← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 76

Sashe 16

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin tace"Toh Zamu gani Ammh dai Nasan kwatar-kwashi kamar Dole ne Ciwon Arne.."Da Sauri Aneesa tace"In Allah ya yarda Bakinki sai ya Sari Kashi Danye ma Kuwa Banza mara Mutumci,Kinga Malama sai anjuma.."B.kaita na Dariya tace da Sauri"yi hakuri Don Allah na Bari bazaki dawo Kwatar-kwashi ba karki yanke Kiran Don Allah.."Tafada cike da Marairaicewa.

Baki Aneesa tatura kafin tace"Kiyi da Hanzari Domin Waya Dake yafara Fitarmin Aka.."B.kaita ta Rike baki kafin tace"Dallh banza Dama Dalilin kiran Naki zan gayamiki Sati mai Zuwa zamu Shigo Abuja ni da Umma Biki Insha Allahu zan zo mu gaisa.."Tsalle Aneesa Ta Daka bayan Ta Mike tana Fadin"Da gaske Billy..?

Billy na Dariya Tace"Wlh Allah.."Aneesa Tace"Kai Naji Dadi Can Wait to see u B.kaita.."Cikin Farinciki tace"Me too.."

Basu yi sallama ba sai da Kudin Wayar Maman Billy ya kare kana Suka Saurara Saboda Jin Dadin Zuwa B.kaita da Hanzari Aneesa Ta Lalubo Lombar Wayar gidansu S.Jibiya dama Tana Dashi Domin Suna waya Lokaci bayan Lokaci Ammh sai Wayar Taki Shiga ganin Haka yasaka Aneesa Ta Kwashi Gudu Zuwa Shashen Daada Tana sanar dasu Zuwan Billy Tana Murna Tana Tsalle Daga Daadan Har Anty Rahila da Kallo Suka bita na Mamakin Halin Aneesa Domin ba Wanda baisha Lbrin Fadan Da Sukayi da B.kaitan ba Ranar Hutu Ammh Ji yadda Take Murnan Zuwanta,Aneesa kenan Manyan mata.

*******

*BAYAN KWANA BIYU..*

Ba wanda ya sani Ashe Bello baya Abuja ya Tafi kano Tun Washegarin Ranar da Abun ya Faru Ba Wanda ya sani Daga Anty Rahila Har ya Muktar Wanda bayanan ya Tafi Maiduguri,Taron Sojoji Shuru taji yasa Ta leka Mension Dinshi Sai dai ga Duk alamu bayanan Ta Fito zata koma barayinsu Suka ci karo da Mallam Inuwa bayan Sun gaisa ne yake Tambayanta Ko zata Fita ne..? Sai tace A"a Tazo Shashen Bello ne Ashe baya nan,Cikin Ladabi Mallam Inuwa ke Fadamata Tun Shekaran Jiya ya kaishi kano gidan Abokinsa da Suke Koyarwa Tare Uncle Aminu.

Anty Rahila batayi Mgana ba illah Gyada kanta datayi Ta sallami Mallam Inuwa ta koma Ta koma Cikin Gida Muktar kadai Ta sanarmawa Saboda ya Damu da Bellon sosai Lokacin Datace yana Kano sai da kwalla ta Taru Acikin Idanuwansa Cikin Tsausayi da Rauni yace"Rahila Har Wani Aboki yafini Awajen Bello,da zai zabeshi Fiye dani.."?

Anty Rahila Tace"Bai Fika ba Ammh yafika kiyaye Bacin Ranshi Shiysa ya Fifitashi Akanka.."Shuru yayi yana Jinta kafin yace"Toh ya Zanyi Rahi..."

Gyara Zama Tayi kafin Tace"Kana da yarda zakayi Tunda bayason Hada Komai Dasu Toh kaima ka koyi yadda zaka Nisantashi dasu..."Ajiyar Zuciya ya Sauke kafin yace"Shikenan U took later..Gobe ina Hanya.."Daganan Suka Cigaba da Tattauna Maganar kuma Duk Akan Bellon ne.

Daada ma sai Daga baya Taji Daga Bakin Bellon Daya Kirata Awaya Daada Batace komai ba Ammh Tace ya Dawo Gida Shi kuma yace bazai Dawo ba Sai Su Zubaida Sun Tafi,Daada bata kara matsamai ba Domin Tunda yace Haka toh bazai Taba Chanza Ra"ayi ba.

Su Zubaida kuwa Tunda Suka Fahimci Uban gayyar bashi Agidan Duk sai Gwiwansu Tayi Sanyi Sati Daya da yin Haka Zubaida Tafara Wucewa gidan Yaya Hashim,Ta bar Zulfa don Tace sai Sati na sama Aneesa ko Ajikinta Dadi ma Takeji Acikin Ranta Tana Addu"ar Allah ya sa karya Dawo Domin Ita bata Kaunar Hada Inuwa da Bello Tsabar yadda Ta Tsaneshi Toh Itama Zulfan bata kara Sati ba Tayi gaba Bayan Muktar ya Cikata da Kayan Arziki Ta Tafi cike da Takaichin Wannan karon ma babu Wani Cigaba Ta bangaren Bellon.

*****
Shiko Bello yana Tarauni Dake Kano Gidansu Uncle Aminu Wanda Ke Zaune da Mahaifiyarsa Ammi da Kanwarsa Raihana Domin Allah yayima Mahaifinsa Rasuwa,Aminu yaji Dadi Sosai Na Zuwan Bellon Duk da ba Zuwansa na Farko ba kenan Koda Aminun ya ganshi Cikin Damuwa bai matsamai da Mgana ba sanin Halin Bello marason Hayani sai ya kyaleshi yana samun Hutu Abunda dai ya Tambayeshi Shine game da Ciwon Hannunshi Ammh Har yau bai ce Masa Komai ba Shi kuma sai ya kyaleshi Sanin Halin Mutumin Nashi.

yana Kanon batare da Sanin Kowa ba yagama ma Aneesa Duka Shirin Komawa Kwatar-kwashi SS1 ta Waya Sukayi Mgana da principal din makarantar Saninshi Amkranta da Kuma Tasarinshi yasa ba Wani Bata Lokaci ba komai ya kamallah Saboda Haka kamar Zuwan Farko Aneesa zata Dawo Tare da Sauran Sabbin Daliban SS1,kwana Goma yayi Agarin kano Kafin Su Dawo Abuja Shida Uncle Aminun Ammh bayan Daada Ta Kirashi Tace sai ya Dawo Domin Su Zubaidan Sun Tafi

Aneesa Zuciyarta ta Kusa Bugawa Sanda Tayi Tozali da Uncle Bello da Uncle Aminu Lokaci Daya Cikin Falon Daada Saboda Razana ko Gaishe su batayi ba,ammh Saboda Salon Mugunta Irin na Uncle Aminu bai Duba Tana Gida bane Haka ya Kirata ya saka ta Kneel dwon Gaban Daada ya murdemata Kunni ya Dankwasheta akai da Cewar Bata gaisheshi ba.

Saboda Takaichin Abun Sama Ta Haye Bedroom din Anty Rahila Taje Ta Kwanta Hibba na Damunta da Surutu ta korata Shashen Daada Tana Kwance Tana Durama Uncle Aminu Allah ya isa Wayar Anty Rahila Dake kan Dresaing Mirrior ta Dauki Tsuwa Da Sauri Aneesa Ta Mike ta Isa ga Wayar ganin Wacce ke Kirane yasa Ta Dauka da Sauri nan B.kaita Ke Fadamata gobe Jumma"a Zasu Shigo Abuja Ita da Ummanta Dayake An Daga bikin basu samu zuwa Wanchan Satin ba Aneesan Naso Ta gayama B.kaita Zuwan Uncle Aminu Ammh sai Ta Kashe Wayar Kafa Aneesa ta Buga Tana Kunkuni Ita kadai.

*How to pay....â‚?300 0552179550 JAMILA UMAR GTB, VIPS..â‚?600...or MTN card aturo ta wannan Nombar 09069067488 hade da Hoton Tracsation*

_akwai garabasanmu Na Sanyaya biyu,👭 Matar Naseer Da Mr Belll guda 2 �500 ne,VIP �1000, Single one �300 ne zaku biya ta account Detail din sama,Mutanen Niger zasu tuntubi wannan lambar +22794775574 sai kunzo_

*ANITHA*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
       

*🅿�9*

"Washegari Wajen Misalin Karfe 12:00pm na Rana Sai ga Wayar Security Din bakin Get Zuwa Cikin gida Suna Tambayan Shin Aneesa Tasan Da Zuwan Wata Bakuwa Wai Bilkisu Kabir kaita?Alheri ce Ta Daga wayar bata Basu Amsa ba,Sai da Ta Shiga Dakin Daada nan Ta Iske Aneesa Cikin girmamawa Take Sanar da Ita ko tana da Wata bakuwa..? Ko Sauraranta Aneesa batayi ba Ta Fice da Sauri Cike da Murna Akan Fuskarta Daada na Mata Dariya.

Tana Fitowa Haraban Gidan Cikin Daga Murya tace"Plz Open d Get..."Tafada Cikin bada Umarni,Jiki na Rawa Securitys Din bakin Katon get Din Suka Wangalema Direban daya kawo B.kaita get Motar su kirar prado Baka ta samu Damar Sulalowa Cikin Gidan.

Bello da Uncle Aminu Dake Zaune saman Wasu Fararen Kujeru,Daidai Wajen Saman Mension Din Bello Suna Hango Duk Abunda ke Wakana Aharabn Gidan,Bello yana sanye da Riga da Wando Duka White ammh Rigar bata Da Hannu hakama Wandonsa 3quater ne,Karamin Tebur ne Agabansu Dauke da Madaran Hollandian sai Farantin kayan lambu da Ruwa,Gefe Daya Kuma Kafafun bello ne Farare Harde Saman Teburin ya maida kanshi baya bisa Kujeran Dayake zaune Magzine ne ahanunshi yana Karantawa Ayayinda Shima Aminu ke sanye da Irin Shigarshi Sai dai Shi Wayarsa ce Ahannunsa yana Faman latsawa Shiyasa Yafi Bello Lura da Filin Haraban Gidan Wando Sojoji ke ma Safa da marwa.

  Uncle Aminu Idonshi na kai Sanda Aneesa Ta isa da Sauri Ta Budema B.kaita bayan Mota ta Fito Tana Sanye da Shadda Ruwan kasa Tayi Dinkin Riga da Sikat an mata Stone Work karamin Gyale ne Akanta Sai Flat Shoe dinta kalan Kayanta Cike da Ihun da Suka Saba Suka Rumgume Juna Harda Tsalle kamar Wasu yara,Mallam Inuwa Dake Kofar Barayinsu Daya ke Dakunansu na Kwana yana Ta baya da Sauri ya kariso Wurin Yana Washe baki yake Fadin"A,"ah Maraba Hajiya Bilkisu.."

B.kaita ta saki Aneesa Tana Fadin"Yauwa Baba Inuwa Kwana biyu..? Yana Dariya yace"Wlh kuwa anzo lafiya..? Tace"Lafiya lau Alhamdulillah.."Aneesa Tace"Baba,Hira baza Tayi Dadi ba ba S.jibiya.."Mallam Inuwa ya kada kai kafin yace"Ayyah Sai dai in kun Hadu Amkaranta,."Da Sauri Aneesa Tace"In sun Hadu zaka ce Baba ka manta ni Na bar Mkrantan nan Kenan.."Tafada Tana Mirmishi gefe Daya Hannuwansu Sarke da Juna Ita da B.kaita.

Yar Dariya Mallam Lawal yayi kafin yace"Au hakane fa,Toh sai dai kuyi mgana ta Waya ."Yafada yana Kunshe Dariyanshi Shida B.kaita Cikin Farinciki Aneesa Tace"Insha Allahu Baba Bari mu karisa Ciki.."Mallam Inuwa yace"Madallah Nima yanzu Zan Fita zan kai Motarku Wanki ne.."Aneesa bata jishi ba Shiyasa bata bashi amsa ba.

Uncle Aminu Dake Zaune yana Kallonsu yace"Bello kalli kaga kamar Dalibarmu Bilkisu Kabir kaita nake gani Tare Da Aneesa..?
Bai Dago ba Cikin Rashin kulawa yace"Tunda ka ganeta Ita din ce.."Daga Haka ya Cigaba da Abunda yake batare Dayabama mganar Aminun muhimmanci ba balle harma ya kai Duba Zuwa ga Inda yake Nuna mai.

Cikin Saurin Uncle Aminu ya Mike ya Isa Jikin karfen Daya ma Wajen Kwanya Cikin Kaushin Murya ya Furta.."Bilkisu kaita.."Yafada da Dan karfi,Aneesa da B.kaita Dake Shirin Shigowa Kofar da Zata Sadasu da Babban Falon Gidan Suka Dago a Tare  cike da Mamaki B.kaita tace"La Uncle Aminu Gud Afternoon.."Tafada Fuskarta na bayyana Fara"a Domin Daga Inda Suke Tana Hango Uncle Bello Zaune Duk da Jaridar Dake Hannunsa Ta kare Fuskarsa,Aneesa Ko cin mgani ta Fara Tana Kauda kai Aminu na Lura da Ita Cikin Ranshi yana Fadin"Dis gal kamar Wata majanunuwa.."

Cikin Sakin Fuska yace"Afteernoon Too Bilkisu How are u.? Ya Hutu..? Fatan zaku Dawo mana Ku Dora Daga Inda Kuka Tsaya ko .? Cikin Jin Dadi B.kaita tace"Insha Allahu Sir Nida Salamatu Jibiya nan zamu Kareta,Anee ce dai tace Tabarmu Uncle.."yar Dariya yayi kafin yace"Haka tace muku..?karya Take Itama Kwatar-kwashi Dolenta ne.."

Yafada yana Kallon Aneesan Wacce Ta Dago Tana Hararanshi Ta kasan Ido Jin Abunda yace,ganin Haka yasa yace"Ke Uban Wa kike Harara..? Baki da Kunya ko.? Bar ganin Ina Gidanku Kina ganin Sojoji na yawo har yanzu ina Mtsayin malaminki ne sai na Sakko na Chasaki yanzu nan.."Yafada yana Nuna ta baki Ta Tura gaba Tana Kunkuni Baki ya Rike kafin yace"Oy Say Srry Uncle.."
Chapter 16 · 0% Book details