suka Fahimci ana wani Taro,ba wanda yabi ta kansu har suka Shiga cikin gidan Auwal kuma ya Tsaya Daga Haraban gidan da mama Sahura Suka ci karo ta kallesu cikin mamaki tana Fadin"Sannnunku da zuwa...Ku shiga ciki ."Maman Aisha ta gyara zaman mayafin kanta tana Fadin"Yauwa...Baiwar Allah don Allah ko kece mahaifiyar kasim..?

Mama Sahura ta girgiza kai tana Fadin"A"a bani bace uwar ango tana ciki ammh ni Matar kanin Babansa ne Daga ina kuke..? Maman Aisha ta riko hannun yar"ta wacce ke kunshe kanta cikin mayafi tana Rike da Jinjirar Data Haifa cikin Towel tace"Koma Daga ina muke muna Bukatar ganin Uwar kasim da Ubansa Domin Muna tafe ne Daga waje mai nisa muna Bukatar Gama Abunda ya kawomu zamu koma inda muka Fito ne.."..
Chapter 66 · 0% Book details