← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 76

Sashe 19

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kara Mikewa Zaune Aneesa Tayi Idanuwanta Duka Awaje Tace"Aure Kuma Anty Rahila..? Hararanta Tayi kafin tace"Eh Indai bazaki Koma Mkranta ba Toh Tabbas Aure Ya Ali zai miki kin manta mganarshi Ta karshe..."Shuru Aneesa Tayi Tana Kifkifta ido Daada na kallonta kamar Tayi Dariya sai ta kanne Cikin Hawaye Aneesa Tace"Ni bazan yi Aure ba.."Tafada Cikin Tsawa Zakuda Kafada Anty Rahila Tayi kafin tace"Toh ki zabi Daya ko karatu ko Aure.."Jin Haka yasa Aneesa Ta Mike Tana Fadin"Ni dai Wlh An Cuceni Allah ya sakamin.."Tafada kafin ta Zura da Gudu Zuwa Cikin Bedroom dinta Tana Kuka Daga Daada Har Anty Rahila Dariya Suka Kwashe Dashi kafin Anty Rahila ta Fice Tana Fatan Allah ya kara Shirya Aneesa.

Anty Rahila na Komawa Dakinta Ta Iske Missed call din Anty Nafee,Nan take ta bi bayan Kiranta nan Suka gaisa Shine Take Tambayanta Ina ta Shigane Take ta Kiranta bata Daga ba..? Nan Anty Rahila ke bata lbrin Diramar Aneesa.

Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Kema Rahila kinso sakama kanki Damuwa ne,Ko Su Ya Ali Aneesa Ta gagaresu ballatana ke,Kawai ku Tarkato ta Tadawo Gida Tunda Taki karatu Su Ya Ali su samu wani Garaugarai Su Auramata taje chan Ta karata Tunda Bata da Mutumci.."Tafada Cike da Jin Haushin Aneesan Domin Tana Bakinciki yarda Rahilan Ta Dauki Aneesa Taso Ace Sanah Dinta Rahila ta Dauka Domin Duk Ciki batakai su Karfi ba Mijinta bai da Wani Hali Sosai.

Mirmishi Anty Rahila Tayi kafin tace"Kayya Anty Nafee,Kema kinsan Duk Wanda yama Anee Aure yanzu Wlh yajama kansa Domin karamar Bazawara zata zama,Bajin mgana take yi ba Yanzu dai Dole ta koma Makranta Bello ne Daidai da Ita.."Tafada Tana Dariya Tabe baki Anty Nafee Tayi kafin tace"Hmumm kamar Ta koma Sakara kawai ta samu gata bata sani ba,In Da ace Sanah ce kika Dauka Rahila ba Ruwanki da Damuwa kindai Santa yarinya ce mai Natsuwa kamar Uwarta Rahila.."Tafada Tana yar Dariya,Tsam Anty Rahila Tayi kafin tace"Ammh nake ga Da Aneesa da Sanah Duk Dayane Awajena Anty Nafee,Kuma karki Manta Aneesa Kanwarmu ce Auta take ga Baba kuma kafin mutuwarsa Ya bamu Amanarta ne,in muka barta tayi kukan Maraici Allah zai Tambayenmu. "

Tsaki Anty Nafee Taja kafin tace"Toh..Toh Uwar Tsari da Mgana barni Haka,Muyi mganar dana Kiraki Saboda Ita bana Bukatar Jin Lbrin Aneesa.."Tafada kafin ta cigaba da Sanar da Ita Dalilin Kiran bata  damu ba Ta saki Jiki Suka yi Mgana Sanin Halin Anty Nafee din Tun Farko bata so ta Dauki Aneesan Tama Nuna Jin Haushinta Sosai,ko Mahaifiyarsu Hajiya Yana bata Nuna Jin Haushinta Domin Duka Dayane.

Aneesa kwana Tayi kuka Kamar Ranta zai Fita Babu Abunda ke Tadamata da Hankali sai Dutsen nan da Kuma Debo Ruwa,Kai Gabadaya Mkrantan ma Bata Kaunarta ammh ya zatayi Bello yasaka ma Rayuwarta Ido kya ce Shine Bukar Bulama,Ko ya Ali yadda yake mata wani Abu,gani Take yafi kowa iya  Shisshigi ,Toh in ba Haka ba,me Suka Hada Daga Yayarta na Auran Wanshi Itafa ta gaji da Wannan Ikon Nashi Allah sa Tagama Mkrantar Borno zata koma in ba Haka sai ya kara Sakamata Wani Tsaman.

Bata da yarda Zatayi Tana Kuka da Hawayenta Da Safe Aka saka Duka kayanta amota,Bayan Tayi sallama Dasu Daada,Bayan Motan ta Shiga Ita da Uncle Amunu Shi kuma Mallam Inuwa da Bello Suna gidan gaba Wanda ke Kallon Aneesa yana Kunshe Dariya Ranar ko Ya Muktar batama Sallama ba gani Take Hardashi Aka Hada baki Aka Maida ta Makranta Har Motarsu Ta Fice Daga Haraban Gidan Aneesa na Kuka Wiwi batayi Shuru ba sai da Bello ya Waigo yana Kallonta Cikin Dakewa yace"In baki kama bakinki ba...Zaki Sha Wuya ne yanzu nan.."..

Uncle Aminu kuma Kunnenta ya Murde yana Fadin"Bush gal,Banda Kauyanci Wata Mace kiga tana Gudun karatu,Zaki zama mara amfani Ko Aure kika yi In dai baki da Ilimi.."Tura baki Tayi Tana Kwallah Cikin Ranta ko Tana Fadin"eh din naji ina Ruwanka Mugaye Allah ya sakamin.."Take Fada Tana Share Kwallah Tundaganan Tayi Shuru sai dai lokaci bayan Lokaci Tana Share Kwallah..

Su S.jibiya sai dai Suka ga Aneesa Kwatsam Bayan Sun Dawo Daga Karatu Wajen karfe 2pm,wannan karon ma Hostel dinsu Daya Dr Karima part 1,Kuma Wannan karon ma Ajinsu Daya SS1a,Lokacin da Suka ga Aneesa basu gasgata ba sai ta Ta dago Tana kallonsu Tana Hararansu ga Hawaye na Zubomata ganin Haka yasa Suka Tabbatar da Aneesansu ne Suka Ruga Suka Fada Jikinta suna Ihun Murna,Da Farko Taki kulasu kuka kawai Take Sauran yan Ajinsu na Baya Duk Wanda yazo yama Aneesa mgana ko Kallonshi batayi Daga Baya Taga ba Sarki sai Allah ta saki Jiki,saboda ganin su B.kaita Tare Suka Tayata Shirya provision Dinta Cikin Lokarta Ranar ko pref basu Fita ba,masallaci ma basu Fita ba Cikin Hostel Suka yi Shi Sai Washegari Aneesa Tafara Zuwa Aji Domin Suna Zuwa Mr.Bello ya Damkamata Uniform dinta da Check dinta da Takalmin Mkranta da Jaka da Littafanta Sabbi,Hakanan Ta karba ammh Cikin Ranta bata gode ba.

Ranar Mkrantan Kwatar-kwashi Ta Dauki lbrin Aneesa Bukar Bulama ta Dawo makarantar Ranar ko Sai ga Jidda Tazo Wajenta Har Hostel tana mata Mitan Tana ta Sauraran Kiranta Karya Aneesa Tamata da Cewa Nombar ta bace mata ne Shiyasa Marairaicemata Jidda tayi Tana Nuna mata Irin Son Datakema Mr.Bello gashi Saura Sati Daya su bar Mkranta Ta mata Kokari,Gyadamata kai Aneesa Tayi da Cewa ta bata da Zuwa Gobe Insha Allahu zata san yadda Zatayi Da Haka Suka Rabu da Jidda Tatafi Tana Jin Dadi Itako Anesa Mirmishin Mugunta Take mata na zakici Ubanki ne,Bayan Jidda ma Iri iritan Sun Ta Zuwa Wajen Aneesa Suna mata magiya ita kuma tana Sakasu akwana Aranta tana musu kallon Wawaye.

Wannan karon Seniors Suna Saman Bene ne,Shiyasa Sai Wahalan bata kai na Baya ba,kuma ba laifi Sun san kan Mkranta sai dai Su kalli Sabbi Dauka in sunga suna iyayi,barima New Comers Jss1 Dariya ma Suke basu kafin Sati Sunci Kwal Ubansu Ko Debo  ruwa ma Aka barsu ya Ishesu balle Muguntar Seniors Abun da Zai sake Baka Mamaki Har Ss1 Dinsu Mr.Bello Shine Formaster Dinsu yana Lura da Aneesa Shiyasa Ko Taso Tayi Wasa Batayi Duk da yanzu ya Rage Wata Muguntar Akanta ganin Ta Dan Fara Hankali ba kamar baya ba.

Ranar da yan SS3 Zasu yi Candy,Ranar ne Dukkansu Suka Hau Saman Dutsen na Kwatar-kwashi Suka Debo Gayyayyanki da Sauran Abubuwa wasu da Aljanu Suka Sauko Aneesa Tace kamar Dole mezai aiketa ko Candy zasuyi Wlh bata iya Hawa Wannan Dutsen Domin yana bata Tsoro Haka Lokacin Zafi in ya Dauki Zafi Wuta yakeyi Da Kanshi Lokacin Sanyi kuma yana Fitar da Huturin Sanyi Wani Lokacin ma Bacewa yakeyi Kwata kwata ba Aganinshi.

Da Jidda Ta Mtsama Aneesa da Magiya sai ta Mata karya da Cewa Uncle Bello yace Taje ta Sameshi Haka ta Dingama Saura Acikin Ranta Tana Dariyan Mugunta,aiko kuwa Sunyi Nadama Domin Koran kare Bello yayi musu bayan yayi musu kaca kaca,Kowacce tasha Kuka kafin ta bar Makranta barin ma Jidda da Takejin Soyayyar Bellon Har Cikin Ranta Itakuwa Aneesa Boye kanta Tayi Har Suka bar Mkrantan.

*****

Tafiya tayi Tafiya Cikin Jin Dadi Da Akasinsa Domin gashi Har su Aneesa Sun Shiga Ss2 Abun da zai baku mamaki yadda Aneesa Bukar Bulama ta zama zakaran Gwajin Dafi Wajen Kokari Acikin Mkrantan Duk Dalilin Bello yanzu Aneesa Ta Daina Kukan Zuwa Mkranta Tunda ta Fahimci bello bazai Taba kyaleta ba,Tana Da Kokari Afannin Darasinshi dana Uncle Aminu Domin ita dasu S.jibiya Turanci Abakinsu sai ka Rike baki,Ahutun da suka samu ne na First Time Anty Rahila ta Haihu Ta Haifi Da Namiji Wanda Yaci Sunan Muhammed Suna Kiranshi Junior,Lokacin Haihuwan Duka yan Borno sun Taho Harda mama Falmata mahaifiyar Aneesa da Anty Nafee da Anty Yagana,da Anty Aisha Daga kano sai Matan Ya Ali dana ya Sunusi da Ya"yansu Harda Sanah Tazo wannan karon,Hakama bangaren Su Abba kabiru Hajiya karima tazo ita da Zubaida duk da Zubaidan Tana nan Abujan ne Wajen Ya Hashim tana Shekarar Farko A base University Zulfa ce Take Katsina Umaru musa yar"aduwa.

Zuwanan da Sukayi kowa yayi mamakin Yadda Aneesa ta kara zama sai dai Fa mai Hali baya barin Halinsa,Rashin kunyanta da Tsiwanta na nan bai barta ba Sai dai yanzu ilimi ya Ratsata ta Rage Wasu abubuwa kamar su Faduwa akasa tana Kuka da Wasu Abubuwan,ko da Sunan sai da Takai Zuciya nesa Ammh Haka Anty Nafi ta Dinga kyaranta da Anyi Abu sai tace samun Waje ne,Har Sanah ma Ta iya kallon Banza Saboda Tana Da Girman Jiki tana ganin ta kamo Aneesan Aiko taci Ubanta Don Aneesa bata Daukan Raini gayamata tayi Ita kanwar Uwarta ce ba abokiyar Wasanta ba,Saboda Haka ta Shiga Taitayinta,Dole Ta Shiga Natsuwarta Sanin Halin Aneesan Ko Lokacin Data zauna agidansu bata da Sauki balle yanzu da Girma ya kara kamata ta kara zama yan"mata sosai.
Chapter 19 · 0% Book details