Sashe 7
Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
fahimci an ta a min side bag in, ina bu ewa nasamu takarda a saman anyi rubutu haka. _Zamu fidda ke daga masarautar ki tabbatar kin zuba mishi wannan gubar a cikin abin shansa baya kisa farat aya, sai ya gama cin jikin mutum_ Hannuwana biyu na aura akai na fashe da kuka, tare da cewa. "Na shiga uku na lalace." Mikewa nayi na auki jakar na sakala. Dai daita tsayuwata nayi, na shiga takawa a hankali sabida ciwona. Cikin san a na fara tafiya har na isa bakin falo, ba a kashe ba haske . Saka hannuna nayi naja kofar abin mamaki a bu e take, ina zura kaina zan fita. Naji motsi a bayana alamun an bu e kofa. A sannu na juya Sultan a tsaye sanye da kayan barci dogon wando da rigar me guntun hannu farare kwal, kallo aya zakawa kayan kasan asalin auduga ne, yana tsaye har e da hannunshi a kirji, Mujahidah ce ta fa o min a raina, gashi ya zuba min ido ni ban fita ba ban kuma shiga ba. Lokaci aya na shiga tattara inda ya bayyana a jikina, musaman kirjina ina karesu takowa ya fara, kallon shi nayi naga inda nake yake zuwa. A hankali na shiga ja da baya, jikina na rawa. Abin dariya yana zuwa ya ficce daga falon, ajiyar zuciya na sauke dole na koma naje na kwanta. Ban runtsa ba a daren sai kusan asuba. Barci ya auke ni, saukar ruwa naji a kaina na mike firgit, na zauna tafin kafana sun kumbura tam. Haka kawai nake jin na ata jikina, dan ina lissafin kwanakina na har da kusan sati aya. Kallon basamuden da ya watsa min ruwa nayi cikin raunaniyar murya nace. "Kai baka da imani ne? Idan shi ya baku umarnin zalinci sai ku aikata, yanzun daka watsa min ruwa meye ribarka?" "Eyye! Bakar fata da maganar banza a cikin masarautar larabawa." yace min. Cikin jin haushi nace. "Zaka iya sauya rubutun alkur'ani zuwa farin tawada?" Kura min ido yayi cike da mamaki bakinshi bu e yace. "Lallai zaki wayi gari a barzahu. " "Idan na wayi gari a can kai kayi gad..." Dake aga muryana nake, kusan masu kula da lafiyar Sultan sunji mu. Kafin na karasa sun shigo amadadin su tambayi ba asi. Sai suka shiga zane ni. Da gayya na fara ihu. Yana can akin hutawarshi yaji hayaniya dan sun daina dukana kokari suke nayi shiru, sai ga Amir Ukshe tare da d'anshi Marhum da kuma Amir Abu Zarri. Tare da Wata mace sun shigo gidan, jin hayaniyanmu yasasu leko kitchen in. Cikin kasa kasa da murya Amir Ukshe ya rufesu da fa a, har ya dakatar dasu. Ni kuma aka kira likitan masarautar da nurse suka zo aka duba kafana sai da suka min dress sabida akwai kwala Ana gama min, nurse ts rike ni muka koma can shashin bayi, ranar da muka ga juna munci kuka babu Zakiya. Kwana goma nayi ina jinyar kafar a lokaci kuwa Azrah tazo yakai sau goma akan lallai ina warkewa na koma bakin aikina dan sabida jinyata gashi karen da Sultan e kiyo ya mutu, dan kwana uku ana kai mishi abinci yana kin ci har dai ranar da yunwa ta buwaye shi, ana kai mishi abincin yafarwa mutane garin a san yadda za'ayi dashi ya zarge kanshi, a take ya sheka. Nayi Imani da Allah sai Sultan ya azabtar dani akan haka. Ina zaune na buga tagumi dare yayi su Hindu sun tafi gun rawansu. Dauke wuta kwan akinmu yayi, jakata na shiga lalluba zan kuna torch in wayar da aka saka min naji karan bu e kofa. D'ago kaina nayi dan har waje baka ganin haske sai duhu. Komawa nayi da baya na hantsila kasan gadonmu cikin sauri na shige kasar gadon.