← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 76

Sashe 52

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barcin mai yi wani Nisa ba Na tashi sai lokacin naji kunya ganin yadda na matse mai Hannu,Tashi nayi ina Kauda ido kar mu hada ido Shiko ajiyar ya Sauke ganin namike garau na Fada Tiolet,wanka nayi na Fito,ganinshi Zaune yana kallona yasa na Isa gabanshi na Dauko karamin Qur"ani na Budemai Suratul Bakara na saka mai ahannunshi ina Fadin"Karanta kafin na Shirya kaji..? Bai min gaddaama ba ya karba aransa yana mamakin wai zan mai wayau kar ya kalleni,Ina Shafa mai ina kallonsa ta Wutsiyar ido shikuma sai ya maida kansa ya Jingina da Wheelchair dinsa kamar yana karatunsa Harda mai da kai gefe ganin Haka yasa na Dauko kayana na saka Riga da Sikat na Less mai kalan Blue da Pick,ina Tunanin hankalinsa na wajen karatu Ashe Duk Abun da nake yana kallona sai zan Dago kai sai ya sauke idanuwansa kasa kamar bani yake kallo ba.

Sai da na gama Shiryawa tsab nayi irin Daurin Zahra buhari na Daure gashina da Band,wanda Raihana ta matsamin mukaje aka Gyaramin Kaina,nayi kyau sosai Harda jan baki na Shafa da kwalli bayan na gama na juya ta gabanshi ina Fadin"ya kagani...?Nayi kyau..?kuri yayimin da ido Lokaci Daya naga idanuwansa sun chanza launi Kasa yayi da idanuwan nasa yana mikamin Qur"anin Hannunsa da Sauri na karba,Na maidashi mazauninshi ina Fadin"Ko ka nuna alamun nayi kyau kuma fa wa kai nayi mawa kaima kaji kanka amatsayin Namiji da matarka zata maka kwalliya kagani...."Ban gama mitana ba naji ya saka Hannu ya Fizgoni na Fado Kan Jikinsa,.

yarr."Naji lokacin Daya Rike kuguna da Dayan Hannunsa Dagowa nayi,Ina kallonsa Lokaci Daya hancinmu na haduwa waje Daya,cikin idanuwan nake kallo Shi kuma yana kallona cikin wani Shauki,Lumshe idanuwan yayi ya kara matsoni sosai ni kuma na lafe ina Sauke Jiyar Zuciya bayan na saka hannuna na Dafe kirjinsa Bansan Lokacin Dana Fara Shafa kirjinsa ba Cikin wani Salo,lokaci Daya ina kallonsa Idanuwansa ya lumshe yana maida Numfashi sama sama,bakinsa ya Karkato kaina,Hancinsa na Fitar da Hucin Numfashinsa cikin Wani Shauki da bansan ni Aneesa ina da Shi ba kawai naji lebena saman lebenshi na Dora Lokaci Daya ina kallon kyakyawan Fuskarsa.

Mun Dade Ahaka batare da Nayi yinkurin yimai wani Abu ba Shi kuwa Jira kawai yaji na Fara Sumbutar lebensa Tunda shi bazai iya Sarrafa bakina ba Ganin yadda naga Zuciyarsa na bugawa yasa nayi Saurin Kwace Jikina na Tashi Daga kan jikinsa Lokaci Daya kuma naji Muryan Raihana na kirana Daga Falo Ajiyar Zuciya na Sauke ina Kallonsa Lokaci Daya ina Tura baki,Zuwa nayi gabanshi ina Hararanshi ban Lura da jan baki Dana Shafamai saman kumatunsa ba,da kuma saman lebensa,na Shiga Turasa Zuwa Falo.

Muma Fitowa Naga Raihana Zaune Bisa Cafet suna karyawa Ita da Modibbo baki na Rike ina kallonsu cikin Dariya Suke gaisheni Harara na sakarma Raihana bayan na kai Bello gaban Kujera mai zaman mutum biyu na Koma na Zauna bayan na juyashi yana kallon Modibo.

Raihana ta Shagwabe tana Fadin"Ya modibbo wai me nayi ma Amaryan gidan ne take ta Harara ta Tun Dazu..? tafada tana Dariya yana Tura kwai cikin bakinsa yace"Ah ina zan sani Raiha..Kila Haushi Takeji Suna cikin Soyewarsu da Baffale kika katsesu.."Yafada yana kallon Bello yana Dariya kasa kasa.

Itama Sai Lokacin ta Lura da Jambakin Daya bata ma Bello Fuska Kallon Juna Sukayi suka kara saka Dariya na Harzuka na mike ina Hararan su cikin Bata Rai nace"Eh din,wai ku lafiyanku kuwa kuna ta dariya kamar wasu Shashashun madina.."Raihana ce tace"Gani mukayi Yau kwalliyar Ya Bello har da su jambaki ne."Sai da ta Fada na kallesa na gani sai kunya ta kamani na Rufe Fuska na Kwashi Sauri Zuwa Daki Gabana na Bugawa,Bisa gado na Fada ina Fadin"Karsu cemin wannan anyi zalamarmiya Mutum na Zaune ba lafiya ina kwakwaminsa.."Wata Zuciya tace"shifa ya kwakwumuke Aneesa.."Ido ta Runtse tana Tunanin Yanayin Lokaci daya ta saki Mirmishi ita kadai ..

Modibbo ko Da Raihana Dariya suka kara sakawa Shima Bello ido ya lumshe yana Dariya Cikin Zuciyarsa,Sai da nagama goge kunyata kana na Fito ina Hade rai kamar su karamin Wata mgana basu tankani ba sai Dariya kasa kasa,ban tankasu ba illah Littafin dana maida Hankalina ina karantawa Kwana Sittin na Sumaiyyah Abdulkadir,tun muna mkarata Nida su B.kaita muke taba karatu Dawowarmu kano da Haduwata da Raihana yasa na kara gwanancewa,ita ke siyo min in sun Fita da Modibbo,In ta karatu ina karantama Bello,Alhamdulillah ina karuwa sosai Musamman Littafan marubuta na kamar su Halima Abdullahi k/mashi da Zulaihat sani kagara,Rahma hassan Zaria,Sa"adatu waziri gombe,Sumaiyyah Abdulkadir Takori,gaskiya Yana jin dadin littafinsu su ka kara sakani na kara zama mace sosai na kara wayewa da sanin Duniya,nan ne nake kara koyon wasu girke girken,saboda karatun littafin ne nagane cewa na kamu da matsananciyar soyayyar Bello.

Tunda ni ba Whatsop nakeyi ba B.kaita tayi tayi na Bude mu dinga Haduwa Naki,Raihana,ma har Budemin tayi na goge gani nake Dana Fara Hankalina Zai Dauke Daga kula da mijina.

Raihana ta tattara komai ta kai kichen ta Wanke min Duka Abubuwan Dana bata ta gyaramin Kichen din,ta kuma Fito falo ta gyarashi tsaf ta yi mooping Ta goge Komai na Cikin gida Harda Falon Farko na Modibbo ina jiyo Hiransu Daganan Don na Lura suna yar gyada,Haka takemin koda yaushe In taga Aikin gida sai Ammi ta Turo ta taimakamin Babu Abunda Zamu ce ga Uncle Aminu sai godiya Domin Sun mana komai agarin kano Raihana ina jinta tamkar yar"uwata ta jini,Duk da Anty Aisha ma ta yawan Zuwa Dubamu ita da mijinta.

Muna Zaune suka Shigo Modibbo an sha wanka wai zasu Fita Cikin gari,ko zamu Fita..? Nace adawo lafiya ba inda zamu nida mijina muna gida Dariya suka samun Suna Tsokana na wai ina kishi Bello ne shiyssa na daina yarda muna Fita tare na Tura baki ina Fadin eh din haka suka Fice Ina Fadin suyomana Tsaraba.

Ko Minti goma Sha biyar basu yi da Fita ba na mike ina Fadin"B.love na kawo maka Fruit? Ido ya kada min,Na ijiye littafin Hannuna saman kujera na Nufi kichen yabini da kallo,ina cikin yayyankamai kankanan naji Shigowar Mota nayi Dariya ina Fadin"Tsegumanmu ko sunyi mantuwa ne..? Duk azatona na Su modibbo ne.

Hankalina kwance na gama Shirya komai na Zuba bisa wani Filet mai Fadi na Dauko mana karamin knife guda Daya,wanda zan bashi dashi nima naci Tunda ya koyamin Nima cin Fruit ina Kokarin Fitowa naji motsin Shigowar Mutum Falon da muke ban kawo komai ba na Fito ina Fadin"Meya dawo da ku..?ko kunyi mantuw...."

Sauran mganarne ta makale ne ganin wanda ke tsaye cikin Tsakiyar Falon,yana sanye cikin Riga da wando Na Kamfanin Armani,Rigar jikinsa mai Dogon Hannu ce,fara mai Ratsin baki haka wandonsa kafarsa baki me sai Rufaffen takalmin dake kafarsa,ya kara girma da haske,Fuskarsa na cike da wani munafukin mirmishi Lokaci Daya yana Kada key din hannunsa cikin wani izgilanci.

Filet din hannuna na saki lokaci Daya naja da baya ina Nuna shi da Yatsa bakina na motsi..."K...

Ki biya ki karanta cikin Salama...

*Anitha...*
8/19/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

        *🅿�29*

"KASIM....." Tafada muryanta na rawa Cikin kaduwa.

Mirmishin mugunta ya saki kafin yace"Yes princess...." Yafada yana Kura mata ido cikin kallon Kurillah Cikin kwarewa a bariki Har wani Shafa sajensa na Fuska yake Lokaci Daya yana Sakin Mirmishi.

Aneesa Da jikinta ke rawa ta juya tana kallon Bello wanda Gabadaya Hankalinsa da idanuwansa na kan Kasim ne yana kallonshi cike da mamaki Lokaci Daya Kuma Tsoro ya bayyyana akan Fuskarsa.

Kasa karisowa cikin Falon nayi illah kaina Dana Sunkuyar ina Raba Ido Duk da Nasan kasim da Bello yan"uwan Juna ne ammh Jikina bai bani da Zuwansa awannan Lokacin ba.

Cikin Takun sa na yan Duniya yafara Taku Zuwa gaban Aneesa bata sani ba sai dai kawai Taji Hucin Numfashinsa Bisa Fuskarta tayi kokarin Taja da baya yayi Saurin Riko Habarta Lokaci Daya yana kallon kwayan Idanuwanta,Cikin Aneesa ya sake Daukan Rawa Cikin Rawar murya tace"Don...Allah...Ka....Ka sakeni.."Tafada tana kokarin kwace kanta,sai ma ya Hada da hannunta duka ya rike da Dayan Hannunsa,Yana Dariya cike da mugunta ya waiwaiya yana kallon Bello Wanda Saboda Bacin Rai idanuwansa sun Chanza Launi..

Cikin Wata Murya ya Shiga fadin"Kalli yadda na koma Saboda ke princess na rame na lalace Tunda na rasa ki ban kara samun Farinciki ba,Ammh ke kalleki kina Zaune Babu Abunda ya Dameki meyasa kikeda Taurin kaine..Kice ya sakeki Kizo mu Rayu Tare domin Dani kika fi Dace bada shi ba..."Yafada cikin Muryan Rauni Lokaci Daya kuma yana Sakarmata Makirarrun Idanuwwnsa wanda yake amfani Wajen yaudaran yaran Jama"a.

Itama kallonsa take Cike da Tsana da Takaichi kafin ta Daddage ta Fizge kanta Lokaci Daya da Hannunta Tana Hararansa,Nishi take saki cikin Fada tace"Mallam ka Fice mana Daga gida bama Bukatarka...Kuma ka Rubuta ka ijiye ni Aneesa Bukar Bulama ko Yau aka wayi gari B.luv ya bar gidan Duniya Wlh Tallahi sai dai ka Mutu na Mutu ammh bazan Taba Auran ba..Na Shafe Babinka Acikin Rayuwata sai Bayan Haka ta Faru ne ma na Fahimci ko Abaya ban soka ba kasim kawai Wani Kadadaren al"amari ne Daga Ubangiji yasa na amince Dakai..."Tafada idanuwanta Sun kawo kwallah..

Ran kasim yafara baci cikin Budewar ido yace"Kina Nufin Kindaina sona saboda wannan Musakin Nakashashe mara amfani balle Mamora..?yafada yana Nuna Bello wanda ke Zaune yanaji da zai iya tashi da yanzu kasim yazama sai Tarihi.

Wani mirmishi Aneesa ta saki kafin ta koma bayan Bello Tana Fadin"Eh...kaga wannan,bata bashi Zarafin Mgana ba tacigaba da Fadin"Yafi ye min kai Sau Dubu Miliyan Goma..Kai ne mara amfani kuma wanda baida Mamora ammh ni mijina Yana da matukar amfani awajena da Kuma Rayuwata..."Tafada Tana Dawowa ta gaban Bello Ta Tsaya Lokaci Daya tana Harde Hannuwanta Bisa Kirjinta.
Chapter 52 · 0% Book details