← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 76

Sashe 33

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai Bayan Mangariba kana tawagar Motocin ya Muktar,Suka je Filin Jirgi Suka Taho Dasu Bello Dake Kwance Cikin Bedroom Dinsa Cikin Bargo yaji Dawowarsu Kansa ne ke bala"in Ciwo Tunda Suka Daawo Ganin Halin Dayake Ciki ne ya saka Sani bai Wuce kaduna ba Aranar ya bari sai Washegari,ya Zauna Tare Da Bello,Daga nan ya saka Sani yayi Waya Zuwa Cikin Shashen ya Mukrar akwai Telephone direct Zuwa Kichen,Alheri ce tazo ta kawo musu Abinci da Abunsha Sanin ne kadai yaci Shi Bello Fruit kadai yaci Yayi Taking pracetamol ya koma ya kwanta Zuciyarsa na Kuna Gabadaya Ya Muktar ya batamai bajet,Aneesa fa Bata Daga Cikin matan Dake burgesa ammh Kuma bakin alkalami ya Rigaya daya Bushe.

Shashen Daada aka Sauke Aneesa ita da Kawayenta da yan"uwan babansu,Sauran kuma Su ka koma Shashen baki,agajiya Suke Shiyasa Abinci kadai Suka ci Kowa yabi Lafiyan gado yana Warware gajiya,Aneesa ko yunwa ce Taji Zata kasheta Tatashi Taci Abinci kadan Ta koma ta kwanta Kusa da B.kaita Barci Ranar barawo ne ya Sace Aneesa ammh kwana Tayi kuka,ga Zazzabin Jikinta Saura kuma Suna Dakin Daada chan Suka Kwana.....

Sai da Safe kana ya muktar ya Shiga part din, Bello inda ya Tarar Dashi kwance Cikin Blanket,sai Sani Dake Shirin Tafiya,Gaisawa Sukayi da Sanin kafin ya karisa Gefen Gadon ya Zauna yana yaye bargon da Bello ya Lulluba Dashi Lokaci Daya Yana Taba goshinsa.

Bello Dayaji Motsi sai ya Bude Idanuwansa Da Suka kumbura ya Sauke kan ya Muktar Kokarin Mikewa yake da Sauri ya Rikesa ya Taimaka mishi ya mike Zaune yana Dafe kanshi Cikin Tsausayi Ya Muktar yace"Sannu kan ne..? Gyada kai Bello yayi yana Yamutsa Fuska,Ajiyar Zuciya Ya Muktar ya Sauke kafin ya Mike yana Fadin"Ka Shirya muje Asibiti Anjuma.."Bello ya Dago kansa yana kallonsa bai yi Mgana ba,Saboda Bakinsa yamai Nauyi Lokaci Daya Ya Muktar ya Nemi Hanyar Fita Daga Bedroom din yana cema sani.."Badai Tafiya Zakayi ba.? Kai tsaye sani yace"Eh Ranka ya Dade."

Ya rike Handle din Kofar ya Waigo yana Fadin"Ayyah badamuwa Mungode..In zaka Wuce ina Haraban gida..mungode.."Daga Haka yafice Daga Bedroom din yana Fitowa da wayarsa Wacce ke Aljihun Wandon jallabiyansa.

Sani ya karisa kusa da Bellon yana Fadin"Malamin mkranta Ni zan kama Hanya.."Gyada kai Bello yayi Kafin ya Furta.."Nagode Sani.."Mirmishi yayi kafin yace"Bakomai..Ango plz ka cire Damuwa Aranka Dama chan itace matarka,Mganar kasim kuma karka damu bai isa yamaka Abunda Allah bai maka ba.."

Kallonsa yayi Ido Cikin Ido kafin yace"Nagode Sani..Ammh ni kasim baya gabana karamin alhakine,kai ne zan ce ma ka kula Kada yace zai bataka Wajen aikinka.."Yafada Cikin Sanyin Murna Sani ya Rausayar dakai yana Fadin"Haba bai isa ba ai bashi ya Dauke ni ba,Allah ya baka lafiya.."Yafada Lokaci Daya Suna musabaha kafin Sani ya Dauki Wayarsa ya Fice Daga Bedroom Din Bello yabishi da kallo.

A haraban gidan ya Iske Ya Muktar na mgana awaya sai da ya Jira yagama,kana Suka sake Sallama 50k cash Ya bashi da Farko kamar bazai karba ba sai da Ya Muktar din ya mtsamai,musabaha Sukayi Ya Muktar na karamai godiya Mallam Inuwa Direba ya Daukesa Zuwa Filin Jirgi inda Zai Shiga Wani Jirgin Zuwa Kaduna garin Gwamna

Sun wayi gari Cikin Hidima Abunsu Kamar Babu Abunda ya Faru,Kafin karfe goma baki Sun Fara Zuwa kawayen Anty Rahila na nan Abuja,can sai ga Maman B.kaita ta iso,maman S.jibiya ne Bata samu Zuwa ba bata nan Taje Jibiya,Tuni Dama su Alheri Sun kamallah Girke girke,dama Tun Safe Ya Muktar ya Fice Daga Gidan,Aneesa ko kwanciyarta Tayi Taki Tashi tayi Wanka Tana gani su B.kaita Sukayi Wanka Suka Dau kwalliya bata yi Wanka ba sai da Taga yan Sch dinsu na Kwatar kwashi Sun Fara Zuwa Wata Rabi daga Suleja sai Mariya Daga kaduna Shiya Tilastama Aneesa Wanka ta Shirya Cikin Wani material Riga da Sikat,ta yane Mayafin Material din kamar Lifaya,bata wani yi kwalliya Ba Fuskarta Kodai kodai ba Wanda ya Bi ta kanta gwarama Daada ta Shigo ta mata Nasiha Shine Har ta saki Ranta ta Shige Cikin Kawayenta anata Hira,Su B.kaita Su suka Fara kyankayasama Su Rabi Wanda Aneesa Ta Aura nan suka saka guda Abunda ya kara saka Aneesa Ta Fashe da kuka Suko Suna mata Dariyan Shakiyanci.

Ba laifi Yan makrantarsu Aneesa Sunzo musu,zasu kai goma Kowa Tazo Taji Aneesa ce ta Auri Mr Bello sai Taji Aneesa Tayi Sa"a,Domin Samun Namiji kamar Mr bello abu ne mai Wahala,sai Tambayanshi Suke sai ace musu baya nan Alhalin yana part dinshi yana Fama da Ciwon kai Da Tunanin yaya Makomar Rayuwarsa,Anyi Biki lafiya Sha"ani Yayi Dadi Kowa kagani Cikin Farinciki banda Aneesa da Bello,Wanda Anty Rahila Ya Muktar ya Kira yace Ta Shiga Ta Dubashi da yammah Mallam Inuwa zai kaishi Asibiti.

Duka bakin Washegari Ranar Lahadi Kowa yayi Haraman Tafiya Kawayen su Aneesa Wasu basu kwana ba,Wadanda suka kwana kuma da Safe suka Tafi,Haka B.kaita Tabi mamanta Tun Jiya S.jibiya ne Direban gidansu yazo Ya Dauketa Suka Rabu da Aneesa da Kuka,Anty Yagana da Anty Nafee,da Sanah da Yan"uwan Babansu kuma da La"asar Aka kwashesu Zuwa Filin Jirgi inda Suka Shiga Jirgin Maiduguri,Anty Aisha kuma mijinta ya aiko aka Dauketa ta Wuce kano nan Suka bar Aneesan Falon Anty Rahila bayan Sun mata Nasihohi da kuma Lallashi Data Rumgumi Auranta,Haka Suka barta Tana ta kuka kamar Ranta Zai Fita Daada ma kasa lallashinta Tayi Saboda Tsausayinta.

Sai bayan Sallar Mangariba Bello ya Fito daga Shashensa Cikin Riga da Wando,Duk ya Rame kamar bashi ba,Mallam Inuwa ya kaishi Specialist hop,ya karbo manguguna Dama anan Suke da Fayel,daya Dawo Dakyar ya iya Shiga Masallaci yayi sallar Isha"i yana Komawa Shashen nashi ya Shiga Bedroom dinsa kenan yaji Mganar ya Muktar Da Daada bai kai ga Fitowa ba ya Muktar ya Bude Kofar Bedroom dinsa yana Shigo yana kallonsa.

Kibiya ki karanta cikin Salama.

*Anitha...*
8/19/20, 8:03 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

  
*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_

*Littafina na kudi ne,kibiya ki karanta cikin salama,akan â‚?200 kachal,Vips â‚? 400 ne,kada ki karanta min littafi indai baki biyani ba,Domin neman karin bayani zaku iya nemana ta wannan Nombar 09069067488*

        *🅿�18*

"Kallonsa Bello yayi Lokaci Daya yana Lumshe idanuwansa,bai kariso Tsakiyar Bedroom din ba yace"Ya Jikin naka...? Cikin Sanyin Murya yace"Am better Now..."

Kada kai ya Muktar yayi kafin yace""Daz gud...Ka samemu Afalo zamu yi mgana dakai.."Kai Shima ya gyada mai baiyi mgana ba Har ya Muktar ya Fice Daga Falon da Kallo ya Bisa Lokaci Daya yana Tura Hannunsa Bisa Sumar kanshi Lokaci Daya kuma yana Sakin Ajiyar Zuciya,bai Fito ba Sai da yadan Bata Lokaci kana ya Fito Falon,nan ya Tarar da Daada Da ya Muktar suna kan Kujera mai zaman mutum Biyu Sai Anty Rahila dake kan Mai zaman Mutun Daya Aneesa ke Zaune akasa kanta Duke Cikin Farar Lifaya,Hibba na gefen Abbanta Junior ne ke kusa da Aneesa yana wasa da Gefen Mayafinta.

Cikin Sanyin Jiki ya kariso Gaban Daada ya Zauna Kusa da Kafafunta,kanshi ta Dafa Tana Fadin"Babban Megidana,Duk ka Rame.."Tafada tana kallonshi Mirmishi ya Sakarmata Kafin ya Rike Hannunta yana Fadin"Nayi kewarki Daada.."Yafada yana Sauke Kwayan idanuwansa kasa Lokaci Daya yana gaida Anty Rahila,ta amsa cikin Sakin Fuska,Da Gudu Hibba ta Dane Jikinshi Tana Fadin"Oyoyo Uncle.."Riketa yayi yana Shafa Kumatunta lokaci Daya yake Fadin"Hibbatullahi Ta zama yan mata ko.."Baki ta Washe Ita adole ance Ta zama yan mata Dukkansu Sai da Suka saka Dariya Banda Aneesa dake Hararan Bello ta Cikin mayafinta Shiko Tunda ya Shigo Falon ko kallon Barayin Datake baiyi ba Ballatana ma Har ta samu Wani kyakyawan kallo ..

Ya Muktar ne ya gyara zama yana Fadin"Bello...."Yafada Cikin Muryan ba Wasa,Dago da kansa Bello Yayi daga Wasa da Hibba yana Fadin"Na"am yaya..."Bai Tsaya Sauraransa ba yacigaba da Fadin"Nasan kasan Dalilin Zaman mu anan ko?kowa yasan yadda lamura Suka Chanza yanzu dai ka Tabbata miji ga Aneesa itama ta Tabbata matarka toh gatanan An kawo Maka ita ina Fatan Zaka Riketa bisa amana da adalci.."Yafada yana kallonsa kansa Bello ya Maida kasa yana kananan Sauke Numfashi Cikin Muryan Sanyi yace"Insha Allahu Yaya..."Mirmishi Daada Ta Saki kafin tace"naji dadi Hakan Sosai Megidana naasan bazaka bamu Kunya ba Don Allah ku Zauna Lafiya da Junanku Tasanka kaima ka santa Tunda Duk Gida Daya Kuka tashi...Allah ya baku Zaman lafiya,Ayita Hakuri Aneesa kamar kanwa Take gareka Itama tamkar wa kake gareta In kun saka Hakuri Acikin Zamanku kubama kowa mamaki in kuma kowa yaki Saukar da Halinshi kuma Kusha Wuyan Juna..."Bello kansa na kasa bai yi Mgana ba Illah Wasa da yakeyi da Hibba,nan da Daada Da Ya Muktar suka kara yi musu nasiha Sosai Aneesan ma Suka ja mata kunni Sosai Anty Rahila ma ta mata nata Nasihan Sosai kafin Su Rufe Wajen da Addu"a Sun mike zasu Tafi kenan ya Muktar yace"Ku cigaba da Maneji anan Kafin Kagama Shegen Ra"ayinka ka Fara Aiki mai kyau domin Nasan Ko Cewa nayi ka Shiga Daya Daga Cikin Gidajena na nan Abuja bazaka yarda ba.."

Bello ya Mike yana Rike da Hibba yana Fadin"Allah ba Haka bane Yaya..Na Riga Na Turama BUK C.v  Dina Ta Email dinsu Har Sun Turomin da Sakon naje na karbi Appiontment letter.."Kallonsa Ya Muktar yayi kafin yace"Ok..Chan din Dai yayi maka,ga University of Lagos Tun yaushe Suke Nemanka.."Bata Fuska Bello yayi yana Fadin"Nifa Yaya bana son Zama  a kudu Allah..."Jinjina kai yayi kafin yace"Ba mtsala Duk Dayane Allah yabada Sa"a.."Da Ameen Dukkansu Suka amsa kafin Su yi musu sallama su fice Daga Falon Bello na Biye Dasu Dauke da Hibba Junoir ko Da Kuka ya yarda Anty Rahila ta Daukeshi ya makalema Aneesa Wacce Ke Hawaye.
Chapter 33 · 0% Book details