← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 76

Sashe 25

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai Tsaye yace"Ke mana Aneesa..."yafada yana Kafeta da Ido Lokaci Daya Suka Shagala da kallon Juna har su B.kaita Suka kariso Wajensu suna kara Murza Idanuwansu Cikin mamaki Ganin Aneesa da Wani Abun da basu Taba ji ba balle lbri,bayan Sun Dawo Daga clinic karbomata mgani Suka koma Hostel bata nan Wata Maryam Dake Barayinsu ne Tace Ta fita an zo Nemanta koda suka Fito basu Ganta ba,Jamila hadi ce ta Nuna musu Ita Har Suka kariso suna mamakin Abun ganin basu san da Zuwansu ba ya sanya B.kaita tayi gyaran Murya Wanda ya Dawo Dasu Daga Cikin Hayyacinsu na kallon Kauna da Suka bi Juna Dashi.

Cikin Rage girman Idonta Aneesa Ke kallonsu kafin Tayi mgana B.kaita ta Rigata da Fadin"Sannu mara lafiya ." tafada Tana Hararanta yar Dariya Aneesa Tayi Tana Rufe Fuska Da Gefen Hijabinta Lokaci Daya Tana Satan kallon kasim Dake kallon Su B.kaita Shima yana Mirmishi Lokaci Daya yace"Au ce muku tayi bata lahiya..?
Yafada yana kallonta Cike da Soyayyah.

S.jibiya tace"Eh magani ma mukaje Clinic muka karbomata Ashe Ciwon na luv ne ko Anee..? Ta gefen Hijabinta Take lekosu Tana Dariya Shima dariyan yayi yana Fadin"Ku mata Uzuri nine na bata mata Lokaci ya kamata Tun Around 10 ina Wajen nan Banzo ba sai yanzu.."B.kaita ta gyada kai Tana Fadin"Mufa muna Cikin Duhu ke Aneesa kimana Baya kece kuwa kodai Watace Dabam.."Aneesa Ta Bude Fuska Tana Fadin"Watace Dabam Don mai garinku.."Dariya Sukayi Gabadaya kafin Aneesa Ta gyara Tsayuwa Tana Fadin"Kasim meet my Childhood Friend,Bilkisu kaita and Salamatu s Jibiya Abunda yasa kaji nace Childhood Frnd we are here Together tun Jss1.."Kai ya gyada yana kallonsu yace"Masha Allah Sannunku kawayenmu.."Mirmishi Suka mai kafin Suce"Kaima Sannunka..."

Juyawa Aneesa Tayi Tana kallonsu kafin Tace"And u Meet my Boyfriend Kasim..."Tafada Tana Mirmishi Ido Suka sakarmata Suna kallonta Cike da mamakin mganarta Duk da Tun Zuwanssu Wajen Suka Fahimci Wani Abu,B.kaita ce ta gyada kai tana Fadin"Aneesa bukar bulama u ar a great Player Shegiya Wato Duk kin maidamu Hoto,Tunda muka Dawo Hutu kika zama Wata Iri Ashe Ashe kin Fada Soyayyah ne..."Tafada Tana Hararanta Dariya kadai Take musu kasim na Tayata kafin yace"Toh ai bakuma sani ba Nacita gyara am not her Boyfriend.."Cikin wani Kallo Aneesa Tace"Umh...Am whta.?

Yana Mirmishin Jin Dadi yace"Am Ur Husband to be in d Next of 6month Insha Allahu.."Yafada yana kallon Ameesa Ido ta Zaro ta kallonsa kafin B.kaita tace"Really..?"kai ya gyada kafin yace"Sure...Albishir din Dana keta Rawan Jikin Zuwa na mata kenan bayan Tahowarki mkranta ba mun Rabu zanje katsina na samu Abba Akan mganarmu ba..?

"Kamar Wata kadangaruwa haka Aneesa Ta gyadamai Kai Cikin Sanyin Murya ya Cigaba da Fadin"Toh ina Samunshi Shikenan mgana ta je Wajen Ya Muktar,Daganan kuma ya Kira chan gida Borno,Atakaice dai Satin Daya wuce Suka zo Kuma Aka Sanya Rana bayan An Biya Sadaki,Yanzu dai Kuna gama Candy za"ayi bikin mu ku kaimin Amaryata kaduna.."Ya karishe Mgana yana kashema Aneesa Ido..

Shewa B.kaita da S.jibiya Suka Saki kafin ta su Tafa Suna Fadin"Allahu Akbar kaji masu yi Don Allah..Aneesa As a Bride Woww..Allah ya sanya alheri We are so Hppy.."Suke Fada Suna ma Aneesa Dariya Wacce ke Tura baki Ta bata Fuska Domin Batata zaton Komai zai zo Haka Lokaci Daya ba,Kasim na Tsokanarta su B.kaita nayi karshema Wata katuwar Darduma ya Dauko Daga Motarshi ya Shimfada nan kusa da Motar nashi Suka Zauna Suna ta Hira,kafin su B.kaita su basu Waje suka koma Hostel suna mamaki Wai Aneesa Zata yi Aure ammh kuma Ransu bai musu Dadi ba yadda Aneesa Ta Boye musu lbrin kasim Alhalin Su kuwa ko Saurayi Sukayi In Suka Dawo Hutu Jikinsu na Rawa Zasu kwashe su bama Aneesa lbri Ammh Ita sai ta boye musu Harga Allah Abun bai musu Dadi ba.

Bangaren Aneesa da Kasim kuwa Hirar Soyayyah Suka Sha kamar bazasu Rabu ba,sai Wajen 5 na yammah kana yace mata Zai Tafi Shima bawai Don ya gaji da ganinta bane A"a Saboda kada yayi Dare Ahanya kuma Haraban Mkrantan yan Visiting din Sun Fara Watsewa,Su B.kaita yace ta kira suyi sallama,koda suka zo nan suka ga Aneesa Tayi Narai narai kamar zatayi kuka Haka Shima Baki Suka Rike suna musu Tsiya,booth Din Motarshi ya Bude Ya Fiffito ma Aneesa da Siyayyar Dayayi mata Kaya kamar za"a bude Shago Har sai dai Tace kayan Sun yi Yawa,yana kallonta Cike da Kauna yace"Antytin for u princess kuma ga kawayenmu nan u can Share it together..."Mirmishi Tayi tana mai godiya suma da Godiya suka bishi da Zai Tafi 10k yabama su B.kaita itama 10k ya bata Dakyar Suka karba Bayan Sunga ya Nuna baiji Dadi ba,Har Motarshi ta Fice Daga Haraban gidan Aneesa na Tsaye tana Dagamai Hannu kamar Zatayi Kuka,su B.kaita na kallonta Hostel ta Wuce tana Share Kwallah suka bita da Dariya Wasu Juniors Dinsu suka Kira suka zo suka Daukan musu kaya Zuwa Hostel dinsu.

Suna Zuwa Suka ganta kwance,banza Suka mata Suka Fara Bude kayan Ciki babu Abunda Babu Hadda pad Roll guda Duk da Suma kowannnensu yana Zuwa Dashi Daga gida,baje kayan Sukayi Suna kallo Ciki harda Takeway din Chips dayayi mata Guda biyar,ita da B.kaita Sukaja nasu suka bude Suka Faraci tana gannin Basu kulata ba Tagane Suna Fushi Da Ita bata Bi Takansu ba sai da Taje masallaci Tayi sallah kana Ta Dawo Dakyar ta iya lallashinsu bayan ta gayamusu Farkon Abun Tare da Musu Rantsuwa kafin Su yarda Su koma Tare Suna Santin kayan Lokaci Daya Suna lbrin Irin Bidirin da zasu gudanar Lokacin Bikin Aneesa Ita dai Tana Jinsu Tana Tayasu Da Dariya.

*******

Rayuwa Tana ta gangarawa Domin Da gari ya waye Sai ta maidashi Wuni,Daga Wuni yayi Sai ya zama kwana Da kwana yayi sai Afara Kirga Kwanaki Daga Kirgan kwanaki sai Afara Kirga Sattitika Daga Satittitika sai Afara na Shekaru Ahaka zamu Ta karar da Lokacinmu batare da Mun Fargaba

Acikin wannan yanayin ne gashi Yau da gobe bata bar komai ba Shiryen Shiryen Bikin Aneesa Sai karatowa Yakeshi gashi har Saura Wata Daya Tuni Suka kammallah WAEC sun Fara NECO,shirye Shirye Ta ko"ina Yinshi Akeyi Ta bangaren Gidansu kasimbkuwa suma Suna ta Yin nasu Duk da Umma batason Auren Ammh Abba kabiru ya sakamata Ido Dole Ta Shiga Taitayinta Abunda kuma yafi bata Haushi ganin yadda Mama Sahura ta Shige Gaba Akan Komai kamar Itace Uwar Ango Domin Tunda kasim ya Fahimci Umma bata kaunar Auren sai ya koma Wajen Mama Sahura da Ita yake Dukkan Wasu Shawarwari Hatta Kudin kayan Lefe Ita ya Turomawa Sukaje Dubai Ita da Inna Rukayya Suka Hadomai komai Umma ko Dataji labari kamar ta Rusa kuka saboda Takaichi Abba kabiru yace Komai ya Faru Ita taja tunda ta Nuna bata Ra"ayin Auren.

Bangaren Gidansu Aneesa Ko Borno Suma Suna ta Shirin Bikin Domin Aneesa Ta Tubure kan Borno zata Dawo Tun Ana Saura Sati Daya,Zasu yi bikinsu Ranar Alhamis, jumma Daurin Aure,Ranar zasu Biyo Jirgi Su Dawo Abuja Shima Ayi biki asabar, Lahadi Akai Amarya kaduna Inda Angonta ya gyara mata gidan da Ma"aikatan Dayake Aiki Ta bashi Wanda yake Zaune Aciki Ya Muktar kuma Ya biya Kamfanin MARHABA suka zo Suka kawata gidan Da kayan alfarma Babu Abunda ba"a Zuba ba Sai Wanda yagani Dukiya ne Aka Narka Kamar ba"asan Ciwon su ba.

Ana Saura Sati Uku Biki Su Mama Sahura da Inna Rukayyah Matar Hashim Suka kawo Akwatuna guda goma Gidan Ya Muktar ba laifi an Zuba kaya sai Wanda ya gani Don ma mama Sahura tayi kwangila ta Rage kudi Da kayan sunfi haka an Karbesu Hannu Bibbiyu Domin Anty Aisha Tazo Daga kano Nan ta Fara Sauka Wajen Anty Rahila Tare Duk zasu Wuce borno da Aneesa in Sungama Jarabawa Ta Dawo gida,Harda katin biki Suka Kawo Tare da 50k na Amarya da kawayenta Sunga kara sosai sai yammah Suka Tafi dama Tun Jiya Suka iso garin Gidan Ya Hashim Suka kwana,sai Washegari Suka Jiya,suka bar Matar Hashim din Zasu Taho ita da Zubaida in bikin ya Rage Saura kwana Hudu.

Tsakanin Aneesa Da Kasim Soyayyah sai Abunda yayi gaba...Sun kara Shakuwa da Kaunar Juna,Domin Duk bayan 4weeks yana Hanyar Zamfara Sai dai ko in Aiki ya Rikeshi,Wata Soyayyah yake Numa Aneesa kamar zai Cinyeta Danya,shiyasa Itama Take Sonshi Sosai Kuma yana Burgeta Domin ya Iya kalamai Sosai,ammh Duk da Haba Babu Abunda ya Ragu a neman matanshi da Shaye Shaye sai ma Abunda yayi gaba,ammh bai ta bari Aneesa Ta gane ba,ko iyayensa banda Ya Hashim.

Ana Saura Sati Biyu bikinsu yaje mata Visiting Lokacin Sauransu paper Daya Su kamallah Neco,katin Bikin ya kai mata Dana program of Event Duk da Tace batason Bidi"a Sai da ya Sanya Lonching wanda Zasu gudanar bayan sun Dawo Daga Abuja Dinner kuma A kaduna zasuyi bayan an kawota ,sai Walima wanda zasu gudanar agarin Borno Domin Ya Muktar ya Roki su ya Ali kan Su bari Adaura Auran Anan borno Dakyar Suka Hakura,Ammh Sunso Komai Ayishi a Agarin Abuja..

Gabadaya Meet Dinsu Sunyi Murna da Auren Aneesa Wanda Su B.kaita Suka yi ta raba Katin Bikin Har da malamai Sun Bamawa Sukace Suna gayyatarsu,Meet dinsu Da yawa Sun maAneesa akawarin Inshu Zasu zo Abuja Tunda Borno Tayi Nisa,Bikin ya Rage Saura kwana goma Sukayi Candy Wanda Ranar Tazo da Dimbin Tarihi bayan kwashe Shekaru Shidda A GGSS Kwatar-kwashi,Sunyi murna Sosai Harda Saman Dutsenan sai da Suka Hau Aneesa Tace bazata Hau ba su B.kaita suka Jata ta Hau sai gashi da Tashin Aljanu Ta Sauko Duk da Sun Dade basu Tashi ba,Haka suka kaita masallaci ba Ita kadai ba kusan Rabinsu Sai da Sukayi Borin Aljanu Ranar Hatta dasu B.kaita basu Tsira ba, domin Dutsen Yana da Tarihi dama baka hawa ka Sauko Lafiya.

Mallam Inuwa baizo Daukanta ba sai Washegari bayan Tayi sallama da Su B.kaita kan Zasu Taho In Biki ya Rage Sati Daya Su Wuce Borno Tare Ahaka Suka Rabu Kowacce Direban gidansu yazo ya kwashe Ta ita da kayanta Suka Rabu Suna Hawaye da kukan Sabo na Rabuwa da Juna,Aneesa ta Fara Tafiya sai S.jibiya B.kaita ce ta karshen Wucewa Cike da Kewar Makrantan kwatar kwashi wanda suka kwashe shekaru har Shidda suna gwagwarmaya.

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty_💞
Chapter 25 · 0% Book details