← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 76

Sashe 21

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*KASIM KABIR JIKAMSHI* kenan,Matashin Saurayi mai ji da Kudi da Naira,Kasim Irin Matasan nan ne Masu Budewan Ido Tun Zuwanshi kasar Waje karatu Turawa Suka lalatashi ba Sharholiyar Da baya yi Har giya yana Sha Neman mata kuwa kamar Bunsuru,Daya kyal ido yaga mace Toh babban Burinshi ki bada Hadin kai ya kwalfi Ruwan Dadi Ko da ya dawo Babu Abunda yafasa yana samun Aiki a kaduna wanda ya Muktar ya samarmai yaje ya Dasa Daga Inda ya Tsaya Duka iyayensa ba Wanda ya Taba sanin Halin Dayake Ciki sai Hashim Wanda Ya Taba Riskanshi Cikin Halin Buguwar giya Lokacin Daya kaimai Ziyara agidanshi Dake Kaduna Duk dq ya mai Fada Harda Barazanar zai Sanar da Abba Kabiru bai sa Kasim ya bari ba,Ko yana so ya bari sai yaji bazai iya ba Yadai Furtama Hashim Din Daya bari ammh bawai Don Ya bar Abunda yake aikatawa ba,akallon Farko in kayi mai zaka Gane Cikakken Dan Duniya ne Dayasan Harkan bariki.

Yau kwanansa Hudu Agarin Abuja Sunzo Wani Worshop ne Daga Wajen Aikinsu Gobe zasu koma kaduna Shine bayan ya biya gidan Hashim sun gaisa da Matarshi Shi baya gida,sai kuma yace bara ya biyo ta gidan Ya Muktar su gaisa Da Anty Rahila Duk da yana da Tabbacin Baya gida yanzu,dama ko chan yakanzo Lokaci bayan Lokaci Duk Dashi da Bello kowa najin kanshi ya Isa,ammh bai sani ba Bello ya Fishi Iskanci da Taurin Zuciya,kuma Abunda Kasim bai sani ba Duk Iskancin da Kasim ke aikatawa Bello nada lbri Saboda Akwai Wani Abokin Aikinshi da Suke Aiki Tare a Kaduna,Tare Sukayi Universty of ibadan da Bello,Toh ya Taba ganin Hotonshi Awayarshi,inda yake Nuna ma Wani yana bashi lbrin Irin Iskancin da Kasim ke Zubawa babu babu Abun da yafi Batama Bello Rai Irin Neman Mata da Shan Giya da akace kasim nayi ko bakomai suna da alaqar jini,lokacin Har Abokin na Kasim sani na Fadin garinku ma Daya Muhammed Bello Shima iyayenshi mutanen Jikamshi ne yake kawai yayi koda Wasa Bai Nuna ma yataba ganinshi ba.

Cikin Isa da Takama ya kama Hanyar Kofar da zata sada ka Da Babban Falon gidan,yana Tafe yana Cilla key din Motarshi Kofar Falon ta glass ne na Waje in zai Shigo yana ganin na Ciki  Tun Alokaci idanuwansa suka Fara Masa Tozali da Aneesa Barin ma hannayenta da Suka Fara Jan Hankalinsa sai da kofar Tagama Tatanceshi kana ta Wangalemai kofa ya Sawo kanshi Falon Cikin Siririyar Sallamarshi.

  Aneesa Tayi Nisa Cikin Game dinta batama Jisa ba Kara gyara zama Tayi tana Sarrafa Game din Cike da Salo har Dan kwalinta ya zame gabadaya Kitson kanta ya bayyana Cikin Daskarewar Numfashi da Sarkewar Murya Kasim ya Bude baki yana karema Aneesa kallo Domin Lokaci Daya yaji jikinsa ya Saki Duk yawon Duniyanshi bai Taba Haduwa da Yarinyar da ko gama kallon Fuskarta baiyi ba yaji tatafi da Imaninshi ba Kamar Aneesa ba.

Cikin Sanyin Murya mai Cike da Yaudara ya Furta"Tsarki ya Tabbata ga Allah Shugaban Hallitun Duniya Wanda yayi Wannan kyakyawan Halitar..."

Yafada yana Kafe ta da Ido kamar daga Sama Aneesa Taji Wata Murya na mgana Cikin Sauri Ta Dago kanta Karaf ko Idanuwansu Duka Hudun Suka Hade Waje Daya,cikin Numfashi Sama sama Kasim ke kallon Aneesa yana jin Wani Abu na yawo Acikin Jikinsa Sosai Karon Farko Atarihin Rayuwarsa Daya Hada Ido da mace yaji baya Bukatar ya lashi Zumarta So Daya ya dauwama yana lasarta kuma yana kallon kyakyawan Fuskarta cikin zuciyarsa gayamai take Dakai Wannan Cute Face din Ta Dace.

Aneesa ko Kallon ne ya Sanyayamata Jiki ta Sauke idanuwanta Lokaci Daya Tana Mikewa Dankwalinta taja ta Aza bisa kanta Cikin Sanyin Murya tace"Am Srry Sannu da Zuwa,Zauna.."Tafada Tana kara kallonshi Tana so Ta Tuna Inda ta sanshi Shiko Mirmishi yayi kafin yace"La..No problem karki damu Nafiki jin Dadin Hakan Domin Idanuwana Su samu Damar kallanki Dakyau..",Yafada Cike da Bariki lokaci daya kuma yana Sakarmata ido,yam Aneesa Taji bata yi mgana ba Ta fara Taku Zata bar Falon Rigar Jikinta na Rawa Kowani Sako na Jikinta na Rawa Gabadaya Kasim sai Yaji yakasa Control din kanshi da mayun idanuwanta ya Bita da kallo har Ta fice Daga Falon Wanda Tana Ajikinta Cewa Idonsa na yawo Akanta Duk sai Ta Tsargu.

Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin ya Karisa Kusa da Junior ya saka Hannu ya Daukeshi yana Cillashi Sama Shiko yana bangala Dariya Domin Tunda ya Shigo yake Miko mai Hannu yana Zillo Domin Haka Junior yake yafison Maza Su Daukeshi Fiye da Mata,yana Tsaye yana ma Junior Wasa Aneesa Ta Dawo Wannan karon ta sanya Wani karamin Hijabinta Fari Cikin kallon Ido Cikin Ido Tace"Ka kariso Ciki mana ka Tsaya Anan..."

Lumshe mata ido yayi kafin yace"Toh ai ba"amin Jagora bane...Shiyasa na Tsaya Anan.."Mirmishi Tayi kafin tace"La..ba Haka bane,.."Yana kallonta yace"Toh yane...?

Yafada yana kallonta Kur Cikin Idanuwasa Sauke idanuwanta Tayi kasa Kafin ta Juya Tana Fadin"Afuwan Yanzu mu Shiga Ciki.."Bayanta yabi Da kallo yana Fadin"Angama princess."Wani Iri Aneesa Taji sai Nanata Sunan Take Acikin Ranta Duk da ba yau ne karo na Farko da Maza ke Nuna Sha"awarsu Akanta ba Ammh Dis is d First time da Wani Namiji yake mata mgana Taji ya Burgeta......
.

Falon Anty Rahila Suka Shiga,Waje Ta Nuna mai ya Zauna kafin ta Shiga kwalama Alheri kira da Hanzari ta Fito nan ta Umarceta Data kawo ma Kasim Abun Sha Da Ruwa,kallonsa Tayi Tana Fadin"Anty Rahila na Ciki bari na Kirata.."Da Sauri yace"No...Kyaleta Dawo Mu gama Mgana Princess,In zan Wuce sai ki kirata mu gaisa.."

Da baya Aneesa Ta Dawo Ta Zauna kan kujeran Dake Facing Dinshi Bai samu Zarafin mgana ba Alheri Ta Shigo Cikin Uniform dinsu Domin kaf masu Aikin gidan Suna da Uniform,Katon Faranti ne Cike da Abun Sha Bisa Dan Madaidacin Tebur din Dake gabanshi ta ijiye kafin ta Dauki Kofi ta Tsiyayamai Ta Mikamai Karba yayi da Hannu Daya Yana Fadin"Thanks..."Yafada yana kafa baki Lokaci Daya kuma yana Kallon Idanuwan Aneesa Ita ko Kai ta Sunkuyar Tana Wasa Da Adom Doguwar Rigar Dake Jikinta.

Sai da yagama Sha ya maida Kofin Kan Farantin kana yayi gyaran Murya,Da Sauri Aneesa Ta Dago Cikin Dage mata gira yace"Ya.... ? Kinsanni..? Girgiza kai Aneesa Tayi kafin tace"Naso na ganeka Ammh kuma na Kasa Tuna Inda na Sanka.."Mirmishi yayi kafin yace"Ayyah...Niko kinga ina ganinki na ganeki ba.."Ido ta Waro kafin tace"Da gaske...? To Wacece ni din...?

   Dariya ya Saki yana kara Gyara ma Junior zama Wanda ke Ta Wasanshi Cikin Muryan Takama yace"Ah..Kaji wayau ko..? Bazan Fadi Sunan ba,Sai dai na baki Satar amsa bake bace kanwar Anty Rahila Dake Zaune Awajenta ba.."Yafada yana kallonta Domin baisani ba Cinka kadai yayi Saboda bai Taba katarin Zuwa gidan Sun Hadu da Aneesa ba Domin yafi Zuwa Lokacin Tana Zamfara Abakin Zubaida ne me yake Jin lbrin wata kanwar Anty Rahila na zaune awajenta kuma yana ganin Aneesa jikinsa ya bashi itace ko domin kamar da suke da Anty Rahila.

Dariya Tayi kafin tace"La..Da gaske kuwa kasanni,Niko na Rasa Inda na Sanka.."Dariya yayi mata kafin yace"Sunanki ma Wace...? Cikin Sauri Tace"Aneesa nake..."Dariyan Nasara yayi mata Ckin Sauke idanuwansa Akanta yace"Wow....Nice Name Aneesa..."Yafada yana Yar Dariya sai Lokacin ta gano Wayau yayi mata Hararan Waasa Tamai kafin Tace"Zan Ra ma ne..'"

Bai ce mata komai ba Illah Ido Daya Zuramata kawai yana Kallonta Abun sai ya Dameta Ta sadda Idonta kasa Tana Jin gabanta na Faduwa Cikin Sarkewar Murya Taji yace"Kinsan Zubaida..?
Kanta ta Dago Tana kallonsa Lokaci Daya Tace"Zubaida gidan Abba Kabiru..? Kai ya Gyada mata Cikin Dariya tace"Eh Sosai Ita da Zulfan gidan Abba garba Suna Zuwa Hutu nan Sosai.."cikin Sanyin Murya yace"Toh ni wanta ne.."Baki Aneesa Ta Rike kafin tace"Koda naji... Fuskarta nake gani,Shiyasa Na Rasa Inda na Sanka.."Bai ba mganarta Muhimmaci ba Ya Tsare ta Ido Cikin Dakewa yace"Aneesa...:!Idonta ta saka Anashi,suna kallon Juna na Wani Lokaci kafin Yace"Kina Sona...?Zaki Aure ni...?

Dam! Aneesa Taji gabanta na Faduwa Sosai,cikin Rawan Baki tace"So kuma...? Ba..bangane ba.."Mikewa yayi Dauke da Junior ya iso gabanta bai Tsaya ba kawai sai ya Durkusa kan Kafafunshi Har Gwiwansa na Gogan na Aneesa baya taja da kafarta Tana kallonshi Cikin Wani yanayi Kallonta Shima yake kafin yace"Eh So nace Aneesa..?Tun Shigowata idona ya Hadu da Idanuwanki naji kin Sace zuciyata,naji na samu matar Aurena..plz Aneesa Don"t say no..Ki Amsamin zaki Aure ne...? Kuramai ido Tayi tana gasgata Gaskiyarsa Cikin Ajiyar Zuciya tace"E....."Bata karisa ba Kasim ya Riko Hannunta Guda Daya yana Fadin"Thanks So much peincess zan Tababbatar da Kinfi kowacce, mace Dacen Samun Gwarzo Namiji kamar kamata.."Yafada Cike da Farinciki Da Sauri Aneesa Ta janye Hannunta Lokacin Dataji Wani yam Ajikinta Domin wannan shine karon Farko kenan da Wani Namiji,ya Taba Tabata kuma taji wani bakon yanayi ya Shigeta.,Saurin mikewa Tayi Tana Fadin"Nifa...nifa ban.."Mganarta Ta makale ne Sanda ya Sakarmata Idanuwansa Da Suka Chanza Launi Suna kallonta Shuru Tayi ta kasa Mgana sai ma Sun kuyar dakai Datayi ta koma ta Zauna Tana Wasa Da gefen Hijabinta.

Gefenta Kasim ya Zauna yana Cigaba da Marairaice ma Aneesa yana Cigaba da gayamata kalamai,masu Sanyaya jiki Wanda Daga Dukkan Alamun mganganun nasa Suna Tasiri Acikin Zuciyar Aneesa Suna Cikin Wannan Halin ne,Anty Rahila ta Sauko ganin Kasim Kusa da Aneesa Yayi kasa kasa da Murya sai Abun ya bata mamaki ita ta katsesu Cikin Mamaki take Fadin"A"ah Wa nake gani kamar Kasim..?
Chapter 21 · 0% Book details