← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 65

Sashe 44

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Idan ya kashe ni shi gadin duniya zai, kana damun Safinah, baka taba tunanin idan wanda zak sota da gaskiya ya fusata ko tokarka baza a samu ba. Karka manta tana da Uba! Kani! Uwa Uba masoyi! Idan har acin ran mutane uku nan ya ta azzara ya kake tunanin karka fusatani, dan Wallahi da bugu aya zan saka a atar min da labarinka, ba kai ba hatta Uban matanka wanda kuke kwaryan sama da na kasa, shima ba kyaleshi zanyi ba kafita harkanta." Gya a kai yake kamar kadangare, "Idan kuma nami fa?" "Kana wasa da rayuwarce." Sunyi musayan kalamai masu zafi alwashin da Anim yaci bana wasa bane, fita Dr yayi daga motar. *** Sbigowar Dr rayuwata ba sauki dan a cikin lokaci kalilan ya tafi da zuciyata, amma tsabar jan aji da miskilanci tare da an taurin kai, naki amincewa dan Kullum Ummi sai tatuna min yarana da suke hannuna, gefe aya ga Nannah da muke video call kullum itama, Ga wani irin soyayyar da yan gidanmu suke nunawa yarana. *** Leke leke take mur anta kasa kasa tace. "Na maka alkawarin zan cika maka burinka nima yanzun hankalin Mahaifinsu ya koma kan shegun jikokinsa, har da Uwar yaran......" Me kuma ake kullawa... *Toh yanzun Muhawara zai arke dan nasan ayan tambaya za a wurgawa Dambuje Oum Muwaddah.... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITER'S ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* *_Labarin daban yake da sauran Ina son ku sani duk cikin labaruna babu amar wannan ba dan kome ba sai dan tsayinshi da fa insa Ina ga yaka mata ku nutsu ku bi labarin Idan nai kuskure ku an karar dani domin na gyara dan babu wanda yake cikakke Yanzun muna Book 1 ban gama ba shi yasa na za i na baku Book one Kyauta sauran labarin zaku iya saya a saukakkakiyar Furashi! Masu ganin Feener ta wahaltu a barta haka toh ashe kuwa da sauran kallo, Waye zata aura? Shin meye makomarta? Masu ganin a sake Ashraf! Idan naga comments inku dariya nake, idan kuka bi kome a sannu zan warware wasu kulin na book one kafin na shiga book 2 ku duba wasu abubuwan me kyau na labarin ku zubda marasa kyau na cikin labarin dukda dai duk abinda Marubuci zai saka sai ka samu akwai me kyau akwai mara kyau fatanmu muyi tarayya akan aikin Alkhairi Page. "Toh munafuka annamimiya! Allah ya toni asirinki, wato dake Za a ha a baki a cutar da gidana Nuratu me na tsare miki yau zaki bar min gidana Makirar banza makiran wofi" kwace wayar yayi yaga. Alhaji Anim. "Em...em.. Alhaji ba wan..." "Gafara can zaki kula min wani makircin toh anyi walkiya, kuma Wallahi ki a sake wani abu yasami Y'ata da jikokina, ni hukuncina me saukine, hukuncin da Nana Asma'u zata miki wallahi Allah ka ai yasani." Yana gama fa ar haka ya juya tare da barin falonta, cizon yatsarta tayi tare da cima wani kudiri. *** Rayuwarmu sai muce Alhamdulillah wani irin kulawa muke samu ta bangagori daban daban, Uwa uba Dr da ya zame min wani jigo na rayuwata, dan karfi da yaji ya zamewa su yan biyu Uba, musaman ya kawo min danshi Adil. Ya kwana biyu dake yaron yayi wayo. Kusan shekara hu u. Da zai koma ni dasu Ummi muka mishi siyayya aka cika babban jaka,dake me a wawa ne ganin Abinda mukayi kamar yayi hauka. Dan murna gani yake kamar na amshi tayin da yake, ni kuwa kallonshi nake kawai bawai me min bane, haka kurum nake ji ban masa adalci ba. Kuma dole duk wanda ya fito nima na yayi hakuri har sai na ya e yarana, Daga ni har yaran jego ya amshemu, munyi bulbul. Dan ruwan none yana isansu sosai, sabida Ummi tasan abinda zanci ko nasha ruwan nono ya kawo. Gefe guda tana gyarani ta ciki da waje. Dukda na koma akinta amma bana yawo kafana ba takalmi a cikin akin, balle kuma na zauna babban mayafi ko hijab. Ina samun kulawa gaski a yadda ya dace, dan dudu ma ba abarshi abaya ba, Rigakafi da ake zuwa ni a gida ake zuwa min, abu guda da gaza fahimta shine anki barina ko sau aya na fita koda kuwa bakin get ne. *** Gyara zama Alhaji Kamil Matawalle yayi fuskanshi cike da zallar acin rai. Kallon Abba da Dr sai kuma Dudu. Cikin cunku shashiyar murya yace. "Ina me baku hakuri da abinda Anim yake muku, kuma Insha Allah zan tsawatar mishi." "Ba kome Alhaji! Mungode da ka sauraremu. Allah yasa mudace " "Nine da godiya." Mikewa sukayi sannan suka fita, a waje suka ha u dashi, kowa ya auke mishi wuta, shima ko a jikinshi ya shige. ...... Mikawa Ummi Sajida nayi na mike zan shiga ban aki naji wayata na tsiwa. Ban akin na shiga sannan na fito banbi takan wayar ba na auki Husnah wacce take lashe bakinta, murmushi nayi cikin jin da i nace. "Ummi! Aami ta cika niman rigima kalli yadda take lashe bakinta, kamar bata ci kome ba." Dariya tayi sannan tace. "Aikinga ita Aani bata da rigimarta, ga hakuri." "Hmm! Allah yasa karsu auki miskilanci wancan shashashan uba..." D'im naji an kaiwa bakina duka, da sauri na ago kaina ina dafe bakina cikin rawan murya nace. "Ummi bafa da Dr nake ba, wancan yaro." Sake buge min bakina tayi, na rike kaman zanyi kuka nace. "Ummi sabida Ashraf." Wani dukan takawo min na kauce, cikin jin haushi tace. "Uban yaranki kike kira da shashasha? Har da cewa yaron can ga shaidan yarontaka a hannunki, ima yarone sai ki girmama shi kodan yaranshi, balle." Shiru tayi kodan girman maganar da zai fito bakinta, Ko yayya kika ga 'a namiji ki girmama alamarinsa, da kike kiranshi yaro ai sa'an Abdul ne kuma kinga Abdul yana da mata me yasa baki ta a kiran Abdul da Yaro ba sai Uban y'ay'anki! Bana son reni, ba mamaki Allah ya nuna miki iyakarki ne dan renashi da kike yi, ko ba haka ba?" Abunka da sokuwa( ) sai na shiga bata labarin artabun da mukayi, har lokacin da abin ya faru da kuma dawowa na gida. Cikin tausayawa ta kalle ni sannan ta kalle yaran, tayi murmushi sannan tace. "Lokacin da kika ki maganar auren, kowa yayi mamaki, amna da kika ce karatu zaki, sai naji sam ban amince da tafiyarki ba. Dukda haka na kasa dakatar dake, har Abbanku na gayawa bana son tafiyar dan jikina na bani babu alkhairi." Siraran kwalla suka sauko mata, gogesi tayi tare da sumbatar goshin takwaranta. Sannan tace. "Da nayi yunkurin hanaki, ba mamaki rabonsu ya zama ajalina, tunda Allah ya nufa sai sun zo in toh babu wanda ya isa dakatar da ikon Allah, naji da i da taimako kikayi. Allah yasa hakan ya zame miki izina da duk masu taurinkai irin naki. Sannan kafin Nannah ta tafi taga ya min Baban yaran yana can a saudiya a rufe." A razane na dago kaina inakallonta, jikina sai rawa yake. Nace,. "Ummi! Me ya faru da Sultan in? Kinsan sabida ni yayi murabus. Innalillahi" Kuka ne ya kwace min, ba kome yasani kuka ba sai makomar yarana, ubansu a rufe. Ta gaya min dalili rufe shi, bayan naci kuka na koshi nace. "Zai rina! Dan mutum ne me tsananin ko in kula, ga wani miskilancin da yake ji dashi Ummi Wallahi maganar da kika ga Ashraf yayita sosai ki duba girman Alamarin, maganarshi bata wucce harrufa hu u, itama in dan ta zama dole ce. Ban ta a ganin miskili irinshi ba, zan iya cewa idan da zaki matse shi bai sai meke faru a cikin masarautar ba, shi yasa suka kayi amfani da yardaddenshi ya zuba mishi makaman." "Allah ya kyauta! Wallahi na tausya mishi, yaro karami a cikin miyagu." "Hm! Ummi kenan wallahi na tausayawa matar da zata aureshi dan wallahi makiyanshi sunyi nisa kiyayyarsu akanshi babu sauki zasu iya zubda jinin kowa dan suga bayanshi, kuma abinda zan iya cewa nayi shine ankarar dashi kurakuranshi, da ace har yanzun yana sarkine da na tunatar dashi matan da suke a wulakance a cikin masarautarshi, Ummi kinsan abinda na fahimta ga mulki ga dukiya amma sun gaza samin nutsuwa dashi, gani suke kamar ya hanasu watayawa. Shi yasa sukayita kokarin sai sunga bayanshi, Allah yana kareshi. Akan shi naji na tsani mulki da sha aninta bana kaunar milki, Alhamdulillah ina cikin farin ciki da yaranshi matane kuma basu da gurbi a cikin masarautar da mulkin." "Toh Allah ya tsare! Amma abun da aure kai." "Indai akan mulki da dukiya ce babu aure kai dan kowa yasamu rana zai baza shanyarsa son ranshi." Munyi masa fatan ya cinye wa'adinsa, lafiya. *** *SAUDI* Mika mika mishi iPad in Lawyer yayi cikin girmamawa, amsa yayi, ya kalli yaran cikin wani masifafan soyayyarsu. "Har ta haihu??" "Kamar yadda na gaya maka yarinyar ta fuskanci matsala a rayuwarta, sannan Fahad ya tabbatar min akwai mutane biyu da suke bibiyar rayuwarta, d'aya likitane. Babu sharri a tare dashi aya kuma Fahad yayi bincike akanshi shi yasaceta, lokacin da cikin yaran. A halin yanzun bata fita sabida gudun kar ya kuma saceta." Dunkule hannunshi yayi idanunshi sunyi wani mugun ja ya kuma bu esu, sannan yace. "A tura masu tsaro" "Yalla ai! Ghaniy.." Yadda ya ago kanshi sai da yabawa lawyer tsoro dan har jini jini yake ganin ya kwanta akasan idanunshi, "Baiwata da Yarana! Kome ya faru kaine. Saura wata takwas na fito." Yana gama fa ar haka ya mike, Har ya isa bakin kofa, Cikin yaren Urdu yayi magana(Jama'a me Ashraf yake nufi da canza yare Gulmar ma baza a barni nayo cikin salama ba) Shi kuma Lawyer yace "Toh! Yalla Lawyer na komawa masaukinshi ya ciro laptop in Ashraf ya fara aiki *** Yau yarana watansu Uku, wanda yayi daidai arin da matar dudu. Tayi, dukda Ummi ta hanani zuwa ji nayi hankalina ya tashi, dole na shirya yaran na saka jakar goyon baby na Sajida Wacce nake kira da Aanih, sai Husnah wacce nake kira da Aamih. Aanih a gaba Aamih a baya, sannan na fito tare da bawa Zakari daman ya kaimu asibitin kamar zaiyi kokari sai ya fasa
Chapter 44 · 0% Book details