← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 76

Sashe 2

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

B. Kaita da Abun na Aneesa Ya kaita Wuya sai kawai ta cakumo Aneesa Suka Fara Dambe Tana Faɗin"Ni ba banza bace kece babbar Banza butulu mai Raina Alheri.." Tuni Faɗa ya kacame, S. Jibiya ce ke ƙoƙarin Rabasu da Sauran Student d'in da basu gama Tafiya ba, suka ƙariso Suna Raba Kawayen Juna Faɗa, S. Jibiya ce ke Faɗin "Haba Aneesa, Billy meye Haka Wannan ba girmanku bane Aganku kuna Faɗa da Junanku..." Aneesa Data Shaƙe Wuyan B. Kaita da Hijabi Take Faɗin "Aganmu munayin Mana Uban Waya ja In ba Ita ba Dama Tuni Billy Take Shigan Hanci Da Ƙudundune Wlh yau kafin mu bar Mkrantan nan Sai mun Goge Raini Tsakanina Da Ita.." Take Faɗa Tana Haki tana ƙara Tamke Wuyan B. Kaita Wacce ke Ƙoƙarin Ƙwace kanta.

Daga bayansu Sukaji Ance "Are u Stupid Aneesa Bukar Bulama....?"

Sukaji An Faɗa Daga bayansu Cikin Kakkausan Murya, gaba ɗayansu Suka Waiga Suna Kallon Uncle Aminu da Mr Bello Suna Tahowa, Hannunsu Sarke da Juna, Kamar Wasu Tagwaye Dama Duk Sch d'in ba Wanda baisan Abota Da Shaƙuwa Irinta Uncle Aminu da Mr Bello ba, Uncle Aminu Yana Sanye da Riga da Wando black And White, Sai Wani Rufaffan baƙin Takalminsa na Fatar Damisa Sai Mr Bello yana Sanye da Riga da Wando Rigar Dark Blue mai Dogon Hannu sai Wandonshi mai Ruwan Blue mai Haske, Ƙafarsa sanye da Takalmi Baƙi booth sai kansa Dake Sanye da p cap, wanda ya Rufe Rabin Fuskarsa Dukkansu Dogaye ne masu Surar Jiki Ƙirar Maza Cikakku Masu Zati da Haiba.

Uncle Aminu Fari ne Mai Faɗin Fuska da Dogon Hanci yana da Gemun Shi ɗan Dai-dai Wanda yake Ƙara mai kyau mai Haɗe da Zagayayyen Bakin shi mai faɗi Kaɗan, Mr Bello Fuskarsa bata bayyana ba Sosai Sai dai Daga yanayin Fatar Hannunshi Inda Rantsantsen Agogo na Kamfanin Rado ke Ɗaure A tsinsiyan Hannunshi na kallah na Fahimci Fari Ne Sosai Saboda Yadda Fararan yatsunshi ke Kwance da Gashi Sun Kwanta Zara zara Gwanin Ban Sha"awa, Yana da Faɗi Kaɗan Daga Sama Saboda In yana Tafiya Zaka ga yana Buɗewa, a kallon yanayin Tafiyarshi kaɗai ya Isa Zatinsa da Jarumtarsa Su Dakeka Tun kafin kaga Fuskarsa ma.

Duka Ɗaliban Dake Wajen Suka Fara Matswa Jikinsu na Rawa Suna Tsoron Kada A haɗa dasu Uncle Aminu da Mr Bello A lokaci Ɗaya ai Fire ne, babu Wanda Baisan yadda Suke cin Ƙaniyar Ɗalibai ba Acikin Mkrantan Musamman 'yan Taurin kai Irinsu Aneesa, Aneesa Ko Ajikinta Sai ma Ƙoƙarin Ƙara Riƙe Wuyan Hijabin Billy Kaita Da takeyi Itako Tuni Ta Saki Wuyan Aneesa Tana Ƙoƙarin Ƙwace Kanta Salamatu Jibiya Kuwa Baya ta Matsa Tana Zare Ido Aranta Tana Addu"ar Allah yasa yanzu Motar gidansu tazo Ɗaukanta.

A gabansu Suka ja Burki Uncle Aminu ne ya kalli Aneesa Dake Wani Hura Hanci ga Bakinta na Ƙara Ɗaukan Ido Cikin Tsawa Yace "Leave her Hijab Now Don Ubanki..." Ya Faɗa yana Sakin hannun Mr Bello Wanda kanshi ke ƙasa yana Danne Danne Cikin Wayarsa, Kamar baima san Abunda Ke Faruwa Awajen ba, Aneesa na Ƙunƙuni Harda Ƙwallarta ta Saki Wuyan Hijabin Billy Kaita tana Faɗi ƙasa ƙasa "Nidai ba Ubana ba Wlh.." Ta faɗa Tana Share Hanci ba Zato ba Tsammani Taji Gam!! An Buge mata baki, da Hanzari Ta Dafe Wajen Tana bin Hannun Wanda ya Maketa da Kallo Mr Bello ne Cikin Muryan Sanyi Ammh Cike da Faɗa yace "Ba Ubanki ba sai Ubanwa..?" Ya faɗa ammh Still kanshi na Kan Wayarsa Dake Hannunsa.

Uncle Aminu ne ya Riƙe Kugu yace "Au haka tace Bello? ƙanwar nan Taka fa Zan ci Ubanta, Duk da Mun Riga mun basu Hutu.." Mr Bello Dake Danna Wayarsa yace "As u wish..." Ya faɗa yana Ɗago da kansa Lokaci Ɗaya Ɗaliban Wajen kowani ya fara kama gabansu Wasu ma Jakunkunansu Suka Ɗauka Suna Nufar bakin Get, Jikinsu na Rawa Kada Laifin Aneesa ya Shafesu Domin kaf Mkrantan Kwarta-kwashi ba Wanda baisan Waye Uncle Aminu da Uncle Bello ba wajen iya cin ƙaniyar Ɗalibai Kuma ba Wanda bai san Wacece Aneesa Bukar Bulama ba wajen Rashin kunya da Rashin Tsoro.

Jin Abunda Mr
Bello yace ne ya sa S. Jibiya ta Marairaice Fuska tana Kallon Aneesa Tana mata alamun Ta bada Haƙuri Ita kanta Billy Kaita Tsoro ya Shigeta ganin Uncle Aminu ya isa Bishiyar Dalbejiya yayi Tsalle ya Katso Reshe Ɗaya ya Tsinketa Wata Doguwar Bulala Ta bayyana Kafin ma ya Ƙariso B. Kaita da S. Jibiya Suka Matsa Gefe Suna Rawan Jiki Shiko Mr Bello Baya ya Juya Bayan ya Ɗaga Wayarsa ya Ɗaura a Kunni ya fara Tafiya kamar Zai Fita bakin Get.

Cikin Tsawa Uncle Aminu yace "Kneel Down..." Aneesa Ta kalleshi tana Ɗaga Idonta sama Irin Banji me kace ba Sanin Raininta yasa bai Jirata ba ya Fara Zuba mata Bulalar Dake Hannunshi Cikin Ƙwarewa da Mugunta Tun Aneesa na Tsaye tana Cijewa karta yi Kuka sai da Hawaye Suka Fara Fita Daga Idanuwanta ta Duƙe Ƙasa Tana Kuka bai barta ba sai da Bulalar Ta gama Karairayewa A jikinta kana ya ƙyaleta ya kalleta yana Faɗin "Wannan na Bye bye Kwatar-kwashi ne In kika Dawo First Time SS1 akwai Welcome to GGUSS SS1 kwatar-kwashi Tunda Ke Har yanzu bazaki yi Hankali ba Bush girl kawai wato ba Ubanki ba sai dai nawa ko..?"

Ya fada yana Saka ƙafa ya Shureta Dai-dai Lokacin da Wata Arniyar Motar Buggati baƙa ta Shigo Cikin Mktanta Kallon Farko Kowa yayi ma motar Suka san Motar da Zata Ɗauki Mr Bello da Aneesa Ce Domin duk Faɗin Mkrantar babu Wanda Ake Zuwa Ɗauka da Motocin Alfarma sai Su, Aneesa Dake Duƙe tana Kuka Ko Ɗagowa batayi ba nan Uncle Aminu ya Juya ya Nufi inda Mr Bello ke Tsaye yana gaisawa da Direbansu Mallam Inuwa, Tuni Ɗaliban Mkrantan Masu Tafiya Sun Watse Su kuma 'yan SS3 sun Shiga Jarabawa.

Lokacin da Mr Bello ke gaisawa Da Mallam Inuwa yaja p.cap Ɗinsa Sama kyakkyawan Fuskarsa Ta Bayyana Wow.. Haƙiƙa Allah yayi Halitta Domin Wata kamilalliyar Fuska na Hanga mai Cike da Kyau da Haiba Farin Namiji ne mai Ɗauke da Dogon Hancinsa Har Baka A kallon Farko In kayi mai Zaka Fahimci ya haɗa Nasaba da Fulani Zagayeyyen Baƙin Sajensa ne ke Ƙara mai kyau Wanda yayi ma ƙaramin Bakinshi Kwanya matsakaitan Idanuwanshi masu Ɗauke da Wasu Fararen Idanuwa Masu Kyau da Narkan da Zuciyan 'yan Mata, Sai zara zara gashin Idanuwansa Masu Tsawo da baƙi Da Gashin Girarsa Baƙi Siɗik Haɗe da Wani Kwantaccen Gashin Kansa Irin na Fulani Mr Bello baya barin Gashi Ya Taru Akanshi ko A yanzu Ma Babu Cikar Gashi Sosai

*MUHAMMED BELLO MUHAMEED JIƘAMSHI* Kenan wanda Ɗalibai da Malamai kema Laƙabi da _MR BELLO_  kuma Ƙani ga Cheif Army of Staff na ƙasa Gaba ɗaya Wato *LT. GEN. MUKTAR MUHAMMED JIƘAMSHI* Cikkaken Namiji ne mai Aji da Zati Wanda Kaf 'yan Matan Dake GGUSS kwatar- kwashi ke Rubibi Akanshi, Tun daga Kan Malamai da Ɗalibai, Kan 'yan Junior ne da Senior, Kaf Ɗinsu ba Yarinya Da Zatace bata Crushing Ɗinsa, Mkrantar Tana ji Dashi Domin Tunda Ƙasa Zuwa Sama Shine kaɗai Malami ƙwara Ɗaya Tak da yake Ɗaukan Su Mathematics Sakamakon yana da Master Digree Akansa Wanda ya Haɗosa a babban Birnin America Wato U.S.

Da Sauri Billy Kaita da Salamatu S Jibiya Suka ƙariso ga Aneesa Suka Riƙota Billy na Faɗin "Aneesa Don Allah ki daina Wannan Taurin kan Wahala kawai zaki Dinga Sha.." Aneesa Na Miƙewa Ta Fizge Jikinta Tana Share Kwalla tace "Bazan bari ba Ki Rabu Dani Munafuka Ai Burinki ya cika Tunda Yau ɗin ma Ina Murnan zan Bar Uƙuba sai da Aka ƙara Zalunta ta, In kika ƙara Nuna Kin ma Sanni Billy Allah ya Isa Tsakanina Dake Domin Duk Masoyina bazai so Wanchan Mutumin ba.." Tana gama Faɗin Haka ta Ɗauki Trolley ɗinta da ƙaramar Jakarta Da Wata Jaka Ta Rataya abaya kafin ta kalli Salamatu Jibiya tana Faɗin

"S. Jibiya Sai munyi Waya Ga Mallam Inuwa chan yazo zan Tafi kada yasa atafi Abarni irin na Wanchan Term din.." S. Jibiya bata samu Zarafin mgana ba Aneesa Ta Wuce Ruƙu Ruƙu da Kaya Billy da Salamatu Jibiya Suka Bita da kallo Suna Kaɗa kai Sanin Halin Aneesa na Masifa da Saurin Fushi Ammh Akwai Saurin Sauka Nan da Gobe zata manta komai don Duk Faɗin Kwatar -kwashi bata da kamar Billy Kaita da Salamatu Jibiya.

Tana ƙarisowa Mallam Inuwa Ya Tareta da Fara"a yana Faɗin "A"a ga Ɗiyata 'yan Makranta, Kai Masha Allah Hajiya tace Kin kammallah zangon karatu na Farko.." Ya faɗa Cike da Murna Cikin ɓata Rai Aneesa Tace "Wlh na gama Dawowa wannan Mkrantan Baba kama ji gaskiya Haba na gaji da Wannan karatun Mkrantar Ta Isheni Baba Wahalar Tayi yawa Tunda bana Shiga Aljannah bane.." Ta faɗa Tana Sakar mai Akwatunanta Guda Biyu Ɗauka yayi yana Dariya gefenshi ya kallah yaga Basu Bello Sun gangara Zuwa Quarters d'in Malamai Mr Bello zai Ɗauko Jakarsa.

Booth ya Buɗe yana Zuba mata Akwatunan, Hannu ya Miƙa yana Faɗin "Au hakane fa Kin gama Toh kawo Jakar itama asaka A ciki Karatu kam Kin gama Tunda bana Shiga Aljannah bace Wanda Kika samu Allah samai albarka.." Washe baki Tayi Tana Faɗin "Yauwa Baba Allah sa Yadda ka Fahimta Haka *YAYA MUKTAR DA ANTY RAHILA* Suma su Fahimta ko da yake Ko Sun barni nasan Wannan Mugun bazai barni ba ammh Wlh Wannan karon ko Guduwa ne Sai na Gudu Borno Wajensu Yaya Ali In dai Aka matsamin sai na Dawo Mkrantar nan..." Ta faɗa Harda Sharɓe Ƙwallah..

Kallonta yake bayan Sun gama Saka kayan ya Rufe Booth d'in Motar yana Faɗin "A"a 'yata mai yayi Zafi basai kin gudu ba, Insha Allahu Shima Zai Fahimceki.." Ya faɗa Yana Danne Dariyansa Ganin Tana Wani Taɓe baki gidan baya ya Buɗe mata yana Faɗin "Ɗiyata kinbar ƙawayenki gasu chan.." Jin Haka yasa Ta Juya Tana kallon Salamatu Jibiya da Billy Kaita Suna Tsaye Suna kallonta, Harara ta Makama Billy Harda Murguɗa mata baki Tana Faɗin "Sai Wata rana na bar Muku Mkrantar.." Ta faɗa kai Tsaye Tana Shigewa Mota, Dariya Suka saka Aran S. Jibiya Tana Jaddada Dawowar Aneesa SS1 Dole kamar yadda Yake Awajensu.
Chapter 2 · 0% Book details