← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 76

Sashe 45

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Keken da Matsar gefe tana Fadin"Kana jin barci..? Ya kada mata ido Tashi tayi tana Fadin"Toh muyi karatu kafin mu kwanta gobe da Safe kuma ma cigaba da lbrinmu ko..?Ido ya Lumshe mata Mirmishi tayi tana kallonsa Har ta Dauko karamin Qur"aninta Gadon Ta Hawo gefensa ta Zauna ta Bude Tana Fadin"Bismillah mufara ka dinga yin naka acikin Zuciyarka kaji ko.? Ido ya kada mata taciga ba da Fadin"Kullum mukayi Waya da Mamata tana Fadamin cewa na Laminzi karanta Qur'ni koda yaushe,Shi alQur"ani mganin kowani Waraka ne"

Kallonta kadai yakeyi kansa yayi gefe Bisa Filon Ta Bude Suratul Maryam Tana Fadin"Suratul Maryam zamu karanta.."Daga Haka tayi Bismillah ta Fara karatun cikin Siririyar Muryanta mai cike da gardi Cikin Zuciyarta tana kara godema Bello Domin Shi ya Jajirce Har ta samu wannan Ilimin,Kullum Suna karatun islamiya lokacin Suna Mkranta sai da tayi Haddan Talatin,kafin su gama Tana ta karatu Shima cikin Zuciyarsa yake binta Cike da Farinciki Saboda gajiyarvtafiya yasa Lokaci kadan barci ya kwasheshi bata sani ba sai Zuwa chan ta Juyo ta ganshi ya Bingire kai yana Sauke Numfashi Miyau ya bata Gefen bakinsa Mirmishi ta saki kafin ta Saka Gefen Hijabinta ta Share mai Miyan daya Zuba Saukowa Tayi Daga kan gadon Ta maida Qur"anin bisa Side Drower din gadon,Sake komawa Tayi kan gadon ta Zauna kusa dashi ta karanto Addu"ar barci ta shafamai Duka Jikinsa Itama ta Shafa,inda kafafunsa suke ta maida kanta Bayan ta rage Hasken Dakin,itama bata wani Dade ba barci ya kwasheta mai Dadi

Karfe 4am na Asuba modibbo Ya Shigo Shashen Daada Lokacin Daada ma ta Dade da tashi tana ta salolinta knooking din Dayayi Shi ya tada Aneesa Shiko Bello ya Dade Datashi Daga kwance,Aneesa kuwa cikin barci ta Cukwikweye Kafafunsa Ta yi Filo Dashi Bata sani ba gashi tasakarmai Nauyi,bai iya Motsa kafar ba,ammh Aneesa ta gajiyar dashi Tashi tayi tana Salati ta Kunna Hasken dakin karaf ko Suka Hada ido kafarsa ta bi da kallo Lokaci Daya ta Zaro ido ganin inda ta kwanta Har ya Tara Jini Tsausayinshi ya kama ta abunka da Farin mutum Shafa wajen Tayi tana Fadin"Am Srry Bansan na Danne maka kafa ba wayyo.."Lumshe ido yayi ya Bude yana kallonta itama shi take kallo tana Fadin"Yanzu shikenan ko Cutar dakai za'ayi bazaka iya mgana ba..? Take fada tana Dauke kwallar idanuwanta lokaci Daya ta Sauko Daga gadon Hijabin Jikinta ta maida wanda ya ya zame Saboda barci kofar ta Bude Modibbo ya Shigo yana mata Tsiyan Taji dadin barci da Baffalensa ta kasa tashi.

Bata mai mgana ba Mirmishi kadai Tayi mai,Ita ta Taimakamai Suka Daukosa Daga kan Katifa zuwa Bisa Wheelchair,Abun mamaki bai bata Jikinsa ba Modibbo ke Fadamata bai cika yin Fitsari ba ko wani abu sai ya kwana biyu saboda bai da ciye ciye,Toilet suka Shiga Dashi Modibbo na gwada mata yarda yake mai wanka Dagosa yayi ita kuma ta taimaka suka ciremai jallabiyan Jikinsa,Runtse ido Aneesa Tayi sanda ya Zare mai Boxers din jikinsa,saboda bazata iya kallonshi Naked ba,ko Kirjinsa kasa Kallo Tayi ganin ko"ina ya Cika da kananun gashi,baya ta Juya musu Sadda Modibbo kemai Wanka Shiko Tsiya yake mata yana Fadin"Ashe baki son ladan.."Rufe baki tayi tana Fadin"Ina so ammh sai dai na mai da kaya ajkinsa bazan iya ganinsa Ahaka ba.."Dariya Modibbi yayi yana Fadin"Ba"a wanka da kaya ai...Mijinki ne bawani Abu ba kuma lalurace babu yarda za"ayi.."Itadai batace komai ba Kuma bata waigo ba sai da ya gama mai ya gogemai jiki da Towel,Aneesa ta mikamai Boxer dinshi da Vest dinshi ammh bata Juyo ba Bello sai kallon bayanta yakeyi,Sai da ya sakamai kana yace"Sarkin Tsoro toh an gama.."Sai lokacin ta Waigo ita ta mai alwala tace Modibbo ya Tafi zata shiryashi yace"a'a bari ya Shiryasa sai su tafi masallaci tare..Fita yayi dashi Daga Tiolet din itakuma ta maida kofa ta Rufe ta Tube ta Shiga wanka bayan ta saka kayan Bello Cikin kwandon Wanki koda ta Fito Daga wanka Har Modibbo ya Shiryasa ya Turasa Zuwa masallaci Itama manshafawarta ta shafa na olive ta Saka Wani Riga da Sikat yan kanti na kamfanin DKNY,ta saka Hijabi ta Tada Salla Raka"atanul Firjir tayi kafin tayi sallan Asuba bayan ta idar tayi karatun Alqur"ani Har Zuwa Wajen bakwai na safe sai Lokacin Taji Muryansu Falon Daada bata Fito ba gado ta koma ta Haye ta kwanta sai barci bata Farka ba sai Wajen 9am na Safe Shima Anty Rahila ce tazo ta tasheta Kan tazo ya Ali zai tafi,Fita tayi Falon Daada sukayi sallama da Ya Ali yamata Nasiha sosai Yatafi akan Sati mai Zuwa Zasu dawo gabadaya hadda su Mama Yana,Ya Muktar da Tawagarsa,suka rakasa Har Airport kafin ya Wuce Fadar Shugaban kasa suna da Meeting.

Tare suka karya da Bello ita ta Dinga bashi abaki,domin yaki cin Komai ko an bashi sai ya ki karba,ammh Aneesa na Fitowa ya Daina bata rai,Bayan Sungama Karyawa ne Ta Goggemai baki ta Turasa Suka koma Daki ta zaunar dashi kan kujeran Madubi ta saka wani Abun Aski Tana Fadin"Nidai bari na rage maka wannan Gemun ya maida kai wani Tsoho da yarintarka..",Tafada tana Tura baki kallonta yake bai ce komai ba Tsab ko ta Rage mai tamai gyaran Fuska sai gashi ya Fito sak Handsome Mr Bello,Yana ta kallon kanshi Amadubi ita kuma ta Haye saman madubin tana mai Dariya,Bayan ta gama mai ta Kwashe gashin ta kai Cikin Tiolet Ta zuba cikin dustbin din tiolet din ta dawo ta Zauna Agabanshi tana bashi lbrai saboda Samun Waje na Aneesa Harda Tsatsuniya take bashi Har da lbrin Rayuwarta a Borno Da Irin Dukan Data ci Wajen ya Ali tana bashi lbri yana kallonta wani waje tayi Dariya wani waje tayi kuka wani waje harda bata rai chan kuma sai ta Tura baki tana bata Rai,Shidai yana kallonta Zuciyarsa tana cike da Farinciki in yana Tare da Aneesa Shiyasa koda Minti Daya baya son Tayi Nisa Dashi.

******
Bayan Sati Daya da Dawowar Bello,Har Aneesa ta kware Wajen kula da Bello,wanka ne kadai sukemai tare da Modibbo Wani Likacin ma kafin yazo tamai,sai dai bata Ciremai boxer dashi take mai wanka in modibbo yazo ne yake Ciremai ya chanzamai,ammh wani bashi abinci,gogemai baki da komai ita ke Wahala dashi,Tare suke kwana Wani Lokacin Daada ke kama mata su maidashi bisa gado in Modibbo baya kusa,ko Ya Muktar wanda shima ke iya bakin kokarinsa,Aneesa kuwa bata Nuna gazawarta Duk da tana da karancin Shekaru Kowa ita yake Tsausayi Domin Nakasan Miji ba"abu bane mai Dadi.

Baki ta ko"ina sai Zuwa gaisheshi Suke,Su Abba kabiru da Duka iyalansa sunzo Hakama Ya Hashim da matarshi da Zubaida wacce ta Kurama Bello ido cike da Tsausayin Halin Daya koma,Sai da ta Share mai kwallah Zulfa ko da Suka zo Acikin Ranta Hamdala take da bata Aureshi ba Da yanzu ita ce ke cikin Wahala kamar yadda Aneesa ke Dawainiya Dashi,Mutanen Borno ma Sunzo Mama yana,mama Falmata ya Ali,Ya Sunusi,Da matansu da Ya"yansu Duka Suka kwana Daya Suka koma,Sai ga Malaman Chan Jami"ar Bayero,sun sake Zuwa Dubashi har da Dn na Sch din,lalle Bello mai Mutane ne Hatta da Gungun Malamai da Daliban Mkrantan kwatar-kwashi Tare da Jagorancin Principal din Mkrantan Sun zo Dubashi,Haka suka Tafi da kukan Tsausayin Halin da Bello ke Ciki,S.jibiya ma tazo ita da Mamanta Suka Wuni Suka koma Anty Yagana ma tazo ita da Mijinta suka kwana Daya Suka koma Hatta da Sauran yan"uwansa da suka rage na Jikamshi sunzo Duba Bello kowa kuma da Abunda yake Fadi,ana bada Shawaran Ayi mai na Hausa agani ko Allah zai saka adace.

Anty Aisha Tazo Daga kano,itama da Megidanta Hatta da Inna Rukayyah ma tazo Dubashi,Kasim ne kadai bai zo ba Kuma Abba kabiru yamai Waya kan Bello ya dawo Gida yaje Dubashi yace Aiki yamai yawa in ya samu Lokaci zai leko nan ko bai da Niyyar zuwa yanzu Duk da yana son Zuwa yaga Halin da Bellon ya koma yayi Dariya Sosai ammh yanzu Lokaci bai yi ba yadai kusa Lokacin da Aneesa zata koma tashi har Abada.

Mutanen Adamawa sun zo,Mota guda suma Baffa Hardo,wani Tsohon ne wanda yake Mtsayin Yaya ga Daada ya Tsufa Domin gabadaya Kansa Farin gashi ne tunda suka zo ya ke kallon Bello yana Girgiza kai Sai da Zasu Tafi ya kebe da Daada yana Sanar da ita yaga Sihiri mai karfi Ajikin Bello saboda Haka su Dage da mai karatun Qur"ani da kuma Addu'o'i Shima zai koma yayi Nashi kokarin Daada tayi mamaki ammh sanin Baffa Hardo yasan irin wannan Abubuwa yasa batayi mamaki ba ammh yace tayi Shuru da Bakinta da Haka suka koma Adamawa,zuciyarsa cike da mamaki waye yama Jikansa wannan Mugun Asirin.

Ki biya ki karanta cikin salama...

*ANITHA..*
8/19/20, 11:20 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

            *🅿�25*

Baffa Hardo bai gayama kowa ba Shikadai yake ta bincikensa,a binciken da yayi ne ya gano Sihirin Dake jikin Bello mai karfi ne kuma bazai taba Barin Jikinsa ba sai An Hako Abunda Aka binne da rai acikin Rami,kuma babu wanda yasan ina aka Binne wannan Abun sai wanda ya Aikata mugun Nufin Nashi,ko wanda aka Biya yasa aka aikata ma Bello haka domin a nakasa Rayuwashi cikin Nakasa da kasawa

Sai dai ya kira Daada awaya ya Sanar da ita a nemi Ruwan zamzam rika karantamai Suratul Yasin,Falaqi kafa uku Nasi kafa uku,Qul"huwal lahu kafa uku,ayatul kurusiya da Amanar Rasulu kafa uku uku cikin Ruwan Zamzam din arika bashi ya sha kuma arika Shafemai jiki dashi Safe da maraice,Shima Dagachan nashi Bangaren ya Dage danashi Addu"an Har Aga Abunda Allah zaiyi ammh al"amarin ya wuce Misali,Sihirin mai girma ne anyi aiki akan Sihirin Sosai.

*****
Chapter 45 · 0% Book details