← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 76

Sashe 15

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bello..!" Ya Muktar Dake Saukowa Daga saman Stairs Ya Fada gabadaya Suka Waiga Suna kallonsa Saukowa yake Cikin Kakinsa da alama Fita zaiyi Hulansa Tana Rike a Hanunsa Ammh Fuskarba Babu Walwala ko Kadan Aneesa dake Tsaye Ta Tura baki Tace"Lalle nema wannan Ka kama Wala mallam Dama Su karike Sune naka ni Aneesa bazan Taba zama Ahalinka ba Ina gama Karatuna zan Kama Gabana.."Take Fada Tana kallon yadda yake Huci kamar Wani zaki.

Tunkafin ya Muktar ya kariso Bello ya Saka Hannu Cikin Zuciya ya Daki Center Table din glass Din Dake Tsakiyar Dakin Ya watse Gabadaya,Gabadaya Falon kowa ya Razana Tun bama Daada ba Hannunshi Tuni ya Fara Digan Jini Ammh bai Damu ba Illah Fadi Daya ke cikin Hargagi "Ya Muktar u better Tell dem Kai kake Bukatar Ahali kamarsu Ammh ni Bello Har Abada bana Bukatarsu Arayuwata In Har kana son ka Cigaba da zama dani karkashin Inuwa Daya sai ka sanar dasu kan Su kyale ni nace bana Bukatar su ko Ana Dole ne...!? Yafada Cike da Tsawa Lokaci Daya gudun Jinin Hannunsa na Kara yawa.

Ya Muktar ya Nufeshi da Sauri yana Fadin"Bello baka da Hankali ne.? Ko Sauraranshi baiyi ba kawai ya Juya ya Fice Daga Falon Afusace Ya Saka kafa zai Bishi Kenan Daada tace"Kul kada ka Bishi Muntari.."Ya Waigo Cike da Tsoro yana Fadin"Meyasa Daada..? Kinga fa Jini yake Zubarwa..?

Mirmishi Daada Tayi kafin Ta kariso Tsakiyar Dakin Tana kallon Zubaida da Zulfa da sukayi Wiki Wiki Tace"Ka kyaleshi ko kaje yanzu bazai Taba Sauraranka ba..!Saboda Fushinsa ya Tashi ba yaro bane zai Kula Da kanshi Ammh Muntari Matukar bazaka daina Kusantoma Dan"uwanka Abunda bayaso ba To ina kyautata zaton Watarana Zaka nemi Bello ka Rasa."Kallonta yayi kafin yace"Ammh Daada..."

"Dagamai Hannu Tayi kafin Tace"Bar Mganar Muntari abarta Kawai nace..."Tana gama Fadin Haka Ta Juya zuwa Shashenta Aneesa Dake Tsaye Tana Kanne Dariyanta sai da Ta Fito gabadayansu Suka kalleta tana kyakyata Dariya,Harara Anty Rahila Ta maka mata kafin tace"Zan saba miki Aneesa ki Shiga Ciki.."

Dariya ta kara saki kafin tace"Ikon Allah Shisshigi ba Kwarjini Ance ba"ayi ba"ayi Dole ne..? Kai Wlh Anyi Asara Tunda Tun Ana ma Mutum kora da Hali Harda yau aka kure shi ya Furta baya Bukata A kyalesa Dole ne..? Tafada tana kwaikwayon Bello Da Gudu Rahila ta Bita Tana Fadin"Aneesa..."!Gudu ta Kwasa Zuwa Sashen Daada Tana Dariya Abun yayi mata Dadi Sosai.

Shiko Ya Muktar Tsaye yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya kafin ya Duka Kusa da Zubaida yana Fadin"Am Srry Kinji...Buh kudaina Shiga Harkan Bello Tunda bayaso ku kyaleshi Zuwa gaba Nasan zai chanza.."

Kuka Zubaida ta Fashe Dashi Tana Fadin"Daddy Wai Laifin su Abba sai ya shafemu..? Bafa mune mukayi Wannan Kuskuran ba,sanda akayi bamu da Wayau Meyasa Uncle Bello bazai Dubemu da Idon Dakake Dubanmu ba.."Tafada Tana Kuka Shuru yayi bai bata amsa ba Kama Kujera Tayi Ta Mike Tana Fadin"Wannan Abun bazai saka na Kyaleshi ba...Yanzu Aka Fara Wasan."Tafada Tana Hararan Zulfa Wacce ke karamar Dariya Cike da Jin Dadi.

Hanyar Dakinsu Ta Nufi Tana Dingishi da Alamun kafarta ta Bugu Sosai da kallo Zulfa ta bita Tana kara saka Dariya,Anty Rahila Dake Gefe Ta Riko Hannun Muktar Zuwa saman Dinning Tana Fadin"Relax...Umh...Is ok..."

Kallonta yayi Cikin Raunin Murya kafin yace"Rahila..Ya zanyi...? Bazan guji yan"uwanmu ba... yayyin Abba ne Wanda Muka Taso muka ga Suna Ci a karkashin Dukiyarsa Rahila,..Ya zanyi Da Rayuwata..? Bayan Sun aikata mugun Nufinsu akan su Abba yau wa gari ya waya..? Basu ga Ishara ba .?.!Kuma Allah ya Nuna musu iyakarsu Tunda Dukiyar Da Suke mawa sun mallaketa ammh Ta kare Ta barsu,Ko Ahaka muka barsu Sunga Isharan Duniya...! Rahila bari na gayamki Duk Duniya Su Abba Kabiru basu da Sanyin Idanuwa kamar mu Saboda mun zamesu Bango Abun jinginansu.."Yafada Idanuwansa na Sauya kala

Anty Rahila na Jamai kujeran Dinning Din Take Fadin"Hakane...Kayi Hakuri kabar Mganar Hakanan Suma Hutunsu ya kusa karewa su koma Gidajensu Shima ai ba zama zaiyi ba.."Muktar ya Runtse Ido kafin ya Bude yana Fadin"Meyasa Bello bazai gane bane..? Yaki bama Zuciyarsa damar karban Kaddara balle yazama Cikin masu yafiya..? Anty Rahila Tace"Hakuri zakayi mu kuma Cigaba damai Addu"a Tunda Haka Allah yayishi..Sai Fatan Allah ya Ragemai Fushin Zuciya.."

Bai mata mgana ba Illah Kurama Waje Daya ido dayayi yana Nazarin Wani Abu Ita Kuma Anty Rahila Tana Kokarin Saving Dinshi,Zulfa ko Na zaune Cikin Falon Tana ta Danedannen Waya Cike da Nishadi Kamar ba Abunda ya Faru yayinda Da Zubaida ke Ciki tana Rafzan Kuka Kamar wacce ake yankata Bakinciki Duk ya Cikata na Abunda Bello yayi mata agaban Zulfa Wacce Tasan Wannan Lbrin bazai Tsaya ba Sai ta kaishi Har gidan Abba garba Mama Sahura Ta samu Abun yabama Ummanta Mgana Akai.

Anty Rahila bata bar Muktar ba sai Taga ya saki Ranshi,Har Haraban Gidan Ta Rakashi,Inda Masu Tsoronshi ke Jiranshi ya Shiga Mota Tawagarshi Suka Rufamai baya,Falon ta Dawo Ta Kira Jummai ta bata Umarnin ta gyara Falon Ta Kwashe Glass din Da suka Fashe ta Tsaftace komai.

****
Cikin Bedroom Dinshi ya Shiga Hannunshi yana Zubar da Jini ammh bai Bi takai ba Illah kafa da Sanya ya Shuru gadonsa Wanda ko Motsi baiyi ba Cikin Bakinciki da Fitan Hayyaci ya Sulale kasan Cafet din Dakin yana Ji kamar Zuciyarsa zata Fito Fuskar Mami da Abba yake gani Iyayensu Wandanda Sukaci Burun Su zauna Dasu Har Tsawon Rayuwarsu Sai dai kash Wadanan Azzuluman Guda biyu Wato Abba kabiru da Abba garba Sun yi Sanadiyar Dakushe Duk Wannan Burin na iyayensu Sukayi Sanadiyar Rabasu Har Illah Masha Allah.

Runtse idonshi yayi yana Sakin Ajiyar Zuciya,Lokaci bayan Lokaci,Kafin Wani Hawaye mai zafi ya Kwarayomai Ta cikin kwarmin Idanuwansa Dora kansa yayi Bisa gwiwansa yana Sakin Marayan Kuka Ahankali Gefe Daya kuma Hannunshi na Digan Jini,Ya Dade yana Rera Kukansa Wanda ya Dade baiyi Irinshi ba,Saboda Taurin Zuciya kafin ya Tashi yana Tangadi Saboda Jinin Daya zuba Ahannunshi ya Shige Tiolet ya sakarma Kanshi Shower,bai Dau Lokaci ba ya Fito ko mai bai Tsaya Shafawa ba ya Bude wardrope dinshi ya Dauko Wasu Riga Da Wando Na kamfanin Armani black and White ya Saka Cikin Sauri ya Fice bayan Ya Dauki Wayarsa.

Haka ya Fito Daga Mension Dinsa Yana Duba Hannunsa Wanda Glass Suka yanke Suka Shisshige,Mallam Inuwa na ganin ya Fito ya kariso da Sauri Domin Dama in ba Bello ba sai Hajiya Rahila in zata Fita Shine kadai Direbansu,Yana karisowa Tunkafin yayi mgana Bello yace"Mallam Inuwa Muje Specialist hospital..."

Yafada kai Tsaye yana Wucewa Jikin Motar inda ya Bude ya Shiga Gidan Gaba yana kwantar Da kanshi Cikin Kujeran Motan lokaci Daya yana Sauke Numfashi Da Mamaki Mallam Inuwa ya biyosa Ya Bude Gefen Direba ya Shiga ya Zauna ya Tada Motar Ya zuba Hon Masu gadi Suka Wangale musu Get Suka Sulala Waje Sojojin Dake Tsaron Haraban Gidan Suka Bisu da Sarawa kamar yadda Suka saba.

Dressing din Hannun Akama Bello Aka bashi Mganguna Kafin Su Dawo Gida,Mension Dinshi yashige Babu Wanda yakara Jin Motsinsa Kuma ba Wanda yayi gangancin Nemansa Sanin Halinshi,Bai damu da Abinci Kayan Lambu yayi taci yana Korawa da Madaran Hollandia Gefe Daya kuma yana Jinyar Hannunshi Wanda ya ma kanshi Rauni.

****

*Washegari..*

Aneesa na Zaune Afalon Anty Rahila Tana kallon Tashar mbc2,Anty Rahila ta Sauko daga Sama Rike da Waya Ahannunta Tana Fadin"Anee ga Kawarki na Kiranki.."

Tafada Tana Mika mata Wayar Aneesa Dake Sanye da Riga da Sikt yan Kanti ta Saka Wani karamin Hijabi Fari Ta kalli Anty Rahila Tana Fadin"Kawa kuma.? Ta Ina..?

Hararanta Anty Rahila Tayi kafin Tace"Bansani ba zaki karba Kokuwa zaki Tsaya Tambayana ne...? Mika Hannu Tayi ta Karba Tana Fadin"Allah baki Hakuri.."Tafada Tana Tura baki kafin ta saka Wayar Akunne Tana Fadin"Hello..."

Da Kallo Anty Rahila Ta bita kafin Ta Wuce Shashen Daada Tana Fadin""Aneesa Allah ya Shiryeki Wlh Mijinki yana da Aiki.."Da kallo Aneesa Ta bita kafin Tace"Wake Mgana..?

Dagachan Bangaren Aka ce.."Aneesa Bukar Bulama..."Cikin Isa Aneesa Tace"Yes...Bilkisu Kabir Kaita..."Dariya Billy Tayi kafin Tace"Ashe zaki ganeni..? Tsam Aneesa Tayi kafin tace"Taya bazan ganeki ba B.kaita ban Tsaneki Haka ba.."

Shuru Ya biyo bayan Mganar Aneesan kafin B.kaita tace"Kin yafemin Aneesa...? Kai Tsaye Aneesa Tace"Me kikamin B.kaita..? Ni babu Abunda Kikamin Fadan Ki so kanki mukayi Domin Ina Matukar Tsausaya miki kin Fada Son Wanda bai Dace kiso ba Billy."Mirmishi Billy Tayi kafin Tace"Duk Naji A.bulama,Ammh Duk Fadan na menene..?

Aneesa tace"Na Haushin Duk Yadda Muke Tare B.kaita baki Tayani kin Wanda nake Ki ba,sai ma Wai kina Kokarin Cewa Kina Sonshi Haba Billy kin bani Mamaki Banga Wani Abun so Jikin Wannan ba.."Tafada Tana Wani Tabe Baki Dariya Billy Tayi kafin Tace"Toh naji nidai baki ji nace ina son Uncle Bello kice kika ja nace miki haka ganin Abun naki yayi yawa..Duk ba wannan ba Ammh dai kinsan Lokacin muna Makranta Mr.Bello yayi kokari Akanmu Aneesa bazai saka Saboda Takun sakarku mu manta Dashi ba

Aneesa Tayi Tsaki kafin tace"Mtswss..Sai fa kiyi ni ba Kokarin Dayayi akaina don ba Rokarshi nayi Nace Don Allah ya kawoni Wannan Makrantar ba Saboda Haka aikin sakai ne Ni ban yaba ba balle nayabeshi.."Dariya B.kaita ta saki kafin tace"Wow...Aneesa Wlh bakinki baya Mutuwa,ya zence komawa Makranta Aneesa ki koma Kinga Nima Abba yace Chan zan cigaba Hakama S.Jibiya Jiya Take Fadamin da Mukayi Waya.."

Aneesa Tace da Sauri.."Tab..Sannunku sai nace Allah bada sa"a Don ni ko zan Shigaba da Wannan Makrantar ba sai dai Jeka ka Dawo "Cikin Marairaicewa B.kaita tace"Plz Anee ki Dawo Saboda Mu.."Dariya Aneesa Tayi kafin tace"Ki bar Rokona Karki Cuceni bakisan yadda na Tsani Makrantar nan bane.."Ajiyar Zuciya B.kaita Tayi kafin tace"Shikenan Ammh Mr.Bello kuwa ya sani..? Banajin fa zai barki Aneesa..?

Aneesa na Hararan Wayar Tace Cikin Kufuluwa"Allah Sarki Hala Bellon Ubana ne,To ko Marigayi Alhaji Bukar bulama Allah ya Jikanshi Sanda yana Raye bai Takuramin ba balle Wani banza Cikon Dangi Ke ni Rabani da Wannan Mganar in Abaya ya kaini Lokacin Ban kara Wayewa ba Ammh yanzu yadda Nakejin kaina bamai sakani nayi Abunda Ba Ra"ayina bane.."Tafada Tana Juya Ido Abun sai yabama B. kaita Dariya sai da ta dara.
Chapter 15 · 0% Book details