← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 65

Sashe 5

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

har na dauko miki shi?" Dariya tayi sannan tace. "Ke ba kamar sauran mutane bane kuma idan aka san zuwa kikayi zaki tafi dashi kashe ki zasuyi, ina son ganinki zama tankar sarauniya ki bar tunanin wancan duniyar." Tura baki nayi cikin kunkuni nace. "Nannah! Ni ki gaya min taya zan shig." "Safinat! Masarautar babu tausayi ko imani, dai dai da kwalba idan kika fasa, hukuncine, sai kin wucce get hu u da masu tsaronsu kimanin mutane ari uku, sannan ki isa cikin gidan bayan kin wucce dogon baranda kafin ki isa falon farko, wanda yake auke da karti majiya karfu mutane goma suna tsaron falon farko, ki shige tacikin falon kije falo na biyu inda zaki samu. Wasu masu tsaro har mutane ashirin. Sannan ki yi tafiyar minti arba'in da zai kaiki cikin inda Sultan Ashraf yake. Taya zaki shiga? Wani hatsari zaki fuskanta na matsayinki na Y'a mace? Shin zai yarda ya biyo ki? Idan mugayen da suke tare da shi zasu barki ki fito musu da shugabansu? Idan suka san kudirinki na sace musu shugabansu me kike tunanin zasuyi don Allah ki rufa min asiri karki saka haka a ranki kinji yarinyar kirki." "Amma Nannah ina ganin fit .." Rufe min bakina tayi cikin damuwa tace. "Ina gudun fa a miki kome mutanen suna da nuna kabilanci musaman ke da kike da duhun fata. Suna kyamar bakaken fata." Shiru nayi dan a lokacin banfi shekara goma sha biyu ba. Aukin tambayar tsiya. Bunkasar da Abba yayi ne ya tattaramu muka koma abuja da kasuwancinsa dan yafi karfi tacan da lagos. Bayan na gama scndry naki karatu a jami'ar kasan nan, rimi rimi akayi min kome a medicine inda aka kaini Ghana, ina zuwa can na koma Mass com, inda na shiga karatun babu wanda yasani a gida sai da nayi shekara aya nazo hutu. Suka sani ranar nasha fa a a gun Abba, ganin fa an yaki karewa Nannah tafito tasa baki take Abba ya hakura, amma ya ji bada Wannan dalilin yasa Hajiya Nuratu take kara jin tsanata. Musaman da yanzun kome Abba zai yi sai yaji tabakina. Har na koma. A sannu gidanmu ya fara cika, kafin na gama jami'a gidan an cika ba laifu. Shekaru biyar na dawo daga Ghana, naje bautar kasa a Imo. Ina gamawa nasamu aiki da gidan radio na kasa dake Kaduna, Amma Nannah taki dole aka dawo dani Abuja, dukda shakuwar da mukayi da Nannah baisa idan nayi laifi ta aga min kafa ba, fa a take min sosai. Lokaci ya tafi dan bayan na fara aiki na koma makaranta nayi degree na biyu, abin mamak shine na koma kamar me cutar junnu dan bana kaunar maganar aure, kuma lafiyata lau, ganin haka ya aga hankalin Iyayena. Murmushi nannah take kawai idan taga sun sani a gaba suna min fa a, bata hanasu dan nima da nawa shegantakan, cikin ruwan sanyi manema suke zuwa min karshe basa kwana biyu na koresu, fata fata kuwa. Ni a tunanina idan nace zanyi aure waye zai cikawa Nannah burinta shiyasa naki auren kowa, tunda nasa a raina zan dawo mata da anta na kuma ji na gani. Na taso da wannan burin a raina ko iyayena basu san da shi ba hatta itama Nannah bata sani ba dan tabar min maganar, ni kuwa tausayinta yasani kudirawa a raina sai na dawo mata da anta. Bayan shekara biyu da rabi na gama degree na, na biyu. Wanda yayi dai dai da ha uwana da Anim. Sabon shugaba gidan radionmu, da wasa muka fara sama sama, sai gashi mun kulla soyayya, wanda yaje har gaban iyayenmu. Aka tsayar da magana maganar aure a tsakaninmu, tunda naga haka hankalina ya tashi. Karshe na nemi Aliee dan kasan jordan ne na zaunen syria ne, mun ha u dashi a ghana ne yaje wani course. Nan nima n kirkiro tafiya course in shekara guda. Dakyar a a d'aga bikinmu, dan ma Anim yana da mata har da yara biyar. Kuma dan bokone sosai irin mutanen nan masu akidar boko, dan haka ban sha wuyar shawo kanshi ba ya amince aka. Kwana uku tsakani na wucce jordan. Sau uku ina niman aiki a cikin masarautar suna hanani, karshe sai Aliee ne ya fa a min basu bani aiki ba dole sai nazo a matsayin baiwa, banso haka ba. Amma babu yadda na iya idan na tuna yadda a gidanmu, dukda an aurar da anena haka bai ta a damuna ba Ammi tayi min gori har dasu habaici baisa na damu ba, a yanzun nayi na damar tsallake auren Anim da nayi gashi ba biyan bukata, tunda nazo a baiwa dole naga tasku. Da gatana nazo ana wulakantani dan ko Aliee ban fa a mishi abinda ya kawo ni ba. *** Ajiyar zuciyar na sauke, tare da goge kwallana. Dakyar na mike na shiga jan jikina zuwa ban akin na watsa ruwan zafi me mugun zafi, sannan na fito na maida kayana. Abinci Samin ya ajiye min na auka naci. Cikin jimami yace min. "Me yasa kike da taurin kaine? Ki bar katsalandan a cikin masarautar nan." "Samin kenan aiko mutuwa zanyi sai na fa awa Sultan gaskiya, mulkin zalunci akeyi a wannan masarautar da cin zalin." "Zaki sha wahala!" "Kasan wahala ita shirya masa ake ba" "Kinsan yarone bai da hankali a matsayinki na babba ya kamata kija girmanki, ki kiyayye doka." "Ni zan fa a maka Ashraf yarone tunda. Ganinshi mukayi akanmu, kamar bai ji me muke cewa ba, ya shiga kitchen in ya auki abinda zai auka yafita, yau babu mulkin babu bada oda toh ina ma yake magana, kullum fuskar nan a ninnike, sai kace wanda aka aiko masa da sakon mutuwa. Ina jin Samin ya gma abinda zai yi, bayan ya min sai da safe. Ni kuma na baza hakarkarina a gurin...... Insha Allah ina kaiwa page 10 zan ajiye typing.... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITER'S ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_ _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* Page. Time table in na duba naga jerin abincin kamar haka. Break Fast:+ Roasted nut & Bedouin tea Lunch:+ Kunafa & Zarb tea & fatter. Dinner:+ Mansaf & Shawarma &Fresh Juice. Na yau kenan, abinda na fara kayan ha in na nima musaman na karyawan safiya. Wanda nagani a cikin store abinda na fara shine niman wasu bread masu zubin gurasa, na ha a kayan ha i kasancewa ana ha a roasted nut da y'ay'an cashew ko gya a, kuma naga haka na ha a dukda bani da tabbacin zai ci, bushashen ganyen shayi na bedouin na ha a da minannas da citta da kanunfari na dafa. Kamar yadda naga Nannah tana dafawa idan ina gida. Kafin karfe shida na gama sannan na gabatar da sallah a kitchin in nayi har da alola dan kitchen in har da bayi a ciki. Ina idarwa na shiga juye abincin a manyan warmer, ina fita dasu falo inda aka tanadar da dinner table. Ina gamawa na koma kitchen in na wanke kayan da na ata sannan na goge ko ina nafito dan kome na kitchen in black & whiter ne. D'an jimawa da nayi a kitchen in na fito, ganin masu tsaron lafiyarshi a gaban table in abincin sun zagaye abunci. Juyawa nayi zan koma rigana ya kama wani flower kafin na tare ya fa u kasa, fassss ya bada sauti sai da gidan ya auka. A fusace sukayo kaina jikina ne ya auki rawa, kafin nasan abinyi sun rufe ni da bulala, sai da suka min tiliss sannan suka sani tattara kwala en, na zuba a kwandon shara. Sake sani a gaba sukayi har gaban abincin cikinsu ya sunkuyo da kanshi dai dai fuskana yace. "Ki iba kici." Kwallar ke zuba a idanuna ga zazza in da yake cin jikina na dukar jiya, ga kuma na yau a hankali na kai hannuna na bu e warmer na shiga iban abincin na ci sai ruwan bedouin tea nasha, da kuma normal ruwan kwalba nasha, ina gamawa suka tattara abinci aka fita dashi. Can sai gasu sun dawo suka zuba kwanika, babban ya kuma sunkuyar da kanshi yace. "Girkin yayi kyau, amma Sultan bazai ci abincinki ba kasancewarki bakar fata dan haka zaki zauna a nan kina dafawa karanunkan da kuliyoyinsa abinci sai gyaran gidan kece zakiyi tayu za'a kawo wanda zai na girka mishi nasa abinci naki girkin dabobine." "Ta ijam wa mage da kare zan zauna ina girka musu abinci" Abinda nake fa a knn a raina, bansan sun bar gun ba, sai da na ago naga duk sun bar falon. Wato haka kogin kaddara ta kwasoni zuwa bakin ga ar da bani da hanyar gottawa. Koda na maida kwanikan kitchen zama nayi na fashe da kuka dan duk jikina ciwo suke min ga wani zafin azabar da shatin bulalar yake min. Duba agogon kitchen in nayi naga takwas har da rabi, da sauri na fito na duba Machine in shara na shiga share ko ina, na falon. Ban gama sharewa ba sai karfe goma tsabar girman falon. Sannan na shiga goge gidan tsaf na gama, wani show glass na hango cike da turaruka, tsautsayi ya ja ni zuwa gun. Wai nasaka a falon, ina zuwa zan bu e naga hangoshi sanye da kayan sport wando da rigar ta kamfanin R&B. Hannunshi rike da goran ruwa, sai zufa yake gogewa. Bansan ya akayi ba jikina ya kama rawa ba kafin dai san abinyi nasha wani kwalba ya fa o, tasss ya bada sauti. Feener kin cika shishigi ina ruwanki ki tsaya inda aka ajiyeki mana) Wallahi kaman a kunnen kartin nan fasa kwalbar sai gasu sun shigo kallona sukayi, nima kuwa na tsura musu ido dan har na fara kwalla. Basu duke ni ba sai dai sun sani kwashe kwalbar turaren sannan suka fita dani, aka kaini d'akin sanyi. Suka wurgani. Sai da nayi minti talatin sannan suka fito dani bana numfashi. Ruwan zafi suka watsa min har sau biyu. Kaii Jama'a bawa baida yanci kuskure ka an zakayi kaji ajikinka. Dakyar na farka suka sani a gaba har shashinmu na sake sauya kayana, babu yan matan nan kuka nake ina dana sanin zuwa na masarautar jordan, dole Ashraf yayi mugunta yaro karami ne fa,
Chapter 5 · 0% Book details