← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 76

Sashe 74

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karisa yayi ya saka hannu yana Bude Kolilin Abincin Daya Bayan Daya kamshin ya Dakeshi,Lumshe ido yayi ahankali yana Fadin"Anee....My Anee.."Yake Fada cikin Sanyi da murna kafin ya waigo yana Waige waige cikin Muryan Fushi da Lallashi yake fadin"My Anee where are u plz come out...Karki sakani cikin garari i know wannan kashin baza"a sameshi wajen kowa ba sai wajenki Matata..."Yafada yana lumshe ido Ina kallonsa ina Danne Dariya Dawowa yayi tsakiyar Falon yana neme neme,kafin ya Shiga Duka bedroom dinmu yana kiran Sunana,yagama Dube Dubensa bai ganni ba ya fito ya shiga dayan Bedroom din nan bani ciki Haka ya Dawo falon yana Rike kugu cikin Sarewa yake Fadin"Anee...Wai bazaki Fito na ganki ba...? Yake fada yana Kara ware idanuwansa cikin Tsakiyar Falon.

Bakina na Rufe kada Dariyata ta Fito kaawai sai Muhammed Amin ya tona ni inda yana Wasa da Hannunshi ya Bude Labulen Lokaci Daya yana bare baki da Kuka dama inayi ina Jijjigashi yasa bai sakamin kuka ba cak ya tsaya yana kallona Ni kuma sai na Yi jagale ina binsa da kallo kafin na saka Hannu na Dungurema Amin kai lokaci Daya ina Tura baki kafin na Fito Daga wajen labulen ina yar Dariya Shima Amin kukan ya Daina yana bin Babansa da kallo kur.

Kansa ya Dafe yana kallona cikin Wani yanayi kafin yace"Anee ni zaki bama wahala ko..? Yafada yana Sakarmim Manyan idanuwansa,Kai na lamgwabe ina Fadin"Suprises...."Na Fada ina Dariya bai yi watawata ba ya isa gareni sai ji nayi ya Hadani Nida Muhammed Amin ya Rumgumemu ya kamkame Lokaci Daya yana sakin Ajiyar Zuciya Nima Numfashin na Sauke jina Akirjin mijina Da Nadade ina kewa cikin Rashin Hayyaci yake Sumbatar Wuyana yana Fadin"I love u....Miss u like Crazy my Wifey..."

Yafada cikin Wata murya mai cike da Muradi mai girma nima kara kamkameshi nayi ina Fadin"Love u...more and more...Nayi matukar kewarka Mijina.."Mundade muna Rumgume da juna kafin mu saki Juna muka Bi juna da kallo Lokaci Daya muka sakarma Juna Mirmishi Muhammed Amin ya karba yana Dagasa sama yana Fadin"My Bomboy kana son Appanka sosai Tunda ka Tona ma mamnka Asiri ko.."Kansa na Tallaba ina Fadin"Waya gaya maka..? Toh yafi son mamarsa akan Babansa.."Kallona yayi yana Fadin"Kaina fa kika Dungure.."

Baki na Tabe kafin yayi mgana ta kara Tallabe kanshi ina Fadin"Eh ko zaka rama ne..?Na fada ina Dagamai girata Guda Daya,Ido ya zaromin ni kuma na Murgudamai baki ina Dariya Fuska ya Shagwabe yana Fadin"Mr Bello guda kike Dunguri kamar wani Danki..Karki manta ni ta wani barayin yayanki nake kuma Malaminki nake karma muje Bangaren Aurattaya zan iya Lallasaki bamai min mgana sai ma Godiya da za"a bini Dashi.."Yafada muna Shiga cikin Bedroom dinmu Kallonsa nayi ina Fadin"Au ni zaka Daka...?

Kai ya gyadamin yana Hade Rai,Yar Dariya nayi kafin na Juyamai ina wani taku Lokaci Daya ina Fadin"ai ni yanzu nafi karfin Duka...Mutum ya Dakeni Wlh Anjuma..."Ban karisa ba yashiga Fadin"Allah baki hakuri Anty Anee...Bomboy tayani ba mamanka Hakuri kartamin Horan Da bazan iya Dauka ba.."Dariya na saka shima Dariyan yake yana Fadin"muguwa kawai.."Tiolet na Fada ina Fadin"Ban kai ka mugunta ba Mr Bello.."Yana jina bai bani amsa ba Farinciki ya cikashi Har nagama Hadamai Ruwan wanka na Fito yana ta wasa da Amin,Karban Amin nayi na ijiyeshi kan gado shi kuma na taimakamai na ciremai kayan Jikinsa na rakasa Har Tiolet din yaso ya batamin kwalliyata na Zille ina Dariya na Fice Daga cikin Toilet din na Rufo masa kofa.

Koda ya Fito har Muhammed Amin yayi barci yana shan Nono Shikenan ya bingire yana barci daman Shi Nono ne mtsalanshi yana Jin mai Dumi acikin Cikinsa Shikenan,ni na taimakamai ya Shafa mai ya saka wata bakar Jallabiyansa kafin na kama hannunsa mu fita zuwa Falo sai samam Dining,Ranar nasha yabo da Santi nan take ya bani 50k cash saka albarka kuwa sai da na Rufemai baki Farincikina ya cika bakina yaki Rufuwa Ashe mata Dadamama haka Sukeji in sukayi Wani Abun don Mazajensu suka ci suka yaba musu nidai kam Farincikina ya kasa Boyuwa akan Fuskarta nan yake Tambayata waya Dawo dani na Fadamai Duk Abunda ya Faru Dariya yayi yana Fadin"Allah sakama Su Ya Ali da Abarka...Dasu mama gabadaya....Sun yi matukar kokari wajen gyara min Anee sosai Duk da ta bangaren girki nafara Harba Dashi bansani ko Dayan Harka kuma ya zata kaya dani ba.."Kirjinsa na Buga ina Dariya nace"Kila sai ka Zauce ka Faramin kuka.."Fuska ya Shagwabe yana Fadin"ai ni Tuni nake miki kuka My Anee baki sani ba.."Kallonsa nayi kafin na Sumbaci goshinsa,ina Fadin"Bana Fatan na Rika saka Mijina kuka.."Hannuna ya kama yna Fadin"Ai bana wahala bane na Tsabar Dadi ne...U Drive me Crazy Wifey...Allah yayi miki albarka..."Da Amin na amsa ina kara lafewa bisa jikinsa muna jin Bugawar Numfashin Juna.

Yadda Bello ya Susuce akaina Dakyar ya bari muka karayin Wanka mukayi sallar Isha"i Muhammed Amin cikin Dan gadonsa na Sanya shi chan gefe mu kuma muka Fada Tsakiyar gadon Naked ba komai ajikin mu,Fatarmu na gogan Juna muna Kara samun Body Contact atsakaninmusu,ina kallon Cikin Idanuwansa na saka hannu nayi kasa da Hasken Dakin ko Dumlight din ban kunna ba Sai Hasken Dake Fitowa ta Tsakanin Labule Ana ta walkiya Domin Hadari ne ya Hadu sosai agarin Tunda Anshiga Lokacin Damina.

Cikin Fitar Hayyaci muke Sumbatar Juna Lokaci Daya Hannayenmu na kara kaina Jikin na Juna,lalle na yarda Dagani Harshi munyi kewar juna Domin Dagani Harshi Hawaye muke Shabe Shabe,Shi kuwa gabadaya mangungunar Danasha Sun Taimaka wajen Fitarsa Daga Hayyacinsa,ya shiga cikin Wata Ni"ima wacce bazai iya Fassarrata ba,ana Tsuga Ruwan sama sanyin Damuna ya Hade da yanayi mai Dadi Haka muka kamkame juna muka Shige Blanket muna kara Caccakan juna cikin so da kauna.

Har bayan sallar Asuba sai da muka Dasa,Haka ya Kamkameni yana sakamin albarka alkawruka kuwa sai da na Rufemai baki wasu Magnganun ma baisan yana Fada ba,kalmar ina Sonki kuwa ya Fada yayi cikin Botiki,Nima kamkamesa nayi ina maida Numfashi cikin Muradi mai girma wanda baki bazai iya Furtawa ba,kuma alkalami bazai iya Rubutashi ba balle har ya wallafa.

Dawowata yasa muka Bude Sabon Shafin Soyayyah bamu gajiya da juna gefe Daya kuma muna Kula da Danmu Muhammed Amin kamar mu lasheshi,Bama iya Boye Soyayyar damu ma Juna ko agaban waye kuwa,Ban yarda na bar kaina na lalace Daga Haihuwa Daya ba na mike ina gyara kaina Da Jikina Sanin Halin mijina mai son Ado da kwalliya kuma yana Bukatar kullum ya dinga jin Dadin wajen Harka yan"uwana suna Taimakamin sosai kuma na tabbata ko yau Baba ya Dawo gidan Duniya bazai Tirr dasu ba Saboda sun kula dani kuma sun bani kowani irin Gata

*****

Wata uku da Haihuwa ta Bello yagama Dukkan Shiryen Shiryensa sai dai kawai yazo yana Fadamin ya tura C.V Dinshi Tun last 8 month din Da suka gabata ya Tura ma jami"ar *CLARKSON UNIVERSITY NEW YORK* kuma Alhamdulillah sun Riga sun karbeshi Tun Wata Daya Daya gabata so ya tura musu Duka komai ta Email dinsu yanzu nan da wata Daya zamu tattara mu koma chan da albishir din Nima achan zan Cigaba da karatu na sun bashi gidan zama har illah masha Allah da Motar Hawa sai dai in Shine ya gaji ya Daina aiki Dasu.,Ammh sai yaki karban gidan ya neman mana wani mension mai kyau ya siyan mana komai ta Waya ya gabatar.

Wayyo Dadi murna ta cikani na Daka tsalle na Rumgume Mijina Saboda Farinciki Haka na Shiga Kiran yan"uwa da abokan Arzuka ina gayamusu suna Tayani Murna B.kaita da Salamatu Jibiya sun fi kowa murna,Duk d B.kaita tana Tunanin bazan samu zuwa Bikinta ba wanda aka sanya wata Biyar masu zuwa zata auri wannan dai lacran na Umaru musa yar'aduwa Universtiy.

Iyayena da yan"uwa sun fi kowa Murna Ko Ya muktar bai sani ba sai da muka je musu sallama Jinjina kai yayi yana Jinjina ma Kanin nasa wajen kwanya ya Tabbata kaf jami"o"in Dake cikin Duniyar nan ba wacce Bello zai nemi aiki da ita ta ki bashi Dama Gabadaya Da grade A yake Fitowa Shi kanshi Dayake yayan nashi yana Jinjina ma baiwar kanin nashi Sosai.

Daga Abuja Borno mukaje yi musu sallama Kwana Biyu mukayi Munje Maiduguri wajen Anty Nafee ammh bamu kwana ba,muka Dawo aranar Washegari kuma Muka Hawo Jirgi zuwa kano Anty yagana sai dai mukayi sallama awaya Anty Aisha dai Naje gidanta na Wuni Haka gidan Ammi wanda zuwa Lokacin Bello da kanshi yama Uncle Aminu mganar Raihana da Midibbo wanda ya kusa kamallah Military sch ya kusa Dawowa Itama Raihanar Ta kusa gama nata karatun su Baffa Hardo suka zo wajen Dangin Su Uncle Aminu suka nema ma Modibbon Auran Raihana,An saka Lokaci Wata Goma masu zuwa Lokacin Dukkansu sungama karatunsu Har Modibbo yafara aiki.

Mun gama Duka Shirye Shiryen mu komai namu ya kamallah ba Da wasu kaya bane zamu tafi sai Abunda Ba"a rasa ba,Jami"ar BUK tafikowa Damuwa da kuma Ganin Asaran Rasa Mr Bello,ammh basu da yarda zasuyi Tunda dai cigabane ya samesshi haka Daga Daliban Har malamai aka rabu ana kewar juna Uncle Aminu da Anty Aisha da Megidanta suka Rakamu Aiport Din Mallam Aminu kano Da karfe 8:30pm na Daren Ranar Asabar jirginmu ya Daga zuwa Birnin New york.

Mun Sauka a babban Filin Jirgi na New york a inda muka samu Taxi har zuwa cikin anguwar da Jerin Gidajen da Bello ya siyama suke wato *maahattan Midtown* gida ne mai upstsir mai kyau da Tsari mai Dauke da Falo da 2 bedroom Daga sama sai kichen da Dakin baki Daga kasa Daga waje sai aprtment haka wajen parking din motoci,Muna da makota Wadanda ke kusa damu,Daya barabiya ce karatu Mijinta yazo yi sai Daya kuma Yar Nageria ce ammh kuma bayarbiya ce Mijinta Likitane Shima aiki ya kawoshi Sunanta Adija Tunda muka zo kasar itace ta shigo muka gaisa naji Dadin samun Wani Dan kasata kusa dani.
Chapter 74 · 0% Book details