← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 65

Sashe 24

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"Zo nan uwata!!"
Wani irin rawa jikina ya
auka tare da mugun tsoro da firgici, juyawa yayi ya haura sama.
Ban ta
a sanin haka yan matan da sukayi ci
i a waje suke fuskarta tashin hankali ba, sai yau da ya faru a kaina. Rike Ummi nake cike da tashin hankali,

"Sai anyi magana ace lokacine bai yi ba, nan kuwa ana yaudaranmu ce da cewa miji bai zo ba, ashe anje gun wani katone ya zuba nasa basirar." Inji Mame Hjy Nuratu.
Lumshe idanu Ummi tayi da gudu Abbanmu ya sauko ganinshi ni kuwa na nime guduwa D'akin Ummi, cafko ni Mamie tayi tare da falla min mari. Akan fuskana. Sam idanun Abba ya rufe kawai ya rufe ni da mugun da wayar chajin laptop
in, zafi da azaba da suka gaurayani, kai ko dukar da samudawan Jordan bai ta
a tsoratani ba kamaemr dukan Abba kodan akwai tsoro ne a raina yasa duk na firgice.
"Ai gwara ka daketa yarinya ta zama annobar mace, mahaifinki na zaman lafiyansa kinje kinje ki
auko mishi
an gaba da fatiha, sai anyi magana ace ai mijine bai zo ba makira kuwa kinje sun gama dake shine zaki kwaso abin kunya ki zo masa da shi wannan da nice na haife ki yau zaki bar min cikin gidana dan ba zan iya rikon asara ba.."
A yadda na fahimci Abba babba burinshi bai wucce dukar cikina ba da kafarshi, ina gano nufinshi nayi maza na k'amk'ame ummi, jikina na rawa nace.
"Ummina ki cece ni bazan kuma ba. Wayyo Allah Ummina bazan kuma ba."
"Kaji ko Alhaji! Uwarta take niman ta kareta." inji Mamie.
Finciko ni yayi Ummi ta rike ni gam, cikin hargagi da kuma ingiza me kantu ruwa, yace.
"Maryam! Saketa ko kuma ranki ya
aci"
"Rayukarmu ne zasu
aci, ban hanaka hukunci ba, amma idan zakayi ka fara aiki da hankali yafi aiki da agogo, a cikin shekarun da tayi. Bata ta
a yin abinda zai
ata maka ba, tun tasowarta take kare kanta, da sunanka. Shin d gangan haka ya sameta ko kuwa karfi aka gwada mata, yarinyar da ka
auketa zuwa ghana dan tayi karatu yau dan tazo maka da akasin kaddara sai ka juya mata baya, ka nunawa Ubangiji bai isa ya jarabeka ba, kanunawa Ubangiji baka da karfin Imani, kai Uba kenan ina kuma ni da nake Uwa."
"Wannan matsalarki ce! Alhaji idan baka
auki mataki ba hatta fita waje sai yafi karfinka, cikin shege ta
an gaba da fatiha fa. Da sakel an ba wa me kaza kai."
Gabaki
aya sake haukacewa. Abba yayi cikin tashin hankali da
acin rai yace.
"Nuratu!
auko min wuka a kitchen idan ban kashe Safinah ba nayiwa kaina karya bani."
Abin nima ya samu, da gudu Mamie ta shige kitchen, sai da tayi rawa
"Shegiyar yarinya ta hanani rawan gaban hantsi yau dole ki bar gidan nan."
Da gudu ta
auki wukar tafita zuwa palour, kar
a yayi yayo kaina. Na fasa ihu tare da rike Ummina, kamar zata fa
"Zaki fa
a min uban da ya miki ciki ko sai na miki yankan rago?"
Ya daka min tsawa, duk na kara rikicewa, jin ihuna yasa Umma da Hajja kaka suka fito da sauri, Nannah ta rufa musu baya. Finciko ni yayi yasa min wukar a wuya. Cikin kuka nace.
"Ummina karki tafi ki tsaya."
Cak ta tsaya ita batayi gaba ba, ita batayi baya ba. Taki kuma juyawa ta kalle mu, Nannah ce tasaka hannu ta amshi wukar, cikin
acin rai tace.
"Banda ina ganin girmanka, tabbas da na mareka wallahi."
Wurgar da wukar cikin zafin rai Hajja kaka tace.
"Yau naga jakar uba! Yo da ka
auki zungureren wukar nan wata uwar zaka yi da ita"
"Hmm! Ai da zaku ji abin kunyar da yar gwal
inku tayi da bazaku ga laifinsa ba, domin d'an gaba da fatiha ne a kwance cikin mahaifarta." Inji Mamie ta fa
a tare da kumbura fuska tana hura hanci.
Tsaki Hajja Kaka tayi cikin ko in kula tace.
"Sai me dan tayi cikin shege! Ai gwara ita, wasu asalinsu idan kaji har duniya tatashi bazaka ha
a iri da suba, amma da kaddarar rabo ya ha
a aiki gashi ana zaune lafiya, wai kura na cewa kare mayye, yo wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai daren mutuwarsa, abin kunya gaba ta bashi ba baya ba, kuma ba kanta farau ba, kuma ba akanta karau ba, wasu nasu kazantar ko kuda bazai so hawa kai ba. Balle yarinyar da tayi zaman a wata duniya na tsawon shekaru, dan yau ta dawo sai a nemi kashe min ita, don Allah yankata dan kwal ubanka, wato dan bani ce na haifeka ba, ka nuna min dan ban ta
a haihuwa ba shine zaka kashe yarka ko shawara dani bakayi ba ai da na gaya maka hanya mafi sauki da zaka kasheta. Ke Amnah
auko min igiya ya ratayeta ina ga irin wannan kisar ba a ciki tsananta bincike ba ko."
Wani katon harara ta masa sannan ta dawo kaina riko hannuna tayi, tare zaunar dani jikina bai fasa rawa ba, ta kalle ni cikin jin haushi tace.
"Yar banza da shege idanu kamar yayan kurna, taya kika bashi ya
irka miki ciki, yo yanzun da duniya ta cigaba, aiko wannan kororon roba yasaka, codan yako ko me." (Just for fun
Hajja kaka wooo)
Sunkuyar da kaina nayi dan na lura yau barikancin hajja kaka ya motsa,
Ta
e baki tayi cikin ko in kula tace.
"Toh haka ma yayi koma me nene, duk ciki Yaran maryam kece me shegen taurin kai kamar ganda, baki jin ko fi
is, da wasu soyayyun idanunki nan kamar soyayyer gya
a, kik cika fitina bana wasa ba, gaji duk hakurin irinta Badaru sai da kika sashi ya
i miki bi
i, haka kawai kin zauna ana jibgarki kamar wata lusara. Shashashar wofi"
B'antara goronta tayi cikin nutsuwa tana taunawa, Umma tace.
"Wallahi Alhaji ka bani mamaki yadda, ka ware karfinka akan safinatu, yarinyar da tun tasowarta muke zargin aljanu ne da ita, shine zaka ware karfinka akanta dan wannan abun ya faru. A cikin gidan nan har kake zargin yarka dan kaddara ta fa
o mata, toh kasheta."
Ummi kan falon ta bari, bai kulasu ba ya nufi dakin Ummi, wacce ta fito ban
aki zatayi sallar azhar, cikin bala'i yace.
"Kice ta bar min gidana kafin na dawo."
Ko kallo bai isheta ba tasaka hijab
inta ta tadda sallah,
"Na gaya miki ta fita tabar min gidana"
Banza tayi da shi, har ya fito ya dawo cikin zafin rai yace.
"Idan kika fita, dan kareta ban yaf."
Mika alamuranta tayi ga Ubangiji ta cigaba da sallarta, tana idarwa ta shiga zuba kayanta a cikin babban a kwatinta, sannan tafito zuwa falon ta kalle ni yadda nake kwance na takura guri guda ina kuka, tace.
"Ki shiga
akinki ki kwaso ka
anki."
Mikewa nayi na kalleta naga ta kauda kanta, girgiza kai nayi cikin tashin hankali nace.
"Ummi!!!"
Yatsar hannunta ta
aura bisa bakinta alamar nayi shiru.
Mikewa nayi naje nayi yadda tace,
Ina gama hada kayana najanyo akwatin na fito dashi, dai dai shigowar Nannah, a firgice tace.
"Ina zaki Binti"
Sunkuyar da kaina na
i nace.
"Ummi ce tasani na fito da kayana!"
Riko hannuna tayi, na
ago tare da kallonta, kwantaccen gashin dake gefen fuskarta sak da nashi, har
akin ta kaini tace.
"Maryam lafiya?"
Murmushi me ciwo tayi sannan tace.
"Yace tabar mushi gidansa, toh meye amfanin zamana a gidanshi tunda bai yarda da kaddara ba. Ni yanzun damuwata Safinatu ce, ko zata gaya min cikin waye."
Chapter 24 · 0% Book details