← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 76

Sashe 27

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiko Bello Jikinsa ne yayi Sanyi Har Ya Muktar ya kulema ganinsa,Ajiyar Zuciya ya Sauke Cikin bacin Rai da Jin Haushin Yadda Ya muktar yaki Sauraranshi Saboda Wani Uzuri Nashi mara Tushe Ammh Tsakani ga Allah In Har Suka Auramata kasim Sun cutar da Ita Abun nashi Yayi yawa bayan Neman mata harda Shan giya Haba Zasu kashemata Kuruciya wlh,Cikin Bacin Rai Shima ya bar part din ya Muktar din Zuwa part Dinshi Ranshi na Kona Tiolet ya Fada ya sakarma kanshi Shower Haka Kurum yaji Ransa na Kara baci na ganin yadda Ya Muktar ya nuna yafi yarda Da Bangaren da Suka Cutar da Rayuwarsu Fiye Dashi Abun in ya Tuna yana Kara batamai Rai Sosai.

Baisan lokacin Daya kwashe yana Cikin Shower ba sai da ya gaji da Kanshi yayi wanka ya Fito bayan ya Dauro Alwala,wata jallabiyan ya sake sakawa Wanchan ya Barota Cikin Bucket din Dake Tiolet,Shafa"i da Wuturi yayi kafin yayi Addu'o'insa Daya Saba, Gadonsa ya Haye bayan ya Cire Jallabiyan ya Rage Dagashi sai Boxers,jakarsa ya Bude ya Fito da karamar laptop dinsa Daya Chanza a Malesia,kunna ta yayi bayan ya Kara Haura wa saman Tsakiyar gadon Sosai,ya sakata Atsakiya yafara Shige Shigensa.

Duk yadda yaso yayi aikin Abun ya gagareshi,Duk da Ko ya ci karo da Sakon Farinciki Daga Jami"ar Bayero University Dake Kano BUK tun Yana Malesia ya Tura musu Takardunshi ta Email Shine yanzu Suka Turomai Sakon Sun Daukeshi lecturing a Mathematics Department,Yanzu Suna Jiransa yazo ya karbi Appointment latter dinsa,bayan yazo yayi Reporting,Domin Dama Tunkafin Tafiyarshi yasaka ma Ranshi in ya Dawo zai bar Koyarwa a Makaranta Secondry ta kwatar kwashi Zai koma Wata Jami"ar Agida Nageria Suma Su Amfana da Basirarsa.

Ture Computer yayi yana Dafe kanshi Lokaci Daya Aneesa Ta Fadomai Arai,ya Runtse Ido yayi yana Tunata tun Farkon Zuwanta gidan Har Zuwa Lokacin Daya bar Kasar Tsiwarta Rashin kunya da Tsoronta yake Tunawa Tare da karamin Bakinta,Aranshi yanaji kamar in ya bari Aka Aura mata Kasim ba"a ma Maraicinta Adalci ba,Mikewa yayi ya Fara Zagayen Bedroom Dinshi Lokaci Daya Yana goya Hannayenshi Abaya Kansa ya Dau Zafi bashi da Wani Hop in ba Ya Muktar ba Aneesa bashi da kyakyawan Alaqa da Ita koma yana Dashi yanzu Lokaci yakure,Kansa ya Dafe yana Tunanin mafita kafin Lokaci Daya Wani Abu ya Fadamai Arai da Karfi ya Furta

""Sani....Yes bari na Kira sani Zai Taimakeni Insha Allahu Tunda yasan Komai da Hanzari ya Nufi Wayarsa ya Dauko Contact Dinshi ya Shiga ya Lalubo Lambar Sani,wanda yama Saving da Sani kaduna,har sai da Wayar Ta katse Sani bai Dauka ba,Tsaki Bello yaja kafin ya kara Kira Yana Fadin"Kai pick d Call plz.."Yake Fadi Lokaci Daya yaji Sani ya Daga Kiran yana Fadin"Ah Malamin makranta Yau Agari.."?

Ajiyar Zuciya Bello ya Saki kafin yace"Sani How are u..? Sani yace"am Fine ka Dawo kasar ne..? Don kwanaki in ban manta ba kace zaka Haura malesia ko..? Gyada kai bello yayi kafin yace"Eh naje Yau ma na Dawo kasar."Washe baki sani yayi yana Fadin"masha Allah Sannu da Zuwa An Dawo lafiya.."Bello Cikin kaguwa yace"Lafiya lau,Don Allah sani Ranar Friday kana Available..? Yafada yaji ko Sanin zaije Daurin Auren Ko A'ah..'

Sani yayi jim kafin yace"Gaskiya bana garima gabadaya Borno zamu tafi Wajen Daurin Auren Wannan Abokin aikin nawa kasim Wanda na Taba Nuna maka Hotonshi nace ko ka sanshi Shima Iyayenshi y'an Jikamshi ne..?"Cikin Farincikin Bello yace"Oh Allah Sarki na ganeshi ba Wanda kuke Zencensa kai da Wani Abokinsa kan ya Cika Shigen Neman mata da Shaye Shaye ba.."?Dariya sani yayi kafin yace"Extaly Malamin makaranta Baka da Mantuwa Shi kuwa Kasim Kabir Jikamshi ba, Aiko Zaiyi Aure Kanuri zai Auroma .."Yafada yana Dariya,

Gyara Tsayuwa Bello yayi kafin yace"Ahf toh ya Daina Neman Matan ne Dazai yi Aure? Sani yace"Umh ya Daina mene..? Sai ma Abunda yayi gaba yanzu Haka ina bakin Titi ne Muke Wayar nan naga Wucewarsa Amota Shida Wata kasan Abunda kebani Haushi da kasim..? Bai bashi Zarafin mgana ba ya Cigaba da Fadin"Kazantarshi Tayi yawa bama zai Tsaya ga ya"yan Hausawan mu ba Harda kabila da Arna marasa Addini,kuma Duk yadda yake Fadin yana Son yarinyar dazai Auro Wlh bai daina kwana Cikin maye ba,kuma bai iya Hakura sai ya Kwana Tare da mace,Fisabillahi me Ake da Hali Irin na Kasim kwata kwata ba Tsari Aini Wlh ina Tsausayama Yarinyar dazai Aura Kawota kawai Zaiyi Bakincikinshi ya Kasheta.."Bello yayi Ajiyar Zuciya Takaichi na Cikashi yace"Gaskiya fa..Toh Ba"ayi bincike bane Dagachan barayin Ita yarinyar..'?

Sani yace"Waya saninmu su Kasan yanzu ba Duka Aure Ake ma Bincike ba Indai kana da Naira Alhaji ka gama mgana,balle Shi naji yana Fadin ko Matar Wani yayanshi to kanwarta ne.."Bello yayi Saurin Cewa"Ok Nama Tuna Ranar nima zani Maidugurin Wani Daurin Aure ko zaka Shigo gobe don Allah Sani mu Tafi Tare.."Shuru sani yayi kafin yace"Kash.Gashi Tare da yan Office,dinmu mukayi Booking din Jirgi zamu Tafi."Da Sauri Bello yace"No karka damu Sani Nima anan zan mana Booking Din Flight plz Dont Say No.."Ajiyar Zuciya Sani ya Sauke kafin yace"Shikenan ammh ni bansan Wajen Daurin Auren bafa..? Bello yace"Karka damu ba ga Waya ba.."

Jin Haka yasa Sani yace"Ok goben Zan Shigo Jirgi Zuwa Abuja in na Shigo zan Kira ka,long Time Daman bamu Hadu ba.."Cikin Jin Dadi Bello yace"Yauwa..Sai na Jika.."Daga Haka Suka yanke Kiran Gefen Gado bello ya koma ya Zauna yana Mirmishin Nasara Kafin lokaci Daya ya mike laptop dinsa ya Dauke ya Kashe ya Ijiyeta kan Side Drower,Kan gadon yahaye Lokaci daya yana Lullubewa da Blanket,bayan ya Zuro Hannu ya Rage Hasken Dakin bai Dau Lokaci ba barci ya kwasheshi Cike da Jin Dadi.

******
Washegari Around 4pm Sani ya Kirashi yana Filin Jirgi Shida Mallam Inuwa Suka je Suka Daukoshi koda suka Dawo Sun Iske Ya Muktar ya Dawo Gidan Dama Meeting ya Fita Wanda Suka gudanar Afadar Shugaban kasa,koda Asuba Sun Hadu Amsallaci Bellon na gaisheshi Dakyar ya amsa kamar Wani mai Ciwon baki Shidai Bello bai Bi Tankanshi Domin yana Ji Aranshi bazai Taba bari Kasim ya Auri Aneesa Ba ko bakomai In Hallayarsa ta Fito Filo sai anfi ganin laifi Ya Muktar Fiye dana Kowa.

Koda Sani yazo har Falon Ya muktar ya kaisa Suka gaisa Ganinsa da bako yasa ya saki Fuska Suka gaisa Daganan Mension Din Bello Suka koma Sukayi Wanka Suka Ci Abincin Da Ya saka Alheri ta Hauro musu Dashi,Sai da Suka kamallah Suka Shiga Hiran Duniya kana Bello ya gyara zama yana kallon Sani Lokaci Daya ya Warware mai komai kuma ya sanar dashi Irin Taimakon Daya ke Bukatar ya bashi Gobe in Sun Isa garin Borno.

Zaro Ido Sani yayi Cikin Kaduwa da jin Bayanan Bello yace"Kai Bello gaskiya bazan iya yima kasim Haka ba kamar nafa Tozartashi ne a Idon Duniya karka manta an Taru ne za"a Daura mai Aure..kai gaskiya Bello bazan iya ba Wlh ."Yafada yana Kallon Bello Cike da Wani Tunani.

Mirmishin Yake Bello yamai kafin yace"U hv to do dis Sani kar ka manta Aneesa zamu Taimaka fa,ni kuma na Cire yayana Daga Zargi yazakaji in mai irin Halin kasim yazo Neman Auren kanwarka Alhalin bashi da kyawun Hali kuma,in ka Fahimci Haka Koda Lokaci ya Kure zaka yarda ka Aura mata Shi.?."Tsuru Sani yayi kafin ya girgiza kai yana Fadin"A"ah gaskiya bazan Bata Shi ba kam..Ammh bello baka..'Hannu Bello ya Dagamai yana Fadin"Ba ruwanka kadai kawai Shaida zaka bada ni zan karisa Sauran Aikin ammh Tabbas Ni muhammed Bello Jikamshi bazan Bari Adaura Auren Aneesa da Lallatattacen yaron nan ba Insha Allahu kawai kamin Abunda na Rokeka plz.."

Sani ya Dade yana kallonsa kafin ya Sauke Numfashi yana Fadin"Shikenan Allah ya kaimu.."Mirmishin Jin Dadi Bello ya saki Har fararan Hakoransa na Bayyana Waje yace"Nagode Sani.."Daga Haka Suka Cigaba da Tattauna Batun,Sani na kara bashi Lbrin Wasu Gurbattatun Halin Akuyancin Kasim Abun ba Dadin Ji,.

Sai bayan Sallar La"asar Bello ya karbi Key din Mota Ya jasu Suka Fita yawo Cikin gari Shiko ya Muktar Tuni yayi Waya Zuwa Filin Jirgi An Riga an yi musu Buking Din Flight Dukkansu Harda su Abba kabiru da Kasim da Hisham da Sauran Abokan Tafiya Wannan Nauyin Muktar ya Daukeshi na Zuwansu Borno da Dawowarsu Batare Daya kara Bi Takan Bello ba Bai san Shi kuma anashi barayin yagama Shiryama goben ba.

Ki biya ki karanta cikin salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

*🅿�15*

*BORNO*
_maiduguri_

"""Washegari Ta kama Jumma"a ne Ranar Daurin Aure,Tun jiya Gidansu Aneesa Suka Sha Bikinsu Sosai In kaga Aneesa Lokaci Daya bazaka iya ganeta ba Saboda yadda Takara kyau da Haske Duk inda ta Shiga Tana Haskawa Ga wasu Sirrinka kamshi Dake Tashi Ajikinta Fatarta Ta koma kamar na Tarwada Saboda Santsi,Tasha kyau kamar ba ita ba.

Ita dasu B.kaita akama Kunshi ja da baki Suka kuma je gyaran Kai,Aneesa Ta sanya kayan alfarma sosai Na Cikin kayan Da kasim yayi mata ne Wanda Suka zo da Wasu nan Maiduguri Anyi Shagali Sosai Kowa kagani Cikin Farinciki musamman Anty Rahila da Anty Yagana kamar Sune Suka Haifi Aneesa Saboda Sune kan gaba Bisa Komai.

Yau din An Tashi da Shiryen Shiryen masu Zuwa Daurin Aure ne Daga Cikin Gida kuma Mata nata Shirin Wadanda Zasu Raka Aneesa Abuja Dagachan kuma Su Mikata kaduna,Daga Haraban Gidan Kuwa An Share ko"ina Motocin ya Ali dana ya Sunusi Waje Suka maida su,filin Wajen Aka Kawata Shi Da Fararan Kujeru Daga Cikin Falon su na Baki Dake Wajen Cikin gida Shima an gyarashi Tsab Saboda nan ne Waliyan duka bangarorin zasu Shiga Domin Gudanar da Daurin Aure gefe Daya kuma An Baza Tabarmu Abun Sai Wanda yagani.
Chapter 27 · 0% Book details