← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 76

Sashe 31

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Cikin Falon kowa Cike da Farinciki kowa ya Mike ana ma Juna Musabaha Duk wanda yace Ya yaji Chanji sai ace matsala aka samu Shiyaasa,Bello kuwa yana Mikewa kansa ya Sara kamar zai Fadi Sani Dake kula Dashi ne yayi maza ya Rikesa yana Fadin"Bi sannu fa Bello..."Dago kansa yayi Jajir kafin ya Rike Hannun Sani yana Fadin"Mu Fita Waje Sani ...kaina kamar zai Fashe..Kaini Waje Don Allah..."

Yafada yana Hura baki Numfashinsa na Fitowa ta Baki,kamasa Sani yayi Suka Fito Waje,Takalmansa ya Duka yana Zuramai shiko yana Duke Dafe da Bango Har ya gama shima ya saka nashi ya Riko Hannunshi Zuwa Haraban Gidan Sai ga Kasim Ya Fito Afusace ya Hashim da Abba kabiru na Rikosa Ammh yana Turjewa Harda dai ya Sabule Babban Rigan Dake Jikinsa da Hula ya barmusu kafarsa bako Takalmi ya Tako da Gudu Yasha Gaban Bello Lokaci Daya yaci Kwalan Rigansa Gabadaya Mutane kallon ya Dawo kansa Abokansa Suka Rugo da Gudu Cikin Tashin Hankali Haruna ne gaba gaba Suna Tunanin kodai Kasim ya Fara Haukane Jin badashi Aka Daura Auran ba.

Bello Dayaji An Chakumi kwalanshi ya Dago da Jajayen Idanuwansa Wadanda Suka Chanza launi Saboda Tashin Hankali ya Saukeshi kan Kasim,Kuramai ido yayi yana kallonshi cike da mamaki bai gama Mamaki ba yaji Hannunsa Bisa bakinshi ya Dungule ya Nausamai Naushi Wanda Sai da Bakinshi ya fashe Lokaci Daya Kasim yace"Dama Abunda kake Buri kenan...? Auran Aneesa...? Hhhh,kayi Nasaran Rabani da Ita ka Aureta ammh Ina so ka sani..."Bai karisa ba ya Hashim ya Finciki Hannunshi Daga Wuyan Bello yana Fadin"Baka da Hankali ne,kasan kana Sonta baka gyara Halinka ba kafin Zuwan wannan Ranar,wuce muje Sakarai kawai.."Yafada yana Rikesa Daidai Lokacin da Su Abba kabiru Suka kariso da Su ya Muktar Bayansu ya Ali da ya Sunusi Waje ya Cika jama"a da Takaichin Tonon Asirin Da Kasim ke musu Abba Garba yace"Kai Hashim kamashi Muje Waje.."Yafada da Karfi Da Sauri Hashim ya Kara Damkan Kasim Wanda ke Zillewa,ganin Haka yasa Sauran Abokansa Suka kamamai Suka yaja kasim Zuwa Waje Wanda ke juyowa Yana Nuna Bello Lokaci Daya yana Fadin"Wallahi...Tallahi ka Rubuta ka Ijiye Bello...kayi Nasaran Auran Aneesa ammh bazaka samu Nasaran Rayuwa da Ita ba Ni nan Kasim sai na Kasssara Rayuwarka kamar yadda ban samu Aneesa ba Haka kaima zaka kare Rayuwarka Cikin Kila wa kalan Mutuwarka Bello sai na ga bayanka.."Yake Fada yana Zubar Hawaye Abba garba yakara Turashi Waje ganin Zai kara Sakasu Cikin Wani Bala"in bayan Wanda Suke Ciki

Gabadaya Jama"an Wajen kowa ya Rike baki yana mamakin kalaman Kasim Jikin Muktar da Nasu ya Ali yayi mugun Sanyi Duk Sunji Abunda ya Faru Abakin Rahila na yarda Su Abba kabiru Suka Hamdame Dukiyarsu ammh kuma Tunda komai ya Wuce ba amfanin Tada mgana Bello Dake bin kasim da kallo Har Sukayi Waje Suda Tawagarsu,Wani Mirmishi ya saki kafin ya saka hannu ya Share Jinin dake Gefen Bakinsa,Ya kara Rike Hannun Sani yana Fadin"Muje Filin jirgi Sani..."Yafada Yana kallon kasa.

ya Muktar yace"Sani kuje,muna Tafe muma Don Allah ku kula.."Yafada Cike da Tsausayin Bellon,Ya Ali Dake gefe har Sun Fara Tafiya ya Daga kafa yana Fadin"Muhammed Bello..." cak Bello ya Tsaya Bayan ya Waigo yana kallon ya Ali Wanda ya kariso Garesu ya saka Hannu ya Rike Hannun Bello Guda Daya,Yana Fadin"Nasani Cewa Domin Kada Mu Tozarta Muktar ya yanke Shawaran Aura maka Aneesa Bello...Bamu yi Fushi ba,mun karbi Zabin Allah Hannu Bibbiyu,muna Fatan Allah ya Zaunar Daku lafiya,Don Allah ka Rike Maraicin Aneesa Tamkar yadda Yayanka ya Rike Maraicin Yayarta Rahila.Kuje Allah ya kaiku Lafiya,Babu Abunda ya Isa ya samu bawa sai da Izinin Allah.."Yafada Lokaci Daya Idanuwansa na kawo kwallah Sakin Shi yayi lokaci daya ya juya cikin karfin Hali Bello yace"Insha Allahu..."Daga Haka ya Juya Cikin Dafe kanshi Dake Saramai.

Sani ne ya Taimakamai Suka Fice Daga Haraban Gidan Mutane na Binsu da kallo,nan dai Suka Dinga gaisawa da Mutane ko Waliman da"a kace za"ayi ba Wanda ya Tuna da Ita,Gida ba kwanciyar Hankali Haka kowa ya Watse yana Mamakin Al"amarin Daya Faru gidan Marigayi Bukar Bulama.

Su Abba Kabiru Daganan Filin Jirgin maiduguri Suka Wuce suna Zuwa Hashim yayi musu Cuku cukun Samun Fligt Zuwa Katsina,Abunga da Kudi nan da nan Ko 30m basuyu ba Jirgin ya Debesu Dukkansu Harda Abokan Kasim din Zuwa katsina,wasu kuma da Yawa Sai Suka bi Wanda Zai koma kaduna,Suma Su Bello Jirgin su Kasim din ya Tashi da Awa Daya Suma nasu Wanda zai yada Zango a Abuja ya kwashesu,bello jikin Sani ya Kwantar dakai,Saboda Yadda kansa ke Sarawa kamar ya cire kan ya y'ar Saboda Halin Dayake Ciki.

Bayan su ya Ali Sungama Sallaman Baki Suka Nufi Cikin Gida Saboda Susan Cewa Su ake Jira Aji Bayanin Taya aka samu Wannan Chanji,kai Tsaye Dakin Falmata Suka Shiga inda Gabadaya Su Anty Rahila ke Ciki Da Aneesa Wacce Tunda ta Dawo Cikin Hayyacinta take kuka Su B.kaita ne ke lallashinta ammh kamar kara Zugata Suke,Ya muktar ya Shigo Dauke da Hibba Wacce yacikaro,Atsakar gida tana Wasa,waje suka samu Suka Zazzauna,sai da aka kira Daada Mama yana,Da Falmata da Wasu Daga Cikin Dangin Babansu kafin ya Ali ya Fara kora Jawabi Tunda farko Har Zuwa Karshe Aneesa Dake kwance ta Mike tana Fadin"Da kun Auramin kasim din Hakanan Ina Sonshi Haka Duk da yana Shaye Shaye da Neman mata ya Fiyemin Wanda kuka Auramin So Dubun Dubata...Bana son Bello na Tsaneshi ban taba Sonshi ba,Dama Baida buri kullum sai na lalatamin Dukkan Farincikina Wlh bazan iya Zaman Aure Da Bello ba Dana Zauna Dashi Gwara na kashe kaina.."

Tafada Tana kuka Lokaci Daya Ya Ali ya Mike jikake Fau!Fauyau.! Ya Kwasheta da Maruka lafiyayyu Guda Biyu ya kuma bita da Hauri da Kafa da Sauri Daada Ta Mike Ta Shiga Tsakani Tana Fadin",A"a Tana da gaskiya Ku barta ta Fadi Ra"ayinta ita din ba Akuya ba ce Mutun ne kamar kowa kuma Tana Da Hakkin Akan Zabin Mijin Da zata Zauna Dashi meyasa Kuka yanke Hukunci batare Da Kun Nemi Shawaranta? Ba a haka mganar Gaskiya Baku Kyauta ba,Kuma Shima Bello bai kyauta ba domin Ya yi kokarin Tona Asirin Dan"uwanshi Musulmi Wanda bai kamata ba ko a Addininmun in ka Rufama Wani Asiri Ranar Gobe Kiyama Kaima Allah zai Rufamaka...Dukkanku Baku Kyauta ba,baku kyautama Aneesa Ba kuma baku mata adalci ba.."

Tafada Tana Share Kwallah Anty Rahila ne tazo Ta Riketa tana Fadin"Daada zo ki zauna kada ki Fadi..",Tafada Tana Rikota cikin Fushi ya Ali yace"Mama yana Da Falmata ku Shaida Wlh Tallahi Inhar Aneesa bata Zauni Gidan Mijinta ba Na Zare Hannu na Akanta Har Abada...Mganar bamu kyauta mata bai Taso ba Daada..Mashayin zamu Aura mata Kuma Mazinacin.? Muma Allah zai kamamu da yin Hakan,kuma mganar baki sonshi karki soshi don Ubanki baki da gatan Daya wucesa,da Har zaki Bude baki ki Cima Mutanen Da suka maidake Mutum Mutumci ba Mutuwa zakiyi ba yau ko Gawanki ne sai An mika ki Gidan Mijinki.."

Yafada yana Daidaita Numfashinsa,Ya Sunusi ya mike Shima yana Fadin"Wannam Shine mgana ke Yagana da Rahila ina Nafeeesa da Aisha..? Suka mike Suka Hada Bakin Wajen Fadin"Gamu ya Sunusi..",kai ya gyada kafin yace"Ku cigaba da Shirin komai karfe Hudu kamar yadda Aka Tsara zaku Rakata chan Abuja Allah barshi Dagachan Sai ku barsu musu ita ku Dawo..Duk Abunda Suka yanke Daga Baya Daidai ne Domin Tafita anamu Tundama chan Ita Din Tasu ce..."Daga Haka Suka Nufi Hanyar Fita ya Ali na Fadin"Mgana ta kare..:Muktar Taho muje.."Suka Fada Suna Ficewa,Nan Suka bar Aneesa na Kuka Harda Ihu Anty Rahila Dake Gefe Tayi Jagale Falmata Tashi Tayi Ta Fita Gefen Ranta kuma na Cike da Tsausayin Yarta.

Mama Yana ce Ta saka matar Ya Ali Khadija dasu B.kaita Suka kama Aneesa Tana kuka Suka Nufi Da Ita part din ya Sunusi,Sauran Kuma tace Su Cigaba da Shirin Tafiya,sai Lokacin Kowa ya Fita Tsakar gidan Aka Fara Hada Hadar Abinci Ammh Fa Kowa bai ga laifin Hana kasim Aneesa ba Domin Hallayanshi basu da kyau Anty Nafee ne Acikinta ranta taso da Mashayin Aka Aurama Shegiya Data gane bata da Wayau.

Ki biya ki karanta cikin Salama.

*ANITHA..*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

  
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
   
*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�17*

"Tunda ya Ali yabada Umarni su Anty yagana Suka Cigaba da Shiryen Shiryen Tafiya Abuja da Aneesa Wacce Ke Dakin ya Sunusi Tana Kuka Kamar Zata Shide gashi dama Ga Zazzabin Jikinta bai barta ba nan da Nan ta kara Rafkewa B.kaita da S.jibiya sun gaji da bata baki Sun Koma gefe Sun Zabga Tagumi Ammh har Acikin Ransu Basu Damu da wannan Chanjin ba Domin Uncle Bello yafi Kasim Sau Dubu Sai dai Don Ita Aneesan Allah bai Hada Jininta da shi Bellon bane.

Su ya Ali kuwa Falon Waje Suka Koma Suka Cigaba da Tattauna lamarin anan aka kawo musu Abinci Suka ci,suka Sha,Daga Cikin gida kuwa Sun gama Hada Komai Na kayan Aneesa da Suka zo Dashi sai Turaran Wuta da Aka Hadamata Dana Daki dana jiki sai Abunda Ba"a rasa ba Wasu kayan ma Anbarsu ne Daga baya za"a zo dasu Saboda Tafiyar Jirgi ne bata Mota ba.
Chapter 31 · 0% Book details