← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 65

Sashe 52

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai yanzun na lura da girman da Hajja take cewa yayi min, tsayi yake dashi sai fa i. Kuma yana da mur iyar jiki, kana ganin tarin tsokoki, lumshe idanuna nayi sakamakon kamanceceniyar da suke da Ashu, sabida shima yana da k'iran irinta zaratan mazaje. Hura min iskan bakinshi yayi. Fuskarshi auke da murmushi yace. "Kina tunanin Babansu Twins ko?" Ya aga min gira, tsuke fuskana nayi tare da tura bakina gaba nace. "Baby!!" Ware idanunshi yayi, cikin jin haushi nace. "Ba halin nayi tunani sai kace na wncan yaron nake yi" Dariya sosai na bashi, dan yakasa rikewa yasai yi yake kamar yaga ta iya, haushi ya bani na juya zan koma cikin gida yayi wuf tare da riko hannuna, a tsiwace na bu e baki zanyi magana, muka ha a ido dole na ha iye sannan na kalle hannuna da ya ri "Kiyi hakuri mana" yace cikin wani irin murya, d'ago idona nayi na kalle shi. Bansan lokacin da kwalla ya shiga saukowa daga idanuna ba, sake min hannuna yayi sannan yace. "Kiyi hakuri, wallahi bansan dariyar zai sakaki kuka ba, kiyi hakuri bazan kuma ba." e motarsa yayi ya ako tissue ya mika min, goge kwallar nayi, kaina a sunkuye. Dan kunyar kaina nake ji na kukan da nayi akan abinda bai taka kara yakarya ba. "Kinsan me yasa na miki dariya! Sabida kin kawo abinda hankali bazai auka ba, tabbas Babansu Twins yarone kamar yadda kika ce, amma ya kamata ki aga shi daga cikin jinsin yara ki kaishi cikin na manyan sabida, Yan biyu, da kuma nan gaba zan kara fahimtar dake abinda nake son ki gane." "Meye ha inka da kawar Batul?" na tamvaye shi tare da tsare shi da idona, D'age min gira yayi cikin tsokana, ya shafa kanshi sannan yace. "Idan kin amince, rana d'aya za a kawo min ku." Kallonshi nayi bakina har rawa yake nace. "Kana nufinm" "Eh ku biyu zaku zauna," Kauda kaina nayi cike da zafin rai nace. "Ok, kaje ka zauna da ita dan ni ba zan zauna da sa'ar Batul muna gogayya da ita ba." Mamaki na bashi yadda na ata rai, akan yace mu biyu zamu zauna, murmusa min yayi sannan yace. "Kin cika kishi! Bana fatan rike mata biyu, amma ki sani kishi ke haifar da kishiya, ki sassauta kishinki ni mijin mace aya ce tal." "Wacece a ciki ni ko Ita." Na tambayeshi, gyara tsayuwarshi yayi tare da kura min ido, yace. "Banda sai anyi aure zaki halatta min wallahi da idan auke ki yanzun na kaiki cikin gidana, babu wanda zai kuma kallon tafin hannunki." Kallonshi nayi cikin wani bakon yanayi, haka kawai naji ina tausayawa aina, lokaci guda idanuna ya fara da ruwa. Sunkuyar da kaina nayi sabida saukarsu. Suna d'isa a kasa. "bansan me yasa ba, bansan me nake ji ba, kawai ina tausayawa rayuwata ce idan na rasaka, Dr ka tafi kawai dan ina jin tsoron kar na fara sonka kuma nazo na rasaka." Takowa yayi gabana tare da soka hannunshi a cikin aljuhunsa d'aya yace. "Ki d'ago kanki ki kallr cikin idanuna, ce min kina sona." Girgiza kai nayi wani irin kuka ya kwace min, dafa jikin motar nayi, nace. "Ko baka ce ba, ina sonka mahaukacin son. Wanda zai iya tarwatsa zuciyata idan na cigaba da oyewa, Hameed kaje kawai idan kacigaba da zama dani bazaka karu da kome ba, sai tsantsar damuwa" "D'ago kice min na tafi ni kuma zan iya juyawa." ya fa a min yana kusantar inda nake. "Bana son Adil da Ammah su." "Ke! Lafiyarki kuwa kinzo kinsa garjeje a gaba , kina kuka shi kuma da yafiki shirme yabi ya rikice kai jama'a duniya tayu lalacewar zabi." Da gudu na shige cikin gida ina kuka, koda na isa falon ban tsaya ba na shigesu Ummi da suke zaune. Bin bayana yayi da ido, bai masan me hajja ke cewa ba, shi damuwarsa nice, haka ta gama surutunsa. Haka ya shiga motarsa ya bar gidan zuciyarshi ba da i, na rasa gane meke faru dani matukar zan ha u da Dr tausayinshi nakeji haka mukayi kusan kwana goma, dakyar ya dakatar da shirmen da nake mishi. Tsakanina da Hajja kuwa toh ko Tom nd Jerry sun sallama mana, domin kuwa ta anzo tamin maganar banza ni kuma na shareta idan ta buwaye ni ce mata nake Hajja ko zamu nimo tsohon irinkine a aura muku aure, bata kuma bin takaina. ........ Tsakanina da Dr soyayya arr domin kuwa na gabatar dashi har anyi magana, karewa ma Sadakinsa na hannun Iyayena, an bari sai na yaye yarana wanda suke da wata hu u zuwa biyar. *** Watansu Aanih bakwai aka shirya mana tafiya zuwa Oman, tsakani da Allah nasaka Ummi agaba ina kuka bazani ba, dan nasan idan naje sai su nemi rike min yarana wanda nake ji yanzun kamar rayuwata ce su in ko ciwon hakori su e tare muke dasu, dan har tsokanata Dr keyi wai amka uwar son yara, bana jin kome, gefe guda har da tunanin dr yake hanani tafiya, dake Ummi ta harbo jirgina sai tashiga rarrashina da cewa. "Ayya Uwata kwana nawa ne kamar yau ne fa, har kun dawo." Da ire iren magana masu da i da laushi, tasamu na amince amma sati biyu zanyi, murmushi tayi a ranta tace. *Ta yaro kyau take bata karko* Kin gayawa Dr nayi, ranar da yaji. Ya kirani amadadin nai mishi magana sai na saka mishi kuka, na rasame zance mishi. "Ya isa Beauty! Dalilin da yasa kika oye min kenn bazaki iyafa a min ba sabida kuka zaki min? Karki damu duk inda kike kisa ranki muna tare, insha Allah zan biyoki soon, an jima zanzo." Daga haka ya kashe kiran, ranar nayi kuka me cin rai sosai dan gani nake kamar basu min adalci ba,. Da dare da yazo kasa sake jiki nayi inata ari ari, dake yanzun a falon Abba muke hiran haka ya gama shirunsa sannan ya ajiye min rafan ku in Oman har guda uku, sannan yasa kai zai fita. Cikin sauri nabi bayanshi na rungume shi tare da sake kuka ina cewa. "Kayi hakuri bazan kuma ba" Wani irin yanayi yaji ya sauko mishi tare da kasala me mugun kashe jiki, janye hannuna yayi wanda nasa na kamkame shi, ya janyo ni gaba cikin damuwa yake kallona. Lumshe idanunshi yayi cikin damuwa yace. "Toh ya zan miki! Nazo amadadin ki tar e ni da kalamai masu da i sai kuma kika sani a gaba da kuka, kinsan yadda nake ji. Banda kar na shiga hakkin yaran nan ba, wallahi bazan bar gari yawaye ba tare da kin zama mallakina ba." Lumshe idanuna nayi tare da saka hannuna a wuyarshi na kara tsayina tare da d'aga kafana, a fuskarmu nayi kafin yayi yunkurin dakatar dani, na ha e bakinmu guri guda. Kallon fuskana yake musaman yadda kwalla ke sauka wannan na koran wannan a guje, a sannu ya bu e min bakinshi na rasa yazanyi, kawai sai na nemi janye bakina daga gare shi, rike bayana yayi da hannunshi duk biyu ya zura harshenshi cikin tare da lallu o nawa, bu e idanuna nayi da sauri. Lumshe nashi yayi sannan ya bu e. Yana kallon cikin kwayar idona yake, lumshe nawa nayi, a sannu na kwace bakina ina sauke ajiyar zuciya, kuma sai na fashe da kuka tare da kifa kaina a kirjinshi ina kuka, sunkuyar da kanshi dai dai kunne na yace. "Thanks for thi hot kiss" Yau nayi batsa naji cass... *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo ku insu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...* *Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah* Oum Muwaddah...... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* BOOK ONE.... Page. Sun fito zasu inda motarsu take kawai aka bu e musu wuta, cikin sa'a suka sami Dr a kirjinshi gefen, take ya zube a gurin. Dudu dasu Ummi da Abba kuwa basu same su ba, ana cikin haka wasu maharan suka zo aka fara musayan wuta, abinda ya kuma aga kowa hankali dan ba karamin d'agawa mutane hankali yayi ba dan har cikin inda mutane suke harbin ke shiga. Haka suka ita harbim juna har masu harbin baya suka samu kashe mutanen da sukayi harbi Dr, wani abin mamaki wadancan sunfi su iya sarafa makami, kuma sun iya harbi a nutse kamar suna, shi yasa suka same damar kashesu, suna gaba kashe su. Suka dawo kansu Abba. "Kutashi ga mota can zai kaiku gida, sannan shi Dr zamu wucce da shi Asibiti." Dake a kwai tsoro a ransu haka suka mike, tare da bin umarninsu har cikin motar, suna shiga ana tadda motar zuwa gida. Komawa kan dr sukayi tare da kamashi suka sakashi a motarsu zuwa Asibitinshi. Cikin gaggawa aka amshe shi, ana kokarin ceto rayuwarshi. Cikin kwarewa su Dr Shahban tare da wasu drs suka rufa akanshi, hankalinsu yayi mugun tashi. Kafin wani lokaci labarin harbinshi ya kara e ko in, har takai shugaban kasa da kanshi yazo asibitin domin duba lafiyarshi, Tsawon awa takwas akayi ana faman ceto ranshi, amma ena abun ya faskara dole shugaban kasa yasa hannu aka fiddashi da jirgin fadar shugaban kasa zuwa. India, sabida bullet in ya kuskuri zuciyarsa, abu mafi hatsari a tare da ciwon shine da zaran akace za a cire bullet in da karfi toh tabbas mutuwa zayi. Shi yasa duk suka birkice akanshi suka rasa ya zasuyi dashi. Dole aka tattarashi sai Mumbai. *** Wani irin mafarki nayi me cike da firgice, akan dr zubur na mike tare da janyo jakata na ciro wayata, na fara kokarin niman gida. Abin haushi ashe number kasata ce bazatayi a kasar ba, tilas ni wurgi da wayar ina tsaki, tun bayan sallar asuba na koma barci, duba gun yaran nayi naga suma barci suke, saukowa nayi a gadon, na nufi ban aki. Wanka nayi sosai sannan na fito, na same Nannah tana zaune tasa jikokinta a gaba, tana kallonsu. Dake akwai rigar wanka a jikina, har kusan kwanjina na nemi
Chapter 52 · 0% Book details