← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 65

Sashe 47

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Shiru wanda aka kira Iqibal yayi sannan yace.
"Kawu taya za a lalata sihirin?"
"Allah zai kawo yadda za a warware."
***
Duba agogon Hannunshi yayi ya ga lokacin na kure mishi da sauri ya fita, ya kalle Dudu.
"Kyari bari naje Villa na dawo, daga nan zan wucce gidan gun Ammahna ko zata taimaka tazo taga halin da Safinatu take ciki."
G
a musu kai yayi.
........
Tafiya yake da mugun gudu, taka birki yayi a tsorace ya fito sakamakon mahaukaciyar da ta shige gabanshi.
Tana dariya sosai tace.
"Ka koma bazaka ga Shugaban kasa ba, kaje mayanka acan aka tsuma yar tsanar."
Kaucewa ya
i ya barta tana ta , haukarta. San baya tunanin maganarta gaskiya ne,
Kiranshi shugaban kasa yayi ya gaya mishi, zai shiga meeting.
Bai damu ba ya koma gidanu, yana shiga, katon Mansion
insu ma aikata suka shiga gaida shi, bai bi takansu bai yi ba.
Ya shiga gidan a gigice yana kwala mata kira..
"Ammahna!!!"

Wata farar dattijuwa ce ta fito hannunta rikeda farin casbi. D'aya hannunta rike da sanda, murmushi tayi ciki dattako tace.
"Son! Lafiya!"
"Ammahna! Tana cikin wani hali."
Murmushi takara a karo na biyu tace.
"Safinatu ko?"
Gyada kanshi yayi, addu'o'i ta bashi sannan tace.
"Kaje
akin akwai Shafin shai
anu ka
auko a shafa mata shima yana taimakawa."
Ta kuma gaya mishi yadda zasu kula dani,
***
Cikin kwana biyu rak na koma abar tausayi, dukda ana addu'a. Da maganin gida, karshe dai aka dawo dani gida. Inda na cigaba jinya.
Ganin yadda nake wari ya
agawa kowa hankali, musaman Dr.
......... Ya gama duba wata mara lafiya ya dawo
akin ya kwantar da kanshi akan kujera, wani barci me mugun karfi ya
i gaba dashi.
"Tun ranar da ciwon ya faru muka ce maka kaje mayanka, ka duba inda jini ke zuba zaka samu anan suka lankaya yar tsanan amma kayi biris sabida mahaukaciya ce, toh maza ka
auki
an uwanta kuje can Insha Allah rabb zaku ga waraka."
Firgit yayi tare da mikewa, ya fita daga
akin, ofishinsu Dudu ya nufa, yana zuwa yace.
"Kyari zo muje."
....... Da sauri suka fita, a mota
aya, suna barin garin abuja motarsu na lalacewa, dole suka ajiye motar suka sake niman shatar taxi.
Nan ma dai sai da suka fara tafiya, sannan motar itama ta lalace. Dakyar da ikon Allah suka isa mayankar, nan ma sun sha wuya kafin su
a, sami yar babyn, suka fidda shi, ba tare da wata wata ba. Suka xuba mata fetir tare da wurga mata ashana dan akwai wasu mahauta a gurin.
Suna gamawa suka jiyo abinsu.
***
e idanuna nayi a gajiye. Na kalle Ummi da take rike da casbi.
A hankali nace.
"Ummina! Ina yarana?"
"Alhamdulillah! Safinatu, sannu bari na kawo miki su."
Dauko min yaran tayi ta sakaminsu kusadani, sannan tafita can sai gata ta dawo
auke da magani.
Tallafe ni tayi taban nasha, kiran Abdul tayi ta gaya mishi, sai gasu tare da Dr.
Wanka Ummi tayi min sannan na fito nasa kayana, zama nayi, a
akin sabida bani da karfi.
***
"Hmm! Bansan yadda aka
i suka sami makarin ba, amma tabbas ta sami lafiya sosai. Dan yanzun na dubata sai cin abinci take"
Tsawa ya buga mata, tare da cewa.
"Bashi na tambayeki ba, taya kome yake lalacewa? Sannan waye yake kareta?"
A gigice Mamie tace.
"Yalla
ai!Allah mana. Don Allah ka kyaleni karka sakani a damuwa."
Kashe kiran yayi tabi wayar da kallo kamar doluwa.
***
*SAUDI*
Zama ya
i ya
aura
aya akan
aya, hannunshi duk biyu ya jinginasu akan kujeran,
ame bakinshi yayi ba
an lauyan ya gama masa bayani.
Lumshe idanunshi yayi, sannan yace.
"Ya yarana suke?"
"Ai yalla
ai! Duk lafiyansu lau dama Asma'uHusna ce Uwar ta kwanta akanta, Amma jikinta da sauki"
Bu
e idanunshi yayi, sannan yace.
"Da fatan babu matsala!"
"Eh toh babu kenan amma Fahad ya tabbatar min Uwar yaran ba lafiya."
Gya
a kanshi yayi sannan yace.
"Meke faruwa A jordan?"

"Gaskiya Yalla
ai iyakata Nigeria ka bani damar na tura wasu, Wallahi bani da masaniya da abinda ke faru."
"Yayi kyau."
Yana gama fa
ar haka ya mike, tare da barin
akin ziyaran
a koma cikin gidan.
***
*Jordan*
Alamura sun tsananta sosai, dan har takai ana nunawa juna yatsa tsakanin Ukshe da Abu. Dakyar Ammar da Uzaif suka shawo kansu.
Shi Abu Zarri yace bazai bi shugabanci Ukshe ba dan babu Allah a cikin mulkinsa. Shima kuna Ukshe yace bazai bi Abu Zarri ba, kafin lokaci kalilan sun hautsinawa juna lissafi dan kamar zasu kashe junan,
Ana haka Marhum ya shigo naaarautar domin farautar duk wanda yaje cewa shi zai zama sarki, da du
me hannu a kamashi sai da ya kashe manyan cikin masarautar har mutane biyar.
A sannu zubda jini yazama abin ado a cikin Birnin Amman, domin an samu rabuwar kai wasu nacewa A baiwa Ukshe wasu na cewa Abu Zarri.
Ga kuma Marhum da yake kokarin ganin bayan kowa ya amshe mulkin.
***
Zaune muke ya sani a gaba, sai kunnani yake da tsokana naki kula shi.
"Insha Allah! Idan na kama mutum sai na cinye bakin tsiwar nan, wanda yake kin magana."
Dago idanuna nayi cikin nutsuwa nace.
"Amma baka da lafiya".
Chapter 47 · 0% Book details