← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 76

Sashe 64

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raihana ta rage zuwa gidana yanzu saboda Dagani Har Bello bama kunyarta muna manne da juna ita kuma kunya ke sata bata zuwa kana kuma Habibin nata baya nan yana Adamawa wato Modibbo,Satin mu biyu da dawowa Sai ga B.kaita da S.jibiya sun zo min dukkansu zasu koma makaranta ne nan muka wuni muna Hira da Shewa sukayi ta Zuzuta kyan da nayi da kiba nidai sai dariya domin nasan gaskiya suka Fada Namiji ya budani na zama wata Big mama

Wajen la"asar S.jibiya ta shiga mota zuwa katsina ta koma Makaranta B.kaita kuma sai Dare,kana ta koma cikin Makaranta Ita da yar"uwanta Aliya,suka barmu nida B.love dina muka Dasa Daga inda muka Tsaya akullum wani Sabon kulawa muke bama juna kamar zamu lashe juna saboda so da kauna Duk da mukan samu sabani ammh bama bari yayi tsawo zamu bama juna hakuri saboda bazamu iya taba Rayuwa babu Daya Daga cikin mu ba.

Bello ya Dubomin Result dina nima na samu Duka 9 creadit din Da"ake Bukata bai ce min komai ba ammh yace akwai Shirin Daya ke mana ne kila na Fara karatun anan gida Nageria in kuma Shirin nashi ya Tabbata ko na Fara sai dai mu koma Abraod na cigaba,Nayi murna sosai Domin Nima ina bukatar nayi karatun Tunda na Fahimci makullin komai na rayuwa sai da Ilimi.

Modibbo yana Adamawa Raihana tatafi Sch of hygen tatafi da Sati Daya,kana shi kuma ya Dawo yayi ta Cizon yatsa Duk da Suna mgana ta waya shima din muna Dawowa Daga Hajji zai wuce Military sch Jos,Tunda angama komai Dama Abunda ya Dakatar da Ya Muktar Rashin lafiyar Bello yanzu kuma Tunda ya samu lafiya sai ya cikamai Burinsa.

*****

Aisha kuwa Haka ta isa maiduguri tana kuka kamar Ranta zai Fita tayi alkawarin bazata Boyema mahaifiyarta komai ba ita da w'anta wanda dama mahaifinsu ya rasu yayanta ne ke rike da ita,da ita da Mahaifiyarta

Sun kansu sunyi kuka da Jin wannan Labarin sun kuma yi Tir da wannan Soyayyar da Aisha kema Kasim,Nan mahaifiyarta ta bada goyon bayan Aisha ta Haifi Cikin Jikinta Tunda tasan Uban da yayi mata cikin in ta haifeshi zasu Daukeshi su kaishi inda ya Dace.

Aisha tayi nadamar Biyema Soyayyah da Sharin Zuciya daya kwasheta ta Biyema kasim ta lalata Rayuwarta Kullum Cikin kuka take da Neman gafaran Ubangiji Inda Allah ya Taimaketa Mahaifiyarta bata juya mata baya ba,gwara ma yayanta din yana cikin bakincikin Abunda ta aikata ko gaisheshi tayi baya amsawa,toh ya zasuyi Hannunka baya taba Rubewa ka yanke ka yar....

Haka Aishaa ta cigaba da Renon Cikinta,Tsakaninta kuwa da Kasim ya yanke duk wata alaaqa da Ita Tuni ya goge Nombarta acikin wayarsa ita kuma gabadaya Layin ta chanza Saboda bata kaunar Duk Abunda zai Tuna mata da Rayuwarta Bata Fatan Wata mace ta sake Tafka kuskure irin nata,Duk yadda suka so boye Abun sai da ya bayyyana sun sha mganganu da Zagin makota Harda masu Shigowa ganin kwaf,Aisha tayi kukan yadda ta saka kanta da iyayenta Cikin damuwa ammh acikin Ranta tana kara Tsinema kasim da Fatan Allah ya saka mata akan Abunda yayi mata.

****
Dawowarmu da Sati Hudu aka Fara Azumi,modibbo na nan Tare damu a kano,Wata rayuwa muke gudanarwa mai cike da Sha"awa,har akayi azumi aka gama muna kano Da sallah ne muka Sha yawo Nida Bello mune har Borno Sai da muka kwana uku kana muka Dawo,Sai gashi har maiduguri munje gidan Anty Nafee tayi murna sosai Kunsan Ita tana bala"in so a girmamata,Da zamu tafi muka cikata da kayan arziki,Su ya Ali sunyi Murna da Zuwana ganin na kara kyau na Zama babbar mace Uwa uba kuma Mijina bai iya Boye Soyayyar Dayake man Ko agaban ko waye Mahaifiyata tafi kowa Murna ganin Inganta rayuwata Ni kaina naji Dadin Zuwan mu gida Daki na musamman aka ware mana muna cin Duniyarmu da Tsinke Nida Bello,munyi kiba mun chanza kamar bamu ba.

Har Ibadan sai da muka je,gidan Anty Yagana muka kwana mata Biyu ita da mijinta Sunyi murna da ganinmu,Haka muka Zauna anata Hira muna Tuna baya Mijin Anty Yagana nabama Bello Labarin Tsiyar danayi Lokacin da aka kawoni Ibadan na Zauna Dasu sai dariya nake ina Tuna Lokacin acikin Raina na Shaida lalle nayi Rayuwa,Bello kuwa sai dai ya kalleni yana Mirmishi Domin kaf halayan na ba wanda bai sani ba kuma ba wanda ban gwadamai ba.,Sanah na nan Ibadan tana Wajen Anty Yagana ta kara girma ta zama babban Budurwa Duk da tana da Girman jiki.

Munsha yawo Sosai bayan mun dawo kano Har kaduna muka je gidansu Sani Tayashi Murnan Aure yayi Aure Lokacin Bello na Zaune baida lafiya Shima yayi murna da ganinmu dashi da amaryasa mai kyau Mariya bamu so kwana ba Suka matsamana sai da muka kwana Washegari kuma muka Dawo gida Sai da muka Huta kana Mukaje gidan Anty Aisha na Wunin mata Shi kuma Bello suka Fita da Megidanta sai Dare suka Dawo sai da mukayi Dinner kana muka yi musu sallama muka koma gida.

Rayuwarmu gwanin ban Sha"awa ga wanda ya ganmu Bello dai ke ta complain din ya kosa na samu ciki,ni kuma bana son na samu ciki nafi so sai munje Hajji mun Dawo kana kada mafarkina yaki Tabbata na Ganina gaban Dakin ka"aba.

******

Shiryen Shiryen Tafiyarmu Hajji ta kankama sosai,Dayake zamu Tafi da wuri ne,Madina zamu Fara isa,Shiyasa Duk Abunda ya kamata komai ya kammallah ta Abuja Dukkanmu zamu tashi,Ana saura kwana goma Tafiyar tamu ya muktar ya samu Waya Daga Abba kabiru yana sanar dashi kasim ya samu matar aure in bazai damu ba kuma baida wani Uzuri zai jagoranci Tafiya zuwa kaduna domin Nema masa Auren,Ya muktar bai damu ba yace ba matsala indai nan kusa ne Saboda zasu tafi aikin Hajji sati na sama,sai lokacin Ya muktar ke Fada ma Abba kabiru Warkewa Bello da Dalilin Tafiyarsu makka..

Abba kabiru yaji Abun kamar almara,sai dai kuma ya Shanye mamakinsa,Shi ya kira Abba garba yana Fadamai shima yaji mamaki sosai Acikin Zuciyarsu Tsoro ya Darsu,basu nuna ma bane,Jin haka yasa Suka gaggauta Shirya tafiyan Saboda Suna so Muktar ya jagoranci Tafiyar Tunda Shima wani ne akasar kamar yadda mahaifin yarinya Shima sananne Tunda Dan Siyasa ne.

Ana saura kwana Biyar Tafiyarmu Su ka tafi kaduna nema ma Kasim Aure wanda ba wanda ya sanar dashi warkewar Bello shi azatonshi Haryanzu yana nan Jiya yau saboda Dogara da Maganar Boka.,Dayake ba yawan Zuwa gida yake baida labarin Wasu abubuwa ya Hashim ne shima Sabgogi sun mai yawa bai cika bi takan kasim din ba...

Bayan tafiyar Aisha da wata Biyu Kasim ya hadu da Zainab yar kaduna ce gaba da baya anan anguwar kinkinau,take mace ce kyakyawan kin kowa kin wanda ya Rasa,Tunda mahaifiyarta Bafullatan Yola ce,Lokacin da suka hadu harta kammallah Digree dinta Service take shine aka Turota wajen aikinsu Kasim shikuma ya na ganinta yaji zai iya Auran Zainab bayan Aneesa,Lokacin Daya gabatar da kanshi bata mai gaddama ba Saboda yakai karshe Wajen sace Zuciyar yan mata,Nan da nan suka Fara soyayyah wanda yake jin kamar ma bai taba son wata ya mace ba,sai zainab gata tafito Daga Babban gida Suna da Kudi na Rufin Asiri.

Basu wani jima suna Soyayyah ba Babbanta yace ya Fito Shine Dalilin Daya sanya yaje katsina ya sanarma Abba garba wannan karon Umma tafi kowa murna Domin Har katsinan Kasim ya kawo mata Zainab suka ga Juna ta yaba da ita sosai ga kyau da Hankali ga Nasaba,tayi ta yabonta tana Fadin ko shi fa yanzu ya zabo Abu mai kyau ba wanda yayi Tunanin kasim ya cigaba Da hallayarsa Haruna ne kadai ya sani Shima abokin Shamshancin nashi ne Duk da bai kai Kasim zama Bunsuru ba.

Zuwan ya muktar ya karama musu kima sosai Chief army of Staff na kasa baki Daya Dole akayi komai cikin girma Sadaki Dubu Dari uku Ya muktar ya Biyama kasim su kuma suka Fito da kayan saka Ranar da suka zo Dashi nan take aka saka Ranar Auren nan da wata uku masu zuwa In Allah ya yarda Aka Rabu Cikin Aminci da mutumtawa Haka suka dawo da labari mai Dadi dama su uku suka Tafi Ya mukrar ya Hashim da Abba garba.

Kasim Daya samu labari yashiga Farinciki kansa ya kara Fashewa Jin Zainab na Zuzuta Danginsa masu arziki ne da Sanin yakamata,Ya gama sankanceewa wannan karon kam zai Tubanma Allah ya rage neman mata duk da bawai ya Daina Duka bane,Sai Shaye shaye shikan duk dare sai yayi Tatul yake iya barci bai taba Tunanin wani Abu zai kara Faruwa Dashi ba shiyasa yakara Sankankacewa zai mallaki Zainab Hankali kwance,Aneesa kuma ya Tarrata ya maidata gefe Duk da haryanzu bawai ya cire rai da Ita bane.

*****
Ana gobe tashin Jirginmu Mallam Inuwa yaje ya Taho da Baffa Hardo,Tun safe kuma Su Ya Ali suka iso da Mama yana da Mama Falmata da Ya Sunusi matansu na gida zasu kula da komai kafin su dawo Mu kuma sai Dare muka iso Nida Bello da Modibbo washegari kuma karfe 6:00pm na yammah Tawagar Ya muktar suka kaimu Filin Jirgi Nmandi Azikiwe international Airport Atafiyar Hibba ne kadai da Junior yara,suna Rike wajen iyayensu ni kuma ina Sanye da Bakar Abaya na Nade kaina da bakin Vail din rigar jikina Ajirgin yawo zamu Tafi jirgin na musammane domin Ina Rakube Jikin Mijina,Ya muktar da Ya Ali da ya Sunusi suna tare sai Daada da mama yana da mama falmata sai Anty Rahila ita da Hibba sai modibbo da Baffa Hardo junoir na wajen Babanshi.
Chapter 64 · 0% Book details