← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 76

Sashe 43

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr.philphil Shine yayi musu Bayanin komai Wanda ya kara Raunana musu Zuciya ya basu Tabbacin Bello bazai taba warkewa ba domin Wannan ne karo na Farko da suka taba ma wani wannan Aikin kuma basu samu Nasara ba,ammh basu sani ko kila nan gaba ya Tashi ammh Azhirin batu Duka gwajin Sakamakon Suna Nuna Normal ne Abu ma daya kara Dauremusu kai Duka Joint dinshi lafiya kalau basu da Mtsalan komai Komai na Jikinshi yana lafiya ammh kuma gashi kwance ko yatsan Hannunshi baya iya Dagawa Daga karshe ya basu shawaran Su koma gida kawai Domin Ko wani Asibitin Suka je sai dai su sake Wani Asaran kudin kawai."

Kasa ya Muktar ya Sulale ya Rufe Fuskarsa da Tafukan Hannayensa yana Shesshekan kuka Ya Ali ne da Modibbo suka Rikosa suna bashi baki,Su kansu Jikinsu yayi sanyi Waje ya Fita yana Share kwallah Daada ya kira awaya tana Dauka yasaka mata kuka tana jin Kukansa tace"Ba"a samu Nasara ba ko Muntari..?

Yana Sharban Majina da Hawaye yace"Daada sunce Bello bazai Taba Tashi ba...Kuma Duka sakamakon gwajinsa ya nuna bashi da Mtsalan komai ammh Daada bello yana nan kwance yadda kika barshi ba"a samu wani Cigaba ba..."Daada ta Sulale Bisa Kujera tana Kiran Sunan Allah Lokaci Daya tana Dauke Hawayen idanuwanta da Haban Zaninta cikin Dashewar Murya Daada tace

"Ya zamuyi Muntari bamu da yarda zamuyi In Har Haka Allah ya Tsarama Bello bamu da yarda Zamuyi sai dai mu Tayashi Rumgumar kaddaranshi..."Ya muktar ya Share kwallar idanuwanshi wanda ke Zuba ba Control ya rasa Dalili yana da Jarumta kan komai ammh banda Kan Abunda ya Shafi Bello sam Baya da wani Jarumta Cikin Muryan Amo yace"A"a Daada Insha Allahu ba Haka Allah ya Kaddaroma Bello ba...Da Izinin Lahi matukar ina da lafiya da kudi da Mukami Sai na yawata da Bello Duka kasashen Duniya wajen Nema mai mgani yanzu ma na yanke Hukunci gobe zan Wuce Dashi spain suma su Gwada nasu Mugani Daada.."

Cikin Sauri Daada tace"A"a karma kafara Muntari Maza ka Dauko kaninka ku dawo gida ina ji ajikina Cutar Bello bata yawon kasashen Duniya bace,ku dawo gida mu Jarabamai na Hausa ko Allah zai sa Adace.."Ya bude baki zai yi mgana ta Dakatar Dashi da Cewa"Kayi Abunda Nace Muntari ka Dauko Kaninka Bello ku Dawo Gida.."Daga Haka ta yanke Kiran tana Sharan Kwallah shima Daga barayinshi kwallarsa ya Share kafin ya koma office din wajen su Dr.khan

Bayan godiya daya yi musu,nan take yace Su Rubuta musu Takardan Sallama zasu koma gida,Gobe in Sha Allahu,Duk da Abun ba Dadi ammh iya gaskiya kenan gwara su koma gida ajaraba achan kila adace,kafin Zuwa Waye wan garin sun gama Duka Shiryan Shiryansu na Tafiya,koda Aka Fito da Bello kan WheelChair,likitocin indiyawa da Turawan sai kama Hannunshi Suke suna mai bye bye,Haka Dr khan da Dr.philphil suka Rikemai Hannu Cike da Tsausaya Shikuma sai dai ido kadai ya ke saka musu,Fatan samun lafiya suke mai Har Suka Sakashi amota suka Fice Daga Asibitin da suka kwashe tsawon Wata Uku Aciknsa Shikan Modibbo ya saba da Wasu Da yawansu saboda Zama,duka Rocord din Gwaje gwajen Na bello suka basu bayan sun ijiye ainihin Original din.

****

Babu wanda ya sanar da Aneesa Da dawowar Su Ya Muktar da Bello,Ta damu bayan tafiyarsu bataji wata mgana ba tayi ta Tambayan Daada ita kuma taki gayamata sai cemata datayi wai Ya muktar din bai kira Waya ba,duk ta damu Ciikin Zuciyarta Zullumi ya isheta.

Ranar da zasu dawo Haka tatashi Bata jin Dadi Ciwon kai take Fama Dashi Dakyar ta iya yin Wanka ta saka wata Doguwar Riga kirar Armani,tunda Tu bayan dawowarsu ta Dauko sauran kayanta Daga Shashen Bello Tunda Sauran na kano mgani tasha ta koma ta kwanta nan da nan kuwa barci ya kwasheta mai cike da mafarkin Bello.

Karfe 3:30Pm na Narana Jirgin daya kwasosu Daga Birnin Delhi Zuwa Babban Filin Jirgin Nmandi Azikiwe Internatinal Airport, ya sauke su Tawagar ya Muktar suka zo Daukansa Daga Filin Jirgin Shi ya Gunguro Bello Daga Cikin Jirgi wanda ke kan Wheel Chair,akallon Farko bazaka taba Zaton yana da wata mtsala ba,saboda yadda yake sanye Cikim Riga da wando na Kamfanin DKNY,wandon Sky blue ne Rigar kuma mai Dogon Hannu ce Navy Blue ce,Fuskarsa ta kara Fayau ,ya kara Fari da kyau,hancinsa ya kara Fitowa Sumar kansa tafara yawa Haka ma Sajen Fuskarsa ya kara yawa Baki Silub,fatar Jikinsa ta kara kyai da Murjewa Duka Jikinsa lullube da kananun gashi kafarsa sanye da wani bakin Takalmi mai igiya Hatta Tsitsiyan hannunsa yana Sanye da bakin Agogon Fata na kamafamin Rado

Kowa yamai kallon Farko zai ji yana Son kara kallon Fuskarshi ammh Daya Kara Nazarinsa ya Fahimci yadda Wuyansa ke Zuwa gefe Lokaci Daya kuma miyan bakinsa na Zuba sai ka mai kwallah Namiji har Namiji sai dai kuma ya Nakasa,Modibbo ne ke Fama da Tissue tun acikin Jirgi yake Faman gogemai da Zarar ya Fito dashi saboda kar ya batamai gaban Riga.

***

Bata Farka ba Sai 4 da wani Abu Shima wai mafarkin Bello tayi ya Shigo Cikin Dakin Datake da kakafunsa,shi ya Farkar da ita tatashi afirgice Duk Jikinta yayi sanyi sai kuma taji Hayani a Falon Daada,Mamaki ya kamata kodai baki akayi sai ta kuma Tuna Dazu taga ana ta gyara bangaren baki,bata kawo komai acikin Ranta ba sai tayi Tunanin Dangin su na Adamawa ne domin Taji Daada na Tadinsu kwana nan..

Cikin kasala ta mike ta Fada Toilet ta Dauro alwala tazo tayi sallar azahar ta hada da la"asar ta dade tana addu"an Allah yabama Uncle Bello lafiya kafin ta mike Lokaci Daya tana kwabe Hijabin Data gama sallah Dashi,gaban madubi ta isa tana kallon kanta,tana Daura bakin Dankwalin Doguwar Rigarta Kai Tsaye ta Bude kofa ta Fito Falon na Daada saboda cikinta ba komai yunwa takeji.

Turus tayi ganin Mutane Cike da Afalon idanuwanta suna ta Wulgawa,Ya muktar,Ya Ali,Anty Rahila Dasu Hibba sai Modibbo da Daada gefenta kuma Bello ne kan Wheelchair dinsa,idanuwansu suka sarke cikin na Juna Lokaci Daya ya Saki Boyayyiyar Ajjiyar Zuciya dama Ita yakeson gani Tun bayan Dawowarsu ammh kuma baisan ya zai yi yayi mgana ba,ganinta Dayayi yasa yaji Dadi ya kafeta da ido yana Budewa yana Rufewa alamun Murna,gefen bakinsa kuma na Zubar da miyau.

Kasa gaba tayi ta kuma ta kasa Baya Ya Ali ne yace"yau ga iskancin banza irin na Aneesa mijinki ya Dawo ba lafiya ba sannu ba komai sai kallon Mutane ."Daada tace"Mamaki take Ali Bata san da Lbrin da Dawowarku ba.."Tafada Tana kallon Aneesa wacce ke kallon Bello Lokaci Daya tana Toshe bakinta kar kuka ya kwace mata Juyawa Tayi ta koma Dakinta ta Fada Bisa gado tana Fadin"Bai Warke ba..mafarkina ba gaskiya bane.."Take fada tana kara saka kuka.

Har ta Shige idanuwansa na kanta Kuri yayi gwanin ban Tsausayi ya Ali yabi Aneesa da kallo har ta shige yana Fadin"Tsiyana da Aneesa fa wani Lokacin Sakara ce,toh miye Abun kuka keda kullum ke kukan kina so ki koma ki ganshi yau kuma ya Dawo kuma kina wani Sakarci.."Anty Rahila ta Murmusa tana kallon Bello yadda ya wani bata rai Lokaci Daya take Fadin"Har ka manta Auta ne fa.."Tafada Cike da Tsausauyin Bellon,Daada ta lura da yadda ya tsurama wajen ido sai ta kama hannayensa duka biyun tana Fadin"Karka damu zata Fito haka take kuka kullum saboda Tsausayin halin da ta barka koni da Dan"uwanka Aneesa bata kaimu Damuwa ba...Ka Riketa ko bayan Raina Bello in ka Warke ka sota kuma ka Hidinta mata Ita din mace tagari ne awajenka"Tafada tana kallonsa Hawaye na taruwa acikin idanuwanta Shima kallonta yake Lokaci daya kuma ya Lumshe idanuwansa.

Ko abinci da ya Muktar ke bashi abaki Bai wani da ci da yawa ba,Duk da dama Rabi ya Shiga ne rabi ya Fito Daga bakin,Duka Rabin Hankalinshi naga kofar Bedroom din Aneesa Data Shiga Tundazu Bata Fito ba,Modibbo ne ya gogemai jiki,inda ya babbata da Abinci,lokacin mangariba ta kawo Jiki da zasu Tafi maallaci dashi suka Tafi saboda ko achan bayan an Faramai gashin kashi Da Lokacin sallah yayi modibbi zai mai alwala ya saitashi agabas ya barshi bayan ya gamai yayi sallah yanzu ma Haka suka mai Ya Ali yamai alwala suka Turashi Zuwa Cikin masallacin cikin Sahu aka yi jamm"i Dashi Sukansu ma"aikatan gidan sun zubar ma da Bello kwallah hatta Sojijin dake Tsaran lafiyan gida na Lt.gen Muktar muhammed Jikamshi.

Haka kuma suka Turoshi Zuwa Cikin gida har Shashen Daada,inda Suka bar Ya Muktar da Ya Ali Shashen Anty Rahila suna mgana,Modibbo ne ya kariso Dashi Daada kuma na ciki na Sallah,yana ijiyesa Cikin Falon yadinga kallon Kofar Bedroom din Aneesa Kansa na lamgwabewa ammh bai gaji ba,Modibbo bai kula dashi ba sai da Daada ta Fito daga daki Hannunta rike da Chasbaha ta kariso Falon ta Zauna kujeran dake Fuskantan Bellon tana Fadin"har kun dawo sallar..?

Modibbo dake latsa waya yace"Eh Daada.."Bello ta Kurama ido ammh sam shi baya kallonta Juyawa tayi ganin inda yake kallo yasa tace"Gunta zaka..? Da Sauri ya lumshe ido yana Kallonta Mirmishi tayi kafin tace"Allah Sarkin Baiwa...Modibbo kaisa Dakin Aneesa Wajen matarsa yakeson zama.."Tafada Cikin Tsausayin Bellon Dariya Modibbo yayi yana Fadin"Kinga laifinsa Hajiya Daada lallashi zaka ko Baffa Bello.."(Haka suke kiranshi saboda Bello baban Hassatu Baffansu ne..)

Yafada yana Dariya,Daada ma Murmusawan Tayi tana cigaba da Jan carbi shikuma ya Turasa Zuwa Dakin Aneesa Tura Kofar Modibbo yayi da sallama yana Fadin"Toh kefa matar baffa mijinki yagaji da jiran Fitowarki ya biyo ki.."Yafada yana Shigowa dashi Dakin.

Tana Zaune kan sallaya tana Addu"a suka Shigo Da Sauri ta waigo Jin Abunda Modibbo yace Saurin mikewa tayi tana kallonsu Shiko Bello ido ya kafeta Dashi yana so ya Tambayeta meyasa take kuka..?ammh kuma ya kasa Mgana balle ya tambayeta Yana kallon Cikin idanuwanta wani Abu na Shiga Zuciyarsa Tun Ranar da Abun nan ya Sameshi Kukan Aneesa ya tsayamai arai Bai taba Tunanin zata iya damuwa dashi bayan shi kuma bai damu da Ita,bashi da bakin mgana sai dai yayi ta mgana da Zuciyarsa.

Mirmishin yake tayi kafin tace"La...dama yanzu nake shirin Fitowa.."Dariya yayi yana Fadin"Kedai kyaji dashi jan aji ne kawai a sassautama Baffalenmu kinganshi dai ba lafiya ne dashi ba"Yafada yana Ficewa.

Ki biya ki karanta cikin salama.
Chapter 43 · 0% Book details