← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 76

Sashe 67

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama Sahura tayi jim tana kallonsu kafin ta kada kai tana Fadin"Shikenan mu shiga ciki..Yaudin ma taron bikin kasim din ake duk mazan suna chan kaduna Sun tafi Daurin Aure basu Dawo ba.."Aisha taji kuka yazo mata tayi Saurin Dannewa Kai tsaye cikin Falon Umma ta kaisu kafin tace su zauna inda yan"uwan Umma ke cike sai ma mama Sahuran wani Kallo suke bata damu ba,ta shiga cikin Bedroom din Umma inda take Zaune iya kawayenta ta gayamata tafito tayi baki cikin Yauki da murna ita uwar ango ta Fito tana Fadin"Sahura Tace nayi baki ina suke..? Kuma Daga ina..?

Tafada tana kallon su Aisha Dake zaune suna bin kowa da kallo Maman Aisha tace"Gamu,Ba dole bane ki sanmu ko kuma ki gane daga ina muke Nidai Sunana Hajiya Amina Daga maiduguri wannan Sunanta Aisha yata ce tare muke da yayanta Auwal yana waje yana Jiranmu."Cikin mamaki Umma ke fadin"Topha Bayin Allah lafiya..? Maman Aisha ta mike tana Fadin"Lafiya ba lafiya ba...Abunda D'anku ya Shuka Muka kawo muku Dukkanmu mu taru mu girbe...Aisha mikomin Jinjiran nan.."Tafada tana mika Aisha Hannu Da Sauri Aisha ta mike tana kuka tana komai ta mikama Hajiya Aminar Jinjiran Dake Hannunta tana jin wani daci acikin Ranta na za"a raba ta da Abunda ta Haifa domin yayanta Auwal yace ko zata mutu sai an kai ma iyayen kasim Abunda ya aikata.

Cikin karfin Hali Hajiya Amina ta isa Kusa da Umma tana Mikamata Jinjiran Dake hannunta Lokaci Daya tana Fadin"Wannan Shine sakamakon Abunda D'anku ya aikatama yata...Ya yaudare ta da kalmar Aure yayi mata ciki Daga baya ya Koreta bayan yace bazai aureta ba bayan ta dawo gida,muka rumgumi kaddarar data Fadamana Aisha dai itace yarmu mun karbeta ammh wannan Jinjiran data fito Duniya Shekaran Jiya bamu da wani Iko akanta shiyasa muka yanke Hukunci kawota inda ya dace.."Tafada tana sakarma Umma ita wacce ta sandare atsaye cike da mamaki tana Bin Hajiya Amina da kallo Lokaci Daya kuma tana bin Jinjiran Dake hannuta idanuwanta kyar tana kallonta ba Shakka wannan Jinin kasim ne domin babu inda ta baroshi.

Gabadaya sai falo ya hargize kowa ya mike yana Salati Mama Sahura ta karisa kusa da Umma tana lekan Jaririyar cikin Zaro ido Tana Tafawa take Fadin"Innalillahi..Ba Shakka wannan Jinin kasim ne.."Take Fada Tana Rike haba Umma kuwa tana Tsaye sai tsiyayan Hawaye take Lokaci Daya tana Zufa kafin kace kwabo ta sulale zata Fadi Mama Sahura tayi Saurin Tare Jaririyar ita kuma cikin yan"uwanta wata ta tareta Sai waje ya Dau ihu da hayaniya,Durkushewa Aisha tayi tana kuka itama Jinjiran jin Hayaniya sai ta Saki kuka mutanen Dake Dayan Falom suka garzayo kowa yazo yaga Jinjira sai ya koma baya yana Kada kai Inna Rukayyah kuwa sai da Taji Guduwa kuka take tana Tsinema kasim Umma kuwa Tuni akayi Daki da ita ta sume ana kwaramata ruwa.

Akaro na Biyu gidan Biki ya sake Rikicewa tarihi zai maimata kansa,Daada da Anty Rahila sai al"ajabi kawai Zubaida hannu ta saka akai ta Fashe da kuka mama Sahura ko Cikin Ranta Dariyan mugunta take ma Umma Allah kara Domin tafi kowa sanin yadda take mata gorin Haihuwa yaya maza tana Fariya da kasim Tun Abunda ya Faru na Farko ta karyata toh gashi ya Haike kuma am Haifa ta ganin ma idanuwanta sai ta goya Shegiya abayanta lokacin ta gasgata.

Ganin gida ya Rikice Hajiya Amina ta ja Hannun Aisha zasu Fice Mama Sahura dake Rike da Jinjirar tana kara kallonta tabisu tana Fadin"Ina kuma zaku..? Ai tafiya bai ganku ba ku jira kadan yanzu nasan duk inda Mazan gidan suke suna hanya Don Allah kujirasu in sukazo ku warware musu komai Waka abakin mai ita tafi Dadi.."Da kamar Hajiya Amina zatayi musu mama Sahura ta lallabesu tajasu chan Shashen Abba kabiru,ta kebe gefe ta Kira Abba garba awaya

Su kuwa suna chan ana ta Fadi tashen neman inda aka kai kasim ammh har zuwa wajen karfe 1 bawani labari ma Dadi Kaf offishoshin yan"Sandan Dake kaduna an bincika babu kasim ba Dalilinsa sun bar komai a Hannun Mahaifin Zainab  saboda yace yana zargin kila yan"uwansa yan siyasa ne suka ma mijin yarsa cinne,su Kuma suka Dauko Hanya cikin Tashin hankali zasu koma suma su bincika Nan suka bar ya muktar saboda shi da tawagarsa zasu wuce Barikin sojoji dake nan 1 Division kaduna sai kuma na jaji akwai Taron da zai Hallata ne Shima kuma yana ta Kiran waya Domin Samun wani bayani

Suna Hanyar katsina cikin Tashin Hankali Abba kabiru kuwa baya magana sai kukan Zucci,harda Haruna suka taho,Hashim ne ke Tausan Abba kabiru domin kadan ya Rage bai Fadi ba suka Tallabosa zuwa cikin mota,Suna Wajen malumfashi sai ga Kiran Mama Sahura tace suna ina ne..? Yace gasu bisa hanyar Dawowa cikin Tashin hankali tace toh suyi maza su dawo gidan biki ba lafiya Cikin Tashin Hankali yake Tambayanta meke Faruwa..?kin sanar dashi tayi sai dai tace kawai akwai mtsla jin haka yasa Abba garba sakin salati yana Fadin"Gamunan zuwa...Insha Allahu."

Koda ya gayama su Abba kabiru Abunda mama sahura tace ba wanda ya kawo wani Abu sun dauka lbarin kama kasim ne yaje musu kusan mata da Rudewa shine gidan biki ya Rude gabadaya.

Kibiya ki karanta cikin salama.

*Anitha....*
8/22/20, 10:24 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

 
*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

      *🅿�37*

"....Sai da sukayi sallar la"asar a Dutsenma kana suka shigo katsina Yadda suka ga gidan ya Haigitse ne,yakara sakasu cikin Zullumi kowanne kagani Fuska ba walwala Auwal Dake Zaune acikin Haraban gidan yayi alwala yayi sallah Tunda Hajiya Amina ta kirashi ta gayamai yadda komai ya wakana.

Ganin Shigansu Abba garba cikin Gidan cikin alamun Damuwa da Tashin Hankali yana musu mgana ko lura dashi basu yi ba yasa ya mara musu baya,cikin Falon gidan suka yada zango inda Mutane ke zaune jumgum,Abba garba ne ya Fara mgana Da Fadin"Rukayyah meke Faruwa ne...?

Inna Rukayyah ta mike tana Share kwallah tana fadin"Garba kasim ya cucemu...Kuma ya Cutar da Zuciyarsa...."Hashim yace"Inna Rukayyah ku kwantar da Hankalinku haryanzu bamu gano wani Station aka kaishi ba balle muji wani laifi ake Tuhumarshi dashi ba.."Zaro ido kowa yayi Umma dake fitowa Daga Cikin Bedroom dinta wata kanwarta na Riketa da ita tace"Sun kama shi ne Alhaji...? Mun shiga uku.."Take Fada tana kuka lokaci Daya tana karisowa cikin Falon.

Abba garba yace"A"a wani zence kuma kuke dabam,Inace labarin kama kasim da akayi awajen Daure ne labari yazo muku.."Gabadaya Falon ya Dau Salati Umma ta sake Rushewa da kuka tana Fadin"Innalillahi...na shiga uku ni karima.."Inna Rukayyah ta karbe da Fadin"Baki shiga uku ba karima goma kika Shiga iyakarki ne Allah ya Nuna miki bayan Dan Shege dan naki ba"asan wata Ta"asar ya kara aikatawa ba aka kamashi..Allah wadaran naka ya lalace wlh.."

Ya Hashim yana bin Umma da kallo Cikin mamaki yake fadin"Umma wani Abu ya faru ne bayan wannan.."?Bata samu zarafin mgana ba Mama Sahura ta Sawo kanta Falon Dauke da Jinjira Bayanta kuma Aisha ce da Hajiya Amina Wajen Hashim ta Nufa ta mikamai jinjirar Tana Fadin"Tabbas....Kun tafi ba Dadewa Wadanan bayin Allah suka zo mana da wani labari...Harda karin Shaidama..."Tafada tana sakar mai yar ahannunsa Da Sauri ya karbeta yana kallonta ilahirin Jikinsa na rawa Saboda yadda Kamanin Jinjirar ya zama kamar Kasim ne sanda yana Jajiri Abba garba da Abba kabiru suka leka suna kallon Abun mamaki Haruna ma yana lekawa ya kafe Jinjirar da ido kafin yayi baya yana karema Aisha kallo wacce ke bayan Hajiya Amina tana kuka ammh idanuwanta Tsab akan Haruna.

Jikin Abba kabiru na rawa yace"Bangane me kuke son Fada ba.."?Auwal dake tsaye Tun Dazu ya kariso tsakiyar Falon yana Fadin"Yakamata ka gane Tunda kaga Shaida...Sunana Auwal ni yaya nake ga Aisha wacce D'anku kasim ya yaudara ya Dirkama ciki da Cewa zai aureta Daga karshe yamata Wulakanci ya koreta...Munyi kuka kamar ranmu zai fita mun sha zagi da Tsangwama Duk akan Abunda Danku ya aikatama kanwata na Daina Fita jama"a saboda Nuni.Nayi alkawarin Duk Ranar Da Aisha ta haihu bazan yi kasa agwiwa ba sai na tattarota munzo mun kawo muku Abunda Danku ya aikata in ma kunsani baku yarda ba Daga yanzu sai ku Fara gasgata hakan..."Yafada cikin Bacin Rai Gabadaya kowa Jikinsa yayi sanyi sai Sharan kwallah.

Abba kabiru yana neman Faduwa Domin Jiri ne ya Debeshi Abba garba ya rikeshi da Sauri ya Zaunar dashi kan Kujera,ya Hashim, kuwa Jikinsa ne ya kama Rawa,Duk da yadade da sanin Mugayen Hallayar kasim ammh baita taba kawo ma kanshi haryanzu bai daina Halinsa ba,Hawaye suka cika idanuwansa ganin yadda Umma ke kuka ita da Zubaida Ga Abba kabiru zaune ya sadda kai kasa bakinciki yamai yawa nanata Sunan kasim kadai yake cike da wani Kunci.

Cikin Dauriya Abba garba yace"Taya zamu yarda daku...? Cewa wannan yarinyar Cikin kasim ne .? Hajiya Amina tace"Jaririyar Dake hannunku bata isa Shaida ba...? Tafada kai tsaye Kai ya Gyada yana Fadin"Eh babu shaida mutum...Wanda zai tabbatar mana da Hakan,kuma kasim bashi anan wajen balle mu Turkeshi ya sanar damu gaskiyan Lamarin..."Baki Bude Hajiya Amina ke kallon Abba garba kafin tayi mgana Aisha ta yaye mayafin kanta Fuskarta ta bayyana lokaci Daya kowa ya saka mata ido.....

Cikin Zubar kwallah take Fadin"Akwai shedan mutum...Kuma yana nan anan wajen.."Tafada kai tsaye tana Kurama Haruna ido da Jikinsa ya Fara rawa,cikin mamaki kowa ke kallonta Mama Sahura tace"Ki fade shi ko kuma ki nunashi kowa ya ganshi.."Aisha tace"Ba kowa bane Face Haruna abokin kasim Domin yasan Alaqata da Kasim kuma ina da Tabbacin Abunda Faru yasan komai Tunda Amininshi ne bai iya Boyemai komai..."Tafada Tana Sharbe Hawayenta.
Chapter 67 · 0% Book details