← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 65

Sashe 4

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi, muka wucce, kwalla ne ya shiga saukowa a idanuna, tare da tarin dana sanin mara amfanin da nakeyi tun bamu isa cikin ba. Falon farko babba ne na fitar hankali, ga ka an alfarma a cikinsu. Sannan muka ratsa falon dan mun samu da mutane suna zaune babu wani hayaniya ko magana asalima zaman hutawa suke. Haka muka wucce su babu wanda ya dago ya kallemu, balle kasa ran zasu mana magana, wani dogon korido mai tsayi shima tafiyar minti goma zakayi ya kaika kofar falo na biyu. Muna zuwa aka bu e mana kofa, muka shiga ciki mun sami mutane biyu a zaune kowannensu da abinda yake yi, sannan muka wucce, inda mukayi tafiyar minti ashirin da aya, sannan muka nufi wani tafkeken falon me cike da abubuwan burgewa, irinta gidan sarauta. Babu kowa a falon sai tv da yake aiki. Tsayawa yayi a gun sannan ya kalle ni tare da mika min, takarda yace. "Idan Allah ya nufa zamu sake saduwa toh sunana Sheik, zaki iya tsayuwan jira har lokacin da ya fito sai kisan yadda zaki bashi takardan domin yasan da cewa kece bakuwar da zaki fara girka mishi abinci sannan kiyi takan tsantsar da aikinki domin nan ba'a san kuskure ba kina yin abu ka an zaki ji a jikinki." Yana gama fa ar haka ya juya ya tafi, abinshi. Jingina nayi da bango ina kallon Inda Allah ya kawo ni. Bayan wasu mintoti, na gaji da tsayuwa na zame na zauna, na cigaba da tsammanin fitowar sultan, shiru kake ji. Awa aya ya wucce wasu awowin suka wucce bai fito ba. Can da naga har lokacin sallah yayi bai fito ba, sai na juya na fita niman inda zanyi alola da sallah. Karshe dai sai da na dawo shashin bayi nayi sallah sannan na koma. Ashe ina fita shima yana fitowa, ganin takarda asaman kujeran falon yasashi sanin an shigo falon yana ciki bai bi takai ba yayi ficcewarsa, zuwa masalaci. Koda ya dawo a falon farko ya tsaya sabida mutanen da suka zo masa dubayya, da kuma mishi Jajjen ya jiki. Suma dai matasane sa'aninshi kuma yan Kabilarsa na Banu Hashim, daga cikinsu kuwa har da Jikan Amir Ukshe. A hankali nake takowa sabida ba'a son karar takalmina ko sautin da zai dame mazauna gidan. Da sallama na tura kofar na shiga duk sunji sallamar amma babu wanda yayi yunkurin amsa min, asalima kamar basa gun kare musu kallo nayi anan na fahimci dukkansu yan bana bakwai ne. Abinda yasani cewa haka kuwa ba kome bane sai dan luran da nayi dan akala bazasu wucce 28-29 ba, domin babu wanda ya haura talatin. Ta e bakina nayi na wucce, Har inda aka kaini, tsayuwa na cigaba dayi, wasa wasa banga idanun sarki ba sai bayan sallar la'asar, na gaji da zama na mike zan koma can shashin bayi, ina rike handle kofar zan fita shima ya rike zai shigo. Bazata muka bu e kofar tare, har sai da kaina yayi karo da kirjinshi. Da sauri nayi baya ina zare idanu, bai tsaya bin takaina ba yayi wuccewarshi, bin bayanshi nayi da ido tare da dafe goshina nace. "Wayo ni Safinatu! Toh waye sarkin ne? Toh ko wannan ne? Amma ai lokacin zuwanmu baya falon mutane hu u muka wuce a falon farko, na biyu kuma mutane biyu ne, ai ko shine Sultan Ashraf in?" Ni ka ai nayita lissafin can nace. "Toh kenan sarkinsu yarone, ta dole yayi abinda ya gadama," Tsaki nayi cike da takaici. "Mugu azzalumi sai da ya atawa Mujahida rayuwa dan sun auki mulki sun bashi, Allah ya is...." Ganin fitarshi nayi da sauri nabi bayanshi ina cewa. "Ji mana! Don Allah zoka min iso da Sultan Ashraf." Nayi haka ne dan na cire tantamar dake raina, ko kallo ban ishe isheshi ba, sai ma masu tsaron lafiyarshi da suka tare ni suka kaini wani dakin duhu. Me kula da bakin kofar akin ya shiga yayita zane ni. Har sai da nayi laushi, wanda yaja har na suma, sannan suka watsa min ruwan kankara, a firgice na farka sabida azaba ko kuka ban samu damar yi ba,, cikin kakkausar mutumin yace. "Daga yau ko tsuntsu kika ga zaiyi kuka wanda zaisaka Sultan cikin damuwa ke zaki kora mishi,, sannan ki tashi kije kiyi aikin da aka kawo ki yi, Sannan sultan baya son hayaniya koda kuwa ta fashewar abune toh zaki ji a jikinki" Jawo yayi ya watsa a waje tankar kayan wanki. Dakyar na mike zuciyata na min zafi, lura da nayi dare yayi sosai yasani niman hanyar can shashinmu. Koda naje bu e kofar falon na biyu najishi a rufe dole na dawo falon Sultan, abin bakin ciki koda na shima nasa a rufe karshe sulalewa nayi na zauna, na fashe da kuka. "Wani tsautsayine ya raboni da gatana nazo nan ana wasan kura dani." abinda nace knn ina kuka. *** "Yalla ai Alexandra mun mun sami labarin an sami wata Yar african da." "Benjem kaje kasan meye ya kawo Yar african masarautar jordan." Daga haka yayi shigewarsa ciki dan yayi imani da abinda bokanshi ya gaya mishi. *** Fitowa yayi zai tafi masalaci ya ganni a zaune na cusa kaina cikin cinyoyina, kauda kanshi yayi ya bar gun. Saukar bulala naji yasani mikewa zubur ina sosawa ciki mutumin ya nuna min na shiga, yana bina har kitchen ya nuna min, sannan ya nuna min bango inda aka kafa wata yar allo da aka saka jerin sunayen abincin da za'a girka...... #MD.....Follow me: Mai_Dambu Oum Muwadda... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITER'S ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* Page. Wato akin da aka kaini yafi kowanne axaba, dan yadda kasan gidan bread haka cikin akin yake , ga hayakin tire gas, nasha mugun wuya kafin suka fiddani. A kitchen suka watsar dani zan iya cewa ban ta a cin azaba irinta yau ba nasan mutane zasu so jin taya akayi na bar iyayena nazo nan ake wula antani ka an daga cikin tarihina. Safinat Badr Kyari shine ci akken sunana. Mahaifina ya fito daga kabilar Kanuri ne daga kasar Nigeria. Mahaifiyata kuwa Shuwa arba ce dan ko hausa bana ji sosai sai turanci da shuwa sai larabci. Nice Babba a gidanmu ina da shekaru 32 sai, kanina Abdullahi wanda yake tsa anin 28/29 Yana da mata har da yara biyu sai Nanah Asma'u wacce take da shekaru 25 tana da aure da yaro aya na batarta da tsohon ciki. Sai. Sai Fatima tana da shekaru 21. Kafin an autanmu Khalil yana da shekaru 17 bana ya gama scndry. Mahaifinmu nada mata biyu har da Umminmu uku kenan Hajiya Amnah babarbariya ce daga Bama, tana da Yara hu Maryam suna kiranta da k'iose Tana da shekaru 25 sa'a Nana Asma'u ce. Sai Kaltume tana da shekaru sha tara, sai Sa'ar Khalil dan rana aya suka haihu da Ummi ana kiran yarinyar da Khalilah, Hajiya Amnah muna kiranta da Umma. Sai Hajiya Nuratu fitinanniyar gidanmu kenan, Matar tasaka ni a gaba sosai musaman da taga Nannah ta janye ni ta kuma nuna musu tafi sona sama da kowani yaro a gidan, Hajiya Nuratu wacce muke kiranta da Ammin tana da yara maza babban anta sa'an Fatima ne yana da kusan ashirin yana jami'a shi dasu fatima, sunanshi Abba lawan, sai Salamn shima sa'ansu Khalil ne, sai Ruwaidah tana da shekara goma sha uku, da an karaminmu Anas. Mu goma sha biyu ne cif a gidanmu, Abbanmu haifaffen garin Amman ne nakasar jordan, sabida Mahaifin Ibrahim yayi aiki a karkashin , Sultan Yasir tun kafin ya zama sarkin jordan kasancewarshi na likitar har zuwa lokacin aka kifar da mulkin sultan Yasir, ya tattaro ya dawo maiduguri. Daga baya masarautar ta nemi ya koma bakin aikinshi yaki. A lokacin Abbanmu yana aiki a babban asibitin maiduguri ya auri Umminmu. Da Kakanmu yaga ya dan manyanta sai ya tura Abbana Masarautar jordan. Ya tawo da ummi ya cigaba da kula da sarki Abdullah har aka haifeni, a lokacin Sarki Abdullah ya auri Nana Asma'u daga Masarautar Oman. Tazo tasamu ina da shekara biyu, zuwanta yasa abubuwa suka fara faruwa, ganin haka muka dawo gida ni da Ummi. Sai dai duk bayan wata shida Abba yana zuwa mana. Ina da kusan shekaru bakwai Abbanmu ya dawo shi da Nannah inda tazo tayita jinyar zuciyarta sabida rabata da sukayi da d'anta. Wanda suke sa'anin da Abdullah dan shekarun Abdullah uku. Taso jan Abdul yana ibe mata kewar D'anta wanda bata kiran sunanshi. Sai Abdul yaki. Karshe nice taja, ni kuwa a lokacin da mugun son jiki tunda ta fara jana a jiki na sake zama sakaltacciya. Abba ya ya hajiya Amnah, wacce tana zuwa taga Nannah aikuwa hankalinta ya tashi, dukda Abba yana aiki amma albashin baya kai mishi yadda ya dace, ga fitinar Hajiya Amnah akan sai Abba ya kori Nannah yaki shine tayi fushi har da daka yajinta. Lokacin kuwa Allah ya saukarwa Abba wani iftila'i domin kuwa an koreshi a gun aiki ganin abinda zamu ci zai fi karfinshi Nannah ta kirashi mika mishi jakar da aka bata a masarautar jordan tayi, tace. "Badar! Bazan iya biyan abinda kai min ba, dan ka auko ni daga kasar jordan har nan kasarku, ka kuma auki nauyin cina da sha, kana awainiya dani, dukda kaki fa a min an koreka a gun aiki ga awainiyar Iyali gana yaranka ka auki wannan dukiyar dan ni bansan me zanyi dashi ba, sun bani a matsayin sayan 'ana sukayi, ina tsoron abinda ya faru a kan sarakunan baya ya komo kansh." Muryanta ne ya shiga rawa alamun kuka zatayi fitowa nayi daga akin naje kusada ita na aura, kaina akan kafa arta cikin larabcin da take koya min nace.. "Nannah kiyi hakuri, idan na girma zan kawo miki d'anki nan kinji, kiyi addu'a na zama babba kinga sai kome yazo min da sauku." Tunda tabawa Abbanmu ku in Allah yasanya mishi albarka, sai ma wani irin bunkasa dukiyar yake, dan kasuwanci yake daga dubai, lokaci yaja sosai dan har na gama primary schl zan shiga scndry a lokacin Nannah ta fara bani labarin, masarautar jordan. Dan bani mantawa na ta a ce mata. "Nannah taya zan shiga masarautar
Chapter 4 · 0% Book details