← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 76

Sashe 54

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da na Shirya kana na Fito Cikin Riga da Sikat,na atamfa Rumgume Juna Mukayi Nida Anty Rahila da Daada Ya Muktar kuwa Fadi yake sannu da kokari Anee ta Bello.."Mirmishi kadai nake ina Satan kallonshi wanda ke Sauraran Hirar Hibba.

Sai da akayi sallah kana aka baje Afalo aka ci Abinci Shidai ne bai ci ba Domin dama baya wani Cin Abinci Sosai yana Zaune Bisa Wheelchair dinsa Yana bin mu da kallo Kuma wani Ikon Allah Dagani har shi ba wanda ya sanar ma da kowa Abunda ya Faru na Zuwa kasim muka ja bakinmu mukayi Shuru.

Kwana biyu su Daada Suka mana,Kafin su koma Bayan sun Biya gidan su Uncle Aminu Sun kara musu godiya Harda Ya Muktar,Komawarsu Abuja dama Tun kafin su tafi Ya muktar ya sa akawo masa Tirela guda na Shinkafa yace Duk arabama Mabukata tare da Addu"ar Allah ya Kara bama Bello lafiya.

Daada kuwa Baffa Hardo ta kira tana gayamai Mirmishi yayi mata yana Fadin"Karki damu...Tafiyarma Lokaci kadan ne zai zama Tarihi..."Daada taji Dadi sosai kuwa nan da nan ta saka Suma Ya Muktar ya aika musu da Tirela guda na Shinkafa da masara da Kudi arabama Dangi mabukata,tare da addu"ar Allah ya kara bama Bello lafiya.

Kibiya ki karanta cikin salama

*Anitha...*
8/19/20, 11:23 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

          *🅿�30*

*AFTER 1 WEEK...*

Duk wanda ya kamata yaji Abun Farincikin Daya samemu yaji Barin ma ni,Gani nake duk wanda bai zo ya tayamu murna ba,ba masoyin mu bane,Hatta Uncle Aminu Dake lagos yazo Yaga Bello ya kara Tabbatar da Idanuwansa Haka suka Sarke hannayen Juna Suna Mgana Cike da Shaukin Abota da kuma Farinciki mai girma.....

Abba kabiru kuwa Abakin Ya Hashim yaji labarin Budewar Bakin Bello bai zo ba sai da ya kira ya muktar din ta waya sukayi mgana hakama Abba garba,Shidai ya Hashim din ne yazo har kano shima bai Dade ba ya koma,Zubaida ce kadai ta damu da Halin da Bello ke ciki ammh banda Zulfa wacce Ta Dinga Godema ma Allah,Inna Rukayyah ma Tunda muka zo kano bata leko ba Tun Muna Abujan ma Sau Daya tazo,ba wanda ya damu Hatta ko Shi Uban gayyar Ya muktar Tunda Abun nan ya faru Hankalinsa ya koma kan Bello toh balle Shi Gwarzon da basa gabanshi da Zuwansu da rashin Zuwansu Duk Dayane shi awajensa,Kokarin da Shakikansa Sukeyi akanshi yafi komai yin Tasiri acikin Ransa.

Bangaren kasim kuwa Haka ya koma katsina yana cizon yatsan Rashin Cimma Buransa kan Aneesa,Da kuma Fargaban Samuwar Bakin Bello tare da Motsuwar wasu sassan Jikinsa,gefe Daya kuma ga Aisha ta dameni shi da kira,Akan wai yazo gida ta riga tagama gayama iyayenta komai akanshi Haushi ta bashi ya Rufeta ta daina samunshi Sam,Yariga yasakama Ranshi bayan Aneesa babu wata macen da zai iya zaman Aure na har Abada da ita sai dai ya Yaudareta yaji dadi da Jikinta kawai.

Kwana Biyu Tsakani Haruna yazo Suka Tafi chan kauyen Niger Delta suka samu Bokan Suna mai Complain Abunda ke Tafe dasu ya dade yana Dube Dube kafin ya kora musu Bayanin Halin da"a ake ciki ya sanar dasu Aljanu sunyi kyau Sosai akan Bello Domin Jaki ne Da Ranshi aka Binne Acikin kasa bayan An Cire ransa ankawo masa nan ya Asirceshi kuma yana Sarrafa Numfashinsa Tunda Sunce basu bukatar Bello ya Mutu yanzu suna Bukatar yaciga da Rayuwa ahaka har Abada.

Ya sanar dasu sakamakon Addu"o" da kuma Tsarin Dake jikin Bello shi yake Dakula Sihirin Har Jakin Dake cikin Rami yake iya Motsi da hannayensa ya kuma Iya bude baki yayi kuka,Shine Dalilin daya sanya Bello bakinsa ya Bude Ammh ya sanar dasu su kwantar da Hankalinsu Bello bazai taba Takawa ba matukar ba"a hako wannam Jakin Dake Cikin Rami ba,Wanda kuma ba Mutum bane ya binne ba Aljanun ne suka yi aikin Saboda Haka karsu damu Su koma kawai su zura ido Bello Haka zai kare rayuwarsa Sai Ranar Daya mutu.

Da wannan Lbrin suka juyo gida,Kasim yaji Dadi dama Baya Burin Bello ya warke domin in ya warke Har Abada bazai Samu Aneesa ba,Daya sanar da Haruna Zuwanshi kano Fada ya shiga mai kan yayi kuskure Babba Da"ace Lokacin da su Modibbo suka Shigo sun kamashi Dumu Dumu fa ya zai yi..? Bafa zai taba Fita ba Har Abada,Shidai Kasim Ba wannan ne agabanshi ba yadda Aneesa zata dawo mallakinsa ne kadai ke yawo Acikin Ranshi..

****
Abubuwa Dadama na Dawainiyar Bello ta ragu Domin yanzu da kanshi zai Tura kansa Zuwa Tiolet in yana cikin matsuwa Tunda Wheelchair din nashi mai amfani da Abunda zaka danna kacigaba da Tura kanka ne,sai dai in yana Bukatar wani Abu ya kwalama Aneesa Kira tazo ta mikomai ko kuma ta taimaka mai yatashi,koda Bakinshi ya bude Bai cika yawan mgana ba,Halinsa na nan ya Dawo sai dai yayi ta nacin kallona,yana Min mirmishi Wani Lokaci..

Ni kuma sai na rage Shigemai ganin,haka ba kamar baya ba,Sai dai ban fasa Duka Abubuwan Danike mai ba,Yanzu na Rage zama dashi ina mai hira kamar baya sai dai na barsa da Modibbo afalo ni da Raihana mu Shiga ciki muyi ta Hira,sai in tatashi tafiya Modibbo ya maidata gida,Miskilansa na nan In kaga ya bude baki sai in yana Bukatar wani abu ga wani mugunta Daya samu sai nazo wucewa ta gabanshi ya saka hannu ya Rikoni lokaci Daya ya Fizgoni Zuwa kan Jikinsa,Ina jin kunya da Nauyi sosai shi kuma ko Ajikinsa sai ma saka Hannu da zai yi ya Rumgume Ni Ya saka kaina Bisa Kirjinsa yana Sauke Numfashi haka zamu Dauki Lokaci sai yayi Ra"ayi don kanshi yake sakina,lokaci Daya kuma ya Hade rai ko kuma ya kauda kai,Yafi son zama abedroom ko yaushe in ba Modibbo yafito dashi Falo suna Hira ba..

Samuwar Hannnayensa Sai laptop dinsa ta koma tana Debemai kewa,Sai na Doramai ita Bisa Cinyarsa yayi ta kallensa kallensa aciki wayarsa ne dai har yau take akashe,Ranar ma wayata yace na bashi bansan me zai yi da Ita ba Ashe gabadaya Hutunan mu da na dinga mana Lokacin Baya Duk ya Maidasu cikin laptop dinsa ban sani ba,sai ranar mun shiga zan taimaka mai yayi wanka Bayan na Fito tunda nakan Shiga na Taimaka mai da wani Abun ina Cikin gyaramana Gadon,na Daga hannu zan Dauke Laptop dinsa na ci karo da Hoton mu Nida shi wanda na Taba Daukanmu Ina ta baya na Sunkuyo da kaina ina Dariya na Daukemu Shine ma akan Fuskar Laptop din baki na Rike ina Tunanin yaushe ya samu wannan Hoton,Ban mai mgana ba na Rufemai na Ijiyemai saman Side Drower ina Tunanin kona mai mgana ma bazai bani amsa ba Sanin Halin gogan nawa miskilanci da Aji.....

Haka Ranar Babu kowa agidan Modibbo ya Fita kuma Raihana bata zo ba Ranar Ammi bata jin Dadi,da mukayi waya da Safe ta gayamin inajin ma Chan Modibbo ya tafi domin Bangane musu ba Dagashi Har Raihanar,Bayan na gama gyara Falon na tsaftace kichen din na wanke Abubuwan da muka taba,Na koma cikin Bedroom din ina Sauri yau ban taimaka mai yayi wanka ba Nima Tun na Asuba ban karayi ba,Yana Zaune kan gado ya Jingina Bayanshi da Filo guda Daya,Laptop ne agabansa yana latsawa,ina shiga ban tsaya ba na shiga Tiolet na Hadamai Ruwan wanka na Fito ina Cire karamin Hijabin Dake jikina,Wanda na Dora Bisa Doguwar Rigar Dake jikina mai Hannun Vest.gashin kaina ya bayyana kalaba ce wanda Raihana ta kamamin Tunda bana son kitso kwata kwata.

  Cikin Sanyin Muryata nace"Muje ayi wanka ko..? Na fada ina kallonsa Lokaci Daya ina Tura Wheelchair din gabansa,bai dago ba illah yayi man Banza na kallesa cikin mamaki Lokaci Daya na Tura baki ina Fadin"Mgana fa nake..? Bai kalleni ba yace"Shiwa kike ma mgana...? Yafada cikin Husky Vioce. ..

Ware ido nayi ina Kallonsa kafin nace"Kai mana..."Na fada cikin Shagwaba Mirmishi yayi kafin ya Dago yana Fadin"Ni wa..? Na lura tun bayan fara mgana ta kika daina kiran Sunana mai ma kike cemin B.luv ko..? Yafada yana min Wani kallo kasa kasa Baki na Rike ina Zaro ido kafin na Juya ina Rufe Fuskata cikin Kunya Tattare Naman goshinsa yayi yana Fadin"oya come here..."

Yafada cikin Muryan Amo,cikin Sanyi jiki na karisa gabanshi na Tsaya ina kauda Fuskata laptop din ya Gauda Daga Gefensa Tunda baya iya lakwashe kakafunsa sai dai ya mikar Tunda su haryanzu baya iya amfani dasu,ban ankara ba naji ya saka hannu ya jawo ni Jikinsa,ido na Zaro ina Binsa da kallo Shima ni yake kallo,mutsu mutsu na Fara yi Jina kusa da abar Domin naji tana harbawa Tsakanin Cinyoyina da kuguna.

Sake rikeni yayi kafin ya matseni Sosai har na kwanto Bisa Kirjinsa ina Sauke Numfashi jin Ina Shiga Cikin Wani yanayi Muryata tana Sarke na Dago ina Fadin"Kar na..Zauna kan kafarka tana ci..."Bai bari na karisa ba ya aza lebensa bisa bakina Lokaci Daya yana kallona,Ban iya motsi ba Illah jikina Daya fara rawa Idanuwansa ya lumshe kafin ya Fara Tsotsan Lebena na sama yana Hadawa dana kasa cike da kwarewa nan da nan Jikina da Zuciya ta suka Fara karba sokonshi Tallafemin keya yayi nikuma na Rike Rigar Jikinsa da Wuyamsa ina karban sakonsa Cikin Fitan Hayyaci,

Hannunsa Daya ya maida Bayana yana Shafani Daga Saman Wuyana Zuwa kuguna,yana min tafiyar Tsutsa Tuni na Rikice na sake Rikeshi ina makarkyata Jin yadda yake Shafa Tsakiyar bayana da Babban yatsanshi,kila ganin ina neman Fita Hayyacina ne yasa ya Sakarmin baki yana kallon Cikin idanuwasa runtse ido nayi ina Rike da Rigar Jikinsa da Hannuwa na Biyu Cikin Rawar Murya nace"Zan ta...shi..."

Nafada lokaci Daya Ina jin Sarkewar Numfashi,Kansa ya maida Cikin kunnina cikin Sarkewar Murya ya Furta.."Ai bam hanaki ba,madam ke kika Ji Dadi kika Rikeni ko baki gani bane..? Yafada yana sakin yar Dariya.
Chapter 54 · 0% Book details