← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 76

Sashe 68

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo sai yakoma kan Haruna Ya Hashim ya kallesa cikin Rauni yana Fadin"Haruna me ka sani game da Abunda ya Faru..? Karka boyemana komai Duk da ni Tuni Zuciyata tagaama yadda da komai Tun bayan Tozali Da nayi da wannan Jinjiran.."Haruna yayi kasa dakai yana Share Zufa kafin ya Fara Bada labarin Duk Abunda ya sani tsakanina da Kasim Har zuwa Wulakancin Dayayimin ya kirashi yana Fadamai ya karishe da Fadin"Kuyi Hakuri ammh zencen gaskiya Abunda iyayen Aisha da ita kanta suka zo dashi gaskiya ne.."Gabadaya waje sai ya kara Kaurewa da Hayaniya masu Salati nayi masu kuka nayi.

Cikin Fitan Hayyaci Umma ke Fadin"Mun shiga uku..Yanzu ya zamuyi da wannan Jaririyar sabuwar Haihuwa bata da laifin komai bayin Allah Don Allah ku Debeta ku Tsausaya mana ."Auwal yace"Ba wannan Mganar Na Rantse da Allah Aisha bazata koma mana gida da wannan Yarinyar ba...Taku ce mun Kuma zo mun Damka muku amanarta...In mahaifinta yazo kuma ku sanar dashi...Hakkin Aisha bazai taba barinshi ba..Mun barku lafiya,Aisha Mama muje..."Yafada yana Juyawa suma suka Rufamai Baya Aisha tana kuka jin Nononta yadda yake Zuba Saboda cika Umma na kuka Inna Rukayyah ta mike zatayi mgana Abba kabiru ya Dakatar da ita da Fadin"Karki ce komai Rukayyah barsu...Su Tafi Abunda suka aikata Shine Daidai...ko ahaka Allah ya bar kasim yagama Nuna mai Ishararsa...Ni bai cutar dani ba kansa ya Cuta kuma ya Zalunta Wanda muka ji kenan bamu san kuma wani Aika aikar ya sake aikatawa ba aka kamashi...Nidai Allah na gani Ban bama kasim irin Wannan Tarbiyar ba ban kuma san ina ya Koyota ba.."Yafada yana Dauke Siraran Hawayensa.

Kowa Sai mutuwar Jiki,Jugumjugum ba mgana Umma kuka kawai take bamai Rarrashinta Daga karshe Abba kabiru ya mike yana layi ya Fice Abba garba ya maramai baya Hashim kuma ya mikama inna Rukayyar Jaririyar taki karba Tana Fadin"Mikama Uwarka..Ta Fara Rike sakamakon Hallayarta...Bani zaka bamawa ba.."Bai kalleta ba ya Waiwaya inda Umma ke zaune tana Kuka bai Kalli barayinta ba ya mikama Mama Sahura tasa hannu ta karba Tana Fadin"Allah Sarki...Bataji bata gani ba kinzo Duniya cikin Wahala..."Ba wanda yabi Takanta mazan duk suka Fita zuwa Shashen Abba kabiru kowa ya zauna ya Dafe kai cike da Tashin Hankali,umma kuwa ita keda kuka Inna Rukayyah kuwa Fada take tana saka mata mgana Mama Sahura ne ta Dama madara ta bama Jinjirar ta kama ta goya sai ga yan"uwan nata yabonta wanda abaya sune kan gaba wajen zaginta,Umma dai ba baki sai kuka Zubaida ma Kukan Take Hatta Zulfa sai da Abun ya Daketa.

Su Daada da Anty Rahila sukayi Tsuru da ido Tsoron Allah ya sake kamasu,haka gabadaya Iyalan gidan suka kwana suna cikin Damuwa gashi mgana ta Fita domin makotan dake gidan ajiya sanda su Sadiya suka zo sun Fita da mgana waje domin Tun wajen sallar Asuba aka Dinga Nuna Abba kabiru ana Zunde gabadaya sai Ya Raina kansa,Ya zabge lokaci Daya har washegarin kuma ba wani labarin inda Kasim yake Ya muktar yana Zaria Sukayi mgana da Ya Hashim shi yake sanar dashi Abunda ya kara Faruwa Shi kanshi ya girgiza da jin labarin,Daga Zaria kaduna ya sake komawa Cikin ikon Allah ya samu labarin Kasim yana kaduna State C.I.D waya yayi musu Abba kabiru kan suzo saboda su isa wajen atare lokacin da Labarin yazo musu Abba kabiru cewa yayi ba inda zashi Dakyar Abba garba ya Tausheshi suka Tafi kaduna da Ya Hashim sai Haruna wanda bai koma ba haryanzu.

Sun isa kaduna State C.I.D,Sai kuma Abu yaci Tura saboda Sun Riga Ya muktar ya isa Shi lokacin yana Cikin Barikin Kaduna,kiri kiri aka hanasu ganin kasim kuma Suka ki bada wani bayani akanshi wai ba"a basu izinin ba,Sai da Ya muktar yazo kana Aka Fito da Bayanan kasim bayan Dogon Turanci Inda ake Tuhumarsa da Shiga cikin gidan Matar Aure da Niyyar kokarin keta mata Haddi,wanda ya Shigar da karar yana Bukatar ya makashi a kotu ne,Kuma sunki su bayyana suna sai da Ya Muktar yayi waya da Commissioner yan Sanda na Ajahar kaduna nan da nan sai gashi yazo zuwansa ya saka Dole sunan wanda ya saka aka kama Kasim ya Fito....

Bakowa bane face Mr Bello Muhammed Jikamshi ta Hannun Uncle Aminu Domin Shi yazo ya Shigar da karar,anan kaduna State C.I.D Bayan sun Ji ta bakin Bellon Ta wayar hannu,Mamaki ya cika Fuskar kowa barin ma Ya Muktar cikin Sanyi jiki yake Fadin"Haba dai...Bello fa baya kasar nan wajen wata Uku da suka gabata Taya zai saka a kama Dan"uwansa.."

Yafada cikin Mamaki Abba garba kuwa da Abba kabiru tsoro ya cika musu mara,Bello fa yafara musu Dauke Daya Daya Saura su kenan Wayasani ma ko ya Shigar da nasu karan ganin ba mafita yasa Ya muktar ya Danna ma Bello kira Lokacin ma muna Shagon Siyayyar kayan Babbys ya barni ya Fita yana Daga Kiran Ya Muktar yashiga Fadin"Bello wani irin Abu ne ka aikata..?

Cikin Mirmishi yace"Finally ya Muktar ina Fatan an zayyano muku korafina da kuma Akan me nake karas sa.."Cikin bacin Rai Ya muktar yace"Ba wannan na Tambayeka ba Why..? Kar ka manta ko"ina akaje kasim Dan"uwanka ne,ko me ya maka bai dace kasa a tozartashi irin Haka ba.."Cikin Fada Bello yace"Wlh bai isa ba Yaya koda ciki Daya muka Fito da Kasim bai isa ya Shigo har cikin gidana ba Yaso ya ketama matata Haddi na kyaleshi ba...Sai na kaishi Kotu ta yankemai Hukuncin Daya Dace dashi.."Daga haka kawai ya yanke Kiran zufa ta dinga Ketoma Su Abba kabiru domin Suna iya Jin Maganganun Bello Cikin Bacin rai .

Ya muktar ya Dafe kai yana Fadin"Innalillahi...Bello he is very Storeborn wlh...bashi da ikon kai Kasim Kotu Tunda bashi da Shaidan Hakan.."Haruna dake Tsaye yace"Nine shaida...Sir."Gabadaya kallo ya koma kanshi cikin mamaki ya Muktar ke Fadin"Kaima kasan ya Je har gidan Bello yayi kokarin ketama Aneesa Haddi.."Haruna ya Sharbe Hawaye yana Fadin"Na sani Bayan yaje har gidanshi Dake kano Lokacin yana cikin Rashin lafiya,wanda kasim din baida labarin warkewar Bello wanda Nima sai yanzu na sani,Tabbas yayi kokarin ketama Aneesa Haddi sai kuma Allah bai bashi sa"a ba,Shi da bakinshi yake sanar dani komai har namai Fadan Abunda yayi bai kamata ba."Yafada kawai sai ga Hawaye Lokaci Daya kowa yayi kuri kawai yana binsa da kallo Yan sanda kuwa nata Daukan Bayanai cikin Sharan kwallah Haruna yafara Fadin"zan fadi wata gaskiyan ma bayan wannan.."

Gabadaya aka sakamai ido ana kallonsa cikin Rawan Murya Abba Kabiru ke Fadin"Ya isa Haka Haruna...Na tabbata in ka kara Fadin wata mgana zuciyata zata fashe saboda bakinciki.."Haruna ya girgiza kai yana Fadin"zan fada...na gwammace na Fada Tunkafim Lokaci ya kuremin na Tabbata Abunda muka aikata ne nida kasim yafara bibiyarsa,Mganar gaskiya mune Silan Ciwon Bello.."Gabadaya kowa sai ya koma yana Sauke ajiyar Zuciya Cikin mamaki ya Muktar ke Fadin"Kamarya fa bangane ba..?

Haruna ya sadda kai yana Fadin"Ni na bama kasim Shawaran zuwa wajen wani boka agarin Niger  na rakasa mukaje akayima Bello Asirin da zai Rayu kamar matattace,Kuma an tabbatarmana Haka zai kare rayuwarsa bai tashi ba,Sai gashi kuma Tun ba adau Lokaci ba yafara warkewa wanda kasim yayi Hakane Domin Aneesa ta Daawo Hannunsa kuma Burinsa bai cika ba.."Yafada yana Kara Rushewa da kuka gabadaya sai wajen ya Dau Salati Ya muktar kanshi ya kama yana Kiran Sunan Allah.

Sai da ya Daidaita kanshi kafin yayi mgana..."Abu baiyi Dadi ba..."Abba kabiru na Hawaye yace"Barewa bazata yi gudu Danta yayi Rarrrafe ba Muktar ka manta muma irin Zaluncin da mukayi muku Nida Garba..Ya zama Dole mu ma mu karbi Hukunci..."Da Sauri Ya muktar ya Dakatar Dashi da Fadin"A"a Abba wannan kuma wata mgana ce Dabam...Commissioner plz mu na bukatar Belin Kasim.."

Commissioner yace"Zasu bada Belinsa ammh har sai Dan"uwanka yazo sun cike Takardun Bayan kuma Hukuma Ta Shiga Tsakani Duk da Abun na cikin gida ne.."Kai ya muktar ya Gyada kafin yace"insha Allahu nan da kwana biyu zamu zo tare.."Daga haka suka Rabu da Commossiner yabi tawagarsa ya koma Suma Daganan suka Dumgumo zuwa katsina Dukkansu wanda ba yarda basuyi ba kan Su ga kasim ba ammh aka Hanasu bawai domin matsayin Muktar bai kai ba sai domin Bello yasan cewa Muktar zai iya zuwa ya nuna karfin iko akan hakan shine ya Shirya komai cikin Hikima.

Ya muktar yajinjina ma lamarin Sosai ta wani Fannin kuma baya ganin Laifin Bello Domin An Zalunceshi.Allah nagani baitaba Rike kowa acikin Zuciyarsa ba...Kosu Abba garba Tuni yaji ya yafe musu har cikin Zuciyarshi Suna komawa gida Abba kabiru shi yatara su Umma yana Fada musu Abunda su kasim suka aikata Haruna dama tun Akaduna suka Rabu yana Neman gafaran Ya muktar Shuru kadai ya mai Domin Abun ya gama Kashemai jiki,Duk wanda yaji labarin Abunda kasim ya aikata sai yayi Tir dashi Daada Da Anty Rahila Ranar suka bi Ya muktar suka koma Abuja sai da suka isa gida yake basu lbarin da Haruna ya basu na Asirin da suka ma Bello.

Daada ta rike Haba tana Fadin"Haba...Koda naji...Dama na san Ciwon Bello yana da Nasabarsa Mutum fa ya kwanta Lafiya lau,yatashi cikin lalura...Allah mun gode maka Dama ba Tunyau ba Bello baya Kaunar Ahalin nan naku Zuciyarsu kwata kwata bashi da kyau.."Ya muktar dai ba magana Domin wannan karon baida tacewa.

Washegari Ya muktar ya kira Bello awaya yace rokeshi kan Don Allah mu dawo Dama Aranar Daddare Jirgin mu zai Tashi Zuwa Nigeria dama Siyyayyar Kayan Haihuwa muka Tsaya yi,Ranar da Daddare Jirginmu ya Tashi Daga Epypt zuwa Gida Nageria ta  Filin Jirgin Murtala Muhammed Lagos muka Sauka da Safe muka bi wani Jirgi  Zuwa Abuja Mallam Inuwa yazo ya Daukemu Da muka Sauka afilin Jirgin Nmandi azikiwe Internatinal Airport.

Kowa yayi mamakin ganin yadda Dagani Har Bello muka chanza Ni kuwa ga Kibar ciki ga kyau Dana kara Anty Rahila sai kallona Take cike da Sha"awa Ya muktar ne suka Shiga Shashen Bello Suka Dade suna mgana kafin su fito,Dakyar yayi Convicing dinshi kan zuwa kaduna gobe,Da Sassafe kuwa suka Tafi kaduna Uncle Aminu ma ya Dawo Shima Ya muktar ya sanar dashi su hadu a kaduna din Hakama Bangaren su Abba garba wadanda ke cike da Nadamar Abunda suka aikata Tunda gashi yana Bibiyarsu.
Chapter 68 · 0% Book details