Sashe 28
Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai ni zan fa a mata gaskiya Safina ce ta zubda cikin, kinsan da zata tafi me tabani, wallahi wani akwati ta bani zallar sarkoki da yan kunaye ne a ciki a na sayar na dinga saya mata abinda take so, kinga wannan alert in yau da safe aka turo shi da dallar amurka zunzuruntu kaunar da takewa wancan sakarya, da abin cikinta, azun sai da takirani ya take ya cikin wallahi yau sa safina kasa dani take tana tashi sai na mata dukar kawo wuka." Shiru sukayi kowa da abinda yake yawo a ranshi, har Baban Sabir yazo tare da Annur. Sai karfe tara da rabi suka tafi, aka barmu daga ni Fatima. Abdul ya koma gida. ........ Washi gari da safe Nana ta kawo mana abin karyawa, karfe goma sai ga Ummi tazo. Har lokacin ban farka ba. Sai karfe uku da rabi na farka dishi dishi na fara bu e idanuna, a hankali idanuna suka bu e. Ummi da Abdul na gani a zaune Fatima ta tafi makaranta, Nana kuma ta koma gida yin abincin rana. Gyara zama Ummi tayi cikin acin rai tace. "Zubda cikin kikayi? Duk wahalar da na i da rasa aurena da nayi ya zama a banza, na koma gida a matsayin bazawara Kin min adalci Safinah, laifin meye Muka miki da zaki za i zub da cikin, Wallahi idan Hajiya Asma'u taji abinda kika aikata har abada bazata ta a kallonki da kima ba, nagode da abinda kika aikata min, banda Hjy Asma'u daga ce mata cikin jikinki na D'antane har da rawan jikinta ta amshiki, toh wallahi zan gaya mata cewa cikin ba na Ashraf bane har kin zubar da shi." Lumshe idanuna nayi, tare da komawa na kwanta. Kwalla nabin gefen fuskana, ji nake kamar na fasa ihu. Fita tayi Abdul yayi yana share kwalla, domin ina jin sautin kukan Ummi, kokarin tashi nake amma bani da karfi komawa nayi na kwanta na cigaba da kuka. ......... Sai da Nana ta kawo abinci Ummi ta koma dan tace matu ar ta cigaba da ganina bakin cikina ne zai kasheta, Ummi da Abdul fushi suke dani, ina samun sassauci ta angaren Fatima da Nana, Khalil da Khalila, Abba Lawan sau aya yazo ya koma, dan Umma ta gaya mishi. Ganin halin da nake ciki ya aga mishi hankali, dan sai da ya same Abba da maganata. Karshe yayi masa bibi i, suka rabu dutse a hannun riga. Kwana na biyu aka sallame ni, koda na dawo gidan Abdul bai nunawa Matarsa muna rigima ba, sai dai ya auke min wutane sosai. Duk sai na shiga damuwa, amma ina kokarin jan saura kimata da ta rage. Dukda naso kin biyewa Matarshi da take min iskanci, idan ina jin yunwa Atm ina nake auka da keyn motana, tafiya gidan Abinci nake naje nasayo abincin da raina ke so. *** Kwanaki sun haura satitika, satitika sun haura watanin, a yanzun kusan wata Hu u babu Ashraf ba labarinsa, nayi kuka sosai gashi babu wanda ya fa awa Nannah cikina ya zu ........ Duk iskancin da Sophia take min ban tankata ba, haka zata zo idan ina falo tayita habaici har sai na bar falourn zata hakura. Wani abin da yake damuna, yawanci kamar jaka. Idan nasaka abinci a gabana sai naga bayan kwanu, ga kuma kwa ayi. Idan naji kamshin girkin Sophia kamar xanyi hauka, amma dan rashin mutunci bata bani. Yau ina jin kamshin abincin da ya cika gidan na mike a hankali dan kwana biyu jikina nauyi yake min, ga ciwon jikn da bansan dalilinsa ba. Na nufi kitchen inta tana fama da aiki na shiga da sallama nace. "Don Allah Sophi abincinki zaki samin ko ka ane" Wani kallon banza tayi min sannan tace. "Toh kwartonki bai kawo miki bane? Ko ku in da ake min burga ya kare ne." Girgiza kai nayi cikin tsananin bukatar abinci nace. "Dan girman Allah ki bani koda ka ane kika ce na biya zan biyaki." Dariya ta fasa tare da tafa hannunta tace. "Wow kice kwartonki yana sake miki ku i, ok ga Acc numberna naji 50k" Jikina na rawa na koma aki ma auko wayata na tura mata, tsabar wulakanci ku in na shiga tace. "Zan baki amma sai kin min wanke wanke, ki wanke min kayana sai nima nasaka miki." Sunkuyar da kaina nayi tabbas duk macen da ta zubda kimarta sai an wani gari sa'an kaninka shi zai sakaka aiki, murmushi nayi tare da cewa. "Bani wankin, na fara dash.." "Bazaki wanke ba! Ni Sophia kika ciwa mutunci yayata kikewa haka? Ba damuwa Didi jeki aki zan kawo miki abincin da ku inki." Kamar zanyi magana sai na fasa, shiga kitchen in yayi itama ta ata rai tace. "Ai nayi kokari tunda Uban da ya haifeta ya kor..." Abincin ya iba har yazo bakin kofa yace. "Ki ajiye mata ku inta, sannan kuma ki ha a kayanki idan zan koma zanyi ajiyeki a gidanku, aai kuma ina miki albashir da next week zanyi aure idan na kaiki ki musu bayani azo a kwashe kayanki......... **** Ban kar zo man ba ... ...... *(Ina kira gareku ban manta Ashraf ba, ina sane dashi babu yadda saudia zata yanke mishi hukunci har sai ta sami shaidu da kwarara akanshi ku biyo ni cikin labarin me cike da ban haushi da ban tausayi sadaukarwa soyayya, makirci hassada kiyayya rashin fahimta kyashi mugunta,munafuci zalunci, yaudara cin Amana)* #MJ#HZ #Vote.... Oum Muwaddah....... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITERS ASSO_* *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* Page. "Waye shi? Waye zai min iyaka da muradina? Na rantse sai na kashe su." Tura kekensa Amir yayi tare da barin akin, da gudu ya riko keken Amir Yace. "Waye shi?" "Ko waye ne baya bukatar gabatarwa, idan lokaci yayi zaka ga kowaye." Yana gama fa ar haka ya tura keken yayi gaba abinsa. Wato wani irin rikici ya arke a kasar jordan, dangane da mulki wanda yakai duk wanda yayi tari akayi akan mulkin sunanka matacce. Tsabar mulkin zalimci kuma kujerar gata nan amma ta haramci mutane dayawa. Dan haka sai aka fara samun yan hatsaniya da yamutsi. Wanda ya kuma sabunta rigima a tsakanin mgadarar masarautar suna tankawa junarsu. A gefe guda kuwa Banu Nazir da Banu Hussein suna nan suna nasu shirin.. ..... Sati biyu kenan da Ghaniyu ke niman Ashraf bashi ba labarin,, ya damu sosai da rashin samunshi a waya. *** *Nigeria* Abuja..... Kwana na goma kenan laulayi ya sani a gaba, bana iya cin kome sai ruwa aketa aura min, magana me tsawo ma bana iya yinshi sosai. Ga zubda yawu amai kam ba a magana. Bani da karfi a jikina sai yadda akayi dani. Ina matukar jin wahala, har na tsani cikin da me cikin dan wallahi da zanga Ashraf a gabana zan iya mishi abinda ban tsammani ba. Dan ya gama lalata min rayuwata da kuma farin cikina. ....... Dafani Nannah tayi , ajiyar zuciya na sauke sannan na k'akaro murmushi tare da sunkuyar da kaina. Dan yanzun ina matu ar jin nauyinta, Ledar hannunta na kalla naji yawun bakina yatsinke, agwalimace a cike da yar karamar bakar ledan nan, gyara zama nayi ina jin wani mugun da i ya cika ni. Juyewa tayi a wani bowl in da Ummi ta kawo min salat, ta wanko min A ban aki ta kawo min, Dake akin da muke VIP Ward ne, mu ka aine a cikin akin. Tunda na amshi agwalimar nake mata wani irin kallo, sannu na fara sha kamar nasami tuwo. Har wani lumshe idanuna nake, shigowar Abdul yasani bu e idanuna tare da sakar masa murmushi. Dan ya zame min jiki bana magana sai murmushi, shida wata mace yaki ya matsa min naga wacece. Sai lekata nake ina son ganin wacece, karshe matsawa yayi. "Ummina ce" Wancakalar da bowl in nayi tare da dira da karfi naje na rungumeta, kuka ne ya kwace min. Rungume ni tayi tana buga bayana, cikin mita Abdul yace. "Yanzun dan girman Ubangiji meye haka, baki san akwai abu a tare dake bane, wallahi wannan tsalle kamar a zuciyata kika yishi. Kuma ina kishi, kuma ina taya babyna jin b...." Wani irin kallo na masa, dan duk abinda ake bana kaunar maganar cikin, kauda kaina nayi cikin kuka nace. "Wallahi idan bai zo ba zubda cikin zanyi dan cikin y." "Wallahi kika ta a lafiyar cikin nan sai kin kare rayuwarki cikin bakin ciki da nadama,, kuma na rantse wani abu ya faru da cikin ni dake ne, nonsense." Haushi yasashi ficcewa, Kukane ya kwace min, Nannah ta maidani bakin gadon, cikin damuwa zatayi magana na dakatar da ita. "Nannah! Meye laifina dan nace zan zubda cikin nan, Ummina nifa taimako naje. Na gaji da ganin Nannah tana zubda hawayenta, Ummi nasan keda Nannah zaku fahimceni. Wallahi ba yadda kuke tsamani bane na same shi tunda yazo a haka me zai hana na zubda shi." "Waye me cikin?" Inji Ummina. Kaina a sunkuye, na ago shi cikin rawan murya nace. "Ba zakiyi fushi dani ba? Idan na gaya miki." "Akan me zanyi fushi dake? Ai da zanyi da ban saurareki ba kamar Yadda Abbanku yayi miki haka zan miki." Kallon Nannah nayi cikin kuka nace. "Am sorry Nannah!" Girgiza kai tayi tare da nuna min tana ji na. Shigowa Abdul yayi yace. "Ummi naga kiranki." Bata bi tankashi ba, kallonshi nayi tare da mika mishi hannuna, zuwa yayi tare da rikewa, ya zauna a kusadani. Daura kaina nayi a bisa kafa arshi kwalla nabim fuskana lumshe idanuna yayi tare da fashewa da kuka sabida hango ranar nake a idanuna, da yadda nayita rokon Ashraf yakyaleni amma abin yaci tura, ha iye kukan nayi amma naki bu e idanuna nace. "Cikin..." Shiru nayi tare da mugun fargaba ya cika min zuciya, matse min hannuna Abdul yayi cikin kwarara min gwiwa yace. a Safina, kina inda baza'a kalubalance ki ba. Karki ji tsoro mun yarda da kaddara me kyau ko mara kyau muna tare dake," "Na Sultan Muhammad Ashraf bin Abdullah Alhashmiyya." Mikewa Nannah tayi jikinta na rawa, ta riko hannuna cikin wani yanayi, tana kallona kawai sai tasa sake hannuna tabar akin baki aya, tasowa Ummi tayi tazo inda