Sashe 6
Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
taya zai ji tausayin mutane. D'aga sider bag ina nayi naga wata farar takarda da wani kunshi. D'auka nayi naga anyi rubutun da bazasu gaza layi shida ba. _Barka da zuwa Masarautar jordan, a cikin jakarki akwai waya da bluetooth, sai wannan kunshin ku ine ki ji da inki sannan muma zaki mana aiki idan kika ki toh zaki bu e idanunki a lahira_ Wayyo Allah na, nashiga uku ina ne na kawo kaina, buga kofar akayi na tashi da sauri zuwa nafita, suna tsaye sun min zuru zuru. Wuccewa nayi a gaba suka rufa min baya, bansan dalilinsu na biyo ni ba. Amma ba mamaki yana nasaba da sarkinsu. Bayan sun kawoni na wucce ciki a falon farko naji wani abin mamaki, manyan mutane fa dan akalla zasu kai shekaru sittin da auriya. daya yace. "Akwai dukiyar da nake son fitarwa daga cikin kasar nan zuwa Amurka, shine na kawo takardun yana ciki an kai, dan ma Amir Ukshe yasa baki yanzun haka takardan yana gunsa." D'ayan yace.. "Nima manda ake hakowa a cikin kasar nan musaman mallakin masarautar akwai wasu turawa da suke sone zan sayar musu shine na kawo takardan yasa hannu, da taimakon Amir." Hmm na iya cewa a raina, yadda suke hiransu. Muna shiga cikin gidan naji kamshin falon ya sauya. Hangoshi nayi ya na e kafa aya akan daya, sanye yake da doguwar jalla iya ga wasu mutanen a tare dashi, sallamar da nayi wani daga cikinsu ya amsa. Duk mutanen sun ago sun kalleni banda shi. Shin dama mulki idan ya shiga jikin mutum haka yake. Tsohon da aka kaini gunshi, shine yaketa magana cikin rarrashinsa da yasa hannu a cikin takardan da yake gabansu. Wuccewa kitchen nayi bansan ya akayi ba dan sune suketa magana, sai dai jin da nayi suna sanya mishi albarka tare da jin da in har da godiya, "Anya Masarautar nan tana cikin tsari kuwa? A sani na sarki Fada yake zuwa wannan sarkin toh." Nace a raina kar nayi gajen hakuri da saurin yanke hukunci. *** Kwana na uku a cikin gidan kuma kullum girkina sai dai akaiwa Kare da Mage. A rana na hu u, ne aka kawo wani balarabe, ya fara girkin sultan. Zamana da Samin yasani sake kara sanin halayar larabawa, dan ido da ido yake nuna min kabilanci da wariyar launin fata. Uwa uba, tsangwama. Tafiya yayi nisa dan kuwa na kara fahimtar cewa Sultan Ashraf sarkine a zahiri amma a ba ili ba shine sarkin ba Amir Ukshe da Amir Abu Zarri, duk wani abinda zai fita daga masarautar ta hannunsu ne, sannan rayuwar Sultan Ashraf kamar a hannunsu yake dan sai yadda sukayi dashin, sannan akwai abin alajabi dan yake damuna, game da sultan duk lokacin da aka kawo mishi takardu baya bu ewa sai dai yasaka musu hannu, baya ta a bincika meye takardan. *** Yau na cika sati hu u da aka kawo ni cikin kurkuku sultan a yanzun na kiyyaye abinda zaisa a zane ni sosai. Da wuri na gama abincin mage da karen. Nafita zuwa shashin bayi. Lokacin da naje nasame Yan akinmu jungun jungun. Ganin babu Zakiya yasani cewa.. "Kanena ina kanwata Zakiya." Kuka ne ya kwace musu suka sani a gaba da kuka cikin tashin hankali nace. "Lafiya kuke kuka." Mujahida ce ta iya cewa.. "Kaltu Feener! Zakiya an yanke mata hukuncin zaman gidan kaso har na shekara uk." A tsorace nace. "Akan wani laifin?" "Sabida ta kare kanta lokacin da Amir Sauban ya nemi keta mata haddi ta fasa masa kai da kwalb....." Ban gama jinsu ba na fita daga gidan, da gudu. Sai gidan Sultan raina a ace na shiga yana zaune a falo. Kai tsaye na nufi inda yake cikin kuka nace. "Shin kai wani irin sarkine da baka samawa talakawanka adalci?" Idan dutse zai amsa min toh Sultan Ashraf ya tanka min. "Wato ku kanku kuka sani, daga ku sai danginku, ta rasa ahalinta a yakin siriya tazo nan dan rufawa kanta asiri." Ji nayi an fizgo min, fita dani suka fara yi cikin ihu nace. "Kayiwa kanka Adalci." Tunda suka kaini akin suke zane ni, sai da suka na daina numfashi sannan suka kyale ni. Sai da nayi kwana uku a akin duhu sannan aka fito dani. Tunda aka fito dani hasken waje ya auke min gani na. Sai da nayi awa uku sannan ganina ya dawo dai dai. ...... Koda na shiga kitchen Samin na kallona ya kauda kanshi, yace. "Sorry Feener! Kiyi a hankali dayiwa Sultan Magana kai tsaye, dan zaki iya rasa rayuwarki baki aya, ai da sai kinyi sati za'a fidda ke toh dabobin da kike musu abinci an kai musu abincina sunki ci shine suka fara niman mutuwa shine mai kula da Arduwan yace a fidda ke in ba haka ba mutuwa zasuyi. Sultan naji da kare da magen kamar rayuwarsa." Gya a kaina nayi kwalla na zu o min, haka nasa hannu nayi girki aka kai musu. Na fito zanje shashim bayi aka hanani. Wai ance kar na kuma fita daga shashin har sai sultan yabar kasan, dan saura kwana uku zai bar kasan. Kamar na daka tsalle zai tafi zan koma cikin gidan gun bayi Yan uwana. Haka na koma kitchen dan anan nake zaune bani da inda yafi nan. Tsabar na kagu ya tafi bansan ya akayi nayi Mansaf yayi yaji ba, ranar sai da naci duka bayan an sani sabon abinci wai kare da mage hauka sukayita musu dake suna can gefen gidan ta baya, shine aka kira likitan dababobi ya gano yajin da na cika a cikin abinci Sultan da kanshi yace. " ku mata kaman yadda tayi musu." Wato su bani abinci me yaji kamar yadda na musu Kare mishi kallo nayi bai wucce sa'an Abdullah kanina ba wai shine yake bada umarni a zane ni, ina da matukar zuciya da fushi, shi yasa ban cika shiga tsabgar kowa ba, sai na yaba da halinka. Bansan lokacin da nace masa. "Na zata sawa zakayi a kashe ni kamar yadda kasaba sawa ana kashe mutane." Bai ta a tsayawa ya kalle ni ba, sai yau, ka a kai yayi yace. "Ku jiyar da ita azaba wanda gobe ko hango ni tayi zata sauya hanya." Lumshe idanunshi yayi aka suka fita dani, zuwa akin azaba. Wato wani irin wahala suka bani wanda yasa ko tsayuwa na gaggari yi sai kwalla kawai. *** *Banu Hussein* Yake shi da kabilarsa, kowannensu sai shawara suke badawa yadda zasu kwace mulkin Jordan, da karfin cin tuwo har suka gama sannan ya zauna cikin izza yace. "Na bawa Sultan Ashraf Rania!" "Amir Adna kasan abinda kayi kuwa? Ka auki Y'arka kabawa." "Shakur! Mulkin jordan muke so! Idan Rania tashiga tasamu ciki ta haihu da Ashraf tankar mulki ya dawo cikin kabilar Banu Hussein ne kuje kuyi nazari." Yana gama fa ar haka ya bar musu falon baki aya. *** *Gidan Amir Ukshe* "Abbie!" Gyara zama mutumin yayi cikin girmamawa yace. "Abbie! Sahel ta amince da za inka! Amma meye kasonmu idan Ashraf ya aureta?" Kura mishi ido Amir Ukshe yayi sannan yace. "Me kake tunani akan mulkin Jordan bayan bamu ka ai bane muke kwadayin mulkin, akwai Kabilun Banu Nazir da Kabilun Hussein, ko da wasa bazaka ta a samun koda taki aya ne na mulki tunda Yasir ya sadaukar da karagar babu wanda ya isa arewa da karfin tsiya ka cire ranka a cikin sha'anin mulkin gidan nan. Zaka iya tafiya" Jikin Amir Marhum ya mike zuciyarshi cike da haushin Mahaifinsa. *** *Banu Nazir* "Zoya! Naji Ashraf zai koma Germany ki shirya na nima miki masters a can, kafin ku dawo ki tabbatar da kin shawo kansa, inta kama ma kanki ne ki mika mishi dole na ruguza Daular banu Hashim da hannuna....... *Ku nutsu labarin cike yake da sarkakiya karku min korafi akan duk abinda zai faru idan kuka duba sunan labarin kunsan kome zai faru no more any korafi* #Mai_Dambu #VOTE MJ... Oum-Muwaddah..... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITER'S ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* Page. "Yaro!!" *Samin Ni zan fa a maka Ashraf Yarone." Abinda yayita kai da komowa kenan a ranshi, baji haushin Samin kamar yadda yake jin haushin wancar bakar fatan, kallon kanshi yayi a madubi. Girman jikinshi ya kalla, da irin yadda Allah ya masa kira irinta lafiyayyun maza, matashin me ji da kuruciyarsa, wato Ashraf dogone me matsakaicin jiki, yana da dogon hanci wanda ya karawa fuskarshi kyau, sai idanunshi an dai-dai, yana da cikar gashin gira. Sai kayataccen sajen da zagaye fuskarshi, me ha e da gemu an cass. (Da zaku san crown prince Muhammad Bini Salman, wato yarimar saudiya me jiran gado, toh haka Ashraf yake) Takaicine ya turnike shi bai san lokacin da yakaiwa madubin naushi ba har sai da kome ya tarwatse, kalamar Yaro ne yake yawo akanshi, babu wanda ya ta a masa kallon Yaro sai wancar bakar fatan, haka ya tarwatsa kome sannan ya danna wani karfe sai ga masu kula dashi sun shigo.. Dafe yake da goshinsa yace.. "Ku aukota." Fita sukayi dan cika umarninsa, ina kwance sai ji nayi anyi sama dani, kafin na wartsake an dire ni a cikin fasassun kwala e, dan suna shiga yayi musu nuni da cikin kwalbar dan haka suka cika umarninsa. Suna dire ni cikin kwalbar na sake kara da. "Auuchhhhh Ya ilahi" Fesa turarenshi yayi yasa kai ya ficce a akin, kuka ne ya kwace min. Duk yadda na motsa kwalabe ke shigewa cikin kafana, na ru e na ki ime. Ga baki aya nayi danasanin shigowa Rayuwarshi. A gigice nayita taka kwala en har na fita a cikinsu na zu e a gefe guda ina jawo kafafuna, ina dubawa manyan kwala e da kananu dakyar na ciresu. Ga jinin dake fita a kafar. Bansan iya adadin lokacin da na auka ina cire kwallar da kuka ba, ina gama cirewa na rarrafa na ficce daga akin. Ina fita na mike ina dangala kafata a kasa har na isa kitchen na, ban aki na shiga na zauna dirshan tare da fashewa da kuka, wanke kafar nayi na saka cikin ruwan zafi ga uban azabar da nake ji, haka na gasa kafar. Ina nufar gun kayana na