← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 76

Sashe 70

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Wajen sallar Asuba Abba kabiru ya yanke jiki ya Fadi Aka kwasheshi Ranga Ranga zuwa Asibitin Federal medical Center Katsina Suna zuwa bayan gwaje gwaje suka samu Jinin Abba kabiru ne yayi mugun Hawa Hawan Jini ya Fadeshi,ya fadi Dalilin Haka ya samu Shanyewar Barin Jikinsa Guda Daya,iyalai sai kuka Kowa kasim yake gani aSilar Faduwar Abba kabiru, Abba garba kuwa Tuni Duniya ta Fitarmai Bisa kansa ganin Daki Daki Abunda ke Faruwa da Rayuwar Abba Kabiru kafin Ta Juyo kansa Domin yana da Tabbacin Shima Allah bazai barsa ba...Hakkin Rai da kuma Cin Dukiyr marayu bazai taba barin Ahalinsu su Zauna lafiya ba sai Abunda suka aikata ya Bibiya Ahalin nasu.

*******
Labarin da su ya Muktar suka zo mana Dashi bamai Dadi bane Naji na kara Tsanar Kasim Jin Shine Silan Laluran Mijina Kuma Gwarzona,Wanda naga Tunda suka Dawo ya Kule kanshi Cikin Shashenshi Ranshi bace Mutuwar iyayensu Ta dawomai Sabuwa har sai da ya Fitar da kwallar,ammh sai wata Zuciya ta Tausheshi da Fadin Ka karka damu Bello ka Zurama Sarautar Allah ido kabarsu da Hukuncin Allah kamar yadda ka Fada Tun afarko kadan suka Fara gani.

Da Labarin ciwon Abba kabiru ya samemu ba wanda ya Tsausaya musu sai Ya muktar Daya kwashi Jiki yaje Dubashi kuma ya Zubemusu kudi masu yawa na Hidimar Asibiiti Shikanshi Hashim din bawai Kudin Yake dashi ba,Gabadaya Albashinshi Dashi yake Hidimar gidanshi Data iyayenshi,kasim kuwa bai san komai ba sai Shanshanci da Neman matan Banza babu Abunda yake Tsinanama iyayen,Abba garban ma Ta wajen Hashim ne yake samun Wani Abu domin kaf Dukiyar da suka hamdama ta Riga Ta kare ci tayi tayi kamar gara kafin su ankara ta kare,Taimakonsu Allah Aikin da Muktar ya samoma Kasim da Hashim Shine Rufin Asirinsu,Hatta karatun Zulfa da Zubaida duk Hashim din ne ke Daukan Nauyin komai Bawan Allah Duk ya Rame Lokaci Yana ta karban Laifin iyayensa ba laifi yana ji acikin Jikinsa.

Kasim kuwa sai ka Tsausayamai in ka ganshi Saboda yadda ya koma,kwana Hudu da Faruwar Abun Sakon Takardan Korar Shi Daga wajen aiki Wanda Haruna ya kawo mai har gida,Tare aka sallamesu saboda an diba Sabbin ma"aikata sai aka Rage Malalata wadanda basu da wani amfani,Zama sukayi suna ta kuka Lokaci Daya Da nadamar Rayuwarsu...

Jaririya kuwa An sakamata Suna Fauziya,ba wanda yabi takan Yimata Shakika,Mama Sahura da iyalanta Tuni sun koma gida sai dai tana zuwa Asibiti Kullum Tana Taya Umma zama wacce ta zama mara mgana sai dai Sharan kwallah,ita kanta Mama Sahura jikinta yayi sanyi ganin yadda Komai yake Faruwa Daki Daki Tana cikin Fargaban Su menene nasu sakamakon,Tunda shi kam Abba kaburu yafara kirban nashi Tun agidan Duniya,Shi kanshi Hashim shida iyalansa sun koma shi kuma ya koma bakin aikinsa,Zubaida ma ya Tafi da ita saboda karatunta ita kanta Duk Tayi sanyi Inna Rukayyah ma ta koma ita dasu Hamdiya,Abba garba ke kwana Dashi Su Umma na Wuni Dashi Kasim kuwa na gida yana Fama da Rayuwa Shi ke Rainan Fauziya wacce ake bata madara ya tasata yana kallo yana kukan Tsausayin Rayuwarsa

*****
Sati Daya mukayi a Abuja muka koma Kano Saboda Bello zai koma bakin aikinsa,tare da Hibba na Taho Tunda sun samu Hutun Makaranta,mun samu gidan duk yayi kura Dani Dashi muka zage muka Tsabtace ko"ina ya fita yayo mana sabon Cefane Tunda ya wanci Wadanda muka bari sun lalace sai muka Fitar muka Zubar,Salihu megadi sai Murnan Dawowarmu yake,yana ta Tambayan Modibbo muna munyi kewarsa sai dai muna mgana Lokaci bayan Lokaci Dashi ta waya,yana chan yana cigaba da karban Hora a makaratan Military Sch Jos.

Kwana 2 da Dawowarmu Bello ya Fara Attending Lectures dinsa,Murna wajen Sauran Daliban da malaman ba"a gama Student din Daya Fara Dauka Har suna Ug 2 Abun ba Wuya sai ya koma yana Daukan Tunda ga Ug1 zuwa 4,Tamkar baya komai nashi bai chnza ba Tuni Sunanshi ya Dawo yan mata suka Fara Rubibinsa kamar Baya da Tsoffin Wadanda Suka sansa Tun baya da Sabbin Shigowa,Tun bana ganewa har nafara ganewa Tunda wani Lokacin sai muna tare naga ana kiranshi ko Turamai sako baya maida kai,Nima ban wani Damu ba sanin Halin Mijina na taka tsantsan da Aji bazai iya Kula wata mace ba.

B.kaita ita tazo har gida ta ankarar Dani Domin kaf Buk ta Dauka da Zencen kyawun mijina da ajinsa Yanmata basa Jin kunyar Fadar Suna son Mr Bello ko kuma yana Burgesu Daga masu Fadin ya iya Wanka sai masu Fadin Dreesing dinsa ke Daukan Hankalinsu suna Fatan koda gaisawa suka Rinkayi dashi masu Burin Auraansa kuwa suna da yawa Harda masu Shan Alwashin koda boka da mallam ne,Sai sun Aure shi Akwai wadanda ke Fadin in yana Turanci kamar su saceshi sukeji.

Ranar da B.kaita tabani labarin nan Kamar zan mutu Saboda Kishi,domin akan Abunda ya Shafi Mijina Bani da Wasa Dama ga cikin jikina Wanda ya Shiga Wata na Shidda na lura ba karamin Sakani Fada yake ba Abu kadan za"amin yanzu zan Hau sama nayi ta fada wani Lokacin baya Biyemin sai dai ya kyaleni yamin Banza na gaji na bari wani Lokacin kuma ya toshe bakina da nashi ya shiga yimin Salonsa wanda bana iya Juya baya Saboda matuka gwarzona yasan Hanyoyin da zai sakani natsuwa Lokaci Daya Duk Fitinata na nemeta na Rasa sai ma kara kwakwumarsa Danake kamar wata mage.

Koda ya Dawo Bayan Sallar Isha"i bai Dade ba yace mu Shirya muje Waje muci Abinci Duk da ina jin Fitinata ban musamai ba na Shirya muka Fita Zuwa wani Restaurant Cin Abinci Ni dashi da Hibba wanda Dukkanmu muka Sha Kwalliya sosai,Tunda yaga Take take na sai bai Tankani ba Har muka isa wajen yamana Odar abunda muke so,An kawo mana ko Faraci bamu yi ba,wata budurwan mace Daga bayanmu tataso cikin Fara"a tana Fadin"Wow...So masha Allah Happy Family Mr Bello..."Tafada tana Shafama Hibba kumatu....

Dagowa nayi ina Kallonta cikin Takaichi na Hade Rai ina Hararanta Shi kuma sai ya basar dan yake yamata kafin yace"Thanks..."Daga Haka ya maida kanshi yafara cin Abinci Kamar baisan da Zamanta ba,Kallonsa ta karayi tana Fadin"Am Nadra Famtami Ur Student Mathematics Depertement...Level 1..."Bai Dago kai ba ya Gyada mata kai ammh kamar mayya tanace har tana kallona tana Fadin"Hy....Madam.."Ko kallonta banyi ba sai ma naji kamar zan saki kuka ganin yadda take kure Mijina da manyan Idanuwanta ko Taba abincin banyi ba Na mike na Fizgi Hannun Hibba muka Fice Daga Wurin bai Dago ba sai ma Mirmishin Daya saki Lokaci Daya.....

Cikin Mota muka koma Sai Da yadau Lokaci kafin ya Fito niko kafin ya Fito na cika nayi Fam Abun Haushi Tare suka Fito da wannan mayar yarinyar kuma suka Jero har wajen Motarmu Bakinciki kamar nayi Bindiga,Ina kallonsu ta cikin Mota har yana mata mirmishi Shiyasa koda ya Shigo Bangaren Direba na Kara Tamke Fuska Harda kau da kai Kallo Daya yayimin ya Dauke kai Cikin Ranshi kuma yana Mai Jin Dadin yadda nake nuna Kishi akanshi.

Har muka karisa gida ba wanda ya Tanka Dan"uwansa,Ban Jira ya Fito ya Budemin ba kamar kullum na Balle murfin Mota na Fice Hibba ma Datayi barci Shiya Daukota,yakaita har zuwa cikin Dayan Bedroom Din Datake kwana Koda ya Shigo namu Bedroom din na Fito Daga wanka ina Daure da Towel gaban Dressing Mirrior ina Tura baki Kallona yayi baiyi Mgana ba ya Sabule Rigar Jikinsa na Kamfanin DKNY,da wandon Ina kallonsa ban Tankashi ba ya Fada Tiolet Tsaki naja ganin yadda yayi Biris Dani Sama sama na Shafa mai na Saka wata Rigar barci Doguwa mai Taushi yana cikin Tiolet din na Bude na Shiga Yana tsaye Cikin Shower yaga Shigowata Cikina Daya bayanna yake kallo sai karamin Bakina Daya kusa Tabo Hancina saboda yadda nake Tura bakin,ko Barayinsa ban kallah na Sagala Towel na Shanya cikin Hangers dinsa na Fice da Kallo yabini yana Fadin yanzu zan yi maganinki nasan Abunda kikeso.

Kichen na Shiga na Hada Tea nasha Domin Yunwa nakeji,wajen Hibba na Leka na Ciremata kayan Jikinta na saka mata na barci na mata addu"a na Sake Lullube ta da Blanket,ban damu ba Saboda Dazu kafin mu Fita Tasha Tea so nasan Batajin Yunwa bedroom dinmu na Koma na iske ya Fito yana goge Jikinsa da karamin Towel din Dake hannunsa,gadon na Haye ina Kara Dunkulewa cikin Bargo lokaci daya ina Juya Baya

Yana saka Wandon kayansa na Pjms,yace mata"Haka zaki kwana da yunwa..."? Tana jinsa ta masa Banza,Mirmishi ya saki kafin yace"Ok...Bari nazo nayi Lallashin My Anee..."Yafada yana yar Dariya bai saka Rigar ba ya Hauro gadon ina Jinsa ya Shigo Cikin Bargon ya Rikoni nayi Saurin Zamewa ya kara Rikoni Sai na Fara Kokarin kwacewa,Da Sauri ya Saka Duka Hannuwansa ya Rikoni yana Fadin"Wai ni Duk miye Haka ne...? Kinfa san bana son Fushin Ba Dalili.."Yafada yana kara Tsananta Rikon Daya yimin ganin na kasa kwace kaina yasa nayi lamo ajikinsa,Lokaci Daya na sakamai kuka kaina ya Shiga Shafawa yana Fadin"Shi..iii...Gayamin Laifina Matata ni kuma zan nemi afuwarki.."Cikin Jan kukan Shagwaba nace"To..ba...ba kai bane kowa sai cewa yake yana sonka ance achan Jami"a kamar mata su cinyeka kuma naga Shaida Dazu da muka Fita cin Abinci.."Nafada ina Kara Sakin kukan Shagwaba Da Tabara.

Kara Rumgumeni yayi Lokaci Daya yana Kasa Da Hannunsa Zuwa Cikina yana Fadin"Karma ki Fara saka wannan acikin Ranki my Anee...Mijinki Is a Teacher kuma Dole zai yi Harka da Cakude cikin Mata da Maza Buh karki Taba Zaton Ni Bello Wata macen zata Taba burgeni Bayan ke...Bansan sunayi ba Kema kin sani Tun muna Zamfara...Kina da Shaida akaina Mata basa gabana Tunkafin nayi Aure balle yanzu Da kika zama uwar D"anq ko y'ata Dake cikin ki...Ki Rubuta ki ijiye Bello Muhammed Jikamshi is For Aneesa Bukar Bulama...Only U...Only U Aneeesaa....."yafada Cikin Wani Salo,Da Sauri na Kara kamkameshi Cikin Farinciki Shi kuma yana ta Shinshinar Wuyana Cikin Fitan Hayyaci na Dago kaina na Hade bakinmu Waje Daya Cikin Shauki da muradi mai girma Shikenan Fushi ya Tafi sai kuma muka Hau Siradin Neman Ladan Allah.

Kibiya ki karanta cikin Salama.

*Anitha...*
8/22/20, 10:26 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

 
*Wattpad:Janafnancy13*
Chapter 70 · 0% Book details