← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 76

Sashe 72

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar Yadda Daada tace ko Washegari Aka Duramin kayana cikin Booth din mota,Mallam Inuwa ya kaini Har Borno kafin mu isa kafafuna sun kumbura saboda Zama,mutanen Gidanmu sunsan da zuwana Tunda Anty Rahila takira Mama yana ta Fadamata kafin mu iso ta gyaramin Cikin Uwar Dakinta inda zan Sauka,mallam inuwa yaso ya koma sai Ya Ali ya hanashi Sai da ya kwana Washegari ya koma Duk da ina cikin Damuwar Rashin Mijina Domin yayi Fushi Dani ko na kirashi baya Dauka sai dai na Turamai sako ya Karanta bazai bani amsa ba Duk na Damu ammh ganina cikin Dangina yasa na Saki Jikina Mama yana dasu Ya Ali bansan wanda yafi wani kula dani ba,Haka matansu Ya Ali komai nace suna Rawan Jiki su bani Mama Falmata kuwa Sai kawaichi ammh cikin Ranta tana min Addu"ar Allah yasa na Bude ido lafiya.

Sati na Daya Da zuwa Borno ammh haryanzu Bello bai sakko ba Abun yafara Damuna Sosai Duk da Cikin Jikinna sai na Fara rama,gashi ba"a san masu Juna Biyu su Shiga Tunani,nan da nan kuwa sai ciwon kai mai zafi sai da aka Dangana ni da Asibiti nan akace Jinina ya Hau na kiyaye Da Tunani Saboda zan iya sanun Mtsala Nida Da Abunda ke Cikina nan suka Rikeni sai da na kwana na Wuni kana muka koma gida Ranar ina zaune Kan gadon Mama Yana ina Shan Mangwaro sai ga Kiran Wayata ina Dubawa naga B.love ne.

Duk da Abun yabani mamaki ban yi Saurin Dauka ba na Zubamai ido yana ta Kira ban Daga ba,har  Sau uku kafin ya Dakata da Kira ni kuma ban Daga ba Domin Azahirin gaskiya yagama batamin rai kuma yabani mamaki ban taba zaton koma mai nayi ma B.love zai iya yayimin Irin wannan Hukunci ba balle kuma yafi kowa sanin Bani da laifi.

Nagama Shan Mangwarona kenan Sai ga Khadijan ya Ali ta kawo min Wayar ya Ali wai mijina na Mgana Karba nayi ina basarwa bata Tsaya ba ta Fice ta barni,Ba a dauki Lokaci Ba sai ga Kiransa ya sake Shigowa Tana gabda Tsinkewa kana Na Daga Tunda na Dauka banyi mgana ba cikin Sanyin Muryansa ya Furta"Wani Tunani kika saka Aranki Har yana neman ya Tabamin lafiyanki da Abunda ke cikin ki..?..

Yafada cikin Kaushin Muryansa Ina jin Abunda yace na sakamai kuka,Wiwi Shuru yayi bai cemin komai ba Har nagaji nayi Shuru na koma ina Sharbe Hanci Cikin Muryan Kuka nace"Har ma tambayata kake meke damuna..? Ina da wata damuwan Data wuce ka ne..? ka manta da ni Kwata kwata Baka Daukan Kirana kuma baka Kirana.."nafada ina Tura baki,Mirmishi ya saki kafin ya Koma ya Kwanta yana Dafe Kirjinsa Cikin Wata Irin Murya ya Furta.."Laifi kikaman Anee Shiyasa.."Cikin Tura baki nace"Laifin me nayi maka kuma...?

Yace"Laifin kin tafi kin barni mana my Anee kinfi kowa sanin Ba wanda na saba dashi sama dake....ammh baki damu ba kika Biyema Daada ta Rabani Dake...Ya kike Tsamanin bazan Damu ba...Bana iya barci Saboda kewarki Akullum Sakon ki ne ke Debemin kewa ammh Jiya najiki Shuru kuma nayi ta kiran wayarki Tana kashe na Damu sosai sai na kira Ya Ali shine yace min kina Asibiti baki da lafiya Jininki ya Hau...Na Shiga Damuwa Sosai My Anee Duk da kin Batamin rai buh na Riga na yafemiki fata nima zaki yafemin Kuskurena.."Yafada cikin Alamun Shagwaba..

Ido na lumshe Lokaci Daya ina Jawo Filon Dake kan gadon na Matse Bisa Kirjina ina Fadin"Naki wayon bayan kasa Babynka ma yayi kewarka..."Cikin Mirmishi yace"Zan zo anjuma na lallashi kayana ba Ruwanki.."Dariya na saki ina Fadin"Anee tayi kewar Mijinta sosai..."Cikin Wani Shauki ya gyara kwanciya yana Fadin"Mr bello ma yayi kewar Matarsa Sosai Fiye da yarda Tayi kewarsa..."yafada lokaci Daya yana Sakarmin Kiss Cikin Kunnena Kasa nayi da ido kawai ina Sauraran Labarin Irin kewata Dayayi,Nima nan na shiga bashi labarin Kewarsa Danayi Tuni muka manta da wani Fushin Juna muka Shiga hirar Soyayya sai da muka ji Kiran Mangariba kana muka Hakura wayar Ya Ali kuwa Sai kira mutane suke muna sakasu cikin  Call Waiting,muna gama wayar na lallaba na tashi Zuwa Shashen Ya Ali tunkan na Shiga na cikaro da Yarsa Samiha na mika mata na juyo ina Dariyan Sanin Halin masifan ya Ali.

Bayan sallar Isha"i muka Dasa Daga inda muka tsaya Muna waya Yana kichen yana Dafa Indomie haryagama yaci muna mgana sai da zai shiga wanka muka Hakura bayan ya Fito kuma koda ya Kirani barci ya kwasheni sai da safe naga sakonsa.

*Sleeping Beauty...My Wife...*

Mirmishi nayi Lokaci Daya ina Sumbatar waya kamar Shi nake gani,Tunda muka Shirya sai muka koma bamu da aiki sai waya,in yana gida ko yana makaranta sai dai kuwa in ya Shiga Clasa ne zamu Hakura yace min zai zo ammh sai Weekend.

****
Ranar Jumma"a Tun Safe Dana tashi naji bana jin Dadi Ciwon baya,sai ban Nuna ma kowa ganin Dama ya sabamin irin haka,Ashe Naguda nake bansani ba Sai wani Lokacin naji marata ta Daure Duk ban kawo komai ba sanin naji labarin Haihuwa ba Haka take ba,Su Ya Ali duk basu nan sun tafi masallacin Jumma"a na Shiga Tiolet zanyi alwala na Durkusa zanyi Fitsari naji Wani Ruwa na Biyo nayi kokarin Tashi na Duba ban iya ba Saboda wani Azaba danaji ya kamani Bansan sadda na Fasa Ihu ba Saboda ji nayi kamar zan mutu ne.

Mama yana nake kira Kamar Muryata zata Fashe ita da Falmata suka Rugo zuwa cikin Bayin na Dakin Mama yana suna Saka kansu Cikin Tiolet din na saki Nishi jin Wani Abu na Shirin Fitowa Daga kasata,dafa kasan Bayin nayi ina kuka lokaci Daya da Hawaye Zanin Jikina Tuni ya yaye kanshi Saboda azaba,ko kafin su kariso kusa dani na Saki gatso Lokaci daya ina Fadin"Innalillahi...Hasbunallahi...Mama...mama ki Dubamin kashi ne yaki Fito ko menene.."Na bani Zan mutu..."Haka na ke Fada kafin na saki Nishin da karfi sai ga D'an Da ya Fito Lokaci Daya mama yana ta saka hannu ta jawoshi tana Fadin"Alhamdulilah...Lalle kin gado Falmata Haka tayi Nakudar ki Daga zuwa Fitsari sannu Kinji Aneesa.."Tsakar bayin na koma na kwanta ina maida Numfashi Mama Yana ta mikama Falmata Yaron Daya cika wajem da kukansa Ita kuma tayo kaina Ta shiga matsamin Ciki sai ga Uwa ta Biyo Baya,Mama yana ta Shiga gyarani ita kuma mama falmata ta yanke Cibiyar ta Nade Yaron Cikin zani ta Fita dashi nan da nan Mama yana ta hadamin Ruwan zafi mai zafi ta min wanka ta kamo ni muka Fito,ita kuma Tuni Mama Falmata ta gaya su Khadija Haihuwan sun saka Ruwan zafi sun Wanke Jaririn Tas,sun sakamai wasu kayan sanyi masu kyau,Kafin kace kwabo sun gama gyaramu Nida Jaririna kato mai kama da Ubansa sak,sai dai su Ya Ali suka Dawo suka ganni kwance kan gadon Mama yana nida Jaririna bayan Sun Hadamin Faten wake mai cike da Kayan ciki,da kunun Tsamiya na Daddaka kana na koma na kwanata,kowa sai mamakin Naguda ta yake Cikin Lokaci wai na Haihu kuma agida.

Ni na Turama Bello Text da cewa..." _Alhamdulillah...MR BELLO MUHAMMED JIKAMSHI is Now a father..._ na Turamai ko minti goma ba"ayi ba sai ga Kiranshi cikin Rawan Jiki yana Fadin"Anee wai da gaske kike..?ina Dariya na karamai kukan yaron wanda Tunda ga Fitowarshi Duniya na gane yana da da Rigima Hawayen Farinciki suka Kawo cikin Idanuwansa cikin Murna yake Fadin"Masha Allah Alhamdulillah..Allah Nagode maka Wlcm to the World...Muhammed Amin.."Yafada yana Dariya cikin Farinciki Nima Murnan nake kafin kace kwabo Haihuwata ta Zaga Dangi da Abokan Arzuka,waya kuwa har nagaji da amsawa,sai washegari kana Muka tafi asibiti aka dubamu Nida Jaririna aka tabbatar da komai lafiya kana muka Dawo

Tuni Ruwan Nonona yazo Saboda Mama yana batamin da Wasa abinci nake ci kamar gara,Dama gashi yaron akwai Rigima ga Tsotso,Kwana biyu da Haihuwarmu ango karni ya Diro Shida Takwaranshi wato Uncle Aminu,Haka suka tasa yaron nan gaba suna kallo,ni kuwa agabansu Anty Nafee da Matan su Ya Ali Bello ya Rumgumeni tsam yana Juyi Dani nine ma naji kunya ammh Shi ko ajikinsa sai wajen la"asar suka tafi dama Tafiyar Jirgi sukayi,Su Daada kuwa kwana biyar da Haihuwana Suka Diro borno ita da Anty Rahila da Niki nikin kayan da Bello yamin Wajen akwati Biyu na Fitar Suna
Da kuma Raguna guda biyu na Ya muktar tare suka zo yayi min Barka yabi Jirgi ya koma.

Abun mamaki ana gobe suna Billy kaita da Salamatu Jibiya suka iso basu Dade da zuwa ba sai ga Ammi da Raihana da Anty Aisha na Daka Tsalle muka Rumgume juna da Raihana Saboda Murna nan muka Hade da Sanah sun zo tare da Anty Yagana,Yan"uwana ba karamin kara sukamin ba Komai na Abunda za"aci sun hana Bello da Ya muktar aiko da komai su suka Dauki Dawainiyar Abunda za"a ci Asha Raguna biyar aka yankama Muhammed Amin,Biyu na wajen Ya Muktar Biyu na wajen Mijina Daya kuma Ya Ali ya yankamin,wayyo Farincikina Baya iya Boyuwa saman Fuskata Saboda yadda na zama zarah cikin Wata.

Na shiga na fita cikin kayan alfarma Wuyana Zinare ne ke kyalli,Na samu kyatuttukan kudi Daga wajen Yan"uwana sosai Domin Sun min kara sun kuma Nuna Nidin Auta nake garesu Daga Bangaren gidansu Abba Kabiru kuwa ba Wanda yazo ko matar Hashim bata zo ba,Saboda Jikin Abba kabiru dai yaki dadi An ma maidashi gida ana cigaba da Jinyarsa Komai ya kare,sai Hakuri kawai da Rayuwa Sai dai Sun kirani ta waya suka min Barka,Abun mamaki Harda Zubaida acikin masu kirana gwanin Ban tsausayi mama Sahura ma ta kirani tamin Barka suma Babu komai Inna Rukayyah ce Dake kano take dan Taimakosu itama Babu karfin Hali ne ga Su Hamdiya Dake hannunta komai nasu itace.

Anyi suna lafiya Antashi lafiya Hatta da matar Sani sai da tazo ta kwana daya,Washegari ta Tafi maiduguri,yarta na Aure achan Su B.kaita kuwa Uncle Aminu Suka bi,tun safe yazo Daga lagos yake suka bishi suka koma Ajirgi yana ta mamakin Girman Su B.kaita wai yaana musu Tsiyan sun zama yanmata,Harda Ammi da Raihana dama yazo ya tafi dasu ne,Da zasu tafi nayi ta musu Godiya sosai na basu nama da Sauran Abubuwa.
Chapter 72 · 0% Book details