← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 65

Sashe 15

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

su a fito daga cikin akin, ya kuma bawa masu tsaron kofar izin karsu bar Irfan ya fita, shi kuma ya wucce da mahaifinsa Asibitin. *** Daga falour bakin Amir Ukshe Raziyah tafito fus arta cike da farin ciki, shima bayanta ya biyo ace. "Ki kula sosai, dama Abu Zarri ne ya tsare mana gaba, indai Ashraf ne bani da matsala dashi. Dan wannan halin da yake ciki ma ya ishe shi, haka zai zauna har karshen rayuwarsa kowa ya manta." "Ni haka ma bawai yayi min bane amma bazanki shawaranka ba ai da kasheshi mukayi haka zai fi alkhairi." "Me kike ci na baka sauka, ki jira nan da wani lo aci mulki zai dawo hannunmu," "Dukda haka naso da kashe shi baki aya dan ina gudun kar wani abu yazo ya lalata mana shirinmu" "Idan muka kashe shi zaiyi wuya muma mukai labari, haka ma wadatar dashi." Haka suka tashirya yadda zasu kawar da duk wanda zai kawo musu shunku. *** *NIGERIA* Abuja.... 4pm A firgice Ummi tafarka daga barcin la'asar in da tayi akan abin sallarta, salatinta yasa Khalil da Fatima wacce muke kira da Batul. Da sauri su a nufin kanta, mika mata ruwa Khalil yayi wanda tasha kafin tayi sallar la'asar. "Sannu Ummi! Lafiya..?" Inji Khalil, janshi baya Batul tayi tare da dakatar da shi. Sallama yayi tare da shigowa falon ganinsu cirko cirko akanta yashi tambayar "Lafiya?" Inji Abdullahi, " Ya Abdul Ummi ce mukaji tayi salati, shine muka bata ruwa ko Adda Batul" Inji Khalil, Zama yayi kusada Ummi ya aurs kanshi akan kafa ar, yace. "Ummi! Don Allah ki rage sanya damuwa a ranki, Insha Allah duk inda Safinah take zata dawo lafiy..." "A'a Abdullahi! Safina tana cikin hatsari, naji haka a jikina tana gab da fa awa cikin hatsari na ganta cikin mugun yanayi tabbas tana cikin mawuyacin hali." a raunane ta kai, kafin waninsu yayi magana tasake wani irin kuka mara sauti tasake a hankali me mugun ta a zuciyar me sauraro tace. a Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkakku masu daraja ya Allah ka jarabce ni da abinda zuciyata zata iya auka Ubangiji baiwarka tana cikin wani hali ya RahamanRahim Ya Allah badan na iya ba Ya Allah dan karfin mulkinka ka kare Safinatu a duk inda take." Addu'ar da tayi kenan, duk falourn sai da su a zubda kwalla, shigowar Nannah baisa su fasa kuka ba, Abdul ne yayi ta maza ya fa awa Nannah abinda ke faru, itama dai au tun safe take yawan jin fa uwar gaba tare da tunanin Safinah da ya addabi zuciyarta, gefe guda kuwa na zuciyarta yana son tabbatar mata da zarginta amma bata amince da hakan ba. "Maman Bint ki daina kukan nan haka, Insha Allah Bint tana nan dawowa, Insha Allah ki daina takura zuciyarki da tunanin wani abu zai same ta da izini Ubangiji alkhairi ne zai faru da ita." Da kyawawan kalamai Nannah tashawo kan Ummi tayi shiru, ita ba ome ke aga mata hankali ba ome bane sai idan ta tuna cewa Safinah mace ce, me rauni ce bazata iya kare kanta ba idan wani abun kare kai yazo mata babu shakikinta a tare da ita, waye zai kare mata wani abun waye zai ceceta idan wani ya farmaketa cikin kuka tace. "Mamin Bint!! Mace fa bata da karfi, idan wani ya farmaketa fa? A wannan duniyar da imani yayi karanci idan wasu su a cutar da ita fa, kasancewarta a mace me rauni taya zata tsira, wallahi nasan babu makawa Safin..." Kwarewa tayi wanda ya haifar mata da tari me karfi, sai da aka bata ruwa tasha, ajiyar zuciya ta sauke tace. "Allah kai kafini sanin halin da ta e ciki" Daga haka bata kuma magana ba, sai dai kwalla yaki barin idanunta...... Nannah bata bar gidan ba sai karfe biyar da rabi, lokacin Alhaji Badar ya dawo. *** *JORDAN* 9:pm Ganin dare na kara duhu, ga wani tsoro tare da fa uwar gaba, yasani juyawa zan bar gidan, ban ta a tsamanin zan ganshi ba sai ganinshi nayi a gabana, wani irin yanayi naji tare da tsoron da ya cika min zuciya baya nayi a razane na juya da mugun gudu cikin gidan, aikuwa ya rufa min. Sakama on duhun falon, bansan meye a gabana ba nayi tuntu e dashi take na zu e a gurin, zan mike naji kafar tayi min nauyi. Dole na mike da sauri kafin nace zan gudu ya bangajeni da kirjinshi na fa i can gefe akan hannuna, sai da naji karan kashin hannuna. Kuka ne ya kwace min dukda falon akwai duhu sosai nasha mamakin yadda yake gane inda nake, matsawa nayi da sauri na shige akinsa, nasamu na tura ofar zan rufe ya kaiwa kofar doka, kuka ne ya wace min mi ewa nayi na shiga bin bango da bayana,, hmm ashe makunin wutar akin na ta inda nake ja a jikin bango aikuwa wutar dakin ta kunnu, ashe jiya a duhu na ganshi, au kam a haske nayi ido biyun dashi. Bansan lokacin da ihu ya kwace min ba na rufe idanuna da mugun karfi, fincikoni yayi ya cillani saman gadonshi kaina ya bugu da allon gadon, bibiyu na fara ganinshi, yunkura nayi zan mike yayi maza ya diro kaina, kuka ne ya kwace min nace. "Karka min haka Ashraf, don Allah karka rabani da kome na, gwara ka kashe ni kawai." Kifeni da mari yayi wanda ya auke min jina da ganina, kafin na dawo daga hutun rabin lokaci Ashraf ya keta min rigana har cikina, duka na kai mishi tare da yakushe fuskarshi, amma ina yaci karfina, kuka nake kalaman Nan yana dawo min. _Taya zaki kare kanki? Karki tsomma kanko cikin wancan masarautar kyaleshi inda rai da rabo zamu gana, a matsayinki na ya mace taya zaki fuskancesu har ki samu damar auko shi? Don Allah karki ai ata abinda zanji na tsani kaina, dan matu ar su a ganoki kasheki zasuyi idan uma basu kashe ki ba zasu cut..."
Chapter 15 · 0% Book details