← Book details Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 76

Sashe 24

Mr Bello Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bangaren Gidansu Aneesa Kuwa Kowa Yaji Lbrin sai yayi Murna Su Yaya Ali sai dai Suka Dawo da Lbri mai Dadi,Mama yana ko Har Da Taka Rawa Falmata kuwa Duk Da Tayi Murna bata Nuna ba Saboda Kawaici Sai da Ta Shiga Daki Ta kai goshinta kasa Tana Godiya Ga Allah,Anty Yagana Da Anty Aisha Anty Rahila ta Kirasu Take Sanar Dasu Suma Sunyi Murna Sosai Anty Nafee kuwa sai da Tazo Gida Takejin lbri Abakin Matar ya Ali khadija Abun ko Yamata Zafi Tayi ta maganganu Wai ba"a Dauketa da Daraja ba,Shiyasa ba Wanda ya Kirata,Mama Yana na Mata mgana ko Sauraran Batayi ba Ta bar Gidan Ta koma Maiduguri,tana komawa Ta Daga Waya Ta kira Rahila Ta mata tas,ta Inda Take Shiga bata nan Take fita ba wai Sun Ware ta Suna Abu Su kadai toh da basu Gayamata Aneesa Zatayi Aure ba Sai mene,Itama Allah zai bama yarta Miji na gari,Anty Rahila na So Ta mata bayani Ammh Taki Sauraranta,takashe Wayar Ta kuma Bi bayan Kiran Taki Dagawa Abun yama Anty Rahila Ciwo sai da ta Kira Anty Yagana tana Gayamata tana Kuka Dariya Anty yagana Tayi kafin tacemata kima Share Hawayenki Domin Indai Nafee ne bata da Lissafi ki Shareta kamar ma Wannan ya Dameki nan Take Fadamata Itama ta Kirata ammh Tamata Wal,ko zarafin mgana bata samu ba,Daga Haka Anty Rahila Ta saki Ranta.

Kasim Kuwa Shiryan Shiryan Zuwa Visiting Din Aneesa Yake Wannan Satin,Babu Abunda bai Siyan mata ba na Kayan provision,Jira kawai yake Ranar Sati Yayi ya dau Hanyar Zamfara Domin Yayi kewar Aneesa Sosai,Baisan Itama tana Chan Tana Fama da Kewarsa ba,ko su B.kaita Sunga Chanji Wannan karon Domin Aneesa Ta kara Chanzawa ta kara Natsuwa,ga yawan Zama Ita kadai Wani Lokacin Sai dai Suga Tana Mirmishi Ita kadai,Sunyi Tambayan Duniyan nan Taki Gayamusu komai Sai dai Tace musu Soon Zasu ga Komai Haka Suka barta Suna Jiran Suga koma miye ya maida Aneesa Haka mai Muhimmaci ne.

Mr Bello kuwa Yana kasar Malesia,yana karatunsa baisan Halin Da"ake Ciki ba,Duk da yana Waya da Ya Muktar Da Anty Rahila Daada ma Suna mgana Lokaci Bayan Lokaci,Ammh bai Taba Tambayan Ina Aneesa ba Itama Bataba Damuwa Dashi ba Suma Ba Wanda yayi karambanin Sanar Dashi Abunda Ke Faruwa ganin ba Wani Shiri Suke Da Aneesan ba,shi kuma ko Alama domin yama manta da Wata Halitta Wai Aneesa Karatunshi ya sama Gaba Gadan Gadan ya kosa ya kamallah ya Dawo kasarsa Ta Haihu.

*wannan littafin na kudi kada ki karatamin Littafin indan baki biya ba,ki biya ki karanta cikin Salama domin Neman karin bayani ku nemeni ta wannan Nombar kamar haka 09069067488*

*Shakira...*
8/19/20, 8:02 AM - Ummi Tandama: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*Wattpad:Janafnancy13*
_Mallakar:Janafty💞_
      
*Littafina na kudi ne kibiya ki karanta cikin salama akan â‚?200,Vips â‚?400,kada ki karantamin Littafi matukar baki bayani ba..Domin neman karin bayani asameni ta wannan Nombar kamar haka 09069067488.*

*🅿�13*

"Ranar Lahadi Ta kama Ranar Visiting Dinsu Aneesa,Tun karfe 8am na Safe kasim ya kamo Hanya Saboda Zumudi Jiyama barcinshi Ragagge ne,saboda yadda ya kosa Yazo yaga Aneesa Sai dai kana naka ne Allah na nashi ya kusa Talatan Mafara Motarsa ta samu mtsala,Hankali Kasim ya Tashi Sosai ganin Lokacina Nata Tafiya Dakyar ya Karisa Cikin garin Talatan Mafaran Bayan Wani mai mashin ya Ragemai Hanya yaje suka zo da Bakanike ya Fara Duba Motar Shiko yana Gefe sai Faman Duba agogo yake Har pass 12,Hankalinsa ya Rabu Gida biyu yana chan yana Tunanin Kila Aneesa Zata ce ba zai Cika mata alkawari ba.

Itako Aneesa Tun Safe bata Fito Daga Hostel ba Tana Sanye Cikin kayan Check dinsu ,Pick clour Su S.Jibiya ne ke Waje Suna kula da Komai Tun Safe Taji kanta na Ciwo Tana Kwance,Su Ringa sun zama manya Shiysasa basa Murna In Ranar Visiting Tayi Tunda ba Zuwansu musu Ake ba anfi Zuwan ma na kasa Dasu Su da Suke Sabbin Zuwa,Tun Safe Take saka Ran Zuwan kasim Tunda ga alkawarin Daya Ijiyemata Daga gida kuwa bata san Ran Kowa ba Tunda Bello ya Tafi Sau Daya Anty Rahila da Daada Suka zo mata Visiting Wani Lokacin Sai dai Aturo mallam Inuwa da Sakon kayan provision dinta Shiyasa Bata Damu Da Wanda Zai zo Wajenta ba kasim ne kuma Tunda Taga 12 ta Wuce ta Cire rai.

Bayan Ta chanza Kaya zuwa Uniform dinsu ne Suka Tafi Masallaci sukayi sallar Azahar,Bayan Sun Dawo ne Ita da B.kaita Sukaje suka gaida Wani Uncle din S.jibiya daya zo mata Visiting Uncle yusuf sunanshi Kanin mamanta ne,Sunsanshi Domin yana yawan Zuwan mata Tunda yana aiki ne Ahukumar Inec Dake Gusai,Sun Dade Karkashin Bishiyan Dalbejiya Suna Hira bai wani Jima ba yayi musu sallama ya Tafi bayan ya basu Kayan Dayazoma da S.jibiya Dashi Wata Junior dinsu Suka Kira Tadauki Ledojin kayan Zuwa Hostel dinsu Su kuma Suka bita Abaya.

Suna Zaune Suna Bude kayan Su Uku ne bisa gadon Aneesa Murna Suke tayi ganin Harda Chaculate Din Da Suka ke kauna Dukkansu Kowa ya Dau Daya suka Bare Suna Sha Suna Zuzuta Irin Kirkin Uncle Yusuf,Aneesa dai Duk bata saki Jikinta ba Har sai da B.kaita tayi mgana.."Anee..? Wht wrong wit u..?

Kallonta Aneesa Tayi kafin tace"Me kika gani..? Kallon S.Jibiya B.kaita tayi kafin tace"U look so Silet Today ko Salma..?"Gyada kai S.jibiya Tayi kafin Tace"Nifa Tun Dawowarmu Wannan Hutun nagane Aneesa Ta kara Chanzawa plz ki Sanar damu meke Damunki.."Mirmishi Tayi kafin Ta Sauka Daga kan Gadon Tana Fadin"Allah fa bakomai bana jin Dadi ne.."Da kallon Tsausayi Suka bita kafin Su Hada baki Wajen Fadin"Ayy Sorry Bari muje Cikin makranta mu karbo miki Mgani,ina Angela Itace Health prefect.."Bata Tankansu ba Har Suka Mike Suka Fita bisa gadon B.kaita ta koma ta Kwanta tana lumshe ido.

Wajen Karfe 2pm motarshi Ta Shigo Cikin Makrantan,Kai Tsaye Gefe ya samu yayi parking ganin yadda Haraban Makrantan ya Rikice da yan Visiting Fitowa Yayi Daga Motar yana Latsa wayarsa Lokaci Daya yana kara Bin Harabar Makarantar da Kallo Cikin Nazari Wazai Tambaya,yana Wannan Tunanin Wasu yan Junior su Biyu Sukazo Wucewa Ta gabanshi Cikin karfin Hali yayi musu sallama Suka Waigo Lokaci Daya Suna amsawa.

Cikin Sanyi murya yace"Amrm Don Allah in ban Takura ku ba Wata Aneesa nakeso ku kiramin.."Doguwar Ciki ce Tace"Ok Wata Aneesan..? Kansa ya Shafa yana Tunani kafin yace"Aneesa Bukar...Something Like Dat dai..."Kallon Juna Sukayi kafin Suyi mgana Yayi Saurin Cewa"Zaku ganta Wata Doguwa Baka,baka mai Manyan Ido Haka Dai.."Da Sauri D'ayan Tace"Ok Headgirl.."Kansa ya Shafa kafin yace "I Think so....".

Juyawa Sukayi suna Fadin Bari Su mata mgana,Aneesa na kwance Suka Shigo Tana ganinsu Ta Mike Tana kallonshi Cikin Girmamawa Suka ce"Good Afternon Anty Aneesa.."Cikin Halin ko In kula tace"Afteroon How can i help u..? Tafada Tana kallonsu Domin Indai zakayi mgana Dasu Aneesa u must Speak English Juniors Kuwa Duk Wacce Ta Kuskura ta musu mgana ba Da Turanci ba,Zata gane bata da Wayau Lokaci Daya Makranta Ta Fara zama Normal ba Laifi Suna Kokarin Gwada Turanci Koda basu iya ba.

Dayar ce tace"U hv a Vistor..."Kallonsu Tayi kai Tsaye kafin tace"Vistor...? Who.."? Suka Hada Baki Wajen Fadin"We Don't know Anty.."gyada kai Tayi kafin Tace"Ok u can go Am Coming..."Daga Haka Suka Fice Daga Hostel Din,Aneesa Kuwa Ta Dade Tana mamakin Waye yazo Wajenta Wata Zuciya na gayamata kasim ne,Wata kuma na karyatata Hijabin ta Fari Ta Dauko Ta saka Bayan ta Zura Takalmin ta ta Fice.

Sukowa Suna Fitowa Daga Hostel Dinsu Aneesa Suka karisa Suka Sanar Dashi gata nan Zuwa Godiya yayi musu,kafin Su Wuce Zuwa Inda Zasu,Shiko Jikin Motar ya Jingina ya kurama Inda yaga Sun Fito Ido yana so yaga ko Ta Ina Aneesa Zata Fito koda taFito Ta Dan Tsaya sun yi mgana da Wasu yan Ajinsu suna Tambayanta su B.kaita tace suna Clinic Daganan Ta gangaro Haraban Makrantan Ta Wulga Ido Da Farko,Kasim bai ga Aneesa ba sai da Ta kariso Haraban Makranta tana Waige Waige kana ya ganta Wani Ajiyar Zuciya ya Sauke yana kallon Fuskarta Saboda yadda Ta Fadamai a Ido ganin bata ganshi bane yasa ya Fara Taku Zuwa gareta Daidai Lokacin Data Waigo Zuwa gareshi Suka Hada 4eyes balle ma yadda ya kafeta da Ido Sosai.

Wani yam Taji Tana kara Fiddo Ido Waje Tana kallonsa ganin Haka yasa ya saki Dariyan Jin Dadi Lokaci Daya ya Tsaya Cak yana kallonta bayan ya Saka Duka Hannuwansa ya Rike kugunsa Kuma yana kallonta,takowa Aneesa Tafarayi Zuwa gareshi Lokaci Daya Tana Sakin Mirmishin Jin Dadi Har Tazo gabanshi Hannu ya Budemata Alamar tamai Oyoyo Harara ta sakarmai Tana Tura karamin bakinta kafin ta Wucesa Zuwa Wajen Motarsa Kirar prado,Bayanta yabi yana Jin Wani Farinciki na Ratsashi,bakinta yake kallo yana ji kamar ya jawota ya Rumgumeta ya Tsotsi bakinta.....

Jikin motar Shima ya Jingina yana Langwabemata kai,Hararan sa Take mai Cike da Wani Salo kallonshi Take Tana Morewa Yana Sanye Cikin Wata Farar Gezer Dinkin Zamani Riga da Wando da Hula Aikin Jikin Rigan black ne,Hakama Hulan kansa Rufaffen Takalmin kafarsa ma baki Ne Shima Bakin ya Turamata yana Fadin"Ba gaisuwa wifey..?tura baki tayi kafin tace"Toh ba kai bane kaki Zuwa Tundazu ba ina ta Jiranka.." tafada a shagwabe tana wani juya ido kamar wata yarinya.

Hannayenshi ya Hada Waje Daya yana Fadin"Afuwan princess Tun Safe na Fito motata ce Ta lalace Bisa Hanya sai da na Shiga Cikin gari na Dauko Bakanike Is not my Fuilt princess.."Yafada yana Kara Narkemata,duk ya kashe mata Jiki Tana kallonsa ya kara marairaicewa yana Fadin"Kin Hakura Princess.. ? Kai Ta gyada mai Tana Mirmishi Cikin Jin Dadi yace"Thanks Wifey,I miss u much..Kwanakin da muka Dauka bama waya bana ganki na Shiga Damuwa in kun lura na Rame ko princess.?"Yafada yana Taba Wuyansa Hararan Wasa Tamai bata mai mgana ba,Shiko ya saka mata Dariya yana Fadin"Eh mana ammh ke naga kiba kika Kara kin zama yar lukuta Abunki..."Wata Hararan Ta kara makamai yayi Gefe Yana Dariya Lokaci Daya yana Fadin"Na bani ni kasim Amaryar tawa kuma Hukuncin Harara kawai zata Dinga bani in nayi mata laifi.."Wani kallo Tamai kafin tace"Waye Amaryanka din..?
Chapter 24 · 0% Book details