← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 76

Sashe 50

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Wani kallo Aneesa tace"Saboda Mijina ne..."Ido jidda ta waro tana Fadin"Are u sure..? Modibbo yace"An daura musu aure ba dadewa Lalurar ta sameshi.."Cikin Wani yanayi jidda tace"Allah Sarki...Anee dama na taba fadamiki watarana Kiyayyarki ga Mr bello zata Rikide ta koma soyayyah Allah ya bashi lafiya.."Suka amsa da Ameen kafin su rabu sai da suka karbi Nombar juna,suka rabu jidda na jadaddamata zata zo har gida suka wuce suma suka cigaba da Tafiya,miskin da bata dauka ba kenan sai dai suka karisa wajen Ruwan Zamzam tana kokarin Daukowa taji muryan wata Abayanta tana Fadin"Feedy kalli Namiji har Namiji ga kyau da Zati ammh ya nakasa.."Tafada tana ya fito wacce suke tare Lokaci Daya tana Nuna mata Bello.

Fasa Daukan Goran Ruwan Zam-zam din tayi ta waigo afusace kamar wata zakanya tana bin yanmatan da wani matsiyancin kallo cikin Masifa tace"Ina ruwanki da mijina da zaki dinga Gulmarsa har kina nunashi a kalle shi..? Uban wa yace miki mijina Nakashashe ne,Shegu kawai yan iska masu kallon mazan mutune.."Na fada ina jijjiga jiki tsayawa sukayi suna kallona Modibbo da Raihana suka kariso suna Bani Hakuri shiko yana Zaune bisa kekensa yana kallo yana so yace na bari ammh bashi da baki.

Wacce aka nuna mawan ne ta kalleni ta saki wani Shewa tana Fadin"Au Ashema mijinki ne..? Su masu miji an ji jiki wlh.."Wlh kin ci Sa"a mijin naki dakike hakilo akanshi bai da mamora kemabai miki ba balle ni,da wlh sai nanuna miki ke karamar yar isk..."Bata karisa ba na saka Hannu na Tsinketa da mari Lokaci Daya naci kwalan Riganta ina Fadin"In kika kara Fadin mijina bai da Mamora wlh sai na Datse miki harshe...Kin ci sa"a kura tayi lafiya da lokacin da nake amsa suna Aneesa bukar bulama ne wlh da yau kin gane kuranki banza sakaara kawai.."Nafada ina Huci lokaci Daya ina Ingizata baya ta Fada jikin yar"uwanta,

Dafe kunci tayi tana kallona cikin Mamaki Raihana ne da Modibbo ke basu hakuri niko ko ta kansu banbi ba na isa ga Mijina na Shiga Turasa ina masifa ni kadai kamar Wata Zararriya bansa ya suka kare ba,nidai abakin mota suka sameni ina ta bala"i ni kadai shiko yana Zaune yana ta bina da kallo,Su modibbo na karisowa Rike da ledojin shooping din da mukayi ina ganinsu na Fara masifa ina Fadin"Meye na basu hakuri..? Bakuji me suke fadi ba shegu yan iska kawai wlh sunci babbar Sa"a da ace ada ne wlh sai na koyamata Hankali.."Ta inda nake shiga bata nan take Fita,kawai sai naga sun kalli juna sun kwashemin da Dariya Raina ya baci harda Hawaye na Bude bayan mota ina Tura baki na Shiga kici kicin Sauke shi na sakashi cikin mota,Da Sauri modibbo yazo ya taimakamin muka sakashi cikin mota,shi kuma ya Nade Wheelchair din ya saka Cikin Booth,Raihana ta shiga gaba Shi kuma Modibbo ya Shiga bangaren Direba muka bar Mall ina ta Tura baki da bata rai kansa na kam cinyana ya dameni da kallo ammh naki bari na Mu hada ido.

Har muka koma gida ban saki Fuskata ba,Raihana ko da modibbo da sun kalleni sai su saka Dariya Sai na kara kufuluwa,Har ta tafi gida ban Shiga Harkansu ba,Da na tuna sanda naji suna yabamin miji sai naji wani bakiciki ya cika ni haka in na tuna sanda tace wai namiji har Namiji ba mamora sai naji kamar Zuciyata zata Buga saboda Takaichi har na gama mai Abubuwan da nike mai kafin mu kwanta,ban yarda mun hada ido ba Ranar ma wajen kafafunsa na saka kaina ina tura baki kamar wata yarinya,kamar shi yayimin laifi ko ina ruwan mara lafiya.

Har Washegari ban saki ,Fuskata ba Fara"a ko kadan,Modibbo kuwa bai takaleni ba,sai da Raihana tazo ne na dan saki kadan,har na warware,Shiko Bello cikin Ranshi ma Dariya nake bashi ganin irin salon kishina,Ransa na masa Dadi in ya kalleni Zuciyarsa ta gama Tababbartamai ba iya tsausayinshi nake ba har da soyayyarsa kamar yadda Nawa Son yayi mishi kamun kazan kuku.

*****

Haka muka cigaba da Rayuwarmu cikin jin Dadi da kwanciyar Hankali,Duk bayan sati biyu Ya muktar kan zo ya Dubamu ya barmana kudi duk da bamu da bukatar komai na bangaren Rayuwa sai dan Abunda ba"a rasa ba,iya kula muna samu ba laifi Modibbo da Raihana sun taimaka wajen Debemana kewa sosai,Bello kuma nine Farincikinsa Komai nakeyi yana Nanike dani ko kichen nake ina girki muna tare yana kallona Modibbo da Raihana kullum cikin mana Tsiya suke wai wannan irin Luv haka Sai dai na Zabga musu harara bana bi ta kansu ba.

B.kaita ta kirani awaya take Fadamin sun Dubo Resuilt dinsu ita da Salamatu jibiya,kuma Alhamdulillah sunci duka,har ma zasu Rubuta jamb,in suka ci zasu shiga jami"a nayatasu murna sosai,ammh ni na gayamusu ban Dubo nawa ba domin baya gabana Tunda ko na Dubo ba wani amfani,kula da Mijina Shine Aikina da kuma jami"ata,

Achan borno,kuwa Anty Nafee sai da tayi magana dataji wai har mun koma kano har ni ta kira naki Dagawa Domin kiran Anty Nafee bana alheri bane,ina gani naki Daga kiranta bana son ta Dagamin Hankali ina Zaune lafiya Nida Mijina,aiko tayi ta zagina tana fadin ta cire bakinta,akaina naje na karata babu Ruwanta Ba wanda ya gayamin ni kuma ban damu domin Anty Nafee bata gabana ko Cikin yan"uwana dama bama da wani Shiri sosai.

*****

Yau tun safe dana tashi naji ina kwadayin koko da kosai,Tun bayan da nayi sallar Asuba ban koma ba,Bayan na ma Bello wanka na Shiryashi cikin riga da wando black and white na kamfanin Armani,Da zan tafi kichen ya chanza fuska sai na Turasa muka tafi tare.

Ina sanye cikin Riga da wando na pakistan kaina yana Daure cikin Gyalen kayan,yana ta baya ni kuma ina gaban gas din ina ta faman Juya kosai gefe daya kuma na saka ruwan zafi,na dauko Wata karamar roba inda na Dauko garin kuni na wanda na saka Raihana tazo min dashi Daga Gidansu,Bayan na kwashe Kaskan farko na zuba wani,sai na koma wajen Dama kokon na Dauko karamar tukunyar da ke cike da Ruwan zafi kawai tsautsayi sai Hannu Daya ya Subuce Ruwan ya kware,da Sauri na saki Tukunyar nayi tsalle gefe ina Sakin kara,lokaci daya ina yarfe kafata inda Ruwan ya Tabeni ina Hawaye cikin Son ya mike ya kasa Cikin ikon Allah kawai naga ya Daga Hannnunsa na Dama yana miko cikin Razana da Tashin Hankali.

Ai mancewa nayi da Kunan danayi na isa gabanshi da Sauri ina kallon hannun nashi Dayake mikomin cikin hawaye nace"Kalli fa..ka daga hannunka..."Nafada cikin mamaki yana Rike hannun Shima kallona yake yana kuma bin Hannun nashi da kallo,Gudu na kwasa zan Fita muka ci karo da modibbo yaji ihu na ya Fito cikin Tashin hankali yace"Matar baffale lafiya naji kamar ihunki.?

Ina Haki ga hawaye afuskata nake Fadin"Kalli modibbo ya yi motsi da hannunshi harma ya Daga,duba kagani.."take fada tana nunamai hannun Bello wanda haryanzu yake ta motsi dashi cikin Farinciki da Sauri ya karisa garesa yana Fadin"Allah mai iko..Wlh da gaske. Kuwa..! Yafada cikin murna da Dariya Bansan sanda na isa kusa dashi na Fada jikinsa na Rumgumeshi ina Murna kamar amafarki naji ya saka hannunsa guda dayan ya Rumgume bayana dashi,saboda Farinciki bansan Lokacin dana kai bakina saman bakinshi namai sumba mai tsawo ko modibbo banji kunya ba Shiko cikin Farinciki ya shiga turamu nida shi Saman Wheelchair din yana Dariya har zuwa falo.

Nida Modibbo akasa rasa wayafi wani rawan jiki wajen kiran Waya,ni Daada na fara kirana ina murna ina gayamata shi kuma Modibbo Ya muktar ya kira ya Fadamai gabadaya lbrinmu ya Sanyaya musu rai,haka Ya muktar ya kira modibbo Video call,bayan ya koma gida suka hadu dasu Daada suka gani suka Tabbatar,Farinciki ya cika zuciyar Daada Data ya muktar sai da sukayi kwallah lalle mai Rai kar ya cire hop,shi kuma Bello Ranar Wuni yayi Daga hannu  yana Tunanin kamar in ya maida zai koma ya kwanta kamar baya,Allah Sarki....

Ki biya ki karanta cikin Salama...

*Anitha...*
8/19/20, 11:22 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

        *🅿�28*

Ashe haka kowacce mace takejin Farinciki in Wani Abun cigaba ya samu mijinta,Hakance ta faru dani domin nafi kowa murna nice lbri har Borno na kira su Mama yana ina sanar dasu suma sunyi murna Mama falmata ta sake bani Shawaran na Dage kar na Nuna gajiyawata da Kula da Bello Watarana zai mike ya taka da kafafunsa kamar bai taba irin wannan ciwon ba...

Hakama Daada cikin Farinciki tayi waya chan Adamawa tana Labartama Baffa Hardo cigaban da aka samu shima yana Nuna Tsantsan Murnan,kuma yace acigaba kar afasa,shima yana nan yana tayasu da addu'an Allah ya karya koma menene,saboda jin dadi Kwana uku da Faruwar Haka sai ga Ya muktar dasu Daada sunzo,Sunga ko Abun mamaki Domin Yana iya Rike abu mara da Nauyi da Hannun,Har Junior dake hannuna sai da ya rikemai hannu Muko gabadaya Farinciki yaki barin Zukatanmu nan suka kwana sai washegari suka koma Abuja Sunbar Hibba agida saboda Makranta wajen Jummai.

Ganin irin Cigaban da Aka samu ne ya sanyani na Dage da Karatun Qur"anin da nake mana Duk Dare kafin mu kwanta bayan Ruwan zamzam din da Baffa Hardo ya aiko Daga Adamawa nima ina yin nawa na Tofe da Addu"o'i na bashi yasha kuma na Shafemai duka Jikinsa Safe da rana da yammah,Fatana kawai Watarana Naga Mijina ya mike da kafafunsa kamar kowani Namiji mai Cikar zati da Haiba.

Samuwar lafiyan Hannunsa Guda Daya sai yabashi wani karfi,ko Wucewa nazo yi ta gabanshi yanzu zai saka hannu ya jawoni na Fada kan cinyarsa ya saka hannu ya zagayo dashi Daga bayana yana Kallona domin na lura har karkacewar kan daya keyi yanzu ya Rage hakama Zubar da miyau sai mu Wuni kansa bai karkace ba,Ko wanka nake mai ina kokarin kauda kai bana so mu hada ido ammh sai ya Shammace ni ya Fizgoni na Fada Jikinsa,ya Kuramin ido yana kallona Ni kuma Duk kunya sai ta kamani na Dinga Hararansa ina Turamai baki.
Chapter 50 · 0% Book details