Sashe 36
Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
tace. "Kina son wani abu ne bama jin abinda kike cewa." "Ummi baku fahimtar me nake cewa kenan." Nan ma Nannah tazo tace basu fahimci nake cewa ba. Saka hannuna nayi na shafa fuskana naji bakina ya koma gefe. Kuka nake son yi amma na kasa, da karfi na rufe idanu na, na shiga sauke ajiyar zuciya. Ina jin Ummi tana kiran Abdul tare da gaya mishi halin da nake ciki. Barcin dole ne yayi gaba dani, dan ban farka ba. Sai karfe biyu ina bu e idanu na, sai akan Anim. Mugu an masara ana goyaka, kana karya uwarka. Kukan da ban samu damar yi bane ya kwace min na shiga fisge-fisge saura kiris na fa o daga gadon Abdul da Nannah suka tare ni, fita ABDUL yayi sai gashi tare da Dr Muhsin. Alluran barci suka min Idanuna na kan Anim. Ajiyar zuciya Nannah ta sauke, tare da cewa. "Abdul ko za a cire abin cikine wannan wahalar tayi yawa, kullum babu sassauci daga wannan sai wannan, gabaki a Safinah ta fita hayacinta." "Ai matsalar shine cikin bai cika bakwai ba, amma da zaran ya cika bakwai insha Allah zamu cire babyn, dan girman cikin ma yana rinjayarta." Inji Abdul, "Ni a ganina ku bar cikin ya shiga watansa in yaso sai a cire mata, dan nima na karaya da alamarin Safinah, na yau daban na gobe daban." "Kuma ana cire mata yaron zan bawa Alhaji Zubair yayan Nuratu it.... _A cikin duniyar nan kowa ya tara abin fada, amma kalilan suke iya ajiye nasu, ba sauki rungumar Alamari me wahala ga karamar irina, Hidimar miji da Hidimar yara.... Ba abu me sauki bane aukar nauyin da bai zame maka tilas ba, idan ki a ya sauya dole rawa ya sauya....._ Uom Muwaddah... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITERS ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* _Na sadaukarda wannan shafin ga Iyaye mata masu fafutukar kare Yaransu....A cikinsu Har da Mahaifiyata Allah ya jikanki da Rahama Page. - 28 " Ban tab'a karo da mutum mara mutunci irinka ba, banza mugu fasiki, mujirimi kawai. Kafit." Maganar da ban karasa ba kenan na ha iyen dole, sakamakon jin bakin d'an iska da nayi cikin nawa, duka nayita masa. Tare da ture shi da karfin tsiya, na kuma tofa mishi yawunsa a fuska, kazamin banza shafo yawun ya i, tare da lashewa har yana lumshe idanunshi, girgiza kai yayi da takaici ya kamani. Bansan lokacin da na auki kwallo goriba na kwalle goshinsa, kam uban bala'a alkur'an sai akan idanun Abba. Tsabar na tsorata garin na yunkura zan mike sai da naji bayana ya amsa, tare da zuban abu a jikina. "Safinah! Rashin mutuncinku har ya kai ya ta a mutumin da yake jeka ka dawo akanki, yau zaki gaya musu." Dakyar na mike dan naga yana gun Anim wanda goshinsa ya fashe, zasu fita ni kuma na shige gurin Ummi, ga baki aya na birkice domin dakyar nake aga kafana, ga cikin da yawo kasa baki daya. "Ummi!" Na kwala mata kira da karfi sannan na durkushe a gun, sabida jikina wani irin rawa yake, har cikin kashin jikina rawa suke. Ga zufan da yake karyo min ha e da wani mugun sanyi me shiga jikin mutum.