← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 76

Sashe 3

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu Daɗe ba sai ga Uncle Aminu da Mr Bello Sun Ƙariso Yana Ɗauke da Wata bak'ar jakar Baya, Musabaha Sukayi da Aminu Suka Ɗanyi Mgana kafin Suyi Sallama don Uncle Aminu sai Next Week zai Tafi Sakamakon Ɗaliban SS3 Dasuke WAEC basuyi Darasinshi na Na Turanci ba shikuwa Mr Bello Da yake Malamin Lissafi Kuma Jiya Sukayi Paper, d'in Dat Why Shi Zai Wuce Gida Shima Kuma Uncle Aminu Dake Kano sai Sati na Sama Zai Tafi.

Shi ya Buɗema Mr Bello Ƙofar gaban Motan ya Shiga Suna Ƙara Sallama, kafin ya Rufo ƙofar Motar Mallam Inuwa ya Tada Motar Suka Fice Daga Mkrantan Uncle Aminu na Ɗaga musu Hannu Aneesa na Cikin Mota tana Makamai Harara Aranta tana Faɗin "Mugu sai Abi Wani Sarkin Ba Aneesa ba.." Ta faɗa Harda Yar Dariyanta Karaf Ko Suka Haɗa Ido da Mr Bello Yako Makamata Harara yana Faɗin "Don Ubanki Ɗauke waɗannan baƙaƙen Idanuwan naki Akaina ko nasa Mallam Inuwa ya Faka Motar nan na Wurgaki Dajin nan." Ya faɗa Cikin Tabbatar da mganarsa.

Jin Haka yasa Tayi Saurin Sadda Kanta Cikin Rawan Jiki Saboda Tasan Zai aikata Don Wanchan Term d'in ma Tafiya yayi ya barta sai da tabi Direban gidansu Salamatu Jibiya ta tafi gidansu ta Kwana Washegari Akazo Aka Ɗauketa, Haɗe Rai Tayi kanta ta maida Gefe Tana Ƙunƙuni Acikin Ranta Shiko Gyara Zama yayi yafito da Wayarsa yana latsawa Mallam Inuwa na gefe yana Tuƙi yana kanne Dariyarsa ganin Yadda Aneesa Take Tura Baki kamar Zai Tinko Ya Faɗi Saboda Ƙunƙuni.

Suko su Billy, su Aneesa Suna Tafiya ba DaÉ—ewa Kusan Tare Motocin Gidanasu S. Jibiya da Billy Kaita Suka zo nan da nan Kowacce Ta ÆŠauki Kayanta Suka Loda Amota Sukama Juna Sallamar sai sunyi Waya Kafin Su Dawo mkranta.

*How to pay....â‚?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?600...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �500 ne,VIP �1000, Single one �300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*Anitha...*
*20/07/2020...*✍️a: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_  

          *🅿�2*

#Home..

*ABUJA-Area-GARKI*

  ""Karfe 4pm da wani abu Motarsu Tafara Zuba Hon Abakin Wani Shimfideden Tamgamemen Get Dake Amguwar nan ta masu Kudi ko Nace Kusoshin Gwannati Wato Garki,Tunda ga Layin Sojoji ne ke Tsaye Har Zuwa Cikn Haraban Makeken Gidan Mai kama da Alkarya Guda,Aneesa Bakinta yaki Rufuwa Ganin Sun Kawo Gida,kafin ma Mallam Inuwa ya gama Daidaita parking a parking Space inda Tarin Rantsantsun Motoci na Alfarma ke Fake Sunfi guda goma,Kai Daga Ganin Gidan kasan Wani Soja ne Wanda yake da Mukami mai Matsayi agwannati Tun ballatana ma Dakarun Sojojin Dake yawo a Haraban Gidaan

Da sauri ta balle murfin mota ta Fito da gudu Ta Kwasa Zuwa Cikin Gida Da Jakarta ta Mkranta Goyo Abayanta.

Daga Mallam Inuwa Har Bello da Kallo Suka Bita Shi Mallam Inuwa Mirmishi yayi yana Kada kai, Shi kuma Uncle Bello Tsaki yaja Takaichin Aneesa kamar ya Kasheshi yarinya kamar Haihuwar Hauka Bai Tsaya Sauraran Gaisuwan Tsiraran Sojojin Dake Haraban Gidan ba ya Kama Hanyar Wani makeken Mension mai Dauke da upstair Inda nan na Shashen Uncle Bello Shi kadai Mai kama da Wajen da Za"a Saka mata Goma ma Babu Wanda ya Matsu Wani.

Itako Aneesa da ihun Kiran Anty Rahila Ta Shiga Wani Katon Falo mai kama da Aljannar Duniya Tana Fadin"Anty Rahila.,Daada Ku Fito na Dawo Hibbata kina ina Yau na gama Wahalalliyar Mkrantan nan Na Dawo gida.."Take Fada Daidai Sanda ta Shigo Tsakiyar Falon Tana Dariya Yayinda Duka Fararen Hakoranta Dake Haskata Suka bayyana.

Dariyarta da Murnanta Sun Dauke ne Lokacin Da Suka Hada Ido da *Zubaida* da *Zulfa* wadanda Ke Hakimce Kowacce Ta Samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Tana Dannen Waya Gefe Daya Kuma suna Kallon Katon Wani Magijin Talabijin Wanda yakusa mamayen Bangon Wajen, yan mata ne masu ji Da kansu,Zulfa ce Fara Zubaida kuma Chaculate Colour ce,Dukkansu Atare Suka Dago Suna Sakarma Aneesa Wani Matsiyacin kallo Lokaci Daya Suna mata kallon Sama da Kasa kafin Su Hada Ido Lokaci Daya Suka Saka mata Dariya Zulfa ce tace"Ikon Allah yan Makarantan boko ko Ansha Wuya..."Tafada Tana Kara Saka Dariya.

Abun ya mugun batama Aneesa Rai Ta Kallesu Awulakance Kafin Ta Saki Siririn Tsaki Tana Fadin"Aikin banza Tusa Alasifika Wanda Dai Ake Zuwa Domin Shi bai san Anayi ba Andai Fadi ba Nauyi Wlh.."Tafada Lokaci Daya Tana Runtumawa Da Gudu Zuwa koridon da zai Sadata da Sashen Anty Rahila Wacce Taji Karadin Muryan Aneesa Ta Nufo Falon Hannunta Rike dana Hibba,Suka Ci karo da Aneesa Ta Kwaso da Gudu.

Anty Rahila tace"Innalillhi Anne Bi Ahankali Mana.."Wata Mata nagani Baka mai kyau da Dogon Hanci Kallo Farko In kamata Zaka Ga Tsantsan Kamar da Suke da Aneesa,kallonta Aneesa Tayi kafin ta Rumgumeta Tana Fadin"Anty Rahila nagama karatu.."Take Fada Tana Dariya kafin ta Saketa ta Rarumi hibba yar Shekara Hudu Dake Mata Dariya Tana Fadin"Annee.."Cikin Muryan yara Cafeta sama Aneesa Tayi Tana Fadin"Hibbatullahi Kin kara girma.."Anty Rahila na Gefe Tana kallosu Tana Mirmishi Aranta tana Fadin"Anee Sarkin Rigima wai tagama karatu.."

Dagachan Falon Kuwa Zulfa Ta kalli Zubaida tana Fadin"Kan bala"i Dawa Wannan yarinyar Take..?"Wani kallon Wacece Sakara Zubaida Tamata kafin Tace"Da wanda ya Tanka mana Nidai kinsan bana Sakarmata Fuska Tunda na gane bata da Kunya Gashi Daada Ta Daure mata Gindi Ita da Daddy ba Daman Ayi magana sai Suce yarinta Ke Damunta.."

Wani Uban Tsaki Zulfa ta Saki kafin Ta Mike Tana Fadin"Ni babu Ruwana Tana Kawomin Raini Ubanta Zanci ai gwanda mu gidan D'an Kanin iyayenmu muke itafa Kalan Dangin Daga yayarta na Auren Daddy Shikenan Aka Taremana Agida.."Tafada tana Tafiya Zuwa Falon Anty Rahila da kallo Zubaida ta Bita Dashi Kafin ta Saki Mirmishi Ta Mike Tsam Tana Kara gyara Fuskarta Acikin Madubin Wayarta ta Nufi Hanyar da Zai Sada ta da Waje Cikin Wani Yanga Kamar Wata Wahainiya.

  Koda Zulfa fa ta iso Falon Na Anty Rahila Tuni Aneesa ta Dauki Hibba Sun Shiga Shashen Daada Tsohuwa mai Ran Karfe Kakarsu Bello da ya Mukatar Ita ta Haifi Mahaifiyarsu Hassatu,Anty Rahilan Kadai Ta Iske Tana ma Mai Aikinsu Jumai bayanin Abunda Zata Dafa Tunda Bello ya Dawo,Ganin Suna mgana yasa bata Tanka ta ba sai Ta samu Daya Daga Cikin Kujerun Falon Ta Zauna Wanda Shima iya Tsaruwa ya Tsaruwa An Zuba Dukiya Sosai.

Sai da Anty Rahila ta sallami Jummai kana ta Kariso Tazauna Kusa da Zulfa Tana Fadin"A"ah Zulfa ya"akayi ne...? Dan Sakin Baki kadan Zulfa tayi kafin tace"Wai ni Anty Rahila Tare da Uncle Bello Aneesa Ta Dawo..."?Anty Rahila ta Murmusa kafin tace"Eh Tare Suka Dawo.."Tafada Tana Gyara zaman Sarkan Azurfan Dake Wuyanta.

Baki Zulfa ta Washe Cikin Farinciki Tace"La! Da Gaske..?Shine bai Shigo ba..? Anty Rahila Ta Mike Tana Fadin"Ai kinsan bazai Shigo yanzu ba May be sai Daddy ya Shigo Tukunnah.."Mikewa Zulfa tayi Tana Fadin"Kai Naji dadin Dawowar Uncle bello Daman Domin Shi nazo Wannan Hutu bari na Shiga Kichen na hadamai Dinner kafin Anjuma.."Tafada Tana Nufar Hanyar wani dogon Korido Wanda Zai Sadaka da Kichen din Gidan Gabadaya.

Da kallo Anty Rahila tabita kafin ta Dan Murmusa Afili tace"Dama baki Wahalar da kanki ba Zulfa indai Bello ne zaki yi Nadama Kila Sai kinyi kuka.."Tafada Tana Komawa ta Zauna lokaci daya tana yar Dariya Tuna yadda Zasu kwashe da Bello in ma ya gansu Acikin Gidan Balle ma Wannan Rawan Kafan da Zulfan keyi kuma ko Ita Zubaida Itama Saboda Bellon Tazo Gidan Kuma ta sani Duka iyayensu sun Turosu ne Saboda Ko Bello zai Gani ya kyasa,kamar basusan Waye Bellon ba.

  Dagachan Shashen Tsohuwa Daada Kuwa Aneesa na Hango Zaune kusa da Wata Farar Dattajiuwa mai kimanin Shekarun 66 aduniya Daga ganinta kaga Bufullatana Ta Gaba Da baya,ga Zanensu na Fulani nan Agefe da gefen bakinta Kana ganinta Zaka Tsinkayi Inda Bello ya Samu Hasken Fata da Kuma kyau,bata Sha Wuya ba Domin Kudi da Jin Dadi Sun Zauna mata zaune take kan Wani Lafiyayyen Jan Cafet Dake malale Cikin kayatacen Hadadden Falon wanda yaji Alatun Rayuwa Tana Sanye da Riga da Zani da Dankwali Hakoranta Suna Washe ne har Hakoran Makkanta Guda Biyu Suka bayyana Daga ganin yadda Take Dariya Tana Dafa Cinyar Aneesan zaka san Lbrin da Aneensa Ke bata ya mata Dadi Sosai

Kanta Daada ta Shafa kafin tace"Dakata da lbrin nan Anee Hakanan Tashi ki Tube kaya Kiyi Wanka kiyi sallah kici Abinci sai kizo mu Cigaba Ko kin manta yau Tare zamu Kwana Kiyi Ta bani lbrin Mkrantar Har ki gaji kinji ko.."Aneesa Na Dariya Ta Mike Tana Fadin"Hakane Kuwa Daaada Naji Dadin Gama Karatun nan Dama na gaji Da Mkrantar Da Wahalar Cikinta.."Daada tace"Koni nayi Murna Ina Dadi Irin Wannan Uban Wahalan Dakike bani lbrin Ana baku Ai Shima laifin Mukatar din Dayake Biyema Yaron nan Bello ne"Aneesa na Dariya Jin Daada ta Ambaci bello wanda ba ta iya kiran sunansa saboda sunan marigayi mijinta ne kakansu Bellon kenan

Bedroom dinta ta Shige wanda ke kusa da na Daada ta Fada Tiolet Cike Da Fara"a Domin Tasan Daada bazata bari Akara maidata Wannan Shegiyar Mkrantar mai Aljanun Tsiya ba.

Shigarta ba Dadewa Anty Rahila ta Shigo Dauke da Trolley din Aneesa da Jakunkunanta Guda Biyu Tana Fadin"Aneesa ba Hankali chan ta bar Kayan Nata Sai da Mallam Inuwa ya Shigo Dasu.."Daada dake Wasa Da Hibba Tace"Ina Ruwa Anee yan Mkranta Tadai Shigo ita kan Abunta.."Tafada tana yar Dariya Cikin Bedroom din da Aneesa ta shiga Ta Shigan Mata da kayan Ta Fito ta isketa Haryanzu Tana Wanka Bata Fito ba nan ta Zauna Falon Daada Suna Cigaba da Hira Sama Sama.

****

Zubaida kuwa Cike da yanga Ta Isa Mension din Uncle Bello Wanda Ke upstairs Matattakalan Benen Tafara Haurawa Tanayi Tana Kara gyara Tafiyarta Har ta Iso Kofar Falon Nashi Ta saka Hannu zatayi Kooking kenan Taji Kofar ta Bude Kanta Cikin Jin Dadi Ta Tura kanta Falon da yar Siririyar sallamarta Lokaci Daya Kamshin Turaransa na MAN ya Daketa Wanda Duk Duniya ba Jikin Wanda Take Jin Dadin Kamshin Turaran Irin Jikin Uncle Bello Wanda Hatta bangarensa ma ya Saba da Kamshin mai Dakin..
Chapter 3 · 0% Book details