Sashe 23
Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Fuska Umma Ta bata kan Tace"Ikon Allah Alhaji Shi kasim din yaro ne,balle ace sai an mai Nuniya ko Dole,ko kuwa gidan bakonsa ne? Naga in yana Bukata da kanshi zai Shiga Kichen ya Nema.."Tafada Tana Kauda kai Dariya Abba kabiru yayi kafin yace"Wannan ba Hujja bane,Koda yake Dan Gida amatsayin Bako yake Zuwa Tunda Ba Anan yake Zaune ba.."Baki Ta Tabe kafin Tayi mgana Kasim yayi Saurin Cewa"Ah"a Umma bakomai Na Riga na Tsaya Kan Hanya na karya sai dai Zuwa anjuma.."dariya Umma Tayi kafin Tace"Toh kaji ma kai da Kadamu kanka.."Harara ya Jefamata kafin ya Cigaba da Shan Tea dinshi Umma na Dariya kasa kasa,kasim ma sai da ya Murmusa sanin Halin Abba Kabiru yana da Fada Sosai Umma ce kuma Daidai Dashi.
Cikin girmawa Kasim yace"Abba Dama ina son mgana Dakai ne.."Abba kabiru na Sauke Kofin Hannunshi yace"Topha..Wata mgana kenan kasim..? Kan Kasim na Kasa yace"Kan mganar yarinyar Danake Nema ne.."
Gabadaya Suka Zubamai Ido Cikin Fara"a Umma tace"Masha Allah a Ina ka samu Yarinyar?kuma yar gidan Wanene ne..?Tafada Tana kallon Abba Kabiru Wanda ya Muskuta yana Fadin"Ina Jinka Kasim..
Cikin Karfin Hali kasim yace"Toh Shine Nake so Atura chan Gidansu din,"Abba Kabiru na Mirmishi yace"Ba Mtsala Yar Gidan Waye Yarinyar..? Cikin Sanyin Murya yace"Ai yar gida ce Abba Agidan Ya Muktar Take.."
Daga Abba Kabiru Har Umma Ido Suka Sakarmai kafin Umma tace"Gidan Wani Ya Muktar din..? Badai na Abuja ba..? Kai ya gyada kafin yace"Eh Nan Umma,kanwar Matarsa ce Anty Rahila.."Kafin ma Abba Yayi mgana Umma ta Zabura Tace"Badai Wannan Shegiyar mara Kunyan Aneesa ba..?
Kallonta Kasim yayi Cike Da mamaki kafin yace"Eh Ita Kinsan Tane Umma..?Dakuwa tamai kafin Tace "Bansani ba Uban Waye baisan Wannan mara Kunyar Kanwar Rahila din nan ba,Kul dinka Kasim Bada yawuna ba,nan in kanwarka Taje Huta ba Cin kashin Da bata mata,kai ko Zuciya baka Dashi Alhaji karka Manta Duk Bin kan yaron nan Bello da muke yaso Zubaida ammh Abu ya Faskara sai ma Tozarci ne ya Biyo baya,kai Saboda baka Kishin Iyayenka ko kunya sai kazo kace Zaka Aureta,toh bazaka Aureta ba Kowa ya Jika Nashi yasha.."Takarishe Mgana ta Huci.
Daga Kasim Har Abba Kabiru da Ido Suke Binta Jikin Kasim yayi Sanyi Cikin Kwantar da Murya yace"Karki ce Haka Umma,mganar Bello Dabam kamar ki Sako Aneesa Cikin Mganar nan babu Ruwanta,kuma In kin Duba Shi Ya Muktar din bai Da Mtsala Kuma kanwar Matarsace..."Harara Umma ke makamai Har yagama Mgana Ta Bude baki zatayi mgana kenan Abba Kabiru ya Dagamata Hannu yana Fadin"Ya isa Haka karima bana son Hayaniya.,Kai Kasim ka Hakura Tunda ga Abun Mahaifiyarka tace kuma ko ba Haka ba Nima Hankalina bai Kwanta Da yarinyar ba, in aure kakeso kaje ko"ina kakeso Cikin kasar nan ka Nema ni kuma Zan Shige Maka gaba.."Wani Faduwar gaba ta Samu kasim ya marairaice yana Fadin"Abba karkamin Haka Don Allah..Wlh ina son Aneesa bazan iya Auren ko Wacce mace ba, bayan ita.."Galala Umma ke kallonsa kafin tace"Kaji ko Alhaji Abunda nake Gudu kenan,Bata barshi Haka ba,kai ko Muktar din ba Haka kawai Rahilar Ta barshi ba,bakaken Kanurin nan ba Kirki ne Dasu ba,sai Su Juya maka kan yaro Kwata kwata bayaji baya gani Daga Su sai Danginsu Ina Dalili Wlh Ahir Dinka.."Kallonta kawai Abba kabiru keyi kafin ya maida Kallansa kan Kasim wanda Idanuwansa Suka sauya kala Sukayi Jajir Saboda bacin Rai.
Cikin Lallabi Abba yace"Ka bar Abunda iyayenka Suka ce basu so..Kila ba alherinka bane Tashi Kaje Allah yayi maka albarka..."Kasim yayi Sukutu kamar zai yi mgana Sai dai kuma ya fasa Ya Mike yana Rangaji ya Fice Daga Falon Umma Ta Rakashi da Kyafci Ta Juyo Zata Cigaba Da mgana Abba kabiru ya Daga mata Hannu yana Fadin"Kinga karima ya Isheni Hakanan Nace ya bar mganar bashi kenan ba..?mitar mene kuma zaki Dame Dashi.."Yafada yana Mikewa Tsaki ya Saki kafin ya Nufi Hanyar Bedroom yana Fadin"malama zo ki Fitomin da kayan da zan saka kafin na Fito Wanka ."Daga Haka ya Shige Cikin Bedroom Dinsa yana Jin Haushin Shigen Korafin Karima,itako da Harara Ta bishi kafin Ta Mike Tana Fadin"Eh dai koma menene naji Dadai na bari Kasim ya Auri Wannan yarinyar.."Dahaka ta Rufamai baya Tana mganganu Ita kadai.
Shiko Kasim Sheshensa ya koma ya Fada Bisa gado,hawayen Idanuwansa Suka Gangaromai Taya zai Fara Rayuwa ba Aneesa Yarinyar Data kwancemai Tunani Lokaci Daya,Duk barikin shi da Cin matansa bai ga kamar Aneesa ba,Yana ji Ajikinsa Itace Zatayi Daidai da Rayuwarsa ta Riga Ta zama wani Jigo na Rayuwarsa Wani Irin So yake mata Wanda baisan Iyaka ba,damuwa ta mai yawa Wanda Tayi Sanadiyar ya kwankwadi Giyanshi Wanda Rabonshi Da Tashanta Tunkafin ya Hadu da Aneesa Koda ya koma kaduna kullum yana Cikin Farinciki ne,Sai dai Matan banza Wanda yake Tabawa Domin Kullum gidanshi na Kaduna sai ya karbi bakuwa,bayajin zai iya Daina Neman mantan Shi,watakila in ya Auri Aneesa ya Daina.
Sai da yasha yayi Tatil kana Ya Kwarara amai nan bisa gadon,yakuma Sulale kan gadon yafara Sharan Barci sai yammah Kana ya Tashi Cikin kyamkyamin Halin Dayake Ciki yana Toshe baki ya Tashi ya Kwashe zanin Gadon ya Shiga Dashi Toilet ya Wurga Cikin Bucket din Kayan Wankinsa inda mai Wanki ke zuwa ya Kwashe ya Wanko ya gogesu Tas,kayan Jikinsa ya Cire ya Hada Dasu,wanka yayi ya Dauro alwala ya Fito,Ba laifi yaji Zuciyarsa Tayi Sanyi Shiryawa yayi Cikin Wani Farin yadi Riga da Wando,da Hula zanna Bukar,Sallar Azahar da La"asar yayi kafin ya Zari key din motarsa ya Fice Daga Shashen Gabadaya ko Shashen Iyayen nashi bai kallah ba ya Shiga Motarshi ya Saki Hon Megadi ya Wangalemai get yafice kamar zai Tashi Sama.
Gidan Abba garba Dake Gra Ya Wuce kai Tsaye yayi Sa"a Kuwa ya Sameshi Agida nan Kasim ya marairaice yana Rokonsa kan yaje ya Ma Abba kabiru Mgana kan ya Amince da Zabinsa,Abba garba ya Saurari kasim,ya kuma mai alkawarin Zaije Har gida ya Sami Abba Kabirun Su Tattauna,cikin Farinciki Kasim ya baro Gidan,shi kuma Abba garba Mama Sahura ya labartama Abunda Kasim yazo mai Dashi,Nan mama Sahura Ta bama Abba garba Shawaran ya Taushi Abba kabiru ya yarda Kasim ya Auri Aneesa ko Banza Wanj kusancin ne ya kara Kulluwa Ko babu komai Muktar bazai bari Bello ya Tozartasu ba Balle Rahila bazata Taba so Bello ya Tozarta Dangin Mijin Kanwarta ba,Da Wannan mganar Shima Abba Garba ya Shawo kan Abba Kabiru ya Amince,shima haka ya Dinga Nuna ma Umma Ammh Taki yarda Tace munafuncin Sahura ne,Bude mata Wuta Abba kabiru yayi Dole Taja bakinta ta Tsuke ammh Acikin Ranta Tana ganin Har Abada baza Tataba son Auren ba.
Kasim da Kanshi ya Kira Hashim awaya ya Sanar dashi Abunda Ke Faruwa,shima bai da Mtsala yayi Murna Ya sama Abun Albarka,Ranar da Kasim ya baro katsina Zuwa kaduna Ranar Abba Kabiru yama Ya Muktar Waya kan Mganar Aneesa da Kasim yayi Murna Sosai ya kuma ce Su bashi Lokaci zai Kira Yyayyin Aneesa Dake Chan Borno ya Sanar Dasu Abunda Ke Faruwa.
Batare da Bata Lokaci ba Washegari Tun kafin ya Muktar ya Fita ya Kira ya Ali Sukayi Mgana Inda ya Nuna Murnansa Sosai ya kuma ce ba Matsala,nan ya Muktar ke Sanar Dashi Cewa Suna Tafe Cikin Satin nan,sai ya Ali yace ba sai sun zo ba Shida ya Sunusi zasu zo Domin Aneesa ikonsa ne, Saboda Haka su zasu zo nan Abuja agudanar da komai ya Muktar yaji Dadin karan da Su ya Ali Sukamai Har Sai da ya Furtama Anty Rahila da Daada.
Bayan Sati Daya da Mganar Ranar Lahadi Su ya Ali Suka Diro Abuja dama already tun ana gobe zasu zo suka yi magana da ya muktar ta waya,shi kuma ya kira su Abba garba ya sanar dasu ,su ya Ali sun iso ba Dadewa Abba Kabiru Abba garba da Ya Hashim Suma Suka Iso gidan ya Muktar bayan Gaisuwa da Gaishe gaishe Suka Fara Gudanar Da Abunda ya Tarasu,Su ya Ali Sukace Mgana na Wajen ya Muktar Su Nasu Yan saka albarka ne,Jin Haka yasa ya Muktar yaji Dadi kuma ya tabbatar da Yabama Kasim Aneesa Har Abada,Ya kuma yanke musu Sadaki Dubu 100 ya Hashim ya Ijiye Dubu 200,sai mganar Saka Rana ya Muktar yace abarshi nan da Wata Shida Lokaci Aneesa Ta kammallah Makranta Tayi Candy Dinta,kowa yayi Na"am da Mganar Bayan Kowa yaci Yasha Suka Rabu Cikin Karrama Juna Daga Su Yaya Alin Har Su Abba Garba Juyawa Sukayi Ranar babu Wanda ya Kwana
Sai dai kowa yaji Saka Ranar Aneesa Kwatsam Abun mamaki ,kasim kuwa Da ya Hashim ya Kirasa yake gayamai Kamar ya Suma Saboda Murna Gashi ba Halin Da Zai gayama Aneesa Sai ya Kosa Sati Uku Ta Wuce yajema Aneesa Visiting Tare Da lbri mai Dadi,Zubaida Kuwa da Taji lbri Haka Ta Kira Umma Tana kara Zugata Tana Kuma Aibata Aneesa Ammh Umma bata da Yarda Zatayi Domin Abba kabiru yace in ya karajin mganar Ranta zai baci,Bangaren Zulfa ko Bata Wani Damu ba,Ammh Haushinta Daya Yadda Aneesa Zata Shigo Zuru"arsu Ammh Taji Dadi Tunda Yayan Zubaida ne Zata Aura Ko Banza Zataci Ubanta Dakyau.