← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 76

Sashe 30

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yafada lokaci Daya yana Juyawa yafara Tafiya Zuwa Cikin Falon Baki Bude ya Ali da ya Sunusi ke binshi da kallo kafin Sukalli Juna Lokaci Daya kuma Suka Rufamai baya Har Zuwa Cikin Falon Da su Abba kabiru ke Zaune Suna Jiran Tsammani Tunda kasim yaga Sun Shigo Fuska ba Annuri Jikinsa ya kama Rawa Hawayensa Suka Cigaba da Zuba Lokaci Daya Zuciyarsa na Harbawa...

Basu zauna ba Daga Tsayen ya Ali ya kalli Abba kabiru yana Fadin"Kuyi Hakuri da Abunda zan Fadamuku,mganar gaskiya mun Janye Mganar baku Auran kanwarmu Aneesa awannan Lokaci bisa la"akari da Abubuwan da Suka bayyana,kuma koda Aneesa Take kanwa garemu Tana da Hakki mai girma Akanmu matukar muka Rufemata muka Aurar da Ita ga D'anku Hakika mun Ci Zarafinta kuma Allah bazai barmu ba...Shiyasa muka yanke Shawaran Mu baku Hakuri Don Allah kuyi hakuri mu bar mganar wannan Daurin Auran Fata zaku Fahimce mu,bisa yadda muka sa kuka baro garuruwanku muka bata muku Lokaci.."Daga Abba kabiru Har Abba garba ba baki sai Zufa Suke Sharewa suna kallon Juna Cike da Kunya da Takaichi.

ya Hashim ne da Liman ke Gyada kai Alamar gamsuwa Liman yace"Mganarka gaskiya ne Aliyu...Hakan Shine Daidai..."Shiko Kasim kasa ya sake Durkushewa Yana Fadin"karkumin Haka Don Allah karku ce zaku Rabani da Aneesa Ina Sonta Itace Rayuwata Na muku alkawarin zan bar Duka Abunda nakeyi Daga yau Don Allah karku Hanani Aneesa.."Yafada Hawayensa na kara Gudu Lokaci Daya yayi baya Dafe da Kirji Abba kabiru Dake kallonsa yaji kamar ya Fashe da Kuka Saboda Tsausayin D'anshi.

Baya Yy Ali ya juya bayan ya saka Haban Babban Rigansa,yana Share Kwallar Data Zuraromai ya Sunusi ne ya Rikesa yana Fadin"Kabi Ahankali kasim,kayi Hakuri Haka Allah ya kaddara ina maka Fatan Allah yasa Sanadin Shiryuwanka kenan..."ya Hisham ne kadai ya amsa da Ameen Su Abba kabiru ko kansu na Duke suna Tunanin Wannan Wani Irin Tozarci ne..

ya Muktar ne yayi gyaran Murya yana Fadin"Allah gafarta mallam don Allah Ajirani kadan in Dawo yanzu za"a Daurama Aneesa Aure babu Abunda Zai Chanza..."Yafada yana Juyawa da Sauri ya Fita Zuwa Waje,Kowa da Ido ya Rakashi Cikin Mamaki Hatta ko da Kasim Sai da ya Dakata da Kukan Dayake Yaji Zuciyarsa ta Tsaya cak Lokaci.

Ya Dade yana Waige Waige Cikin Haraban Gidan kafin idonshi ya Hangomishi Bello,Zaune bisa Kujera yana latsa wayarsa,kafin ya karisa Wajensa sai da ya biya ya bama mutanensa Hakuri kan Yanzu za"a Daura Auren,Bello na Zaune kawai sai jiyayi an finciki hannunsa Lokaci Daya kuma anfara Jansa,Da Sauri ya Dago Lokaci Daya yana kallon ya Muktar Dake Jansa Cikin Fushi kuma yaki Bari yaga Fuskarshi bai Direshi ko"ina ba sai da Suka bar Haraban gidan Suka Fita Daga get Din Gabadaya kana ya Sakeshi Lokaci Daya yana Fuskantanshi.

Bello ya tsaya da Kakafunsa yana kallon Fuskar ya muktar bai damu ba Illah saka wayarsa Dayayi Cikin Aljihun Gaban Rigansa,Lokaci Daya kuma yana Saka Duka Hannuwansa ya Harde kirjinsa ganin kallon Da ya Muktar ke mai ne yasa Ya Dauke kai gefe ya Raba gefensa zai Wuce,Da Sauri ya saka Hannu Cikin Fushi ya sake janyosa Zuwa gabanshi Lokaci Daya yana Hararansa,kafin yace"Kayi Nasaran B'ata Auran yanzu Dawa kakeso Adaura...?

Tamke Fuska Bello yayi kafin yace"Bangane ba ya Muktar...? Look nifa Awannan al'amarin Taimakon Aneesan nayi,kuma Kaima na Taimake ka Domin da an Daura Auren Lbrin ya Fito kome ya Faru dakai za"ai kuka."ya fada yana Zakuda kafada Irin ko ajikinsa din nan.

Ajiyar Zuciya Ya Muktar ya Sauke kafin yace"naji...Toh yanzu ya zasuyi da jama"ar da Suka gayyata..? Kai tsaye yace"Su basu Hakuri mana Yaya..."Hararansa ya Sakeyi kafin yace"Ita Aneesan fa...? Baka Tunanin Wani Hali Zata Shiga in ta samu lbri..? Fuska ya bata na gajiya da Irin Tambayoyin Ya Muktar Cikin kosawa yace"Sai ta koma mkranta Is dat so..."Kirjinsa Ya Muktar ya kaima Duka kafin yace"U are Animal Bello...Baka da Zuciyan mutane...Baka da Tsausayi ko kadan,toh baka isa ba Tunda har Ka lalata wanchan maganar toh kai zaka maye gurbin kasim Wuce muje yanzu Dakai zaka Daura Auren..."Yafada cikin Tsawa Lokaci Daya yana Fuzgar Hannun Bellon Da karfi

Shiko Bello Kamar Aradu Haka yaji Mganar,Cikin Zaro ido yace"Ya Illahi ya..muktar Wht of all dis kuma..? Plz dont do dis for me am begging u ban taba kallon Aneesa Amtsayin Wacce zan iya Rayuwar Aure da ita ba...infact ma Ban Shirya yin Aure yanzu ba...plz leave my Hand.."Yake Fada kamar yayi kuka ammh ya Muktar ko Sauraransa Baiyi ba Haka yake Jan Hannunsa Har Zuwa Cikin Falon Mutanen Dake Waje Suka bisu da kallon mamaki Sani Dake Cikin Abokansa ganin Haka yasa Shima da Sauri ya Rufa musu baya.

Ya Muktar bai Dire Bello Ko"ina ba Sai agaban Liman kafin Shima ya Zauna Kusa Dashi Lokaci Daya yana Dafe Hannunshi,domin yaga Bellon kokarin Tashi yake, Hannu Daya ya Zura Cikin Aljihun wandonsa ya Fito da Kudi Bandir Biyu Daya ya ijiye gaban Liman Daya kuma gaban Hashim kafin yace"Wannan Sadakin kasim ne na maido muku da kayanku..."Yafada yana Nuna da Kudin Dake gaban Hashim kafin ya Dora da Fadin"Wannan kuma Sadakin Aneesa ne...Zan ma Kanina Bello Walicci..."..

Gabadaya Falon sai ya Dau Shock ya Ali ko Da ya Sunusi ko Junansu Suka kallah Lokaci Daya kuma Suka Saki Mirmishin Farinciki Abba garba ko da Abba kabiru Wani yam Sukaji Lokaci Daya da Takaichin Muktar da Bellon Gabadaya,kasim ko Bellon Ya Zurama ido yana kallonsa Cike da Wata Tsana mai girma Lokaci Daya dawani Irin Bakinciki Sani kuwa Gefe ya samu yazauna yana Kallon Abunda ke Faruwa.

Liman ya Saki Mirmishi yana gyara Rawanin Kansa yace"Masha Allah Hakika ka cika Musulmin kwarai...Wajen Kokarin Hana Tozarta wani Ahalin Nawa ne Anan..? Kai Tsaye Ya Muktar yace"Dubu 100 Allah gafarta Mallam..."Bakinsa Washe yace"Alhamdulillah...Kai Ali gayama mai Shela ya sanar da Mutane Su matso kusa za"a Daura Aure.."

Yafada lokaci Daya yana Dora kallonsa kan Bello Wanda kansa Ke Duke yana Faman Tunanin kila yana Duniyar nan Mafarki ne,Da Sauri ya Ali ya Fice ya Samu masu Shela yace su Sanar Kowa ya matso kusa Za"a Gabatar da Daurin Aure,nan da nan Suka Fara Shela Suna Fadin"Kowa da kowa ya matso..Lokaci yayi ammh bana Mutuwa ba Lokacin da Shaidu Zasu Tabbatar da Daurin Auran Aneesa Bukar Bulama da Angonta Kasim Kabir Jikamshi..Kowa ya matso.."Nan da Nan Mutane Suka mimmike Dama Sun kagara Wadanda Suka samu Shiga Falon Suka Shiga Wadanda basu samu ba kuma suka durkusa Daga Waje Suna Jin Abunda ke Faruwa.

Daga cikin Falon Kuma ya Sunusi ne yayi Saurin Dafa ya Muktar yana Fadin'"Kaga Muktar Tashi kagani..."Ba musu ya Mike Shi kuma ya koma Inda ya Tashi ya zauna yana Fadin"Zan karbaman Bello Auran Aneesa..."Yafada yana kallon Bellon Wanda Dakyar ya kakaro mirmishi ammh Cikin Ranshi kamar ya saka Ihu Gabadaya Wajen Kowa yaji Dadi barinma Ya Muktar Wanda Suka koma gefe Shida Ya Ali Suka Zauna Cikin Shaidu kafin Afara gudanar da Neman Aure

****

Aneesa Dake Bedroom Din ya Ali Zazzabi mai Zafi ya Rufeta tana Lullebe Cikin Blanket Su B.kaita Sunyi Sunyi Tatashi Tayi Wanka Taki Tashi Salamatu Jibiya ce Taje ta Kira mata Anty yagana Ita tazo ta matsa mata ta Shiga Wanka Koda ta Fito Haka take Rawan Sanyi Tana karkarwa Dakyar ta yarda Ta Shirya Cikin Wani Ubansu Swice less Wanda Akallan Farko In kayimai zaka gane Yabama 50k baya Saboda Kyanshi da Tsaruwanshi,Kalanshi Blue and pick ne,gashi yayi mata kyau Dinkin Diga da Zani ne,Dakyar sai Da Anty Yagana ta Tsaya Akanta kana Ta Tsaya Sanah ta mata kwalliya Tunda Ta iya ko gamawa Ba"ayi ba Ta koma ta kwanta Tana Hawaye,Dole Suka kyaleta sai gabda Daurin Aure ne Anty Yagana tazo Tatafi da Ita Dakin Falmata chan Kurya ta matsa mata taji Abinci Tasha Mgani Ta kwanta

Lokacin Daura Aure na Cika Sukayi ta Sakin Guda da Turaren Kamshi ammh Shuru basu ji masu Shela da Maroka na sheda ba, Abun ya basu Mamaki Anty Nafee Har Leke Ta Dingayi Tana Fadin"Kila akwai Wadanda basu iso bane ."Anty Rahila tace,"Anya Angon ba Tare suka zo da Abban Hibba fa Munyi mgana Dashi..."Dukkansu Suna Falon Falmata ne Dakin Mama yana Duka Acike yake da Dangin Babansu.

Cikin Barci Aneesa Tayi Mafarkin wai anfasa Daurin Aurenta da Kasim da Wani Aka Daura mata,Tana jin jiri da Ciwon kai Haka ta Fito Falo Tana Dafa Bango Daidai Lokacin da Wani mai Shela yake Fadin"Alkawarin Allah ya Cika Aure ya Dauri Kuma Shaidu Sun Bada...Aneesa Bukar Bulama Ta Tabbata mata Wajen Muhammed Bello Jikamshi...Wannan Chanjin Chanjin Allah ne,Lakadan ba ajalan ba..."Da karfi yake Mganar Kuma ga Hayaniyar mutane na Tashi kowa yaji Mganar Har Cikin Gida karaf kuma Akunnan Aneesa Data Fito Falon Kirji Ta Dafe Tana kallon Anty Rahila Wacce Ta Mike Tana Kara Jin Mai Shelan na kara maimata Muhmeed Bello Muhamed Da Aneesa Bukar Bulama..

Anty Rahila tace"A'ah yanake jin Wani Suna Dabam kuma kamar Bello naji ana ambata.."Tafada Cike da mamaki tana kallon Mutamen Dake Dakin Anty Nafee ce Tace"Nima Haka naji ina ce ba Kasim Sunan Angon ba,..?kuma naji ana kiran Wai Muhammed Bello.."..

Anty Rahila Data Shiga Rudani Tace"Eh kasim Sunanshi...Bellon fa kanin Abban Hibba ne,baya ma kasar yana malesia abun mamaki Garin yaya aka samu Wannan Chanjin kuma.."Tafada Cikin Rudewa Basu lura da Aneesa Dake Tsaye ba sai Dai Sukaji Mganarta Murya Shake Tana Fadin"Ni....Ni..Da Bel...Bello...Kuma..? Ina Kasim din..? Tafada Lokaci Daya Hawaye na wanke mata Fuska kafin kaji tim ta Zube kasa Sume nan Fa Daki ya Hargitse da Iface iface Daga Waje ma Mamaki da Cecekuncen Dake Tashi kenan Su B.kaita Dake part din ya Ali Sanah Tazo Tana gayamusu da Hanzari Suka Mike zuna Falon Falmata inda Ake Yayyyafama Aneesa Ruwa Data Farfado sai Takara Bajewa Tana Iface iface Ashe Aljanunta ne Suka Tashi Shigowar Su B.kaita Dakin ya sanya Suma Suka Zube Nasu ya Tashi kafin Kace me gida ya Rikice Dakyar Aka samu Suka Dawo Cikin Hayyacinsu.,Daada Dake Dakin Mama yana Itama lbri ya kawo mata Anty Rahila tazo Da Sauri Tana Gayamata Itama Cike da Mamaki Take Nanata Sunan Bello,acikin Ranta.

Daga chan Haraban Gidan Kuwa Mutane nata mamaki Chanjin Da Suka ji Musamman Tawagar Ango Kasim kowa sai mgana yake Cike da mamaki,lokaci daya Kowa na kallon Kowa Cike da Tambayoyi..
Chapter 30 · 0% Book details