← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 76

Sashe 38

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakyar ya amsa yana Wani Cije baki aranta tace lalle ne ma kama samu ne na gaisheka ne,,Daganan Salihu maigadi sai Shigo da kwalayan Abu yake da buhunhuna da Ledoji Wajen Sahu Uku Kana yagama,Bai mata mgana ba Itama bata kara bi ta kamshi ba ya Dai Shiga kichen Bai Dade ba ya Fito Da Apple Ahanunsa da Madaran Hollandian ya Shige Bedroom dinsa kana tayi Wuf tatashi ta Fada Kichen din Nan Taga Store Abude Shake da kaya Abunda ya bata mamaki Duk Abunda ta Rubuta sai da aka Siyosu,Dama already kichen din Fridge guda biyu ne,harda Freezer sai ta jera Duka Abun Amfani Wanda bazai yi Saurin lalacewa ba kamar su Kwai da Sauransu,aya da Dabinon ma Aciki ta saka Dayan kuma ta jera Ruwa da Madaran Hollandian sai Maltina da kayan Fruit wands ita basu dameta ba tasan kayan Bello ne,Su maggi kuma ta Zuzzuba su Cikin Wasu kananam Robobi data gani a Drower din Kichen din,komai dai ta sakashi Amullalinshi Tayi murna Data ga Harda Fulawan Datace ya Siyomata,abinci su na Kanuri ne Dai bata ga ko Daya ba Acikin Ranta tace"Ahakan ma Ni keda Godiya Mr Bello.

*****
Sati Daya kenan Da zuwansu kano Tunda ga Ranar Daya Siyo mata kayan Abinci Wata Mgana bata kara Hadasu ba,sai ma ta kwana bata sakashi a idoba sanda Zata Fito daga Daki har ya Fita Wani Lokacin kuma Tana Daki tana sallar Isha"i zai Shigo Babu Ruwanta Dashi baya Neman ta itama baya gabanta,Iyakarta tatashi da Safe ta musu Abun karyawa ita da Megadi ta fita takai mai nashi itama taci nata,Tana Share Duka Dakunan Dakinshi ne bata taba Shiga ba Wani lokacin ma Tafi zama Afalon Farko, girki ko bata iya ba sai ta kwabashi Hakanan Don ma Wasu girken girken zamani Wajensu su alheri ta koya wasu koma amkranta Kafin Sati Dayan Aneesa ta sake cika tayi kiba Tunda tana cin Abinci mai kyau ta kwanta Waje mai kyau bata da Damuwar komai sai kewar su Daada gashi bata da Waya Ahannunta abokin Hiranta Shine Tibi Ta Wuni tana kallo bata gajiya.

Shiko Bello kafin ya Rufe Sati Amakarantan BUK sunansa ya Zaga ko"ina barinma Department Dinsa na Mathematics,Yan mata Dadama Kamar su sume saboda ganinsa,Gashi ya iya koyarwa duk Dakikanci ka in har ya koyar dakai sai ka gane,fa iya Sarrafa Harshe Wajen Turanci kace wani mangafok ne,Ga iya Dressing ga Aji da Zati komai dai ya Hada,cikin Lokaci sunansa ya Zagaya cikin Jami"ar ta bayero Kowa sai labrin Sabon malamin Dapartment din Lissafi yake The young Teacher Mr bello muhmeed Jikamshi,Tunda ya Fara daukansu karatu bai yarda Mu"amala ta Shiga Tsakaninsa da Kowa ba ko Acikin Hall din karatu Fuskarsa ba"a sake take ba,abunda ya kawosa kadai yake yi ya Fita ya basu Waje,Tundaga Yan level 1 har Zuwa High clss din yana Dauka kafin Ya Rufe Satin Wasiku sunfi goma Cikin Office dinshi na masu son Kulla Soyyayyah dashi Baya Damuwa Domin Tunyana Makaratan kwatar kwashi yasaba da Irinsu.

*****

Washegari Ta kama Jummatu Babban Rana ne,kuma garin Antashi da Ruwan safe ne sakamakon lokacin Damina ne,Aneesa tana jin anfara Ruwa ta Sake Shigewa cikin bargo barcin na kara mata Dadi ba Ita tatashi ba Sai After 10 lokacin Ruwan yadan Tsagaita,wanka tayi ta Shirya Cikin Doguwar Rigar Material mai kalan ja da Baki ta Nade Dankwalin kayan Bisa kanta yayi Tuntu saboda Gashinta Data Tsife ta Daure da Band, ..

Kichen ta nufa tana Duba Abunda Zasu karya dashi,Dankali ta Fere ta soya musu da kwai sai Tea da Soyayan Biredi da kwai,sai da tafara mikama Megadi nashi kana ta Dawo Falo taci nata Hankali kwance duk Zatonta Bello ya Fita baya gida,Wuni Tayi Afalo tana kalle kalle sai Wajen la"asar kana ta koma Daki tayi sallar la"asar ta sake Fitowa Abunda yabata mamaki Shine Data Fita Falon Farko Ta Bude windown Falo Iska ya Shigo Domin Nefa sun Dauke Wuta kuma Falon Farko yafi Iska Motar Bello Ta Hanga Aharaban Gidan Sai da Taji gabanta ya Fadi Haka Kurum Taji Jikinta bai bataba, Dama bello na nan ne ko kuwa dama yanzu ya Shigo,Ganin bata dame bata amsa yasa ta koma ta kwanta Bisa kujera tana Tunanin Zucci.

Karfe Biyar na yammah ta Tashi ta Sake Labulen Windon nan Falon ta koma Falonsu,kichen ta koma ta Dafa musu Taliya da Miyar Kifi,ta Zubama Megadi bata kaimai ba sai da ta koma Daki ta yi wanka Tayi sallah kana Ta Fito ta saka Mayafi ta kaimai Bayan ya karba ne yana Godiya har Zata tafi taji yace"Hajiya wai ni ko Alhaji Lafiyanshi kuwa yau kwata kwata bai Fito ba..?

Gaban Aneesa ya Fadi ta Waiwayo Tana kallon Salihu megadi Karo na Biyu gabanta ya kara Fadi Dakyar tayi Dariyan yake batasan Sanda bakinta ya Furta"Bayajin dadi ne ammh yaji Sauki,"Cikin Jimami Salihu maigadi ke Fadin"Ayyah..Haba koda na gani yau kwata kwata bai Fito ba Allah ya kara Afuwa.."

Bata samu Zarafin amsamai ba ta Wuce Zuwa Cikin Gida gabanta Haka Kurum ke Bugawa,Koda ta koma Falo tatasa Abincin gabanta Haka kurum Jikinta ke bata ba lafiya Wata Zuciya tace"Karki damu kanki kinsanshi da Shigen zaman daki kamar mace.."Fara cin Abincinta tayi ammh kuma Wata Zuciyarta na Cike da Fargaba bata wani ci sosai ba ta mike ta kai Kichen ta Rufe ta wanko Hannu ta Fito Har zata Wuce daki sai taji kamar Zuciyarta najanta ta Shiga Dakin Bello batare Data sani ba kawai ta Juya ta Tura Kofar bedroom din nashi sai kuma gashi ta Bude Cikin Karamar sallama ta Tura kai Dakin Tana dan kalle kalle.

Gabanta ne ya Harba da karfin bala"i ganin Bello Kwance Akan gadonsa Yana kallon Silin,Irin kwanciyan Dayayi ne ya bata Tsoro,tana Shigowa ya Wulgo idanuwansa yana kallonta,Daga bakin kofar ta tsaya tana Kallonsa Cikin mamakin ganin Idanuwansa Sunyi jajir,kwallah Duk ta Bushemai ta gefen Fuska Domin Dakin yana gauraye da Haske.

Harda Zata Juya tatafi sai kuma ta Fasa tasake Waigowa tana Fadin"Ashe lafiyanka kalau.."Tafada Tana kallonshi bai iya mata mgana ba sai dai Taga ya Lumshe ido lokaci Daya Taga Wasu Hawaye sun Biyo gefen Kunnansa,Zaro ido Aneesa Tayi tana Kallonsa Cikin mamaki da Faduwar gaba Cikin Sarkewa murya take Fadin"baka da lafiya ne...? Tafada tana Kuramai ido Ammh sai taga ya kara Rufe idanuwan ya Bude Wasu hawayen sun sake Zubowa su suka kara sata tagane ba lafiya domim ita bata taba ganin kukan Bello ba Tunda take dashi.

Da Hanzari ta karisa kusa dashi ta Durkusa ta Dora Hannunta gefenshi Taji Wajen ya Jike da Ruwa,idonta takai Wajen tana Dubawa lokaci Daya Ta Taba Kayan barcin Dake Jikinsa Jike da Ruwa,harda Zarni na tashi Hannunta takai hancinta Lokaci Daya ta Zaro ido  "Fitsari kayi akwance..?"Tafada Lokaci Tana kallonsa,yana so yayi mgana ammh bakinsa kamar an Daure yana so ya motsa hannunshi ya kasa,yana so ya tashi,shima ya kasa ga mganar dayakeso ya Fada Tana Cikin Zuciyarsa ammh Ta gagara Fita Daga Harshensa,kansa ne yake kokarin Dagowa sai ya koma ya langwabe gefe Miyan bakinsa na Zuba Dalala lokaci daya Hawaye yana Fitowa Daga Cikin idanuwansa.

Aneesa Dake kallob yanayinsa,Kirjinta na Dukan Tara tara tace"ka kasa tashi ne..? Kokarin Dagamata ido yake ammh ya kasa,Riko Hannunsa Tayi Idanuwanta Sun Cika da kwallah tace"Kamin mgana mana Uncle Bello meya Faru dakai..? Bai iya mgana illah hawaye kawai yana binta da ido Lokaci Daya bakinsa na Zubar da Miyau,Aneesa Taji kuka ya kamata ta Fashe dashi Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna ilaihirraju"un...Karda ace kadaina Mgana,kadaina Tafiya na Shiga uku ni Aneesa.."Tafada Tana Kara sakin kuka,Shima Hawayen yakeyi yana kallonta Lokaci Daya Hallitarsa ya Chanza ya Dawo kamar Wani Gaula.

Gabanta ke Fadi Fat..Fat..Tana kallonsa tana Share kwallah Afili Tace"Allah kenan...Garesa mukazo kuma garesa zamu koma.."Take Fada Wani Tsausauyin Bello na Ratsata na ganin yadda ya koma Lokaci Daya Mr bello fa Shine a kwance Cikin Fitsari bakinsa na Zubar da Miyau kilama Tun Kwanciyaar jiyane Abun ya Sameshi,Hada kai tayi Ta gwiwa tana kuka Wurjajan Tana Tunanin Wajen Wa Zata kai kukanta Wajen wa zata Neman Taimako.?

Wayarsa Dake kan Side Drower din gadon Ta Shiga Neman Dauki,Da Hanzari Aneesa Tadago tana Hawaye ta Dauki Wayan,Bata gane Sunan mai Kira ba Domin Hankalinta Baya jikinta Da Sauri Ta Daga Kiran Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka...

Cikin Firgici da Taahin Hankali Muktar Dake gaban Daada d Anty Rahila yace"Aneesa ta Dauka ki wayar kuma tana kuka.."Kuka Daada Ta Fashe dashi Lokaci Daya tana Fadin"Haba ni naji ajikina Wlh Wani Abu ya Faru da Bello ko Aneesa.."

Cikin Tsoro da Tashin Hankali ya Muktar yace"Aneesa Ki daina kukan nan ki sanar damu meyafaru Tun Wajen karfe 2pm na rana nake Kiran Lambar bello baya Dagawa Gabadaya Hankalinmu ya Tashi meya Faru ne..? Cikin kuka Aneesa Ke Fadin"Bazaku sameshi ba Ya Muktar..Yana jin kana Kira ammh bazai iya mika Hannu Ya Daga Kiranka ba.."

Cikin Tsoro ya Muktar yace"Innalillahi meya Sameshi..? Yafada yana Jin Zufa na ketomai Daada ko kuka take Anty Rahilama Tashiga Tashin Hankali Cikin Sharbe Hawaye Aneesa dake kallon Bello Take Fadin"Ya Muktar Uncle Bello ba ya iya Tafiya ba iya mgana baya iya motsa kowata gaba ta gangan Jikinsa Sai da ido kadai,ko Fitsarima akwance yayi kuzo ku Taimakamana Don Allah..."Take Fada Tana Gunjin kuka Shima Bellon Dake Jinta Hawaye yake Lokaci Daya miyau na kara Dala la Daga bakinsa

Gabadaya ya Muktar da Daada da Anty Rahila Suka Dau Salati Domin Wayar Tana Speaker ne,zamewa Daada Tayi ta Zauna Tana Fadin"Innalillahi Wa"inna Ilaihirraja"un...Wani irin lamari ne ya Faru da Bello...?

Ki biya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
     
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

   
           *🅿�21*

Dafe kai ya muktar yayi lokaci D'aya yana Fadin"Innalillahi Wa'inna illaihirraju"un..."Anty Rahila ko kasa Tayi Ta Dafa Daada tana hawaye,Daada ko kanta ta Dafe tana Sharban kuka tana Share Hawaye da Gefen zaninta.
Chapter 38 · 0% Book details