Sashe 75
Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Dama tun muna gida Nageria Yariga ya karbomin Resuit dina,Ban Fara karatu ba sai da Muhammed Amin yayi Wata bakwai kana na Zama Daya daga cikin Daliban makarantan Da Mijina yake koyarwa,ina karanta Biology,Muhammed Amin kuma Dashi nake tafiya Dayake makaratantar akwai Nannys masu kula da yara wajensu nake kaishi sai mun tashi tafiya gida mu karbosa mu Dawo gida Soyayya muke gudanarwa mai cike da Tsabta kamar zamu lashe juna.
Ban samu zuwa Bikin B.kaita ba sudai na Tura mata kudi masu yawa Gudunmmuwa,duk da Banjin Dadin Rashin Zuwana ba Bani da yarda zanyi ko ba domin komai ba Saboda karatuna...ga Kuma Mijina ban zan so na zama ina Rabamai Hankali ba ammh koda yauahe muna waya da yan"uwanmu da iyayenmu Lokacin da muka samu Shekara Daya a New york Anty Rahila da Ya Muktar suka kawomana Ziyara nan ne naga karamin cikin Jikinta yawon Bude ido suka zo Domin Hibba da JUnior Suna gida wajen Daaada.
*****
*SHEKARU UKU BAYA...*
Acikin Shekarun ukun Da Suka gabata bazamu ce komai ba sai Dimibin Godiya ga Allah,Domin Ababen Cigaba ne suka Lullube Duka Rayuwarmu,Duk da mun Kurbi Ruwan Rashi Sosai na Rasuwar Daada wanda shine Dalilin Zuwanmu gida na Farko Allah yasa Lokacin mun samu Hutun Makaranta mun ji Mutuwar Daada sosai barin ma Bello da ya muktar da suke ganin Tamkar Daada itace uwarsu da Ubansu,
Bamu koma ba sai da muka Tsaya Bikin Uncle Aminu Wanda suka Daidaita da Salamatu Jibiya muka Sha biki Tabi angonta Zuwa Lagos Raihana kuwa kaduna take Zaune ita da Mijinta Modibbo wanda ke aiki anan Heaquaters na yan sanda Dake Jahar kaduna suna Zaune Shida Matarsa Raihana,Munje mun yi musu kwana 2 har gidan Sani sai da mukaje nayi ma matarsa barka ta kara Haihuwa,Naje katsina gidan B.kaita na isketa da cikinta, Muhammed Amin kuwa yayi yawo ba inda baya zuwa,Sanah ma an saka Lokacin Bikinta da wani Ma"aikacin Costome Dake aiki a partacourt,
Da zamu koma New york bamu koma da Muhammed Amin ba muka bar ma su ya muktar Tunda ina da karamin ciki alokacin,Dawowarmu ko Wata Biyu bamu yi muka samu Labarin Rasuwar Abba kabiru damam Tun Zuwan mu Rasuwar Daada muka samu labarin yana halin Jinya sosai Tunda ga lalurar Data sameshi,gabadaya duka arzikisun ya kare wajen siyan mgani Hatta gidan da suke ciki sai da suka Saida Gidan Hashim suka koma da zama,Gashi bashi kadai bane domin Ramin mugunta ya koma ma Kasim Ya zame a bandaki kashin bayanshi ya karye yanzu Shine ke Rayuwa Bisa Keken guraku,Abokinsa Haruna kuwa Hatsarin Mota yayi Allah yamai Rasuwa komai nasu yagama karewa Shi kanshi Hashim din karfin Hali ne da Godiyar Allah ammh aikin kamfani Har yaushe zai Rikeshi Inda Allah ya taimaka Zubaida ta Samu miji cikin Abokansa ta aura Matansa Biyu itace ta uku tana Abuja ammh tana cikin Jin Dadin Rayuwa har ma tana taimaka ma iyayenta.
Bangaren Su Abba garba kuwa Abun yayi muni sosai,Suma komai ya kare ga cikin Shigen da Zulfa data Dauko musu bakin ciki kamar ya kashe Mama Sahura Inna Rukkayyah ce kadai Allah ke Rike da ita ta samu ta Aurar Da Hamdiya anan garin kano Ummu ce ke gabanta yanzu itace kedan Taimakonsu itama babu komai sai godiyar Allah,Bello ne kadai yazo gaisuwar mutuwar Abba Kabiru sai Alokacin yaji azuciyarsa ya yafe musu ko ba komai sunga Hukuncin Allah Tunda agidan Duniya Shiyasa wani lokacin da gwara ka bayyyana kan ka a gaban Hukuma ta yankema Hukunci,da ka zauna Hukuncin Allah ya Faru dakai tun agidan Duniya Haka Abba garba ke kuka yana Rokan Gafaransa,Kasim kuwa Duk yagama lalacewa yana Zaune Bisa Wheel chair din da Bello ya tashi akai,Yarsa kuwa Fauziya da Kudiran Allah ta Rayu ammh fa cikin kaskastacciyar Rayuwa, Rayuwa kenan nan yake Shaida musu shi ya siya Ragowan kamfanin mahaifinsu Dake Lagos wanda yanzu haka ya na nan yana aiki ta hannun manajan mahaifinsu Mr James,sunyi matukar mamaki Abun da kuma ya basu mamaki Shikanshi ya muktar ya Jinjina mai kanin nashi sosai inda yace"Yaya bazamu bari...Komai na mahaifinmu ya kare ba...Zamu ji Dadin in muka Tsira Dako Da Abu Dayane.."Rumgume juna sukayi suna kukan Rashin Iyayensu.
Ba Dadewa da mutuwar Abba kabiru,Gidan da ya Ragema Abba garba cikin Dare aka tashi da gobara Dakyar suka Fita sai dai Zulfa ce dake cikin Daki ta kone sosai Asibiti aka kaita kwanta Biyu tace ga garinku nan Gidan kuma ko Tsinke ba"a Fitar ba komai ya gama konewa Wanda ba wanda yasan Daga ina gobarar da take,Mama Sahura tayi kuka kamar ranta zai Fita,Komai ya kare yar nata kuma Allah yayi ikonsa da ciki ajikinta karshenta dai Kauye suka koma Wato Jikamshi dangi Duk sun kare Gidansu na baya wanda yagama Zubewa suka samu Daki Daya Hashim ya tallafa musu suka gyara wajen zama saboda shima bashi da wajen da zai ijiyesu sakamakon Shima an ragemai matsayi acampany Dayake aiki Ya muktar kuma Bello yahanashi basu Taimako Yace ya kyalesu bazai iya karesu ba Hakkin Rai ne da kuma hakkin Dukiyar marayu da suka ci bazai barsu ba.
Aisha maiduguri Tuni tayi Aurenta agarin maiduguri wani Dan"uwanta ta Aura,dan kasuwa ne a kano yake kasuwanci yadaukota suka dawo kano inda yayi gida,Yariga yagama sanin labarin Abunda ya Faru da Aisha Tun Farko,sai bayan Rasuwar Mahaifiyarta ne tayi Auren ya"yanta biyu yanzu Saboda Mijinta yana da Fahimta yasa suke zuwa Har Abuja ganin Fauziya Suna mata alheri Aisha tayi kuka kukan Nadamar Rayuwarta ta baya da yadda Rayuwar yarta ya kasance,Yayanta ya riga yayi Rantsuwa Aisha bazata Rike Fauziya ba,Dangin Ubanta zasu Riketa Kasim kuwa yana kuka Yana Rokon Aisha gafara domin yana da Tattabacin Harda Hakkinta ya kamashi,Me zatace banda ta yafemai ko ahaka Kasim ya Tsaya Allah ya nuna mai Isharsa Zainab Alhaji isa ma Tuni tayi Aurenta Kasim dai yana Zaune yana Girban Abunda ya Shuka In ya Tuna Rayuwarsa sai yaji da ace Allah zai bashi dama daya Sauya Rayuwarsa ya dawo Nagari,sai dai kuma kash Lokaci ya Riga ya kuramai.
Danaji labari sai da naji ba Dadi acikin Zuciyata ina Addu"ar Allah ya Rabamu da Cin Dukiyar maraya da kuma aikata Abunda zai zo ya dinga bibiyar alhalinmu Ameen.
Ayanzu haka na kara Haihuwan Mai sunana Wato Aneesa kenan muna Kiranta Anee,sai kuma mai sunan Daada muna Kiranta Daadan,cikin Shekaru uku na haifesu ni kaina na san na Taka gwarne,B.kaita ta haihu namiji Hakama Raihana Sun haifi Little Aneesa,Sanah ma tuni har anyi Bikinta ta tare agidan mijinta Muhammed Amin kuwa yana Wajen Anty Rahila achan aka sakashi a makarata mukuma muna New york nida mijina da Ya"yana Lokacin har na kamallah karatuna ina Service ne.
*****
Ina cikin kichen da misalin karfe 7am na safe cikin kayan barcina Riga da wando masu Taushi ina Hadamana kalaci sakamakon yau Weeked ne Dagani har Mr Bello muna gida
Ina cikin Soyamana Fanke dama ina zuwa da abubuwan amfanina in mukaje gida Nageria naji Kukan Daada Da hanzari na Fito Ina Tambayan meke Faruwa,Ganin Anee tana Dariya Dauke da Choculate din da na bama Little Daada Dake zaune bisa kekenta na zama na gane Dalilin kukan ban tsaya bata Lokaci ba na isa kusa da Anee na make mata kai ina Fadin"me nagaya miki Don kaniyarki..?
Nafada ina jan kunnata,Baki ta bare,Ban tsaya Sauraranta ba na kwace mintin bakinta ina Fadin"Muguwa kawai...katuwar banza,wacce batasan kanwarta ba Wlh in nakara jin kukanta na Fito sai na lahira yafiki jin Dadi.."Nafada ina Turata baya ta Saka kuka kiris sai ta Fada Jikin Babanta wanda ya Sauko Daga sama yana sanye cikin Kayan Barci na pjms Masu Ruwan Toka,Yayi kyau ya kara kiba kamar ba Mr Bello da alama yana kara jin Dadi Sosai.
Riko Anne yayi wacce ke kuka Harda majina kamar wacce ake yankawa yana Fadin'"Me kuma tayi Tun safe kin Fara zaluntarmin ya..? Yafada yana Sharemata hawaye Ko kallonsu banyi ba na Duka ina lallaban littale Daaada na saka mata mintin Cikin bakinta kafin na mike ina Fadin"Dukan Min y"a tayi kajama yarka kunni Wlh in tace mugunta ce Dabi"arta zata sha Wuya ahannuna.."Nafada ina Huci Saboda Rashin ji Aneesa yafara isata wlh yarinya kamar bugun jinnu.
Mirmishi yayi yana Kara Rumgume Anee yana Fadin"Koma miye dai Kar a takura mana...Ai gado tayi.."Ina kallonsa nace" gadon wa...?gira ya Dagamin yana yar Dariya Mirmishi nayi kawai na koma kichen ina Ma iyayena Addu"a acikin Zuciyata saboda indai ko Hakane sun shaa fama dani sosai.
Ina cikin Juya Fanken Dake cikin Mai naji Hannunsa bisa cikina ya Rumgume ni ta baya ajiyar zuciya na Sauke lokaci Daya ya saka kansa zuwa wuyana yana Sumbata ta dan zillewa nayi yayi Saurin Riko hannuna yana Rikewa Lokaci Daya muna juya fanken atare Cikin Sanyin Murya yake Fadin"Hausawa fa sunce magaji mafiyi..Anee gabadaya kece sak daga kamaninku zuwa Hallayanku...So ki godemana yadda muka Wahala akanki.."Ban yi mgana ba illah Dariya Da mirmishi dana saki Lokaci Daya ..