← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 76

Sashe 39

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ya muktar ya saki kafin yace"Daada ku Shirya mu tafi Saboda Aneesa yarinya ce bazata iya da Bello ba.."Da Sauri Daada ta mike tana Fadin"Toh...toh...Muntari mu Hanzarta muje muga Halin da Bello ke ciki ."Bai kara mgana ba ya Fice Anty Rahila ta mara mai baya basu Tsaya Daukan Komai ba Daada ta Dauko mayafi Haka Anty Rahila tana goye da Junior ya Muktar na Dauke da Hibba Wayarsa kadai ya Dauka Suka Fito mallam Inuwa ya Tukasu Sauran Tawagarsa kuma suka Rufa musu baya,kafin su Fita Anty Rahila tama su Alheri magana tare da Sanar dasu su kula da gidan sai sun dawo suma sun jajanta lamarin Jin Mr bello ba lafiya.

****

Aneesa ta Salubar da Wayar Daga Kunnanta tana kara Sautin Kukanta,Bello yana kallonta yana so yayi magana aammh kuma ya kasa sai dai yana kallonta da idanuwansa Wanda Suka gaji da Zubar da kwallah,Aneesa Ta matso Kusa dashi ta Rike Hannayensa tana kallonsa kai Tsaye bata samu zarafin mgana ba illah Fashewa Datayi da kuka Saboda Tsausayin Dayake bata in ta kalleshi gefen gadon ta jinginar da kanta tana kuka kuka mai cin rai da Tsausayin bawa sun Dauki Tsawon Lokaci Ahaka kafin ta mike zaune tana Share kwallah kallonsa tayi tana Fadin"Nasan kagaji da kwanciya ko..?kuri yayi mata da ido cikin zubar hawaye tace"Nasan kuma kana bukatar achanza maka kaya da wajen kwanciya ko..? Lumshe ido yayi ya bude yana kallonta Kuka Aneesa takara Fashewa Dashi kafin tace"Ya zanyi...?bansan ya zanyi ba.."Take Fada tana kara Dukewa kuka nakara Ciyota nan ma sai da Tagaji da kukan kana ta tashi ta Fara Kokarin Dagashi ammh ta kasa sai ma Fadawa datayi kanshi tana Nishi Dagowa tayi tana kallonsa tana Share kwallah rasa yadda Zatayi dashi tayi sai kawai ta Fice Daga Dakin tana Share kwallar Tsausayin Halin da Bello ke Ciki.

Haraban gidan tafita tana kuka Salihu megadi na ganinta Haka Hankalinsa ya tashi yana Tambayanta ko lafiya Cikin kuka Aneesa tace"Don Allah kazo ka taimakamin..."Cike da Tsausayinta ya kalleta kafin yace"Jikin Alhajin ne...? Kai ta gyada mai kafin ta juya ta koma Cikin Gida yabi bayanta Tiryan Tiryan har Zuwa Bedroom din Bello Halin da Salihu megadi ya Iske Bello aciki Shima sai da yamai kwallah Cikin Hawaye ya Durkushe gaban gadon yana Fadin"Hasbunallahu wani'imal wakil..Alhaji Meyafaru dakai haka..? Aneesa Dake Sharan kwallah kanta haryafara Ciwo saboda Kuka tace"Don allah ka taimakamin mu Chanza masa Kaya..."Tafada Tana Share Hanci.

Cikin Sauri ya mike yana Fadin"Toh..Toh..Allah Sarki.."Yake fada yana Share Kwallah Shima,wajen kanshi ta Dago Shi kuma yakama wajen kafafunsa,Suka Sauya mai Wajen zama suka maidashi Tsakiyar gadon Saboda Wajen ya Riga ya baci da Fitsari,Da hanzari ta Bude Wardrop dinsa ta lalubomai Jallabiya,ta mikama Salihu maigadi,ita tayi karfin Halin zaremai Rigar Barcin dake Jikinsa Tana yi tana Sharan kwallah,Haka zalika ita ta Ciremai wandon barcin jikin Nashi Salihu na taimakamata Kasa Juran kallonsa tayi baya ta juya tana Fadin"Ka chanza mai Wandon Jikinsa bazan iya ba.."Tafada tana Share kwallah Wajen Wardrope din ta koma ta Sake Ciromai ,Boxers ta mika ma Salihu Duk da Haka bata Juyo ba Salihu megadi shi ya ciremai boxers din Jikinsa wanda yagama jikewa da Fitsari,Ya saka mai wanda ta mikomai wajen saka Jallabiyan ne sai da ta taimakamai,Suka maidashi suka kwantar yana binsu da ido wannan karon babu hawaye sai dai Daga ganin yadda yake Lumshe ido zaka Fahimci Tsantsan Halin Dayake Ciki.,Kwashe Kayan Da Suka ciremai tayi ta Shiga Tiolet dasu Ta Jikasu cikin botiki ta fito.

Nan Salihu megadi ya Fice ya barta tana Zaune Akasan Cafet din Tayi Tagumi Lokaci bayan Lokaci Tana Share kwallah,Wayarsa Dake yashe akasa ta dauka kodata Duba Wayar ta mutu,Saboda Tsabar kira Tun Safe,tanan nan Zaune tana kalllonsa Lokaci Bayan Lokaci Shima yana kallonta Kafin kuma taga ya Lumshe idanuwansa Sai ya Dade Ahaka kafin ya sake Budewa Tun tana Share Hawaye har idanuwanta Suka bushe Tunawa Datayi batayi sallah bane yasa ta Zabura ta mike tafada Tiolet dinshi ta Dauro alwala,Ta Fito kenan sai Ta Tuna
Bata da Hijabi adakin,Da hanzari ta kama hanyar Fita daga bedroom din sai taji kamar yana kallonta tana juyawa Taga idanuwanta Akanta Tsausayinsa ya kara kamata cikin muryan kuka tace"Zan dawo hijabi zan Dauko..."Yana so yayi mgana aammh kuma ba Halj Lumshe ido yayi bude har ta Fice Daga Dakin Zuwa Dakinta Hijabinta ta Dauko,Ta Dawo bedroom din Yana kallonta ta kabbarta sallah Shima yana so Tun Dazu yace Zaiyi sallah ammh babu baki kuma babu alamar da zai nuna Haka.

Bayan ta idar Da sallar isha"i Shafa"i da Wuturi tayi Ta Dukar Dakai tana Addu"a tana Hawaye tana waigowa suka hada ido Cikin Tsausayinsa tace"kana so kayi sallah...? Lumshe ido yayi ya Bude mata alamar Eh mikewa Tayi ta cire Hijabi kafin ta isa kusa Dashi Dakyar ta iya Dago kansa ta karamai Wani Filon Abayansa yadan Dago,baya Taja Tana Numfashi tana kallonsa sama ya maida Idanuwansa kawai yana Kisima yana alwala kallonsa Take Cike da Tsausauyi Lokaci bayan Lokaci Tana Sharban kwallah.

Yanayi miyau na Zuba ta gefen bakinshi,in Aneesa na kallonsa Ji take kamar ta saka kuka ammh Kuma Zuciyarta ta kekeshe da Tsausayin Bello tanan nan Zaune ta tasashi gaba tana kallonsa Karfe 10pm na Dare Aneesa Taji karan Bude get, da Shigowar Motocin Tawagar ya Muktar Salihu maigadi ne ke musu barka da Zuwa Basu da Sukunin karbawa Suka nufi Cikin Gida Daada ce agaba kamar tayi Tsintsuwa ta gabanta Gaban Bello...

Sun wuce Falon Farko Suka ji basu Ji motsin kowa ba Sun isa Falo na Biyu Suna Rafka sallama Aneesa Ta Zabura ta mike ta Bude Kofa  idanuwanta Sun kumbura saboda kuka.Tana ganin su Daada ta isa jikin Daada Tafada lokaci Daya tana Sakin kukan Datake makalewa Tundazu Cikin zuciyarta Rumgumeta Daada Tayi tana Fadin"Bar kuka Aneesa.."Take Fada itama tana Sharan kwallah Ya Muktar bai tsaya ba yanufi Cikin Bedroom din Dauke da Hibba Datayi barci Anty Rahila tabi bayanshi Daada ta Riko Hannun Aneesa suka mara musu baya Aneesa nata Sharan Kwallah...

Dukkansu Turus sukayi akofar Dakin ganin Bello gashi kwance Filon da Aneesa ta karamai baya Dashi ya Zame kanshi yayi gefe miyau na Zuba Daga bakinshi Jikin ya Muktar ya Shiga Rawa Daada kuwa sai ta Damke Hannun Aneesa saboda jitake kamar Zata Fadi,Anty Rahila ko Tana kallonsa Tana Hawaye Lokaci Daya tana Fadin"Bello..."Cikin Wani yanayi mai kama da Dimaucewa.

Cikin Sanyi jiki ya Muktar ya karisa gefen gadon ya Durkusa Bisa gwiwoyinsa bayan ya kwantar da Hibba gefen gadon,.yana kallon Bello Bakinsa na rawa Cikin Taruwan Hawaye acikin idanuwansa ya Riko Hannunsa Guda Daya yana Fadin"Bello...Bello...Kai ne Haka...? Yafada Duk yadda yakai da Dauriya da Taurin Zuciya sai da Hawayen idanuwansa suka Zubobganin yadda Shima Bellon ke kallonsa Tunda Suka Shigo Yake Tsiyayan Hawaye lokaci Daya Muktar ya Rumgumesa kawai ya saki Muryansa Cikin Kuka yana Fadin"Ka tashi don Allah..Bello kai kadai nake Dashi Dan"uwana Danake gani naji Dadi..Don Allah katashi Zuciyata tana Rawa in na kalleka acikin Wannan Halin Daada...Zoki gani Zokiga yadda Bellonki ya Dawo.."Yake Fada yana Sakin Shesshekan kuka.

Daada Dakyar ta saki hannun Aneensa ta karisa ga Bello da Muktar Hawaye na Zuba Cikin kwarmin idanuwanta Kallon Bello take bayan ta Hau kan gadon ta Karbi Dayan Hannunshi ta Jimke Cikin nata,Kallonta yake Cikin idanuwa,Hawayensa na Zuba Lokaci Daya Da Miyan bakinsa Hannu Daada ta saka tana Share mai gefen bakinsa Take Fadin"Innalillahi..Wa"inna illaihirraju"un..."Allah gareka muke Muka gareka zamu koma Allahuman Ajirni fi musubatihi..."Take Fada kafin itama ta kifa Hannun Bello kan Fuskarta tana kuka mai Taba Zuciya Bello kuka ya Muktar kuka Daada Kuka Aneesa ma Durkushewa Tayi tana Kuka Hakama Anty Rahila kukan Take,Sosai na Tsausauyin Bello da Makusantanshi.

Sai da Suka yi kuka mai Isarsu kana ya Muktar ya Dago ya saka Hannu yana Sharema Bello Hawaye da miyau lokaci Daya yace"Na maka alkawarin koda Zan Rasaka Duka Dukiyata zan Tashi na Nemarka lafiya Bello..Da Izinin lahi zaka warke zaka kara takawa da kafafunka Dat iz my promise.."Yafada kafin ya mike Lokaci Daya yana Share kwallah Dakin ya Fita yakoma Falo wayarsa ya Fiddo ya lalubi Dr Nura na Asibitin Murtala Aminu kano yaci Sa"a bugun Farkon ya Daga Ko gama gaisawa basuyi ba Muktar yake sanar da Dr.Nura zai kawomai Wani Emergency yanzu Cikin mamaki Dr.Nura ke Fadin"Bataliyan Sojan kasa Waye ba lafiya kuma..?

Cikin Share kwallah Muktar yace"Bello ne...Kanina ne Bello Muhammed Jikamshi.."Cikin Tashin Hankali Dr.Nura yace"Subhannallah meya sameshi..?.

ya muktar ya Hadiye Kukan Dake Cin Ranshi yace"Don"t know How to Explain Dr.Buh dai muna Tafe Dashi yanzu..? Yafada yana Jin kamar ya kara rushewa da kuka,Jin Haka yasa Dr.Nura ya amsamai asanyaye Suka yanke Kiran Dr.Nura da Muktar abokai ne Tun na yarinta Domin tare Sukayi primary sch dinsu har Zuwa matakin Secondry kuma Tare Suka Tafi kasar Chicago Hado Digree dinsa na Farko Shi Bayan sun gama ya Dawo yayi Joining din Amry,shikuma Dr.Nura yatafi kasar Malesia ya karancin Liktanci Bangaren kashi ammh.

Ya Mukrar bai koma Dakin ba sai da ya Zauna Bisa Daya Daga Cikin Kujerun Falon ya Rufe Fuskarsa da Tafukan Hannayensa ya Sharbi kuka son Ranshi Sai da yayi ya koshi kana ya Share Hawayensa ya Mike ya koma Daki Haryanzu kukan Suke Babu mai Rarrashin Wani Daada gwanin ban Tsausayi ga Tsufa da Jarabawan Allah eh mana Jarabawa ce mana Wanda bawa bai yi Tsammani ba,bai kuma bai isa ya tsallake ba

Dafa Kafadan Daada ya Muktar yayi wacce ke Faman Share ma Bello Hawaye da Miyan Dake Zuba Daga bakinsa,yace"Daada kibar kuka Hakanan Jarabawan Ubangiji ne Addu"a zamu tamai Allah ya bashi lafiya.."Daada na kallon Bello take Fadin"Dole nayi kuka Muntari Kaduba kaga Bello fa lafiyanshi kalau Aneesa Tace Jiya koma miye Cikin Dare ya sameshi Zuciyata na Bugawa ina Tunanin meya samu Bello Haka..? Ko kuma waye yama Bello Haka..? .
Chapter 39 · 0% Book details