← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 65

Sashe 41

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita in dadironkace, ko abar kaunarka ce? Gata nan da cikin jikinta na shayar da ita madaran jikina ko karya ce na miki? Da kanta tazo gurina muka tsallaka tsakiyar taku da ita har na wata gud.." "Azzalumin macuci Allah sai ya gwada maka iyakarka, wallahi babu abinda ya ta a ha ani da shi, Wallahi ni ba fajira bace" na fa a cikin kuka, "Toh cikin da kika haifa taya kika same su?" Dafe goshina nayi dan tsakanin da Allah Anim yake son lalata min farin cikina, a yanzun da nake kokarin tattara d'an kuzarin da na rasa shine bari ya lalata min su, ban tsammaci jin magana me kyau daga bakin Dr ba sai da ya doki dodon kunnena. "Malam! Idan na fahimta kana yin haka ne dan taki amincewa da kai ? Ni a tunani na idan kana son mace kuma ka ganta a gidan karuwai, babu abinda ya dameka aukota zakayi ka aureta, sai gashi kaddara da rabo sunsa kana cutar da zuciyarta da ruhinta, kuma kana kiran haka da *SO* bayan babu wani masoyin gaskiyan da zai so cutar da abokiyar soyayyarsa, zan fa a maka wani abu guda ba a haka zaka nuna soyayyarka ba, dan kana kusantata da acin rai yana rage kima a idanunta." Tsaki yayi zai magana, sai gashi ya fita. A zafaffe Dr ya juya gareni tare da tsare ni da mayun idanunshi masu, matukar karfi da haiba. "Taya kika same su? Iya gaskiyar da kika fa a shi zai bani damar dakatar dashi." D'ago kaina nayi na zuba masa ido, a sannu nayi kasa da kaina. Sannan na fara basu labari dan bashi ka ai bane a akin har da Umma da kuma Abbanmu wanda ya kira Abdul ya kawo shi. Da nazo inda kaddaran cikin yaran kasa fa a musu kome nayi, kuka na sake me ta a zuciya da ruhin me sauraranshi, sai da nayi ya ishe ni sannan na ago kaina na cigaba da cewa. "Sam baya cikin hankalinshi, dan sun masa sihiri da ya samu ta en hankali, nasan waye Ashraf dan na zauna dashi kafin faruwa alamarin bai taba kallona cikakke na sec, balle na mint. Mutum ne da ya kame kanshi daga masha'a da ace zai min haka da tuntuni yayi min, amma haka ya tsare kanshi har na shiga rayuwarshi." ago kaina nayi na kalle Abba, tare da girgiza kaina nace. "Abbana! Nasan dalilinka na korata dan zan zubar maka da kimarka, wallahi ko da wasa ban taba barin wani ya ta a kimarka ba, da sona ne yaran nan bazasu kasance a raye ba, amma sun zame min kaddara wanda bazan i a kankaresu ba, don Allah ka kira Nannah ta aukesu zan zauna da kai kuma zan maka biyayya." Kura min ido yayi cikin zubda hawaye yace. "A'a ki shayar da yaranki!" Girgiza kaina nayi cikin kuka nace. "A'a Abbana! Ta tafi dasu kawai tunda suna da gatansu, kuma bugu da kari kabilar larabawa basu cika baiwa Yaro nonon mahaifiyarshi ba, dan sukan aukesu zuwa gun reno." Duk yadda suka so na amince da yaran fir naki, abin ya basu mamaki, haka suka watse zuciyarsu ba da i. Ni kuma dalilina nakin yaran ba kome bane yaja haka sai dan karsu fuskanci matsala. A rayuwarsu kuma bana son shakuwa ya shiga tsakaninmu yadda rabasu dani zai zama matsala. *** Washi gari aka kuma tashi akan batu aya, nima kuma na kafe akan ra'ayina, da aka kawo abin karyawa har da kunun tsamiya, aikuwa nasha sosai, bayan awa guda nonuwana suka cika sosai. Har ya kai dakyar nake d'aga hannuna, sabida cikarsu na kuma yi shiru. Dan kar ace na bawa yaran nono. Shigowar Dr yasa aka kawo min yaran, ina tura bakina ina kunkuni haka na basu suka sha har suka koshi, kallon Umma nayi cikin mamaki nace. "Ummanmu! Yaran nan da shegen wayo suke dubi yadda suke shan nono kamar wasu mayunwat..." Maganar tamakale min ne sakamakon shigowar Nannah da wasu tawagar mata da maza, har da Ghaniyu kamar na watsar da yaran nace. "Akhee Ghaniyu!" Murmushi yayi cikin girmamawa yace. "Amirah Safinatu, sannu uwar gimbiyoyin Jordan, Ina mika gaisuwata ga Sarauniyar gobe a birnin Amman, Umarninki nake jira Sarauniyata." Duk sai naji wani iri lokaci guda wani irin girma da dauk'ak'a sun hau kaina lokaci guda, haka tawaga Nannah suka shiga mika min gaisuwa, wasu mata suka zo gun yaran suka fara dubasu, abinda bamu ta a lura dashi ba kodan ba a gun mu suke ba, tsakanin kirjinsu zuwa bayansu akwai wani abu kamar tasiwera(Map) wanda ya kara tabbatar musu yaran nasune, take suka shiga ambatar barakallah. Cikin murmushi nan ta kalle wata dattijuwa tace. "Amirah Humaidah na gaya miki binti bazata ta a min karya ba, kinga shaidar toh haka ma Ashraf shima akwai tasweran masarautarsu a jikinsa." Ni dai ido nake binsu dashi nan suka shiga godiya da kuma ban hakuri ga Umma, fita sukayi da yaran. Nace "Allah yasa su tafi dasu nima na huta." Make min bakina Umma tayi, dake sun fita. B'are musu baki nayi tare da sake kukan sa alci kamar karamar yarinya nace. "Allah bana son yaran! Gwara su tafi dasu." Shafa sajenshi Dr yayi cikin murmushi, yace. "Kina fama da yaranta! Babu wanda ya isa rabaki da yaranki." Galla mishi harara nai tare da murguda mishi baki, nace. "Ai kana da nono ka bas.." Sake buge min bakina Umma tayi, cike da takaici tace. "Amma baki da mutunci Yakolo, rashin kunyarki ya shahara, kuma ki fita idanuna." Kuka nake har da majina, *** A gidanmu kuwa, cikin girmamawa Ummi ta amshi bakin dan tasan da zuwarsu, hidima sosai a a musu, dan har Sophia da Nanah Asma'u suka ha u akayi musu abubuwan tar a. Nannah tana gaya musu irin rikonda aka mata, godiya sosai sukayi. Sannan suka bawa Ummi da Abba hakuri da kuma irin abinda ya faru. Murmushi Ummi tayi dan haka kunya ya hana shi magana. "Babu kome jarabtace kuma babu wanda ya isa kaucewa kaddaranshi, Allah yasanyawa rayuwarsu albarka." Sunji mugun da i, tare da godiya. Sannan sukayita godiya, tare da alkhairori masu yawa, sannan Nannah ta gabatar da Nurse in da zata kula da yaran har da ita kanta. Kyauta masu daraja suka bawa yaran dani kaina, wasu manyan akwatina glass aka kawo suka ajiye a gaban Ummi sannan suka bu e nan aka ciro wasu kambu, na yaran wanda akayi su da farin zinari wato (Whiter gold) sannan aka bisu da wasu beart na diamond(Lu'ulu'u) Mikawa Abba Yarinyar farko Nannah tayi, tace. "Ka za a musu sunaye masu daraja, da kima." Kar a yayi ya musu hu uma sannan ya mika mata, ta mikawa Dattijuwar, Aka sake bashi d'ayar yayi mata Hu uma, sannan ya mika mata. Cikin girmamawa, Ghaniyu ya sunkuya gare shi yace. "Kakan gimbiyoyin Jordan wani suna ka sanyawa uwanye akina?" Kallonsu yayi cikin nauyin baki yace. "Tafarkon na mata Hu uba da Asma'ulHusnah Tabiyun namata Hu uba da MaryamSajida" "Allahu Akbar!!!" Kunya ya hanashi ago kai sai kwalla da yake sharewa, Ummi kan takasa magana, sai bin Abba take da ido. Kowa a falon jikinsa yayi sanyi, dan Abba bai ta a cin karo da nadama irinta yau ba. Mikewa Bakin sukayi sannan su a ce. "A fa awa Sarauniyar Jordan na gobe sun gode zasu koma idan yaran sunyi kwari akai musu suga dangin Kakarsu." "Insha Allah zasu zo." Inji Abba, rakasu duk yan gidan sukayi sai da suka ga tafiyarsu sannan suka dawo, Abba da Ummi suka dawo min da yaran, har da nurse sun zo sun samu anata rigima dani. Dudu yana tare dasu Nannah, har dasu Nana. Cikin aurewar fuska Abba ya ajiye min yaran, sannan yace. "Shayarda su." Ba musu na basu, sai da suka koshi sannan na cire su. Ban aki na shige na sake ruwa sai da nayi kuka ya ishe ni na fito, lokacin Nannah har ta iso, gani nayi ana tattara kayanmu. Dr ya kalle ni sannan ya ajiye min kwalin waya, ta kowa yayi gaba dan har sun fita ni aya ce, na rage zan saka hijab ina. "Kiyi hakuri ki shayar dasu." "Bazan iya ba, sanadin cikinsu na shiga garari." "Karki butulcewa Allah rahamar da yayi miki" yace min a hankali. Ina jin idanunshi a cikin jikina, dakyar na d'ago idanuna sai naga ya cika min ido nace. "Ni ka kyal." "Bashi zaki fa a ba, me yasa kika kasa fa Cikin mutuwar jiki na 'ago a karo na uku nace. "Abinda nayi niyya kenan" Zuba hannunshi yayi cikin aljuhunshi, tare da lashe lips inshi. Lumshe idanuna nayi sabida ya tino min da Ashraf, bansan ya akayi ba sai ji nayi nace. "Ina kewar Ash." "Kina kewar Ashraf ko! Toh haka ma yayi ga waya nan hot8 ce bata da tsada ki rike sai ki welcome back, akwai numbeta zan na kiranki ina jin yarana ya suke. Sanna wancan shashashan bazai kuma damunki." Motsin da naji a bakin kofa yasani lekawa,Abdul ne ya bu e sai kuma ya koma, ra a gefenshi nayi na auki hijab ina, ban kula wayar ba. "The phone!" A hankali nasaka zararan tsintsiyar hannuna na a, na fita ahankali yana take min baya, duk wanda ya kallemu a lokacin sai ya kuma kallonmi, sabida munyi wani irin dacewa ne da juna, musaman da ya kasance fatarmu kusan aya ne, dan shi ya fini hasken fata. Wucce ni yayi yaje ya bu e min motar, na shiga a hankali. Sannan ya rufe tare da cewa. "Ki kula da yaran don Allah." "Hm" nace mishi, haka Abdul yaja motar yana tsaye a gun. Shafa kanshi ya i zuciyarshi fess, yana hango yuwar nasara a cikin alamarinsa, dunkule hannunshi ya i ya an daki gefen kirjinsa, yana cewa. "Miskilancinki ya girmama anan." Yayi tap in gefen kirjinshi, har da wani lumshe idanunshi. *** Koda muka isa gida, side in Umma aka wucce dani, ita kuma Nannah ta wucce side inta, nan aka shiga hidima dani. Kamar ba gobe. Hmm idan nace larabawa suna da mugun son yara banyi karya ba dan na gani akan idanuna, da dare aka kawo min yaran na basu nono fir naki nace barci nake ji. Fita nurse in tai sai gata
Chapter 41 · 0% Book details