← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 76

Sashe 12

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watan Aneesa Biyu Ko Visiting Bello bai bari An Zo mata yace Kada Wanda yazo in ba Suna Son Karatun Data Fara ya Tsaya bane Don Wuya da Dole Aneesa Ta maida Hankali Akaratu Tana Enjoy din Sabuwar Rayuwarta Yanzu Sun zama kawaye Sosai Su Uku Dukka inda zasu Tare kuma kullum In Aka Tashi pref Suna Zuwa Islamiyan Yammah basu Dawo wa Hostel Sai Angama mangariba da Isha"i Anyi Ta'alim Hade da Addu"o"in barci kana Suke Komawa Hostel Kafin Aka C.s Kowa ya Kwanta yanzu Sun Waye basu karban Tuwon Dare sai dai Su Jika Complex da madara Su Sha Ta Wannan Fanni kan Aneesa na Shan Gata Domin Hatta pad bello ke Siyan mata Babu Abunda Tanema ta Rasa Sai jin Dadi Acewarta baya mata da Hausa Dukanta yake in Tayi Wani Abu bayama Nuna ya santa Indai Aharkan Karatu ne Noma Kuwa Sun Sha Zuwa Quarters Dinsu Yasasu Noma tun barema Ita da B.kaita da basu Jin Mgana Arana In basu Fada da wasu ba basajin Dadin Seniors kuwa in Suka Rainaki kin Bani Musamman ma Kabila Arnakun nan Sunfi Raina Musu Kura Gashi Aneesa babu Abunda ya Ragu Ara shin Kunyarta ma sai ma Karuwa yake Zuciyarta ta kara Kangarewa da Rashin Kunya da Rashin Mutumci Kaf Makrantan Kwatar kwashi Ba Wanda baisan Aneesa Bukar Bulama ba....

Kafin Su Samu Hutun First Ta Koma Gida Anty Rahila ta Haihu Koda Ta Koma ta Isketa da yarta Hibba kyakyawan Hafsat Sunanta Cemata Hibba,Dawowar Aneesa Daga Mkranta yabama Kowa mamakin Ganin Abubuwanta Sun Chanza kamar ba Ita ba Sai dai More Rashin Mutumcita sai ma Karuwa yayi Domin Cikin Hutun Sukaje Borno Ita da Anty Rahila wai ya"yansu ya Ali Sun Ci Ubansu da Duka Da anyi Mgana Sai Tace Suma Haka Babaninsu suka mata🤣Aneesa na Lokaci fa Anty Yagana Datazo Suka Hadu kuwa Sai da ta Mangare mata kai Tana Fadin"Ja"iran yarinya ta bamu Ciwon kai,Anty Nafi Kuwa Zaginta Ta kama yi Tana Dunguremata kai kuma bakomai Takejin Haushi ba Sai yarda Aneesan Ta samu Jin Dadi da Chanjin Rayuwa Haka Ta Dingama Anty Rahila Korafin Wai Suna Kashemata Kudi Saboda Kunata da Rashin Godiya Cikin kayan da Aneesa tazo Dashi sai da Anty Nafi ta Dibarma Babbar Yarta Sanah,wai Sun ma Aneesa Yawa itako Abun bai Dameta ba Bata Kuma gayama Kowa ba sai da Suka koma Take gayama Anty Rahila Wacce Mamakin Anty Nafin ya Cikata,Tafa Zoma da Sanah kaya ammh Idonta na kan Aneesa Sai Tuna yarda Ta Dinga mata Surutun wai Sun bar Aneesa na Jin Dadi bata komai Agida Zasu kara Sangarta ta bata dai Kula Anty Nafin bane Ammh TaFahimci Daukan Aneesan Datayi bai mata Dadi ba, mama Falmata Kuwa Ko bata Fada ba Taji Dadin Ganin Aneesar Tayi Hankali ba kamar Da ba,Duk da babu Wani Shakuwa aTsakaninsu Ammh Akwai Soyayya da Shakuwar Uwa da yarta.

Kwanansu Hudu Suka Dawo Abuja ba Dadewa Takoma Makranta Wannam karon ma Da Kuka Aka Koma Sai dai bai kai na Farko ba,A term din ma Aneesa Ta yi kokari Sosai Tamaida kai ga Karatu Ammh Masifarta da Tsiwa bai Ragu ba Kullun a Hostel dinsu cikin Dogon Daki sai Anyi Fitina da Ita Batajin Mgana Kullum Cikin kai ma Mr.Bello kararta Akeyi Ya Kirata Har Quaters Dinsu yasata up And Down bayan Tagama yasa Ta Shara Da Noma sai ta Jigata zai Sallameta,Wadanan Abubuwa Su Suka kara Wutar Kiyayyar Bello Acikin zuciyar Aneesa,Shi kuma Ba Itace ya Tsana ba Hallayarta ya Tsana Lokaci bayan Lokaci Wani Abun nata ma Dariya yake bashi da Mamaki.

Tafi Tafi Haka Rayuwa Ta Cigaba da Gangarawa Har su Aneesa Suka gama Jss1 Suka Shiga 2 sai A second Term Kana Su Daada Suka Zo Mata Visinting Ita da Anty Rahila Harda Yaya Muktar Wanda Mkrantar Kwatar_kwashi Ta Rude da Zuwan Chief Amry Of Staffa,na kasa baki Daya Mutane kuma da Sauran Dalibai Suna Mamakin Yadda Bello yake Koyarwa Alhalin ya Wuce nan Nesa ba Kusa ba Kuma baya Nuna Shi Wani ne Domin Ko Motar kanshi Bello bai yarda yana Zuwa da Ita Mkranta ba Sai dai in zasu Dawo Mallam Inuwa ya Kawosu In Anyi Hutu yazo Ya Daukosu Shi Mutum ne Mai karancin Fara"a Gashi Miskili marason Hayaniya Fushi da Saurin Hasala Ko Acikin Mkratan bai Cika Shiga Abunda bai Shafeshi ba,Shi Abunda ya Sani Koyar da Dalibai,da Kuma Lura da Tarbiyansu.

Suna Gabda Shiga Jss3 Uncle Aminu yazo Mkrantan Wanda Tasu Tazo Daya da Bello Kuma Suna Cikin Gida Daya Cikin Lokaci kankani Suka Kara Haskawa Ciki Mkranta Saboda kyansu da Kwarjinsu Uwa uba kuma basu da Wasa Kusan Suna gyarama Kowa zama Acikin Mkrantan Principal kuwa Tafi Kowa Alfahari da Samunsu Acikin Mkrantanta,Wasiku ko na Dalibai bello ya Tarasu ba Adadi Hakama Uncle Aminu basu Maida kai ne Kawai Kuma ba"a Iya Taransu Saboda Suna da Kwarjini Ko Cikin Aji ne In Suna Koyarwa kika kawo Musu Wani Wargi yanzu zasu Waje Dake Su Zane Miki Jiki.

Bello yasan Mata dayawa Suna Sonshi Kuma Suna Rubibi Akanshi Ammh bai Taba Nuna ya sani ba,Bai Taba yarda yabama Wata Daliba Fuska ba,Bayan Aneesa ba Wacce ya ke Shiga Harkanta sai ko Kawayenta Su S. Jibiya Wanda Suke kara Girmamashi Amtsayin shi na Malaminsu Kuma Yayan Aneesa Ammh Ita Akoda yaushe Fadi musu Take Ita ba Dan"uwanta bane Babu Abunda Suka Hada Mutane dadama Suna Mamakin yadda Aneesa ke Nuna Tsana ga Bello ko Jin Haushi Masu kama Kafa da Ita,Dayake su B.kaita Sun san Halinta sai Sukaci Mganin Zama da Ita musamman ma S. Jibiya Gwara B.kaita Wani Lokacin Suna Taba Tsiyan nasu.

   Babu Ranar da Su Aneesa ke Shan Wuya Amkranta Irin Ranar Alhamis Ranar General Work Kenan Ko'ina sai Angyara An Tsabatace ga Bayinka basu da Kyau Sosai Domin Akasa Ake Kashi Haka Seniors Zasu Sakasu Kwashewa da Kwano koda Chokali,Abun na Cima Aneesa Tuwo Akwarya Tagaji da Mkranta Ta Gaji Sosai Ammh yazama Dolenta Domin Uncle belli na Lura da Duka Motsinta,Sunfi Ji Dadin Ranakun kamar Ranar Laraba Sport,da Kuma asabar Da"ake Inpection Ranar Hause kenan Inda za"a Bama Dukan House din Dayaci na Daya Kyauta dama Kuma a K'a kida Hause dinka Toh Hostel dinka Kuma Kalan Check Dinka Toh Su Aneesa Suna Jida Ranar Saboda House dinsu ke Zuwa Na Daya Duk Sati ba Laifi Suna da Kokarin Tsabaceshi Ammh da Zararan Angama zai koma Gidan Jiya.
 
Hutun da Aneesa Ta Dawo na Farko bayan Shigansu Jss3 Su Zulfa Suka Fara Zuwa Hutu,gidan Ya Muktar,Wanda Bello kamar yayi Bindiga Saboda Fushi Da Farko ma Yaji yayi ya Tafi Yola sai da Daada Tayi ta ban Hakura Awaya kana ya Dawo Bai sani ba Ashe Daga Zulfa Har Zubaida Kowacce Sonshi Takeyi Kuma Daga Abba Kabiru Har Abba garba Kowanne ya Turo yarsa ne ko Bello yagani ya kyasa Wanda Tunda Abun nan ya Faru ko Sunzo Abuja in ba Ya Muktar ya Matsamai ba Ko Kallo basu isheshi ba in ko suka samu Sa"a ya gaishesu sai dai Daada ko ya Muktar Sun Matsamai Ammh bacin Haka Su kansu Sun Fikowa sanin Basu da Wata Daraja a idon Bello.

Hatta Inna Rukayyah Dake Kano Tana Zuwa Tayi Kwanaki Wai Su yanzu Suka san da ya"yan Muhammed Wanda Sukayi Sanadiyar Mutuwarshi Har Lahira Shida Matarshi,In Bello ya Tuna da Mganar Kamar ya Mutu Haka yakeji Saboda Bakiciki Rayuwa Uku fa Su Abba Kabiru Suka Salwartar Ammh ace baza"a Dauki Wani Mataki baa Domin Daada Ta basu Lbrin Irin Rayuwar da Muhammed Yayi Shida Kanwarsa Hidiyar Har Allah yayi Mata Rasuwa,Wannan Abun Shi yake Kara Dakula Zuciyar Bello Yaji Kwata Kwata ya Tsanesu bayason Hada Ko Wata Mu"amala Dasu Wani Lokacin In Abun ya Tasomai Ko Daada da ya Muktar Sai Abun ya Shafesu yayi Kwanaki in yana Gida bai Bude Kofar Bangarensa ba ko masu Aiki Sunje kai mai Abinci Haka zasu gaji da Bugawa Su Dawo Anty Rahila ce kadai Ke IyaTursasa Bello Wani Lokaci Saboda yana Bata Girma Sosai.

  Ko Hashim Dayake Zaune A Cikin Garin Abujan Shida Iyalansa A Maitama yana Aiki da Wani Kamfani Wanda Shi Muktar da Kanshi ya Neman mai aikin,Bello Bai Taba Taka Kafarshi Zuwa Gidan ba Ko Gidan yazo bai ma yarda Su Hadu ballo Har Su Hada Hannu Da Sunan Gaisuwa,lambar Wayarshi Kuwa Kowa Na Dashi Ammh basa ma Gangancin Kiransa Domin Sanin Waye Bello kamar ma Tsoronshi Sukeji Sunyi Iya bakin Kokarinsu Wajen ganin ya yafemusu Kamar Muktar Ammh Sun Makaro Domin Har Abada Bello bai Taba Jin Zai iya yafema Ahalin Datayi Sanadiyar Mutuwar Iyayenshi da Kanwar Babanshi ba.

  Ya Muktar da Daada Sunyi Ban Baki da Mganar Ammh Duk Abanza Tunda Haka Allah ya Halicci Bello ba yadda Suka Iya sai dai Suka kawo Ido Suka Sakamai Shiyasa Wani Lokacin Muktar Kan Kira Bello da Sturborn Saboda Yana Bashi Ciwon kai Ko Awannan Koyarwar da yakeyi Bayajin Dadi Domin Kaf kasar nan Asanshi Ansan wayeshi Ammh Ace Duk Matsayin Daya kai Wai Kaninshi Uwa Daya Uba daya Yana Wahalar Koyarwa Awata Mkrantar Kwana This dis unpair,Ammh Ina Bello yace Abunda Yake Ra"ayi Kenan Kuma Albashinshi ya Isheshi baya Neman Kari Akyaleshi Haka yana Jin Dadin Rayuwarsa Haka Dole Daada Tacema Muktar ya Rabu Da Bellon yayi Abunda ya Zab'a ma Kanshi Tunda Shi ba Yaro bane.

Ko Kasim Da Suke Sa"anni Yayi yayi Suyi Abota da Bello Ammh Ina bai ga Fuska Ba Domin Bello Bai Ta ba yarda ko Mirmishinsa Sun Gani ba Shima Ya Muktar ya Nema masa Aiki yana Aiki da Gidan Ruwa ma Jahar Kaduna ya Mallaki Motar Hawa da Kudade masu Dama,Ammh ko kallo bai ishi Bello ba Shiyasa Iyayen Kowanne keson Yarsa Ta Jawo Hankali Bello Domin Suna ganin Zasu iya Mallakanshi kamar yadda Suka mallaki Muktar,kodan kada tunanin da suke na zai iya kaisu watarana kotu akan hakkin Rayuwakan iyayensa.

*How to pay....â‚?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?600...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �500 ne,VIP �1000, Single one �300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*ANITHA....*
Chapter 12 · 0% Book details